DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   31 / 39

90K to 93K   out of 116.4K words

aka tsaka da wannan lamarin Allah ya karɓi rayuwar Yaya Usman a lokacin Anty Muhibbat tana ɗauke da cikinsa, a sa'ilin da ta sanar da Yaya Saddam da ake ciki ya shiga cikin matuƙar tashin hankali ya nema a zubar da cikin amma ta nuna hakan ba zai taɓa yiyuwa hasalima ko dai ya aure ta ya rufa mata asiri ko kuma ta je ta bayyanawa ita mahaifiyar Yaya Usman ɗin halin da ake ciki".

Ya dakata ta hanyar jan dogon numfashi ya fesar kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya"idan akwai wanda mahaifiyar Yaya Usman ta yarda da shi ta kuma aminta da shi to a bayan Yaya Saddam yake. Wannan matar ta taka rawan gani a cikin rayuwarmu gabaɗaya, a gidanta ya yi karatu ba ta taɓa nuna masa bambamci tsakaninsa da ƴaƴan da ta haifa ba, hatta ni ta nuna min so da ƙauna lokacin da iyayenmu suka rasu ta ja mu a jikinta ta maye mana gurbin duk wani abun da muke jin cewar mun yi rashinsa. Wannan dalilin Yaya Saddam ya dubae har ya abin ce da auren Anty Muhibbat bayan sun yi yarjejeniyar za a zubar da jikin da take ɗauke da shi. Ba na mance kukan farin cikin da mahaifiyar Yaya Usman ta yi lokacin da ta ji cewar Yaya Saddam ne zai auri Matar da Yaya Usman ya so aura Allah bai yi ba. Ta yi hidima sosai a bikin har Allah ya ƙaddara musu kasancewa a matsayin mata da miji har da rabon haihuwar Aryan da Ayan. Sun yi auren ne kawai amma Anty Muhibbat ta san cewa babu ko da ɗigon soyayyarta a cikin zuciyarsa, tun daga wannan lokacin zuciyarta take ayyana mata cewar za ta jure komai daga gare sa don dai kawai wannan sirrin da suke rufe bai fito duniya kowa ya ji ba. Don ya kasa yarda da ita duk da kuwa mutuwar Yaya Usman ya sanya ta sauya". Al'ajabi da mamaki suka taru suka hana mu magana daga ni har ragowar mutanen da suke zaune a cikin falon. Anty Sawwama ta yi ta jinjina lamarin tare da yi mana nasiha mai ratsa jini da jijiya ta ƙarƙare da jan hankulanmu akan mu ji tsoron Allah a cikin dukkan abin da za mu aika. Har aka gama komai ban ɗago kaina ba balle na ce wani abu aka gabatar da addu'ar neman gafara da rahama ga Ummata kana suka fara haramar tafiya. Ko cira kai ban yi na dube su ba sai jin Muhammad Taufik na yi tana magana da Yaya Alhassan cikin girmamawa.

"Yallaɓai idan babu damuwa mu na son magana da Amatullah a waje".

Ba tare da nazari ko dogon tunanina ba Yaya Alhassan ya furta"ba komai ai, mu je daga wajen sai ta fito". Daga haka suka fuce. Anty Sawwama ta dafo kaina da na kwantar jikin ƙafafunta"tashi ki je ki ji abin da za su gaya miki".
"Me ye kuma za su ce mini Anty? Duk abin da za su faɗa ai sun faɗe shi a cikin falon nan. Gaisuwar rasuwa suka zo yi kuma sun yi mene ne kuma ya yi saura?". Cikin lallashi ta ce"ki yi haƙuri ki tashi ki je ki ji abin da za su ce da ke kin ji Uwata?". Ba don raina ya so ba na tashi na nufi wajen ina goge guntun ƙwallan da yake ƙoƙ zubowa daga cikin idanuna. A ƙofan gida na iske su tare da Yaya Alhassan da Amir na iso wajen bakina ɗauke da sallamar da suka haɗe baki wajen amsawa. Yaya Alhassan da Amir suka yi musu sallama ta hanyar yin musabaha kana suka koma cikin gidan suka bar ni tsaye da su.
Kusan mintuna biyu cikinmu babu wanda ya yi magana kafin can Saif ya ce"daman godiya nake so na yi miki sannan kuma na ba ki haƙuri akan duk abubuwan da suka faru, haƙiƙa na aikata miki ba daidai ba". Ban bar shi ya ƙarisa ba na ɗaga masa hannu alamar ya dakata.
"Kamar yadda tun a ciki aka buƙaci na manta da duk abin da ya faru, to ka ƙaddara cewa komai ya wuce". Ya sadda kansa ƙasa yana murza zoben dake saƙala a ƴatsun hannunsa kafin ya ce"na gode".

"Amatullah".
Muhammad Taufik ya furta a karo na farko tun bayan da na fito waje, na ɗaga idona ina kallonsa yayin da shi ɗin ma ni yake kallo, take na ji wasu hawaye su na bin kuncina ba zan iya juran irin kallon da yake yi mini ba don haka na juya na shige cikin gida da hanzari, kai tsaye ɗaki na wuce ina shiga na faɗa kan katifa ina kuka marar sauti. Haka na wuni a cikin ɗakin in a fito waje to alwala zan yi ina yi nake koma wa cikin ɗakin.
Washe da safe bayan mun yi karin kumallo ina zaune a ɗaki kawai na ji an yi sallama, idanuna a lumshe na amsa sallamar da hakan ya ke daida da ba ta iznin shigo wa.
"Amatullah".
Take na wartsake na tashi na miƙe tsam sa boda amon muryar ba ta kasance baƙuwa ga kunnuwana ba. Na ware idanuna akan ta kafin na ce"Amira ke ce?".
"Ni ce Amatullah". Ban san lokacin da na ji wani ƙarfi da kuzari ya mamaye jikina ba, taku uku na yi na iso gabanta muka rumgume juna ni da ita, muna kukan da takamanmen ba za mu iya bambamcewa tsakanin kukan farin ciki ne ko na akasin sa ba.

[12/22, 3:46 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 7️⃣6️⃣

Mun ɗauki tsawon lokaci muna kukan kafin na ja hannunta muka isa bakin katifan muka zauna muna fuskantar juna, yayin da muke ta ƙarewa junanmu kallo. Tabbas wannan Amiran da take zaune a gaba yanzu ta sha bambam da ainihin Amiran da na sani a lokutan baya. Wacce na sa ni ƴar gayu ce na buga wa a jaridar Aminiya, saɓanin wannan da take zaune a gabana cikin suturun ba su rufe mata kattara ba. Wacce da na sani ma'abociyar ta'ammali ce da kayan gyaran jiki da ƙamshi ne saɓanin wannan da babu wannan abubuwan a tattare da ita. Wancan da na sani fatarta kullum cikin gyara da ƙyalle yake yi saɓanin wannan da ta yi duhun gaske.
Na kasa jurewa har sai da na furzar da mamakina na ce da ita"Amira yanzu ke ce haka? Me yake faruwa ne? Don rasuwar Umma ban gan ki ba kuma ban sama nutsuwar da zan tambaya inda kike ba".

Numfashi mai dogon zango ta saka kafin ta furta mini dunƙulalliyan maganan da na kasa fahimtar inda ta dosa.
"Amatullah rayuwar ce ta yi min atishawan tsakin barkono, tabbas na fahimci idan ka san farko to ka kiyayi ƙarshe". Na ɗan waro idanuna waje kafin na ce"me yake faruwa ne Amira? Shin ina Mansur? Ina alƙawarin da kuka yi wa junanku?".
Wani murmushin takaici ta saka kana ta furta"Mansur yana nan mun yi aure da shi, yanzu haka maganar da nake yi miki ni da shi miji da mata ne". Na rarumo hannunta na riƙe gam cikin son gaskata abin da ta faɗa.

"Don Allah Amira wannan zancen da gaske ki ke yi, kun yi aure da Mansur? To a ina kuke zaune kuma me yasa na gan ki cikin wannan yanayin?".

Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta ce"Amatullah za ki yi mamaki idan na shaida miki cewar yadda Mansur ya bayyana kansa a gare ni ba haka yake a zahiri ba, ya nuna min soyayya a zahiri alhalin a baɗili ba hakan ba ne a cikin ransa. Bayan barinki gida sau uku yana ƙoƙarin keta min haddina Allah ya na kuɓutar da ni, lokacin da iyayensa suka zo gidanmu aka sanya ranar aure sai ya mayar da ni tamkar matarsa ba ya shayi ko shakkan taɓa ko wani gaɓa a cikin jikina. Ya lalata min rayuwata yayin da hankalina ya gushe da tunanin tun da aure na zai yi hakan ba matsala ba ne, ban sa ni ba ashe wuƙa na ɗauka na burmawa cikina. Idanuna sun gama rufe burin auren mai kuɗi kuma ɗan soyayya kawai nake hangowa. Haka aka yi bikin ya yi da ya yi min ɓarin Naira kamar bai san zafin nemansu. Ya ɗanɗasa min gida na gani na faɗa komai na cikin gidan shi ya yi da ƙudinsa daga ni sai kayan jikina aka kai ni cikin gidan. Ban cika satikai biyu masu kyau a cikin gidan ba na fahimci na yi zaɓen tumun dare don na gani Mansur ƙwararren manemin mata, har daga wasu jihohin ake yi masa dillancinsu. A lokacin hankalina ya tashi matuƙa babu kalar bazaranar da ban yi masa ba amma ya murzawa idanunsa toka daga ƙarshe ma ya ba ni zaɓi ko in kwantar da hankalina na zauna na ci azurki na bar azurki a inda na same shi, ko kuma ya sauwaƙe min ungulu ta koma gidanta na tsamiya".

Ta tsagaita ta hanyar jan dogon numfashi ta fesar da shi daga bakinta kafin ta ɗaura daga inda ta yi birki"dole na ba da kai bori ya hau don ba zan iya rabuwa da shi, bayan soyayyan da nake yi masa hakan ina gudun dariyan da magauta za su yi mana ni da Umma idan aka ji cewar Mansur ya sake ni tun kafin na rufa wata guda a cikin gidansa. Haka na yi haƙuri na shanye dukkan baƙin ciki da takaicin Mansur a lokacin ko zanen lallen da aka yi min na bikin bai gama goge daga hannaye da ƙafafuna ba. Tun ina kuka da shiga damuwa har na saki raina na sa ba don har akan gadonmu na sunna yana waya da ƴan matansa, idan na ce zan tayar da hankali sai na ga ba ni ma da wani dalilin yin hakan tun da bai rage ni da komai ba. Bai hana ni ci ba balle sha haka nan sutura sai wanda na zaɓa zan saka a jikina. Ko da na sanar da Ummata sai ta ƙara ƙarfafa min gwiwa akan na zauna da mijina a cikin dukkan yanayin da na tsince shi, ta ƙara da cewar mazan wannan zamanin daman duk haka suke ko sun yi aure ba za iya rabuwa da ƴan matan da suke mu'amala da su, na yi matuƙar juriyan zaman da shi don a wasu lokutan har cikin ɗakina yake kawo mace sun yi duk abin da ransu yake so ba tare da na iya cewa da shi uffan ba har sai da ya kai jallin da na ji gabaɗaya auren ya fice min daga cikin raina. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duk halin ƙuncin da zan shiga ba ya ɗaɗa Ummata da ƙasa in dai har zan kawo mata ƴan sulalla to baka lafiya ciki lafiya, shuru za ki ji tamkar Malam ya haɗiye shuruwa. Rana tsaka Mansur ya soma jinya tamkar ba zai yi rai ba ko da aka je asibiti aka tabbatar da cewar yana ɗauke da cuta mai karya garkuwan jiki, da aka gwada ni ma aka same ni da cutar a tattare da ni sai dai nawa bai yi ƙarfi tamkar na sa ba. Ina da yaƙinin cutar ba ta yi min illa kamar yadda tunani da halin ƙunci da kukan da na shiga ya yi min illa ba, lokaci guda na rame na fige na fita daga cikin hayyacina. Ko da na buƙaci ya sake don ba zan iya zama da shi ba Umma ta lashi taboki akan in har na kashe auren to babu ni babu ita kuma daga ranar na dai amsa sunan ɗiyar da ta haifa, haka na rumgumi haƙuri ya zama min abokin rayuwa, aka ce gani da wane ya isa wane tsoron Allah sai dai wanna karin maganar ba ta yi tasirin akan Mansur ba bayan faruwa waɗannan abubuwan aka kama shi da wata a wajen aikinsu yana lalata da ita, take aka rubuta takardan kora ya dawo gida ya zauna babu aikin fari balle na baƙi".

Daga haka ta fashe da wani gigitaccen kukan da na ji sautinsa yana ratsa wa har cikin ƙoƙon kaina, na kasa yin komai balle har na sama ƙarfin gwiwan lallashinta na haɗa mata da kalaman ban haƙuri. Haka ta yi ta gaji don kanta ta tsagaita tare da ɗorawa da faɗin"kin san an ce zara ba ya barin dami kuma yau da gobe mai ƙarar da sabulun wanzami, duk wani dukiyar da Mansur ya tara sai ya zo ƙarshe cikin ƙiftawan ido tamkar ki haɗa auguda ki cilla musu ashana. Nan fa rayuwa ta yi mana tsauri tun muna cin abinci sau uku a rana ko da kuwa babu daɗi muka dawo ci sau ɗaya ma yana neman gagaranmu. Dole ƙanwar naƙi Mansur ya ajiye duk wani girman kansa a gefe ganin yunwa yana neman halaka mu, ga shi tun lokacin da aka kore sa daga wajen aiki sa boda munin abin da ya aikata iyayensa suka yi fushi da shi suka janye masa dukkan tallafi. Yanzu da nake yi miki wannan maganar adaidaita Mansur yake ja don mu rufa wa kanmu asiri, ya yi nadama dana sanin abin da ya yi a baya ya kuma durƙusa a gabana amma duk da haka zuciyata ta ƙi amsar tubansa balle har ta yafe masa irin cutarwan da ya yi mata".

Har ta ƙare zancen na gaza motsa wa daga inda nake zaune, tamkar gunki na koma ba na iya yin komai illa kafe da ido da na yi yayin da hawaye suke kwaranya daga cikinsu. Cikin ƙarfin hali na furta kalmar"innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta tsuƙe majiyan kukan da ya zo mata kafin ta furta"ki na mamaki ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar ci gaba da cewa"to kar ki yi mamaki duk abubuwan da na faɗa miki babu kuskure ko kuma ƙage a cikinsa. Yanzu ma shi ya kawo ni har ƙofar gidan nan kuma shi zai zo ya mayar da ni, wallahi ban ji rasuwar Umma ba sa boda babu waya a hannuna da tun ranar na zo ni, sai yau da na zo Ummata take sanar da ni". Nauyin da ƙirjina ya yi mini ya hana mutane samun damar cewa da ita komai illa jinjina kaina da na ci gaba da yi ina amsa addu'ar neman rahama da take yi wa Umma a cikin zuciyata sa boda bakina ya gaza.

Muna nan zaune har aka yi ƙiran sallan zuhur muka fito muka yi alwala muka yi sallan tare da ita muka yi girkin rana muna aikin muna tattaunawa da jajanta lamarin da suka faru, bayan ni ma na kwashe duk irin rayuwar da na yi na sanar da ita ta jinjina lamarin ainun tare da tausayawa a gare ni. Sai da muka gama aikin girkin tsaf na zuba mana namu muka shiga cikin ɗakin, duk yadda ƴaƴan hanjina suke kukan yunwa na kasa kai ko da loma ɗaya na dafa dukan shinkafan cikin bakina illa juya cokalin da nake yi a cikin abincin na kallo ta na ga yadda take cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, take na ji hawaye ya ciki mini kurmin idanuna wani irin tausayinsa ya mamaye mini rai da ruhina, tabbas rayuwa abar tsoro ce matuƙa kuma na yarda da wannan karin maganan da ake cewa duniya budurwan wawa ne.
"Ban taɓo zato rayuwa za ta zo mana a haka ba Amira. A duk sa'ilin da na rufe idanuna sai na din ga tuno irin rayuwar da muka yi baya sai na ji hawaye suna zuba daga idanuna ba tare da ni kaina na sani ba. Ki duba duk irin soyayyan da ku ka yi da Mansur da yadda yake ba ki kulawa yake kuma tarairayanki kamar ƙwai amma hakan bai hana sa wulaƙanta ki a cikin gidansa ba, hakan bai dakatar da shi daga neman wasu matan ba. Ki dube ni duk yadda nake ƙoƙarin kame kaina da killace mutumcina sai da na yi ciki ba tare da igiyoyin aure sun hau kaina ba, duk yadda nake martaba kaina sai da ƙaddara ta ja ni izuwa can inda ban san kowa ba, na yi zaman kaina a cikin gidan karuwai". Ban ƙarishe zancen ba sa boda kukan da ya kufce mini da ƙarfin gaske, ina yi Amira tana taya ni a haka Anty Sawwama ta zo ta iske mu ta din ga ba mu baki da kuma yi masa nasiha tare da ba musalai kala daban-daban.

Wunin ranar tare muka yi shi da Amira sai da muka yi sallan magrib Umar ya shigo ya shaida mana cewar wai ana magana da Amira a waje in ji mijinta. Kafin mu fito daga ɗakin har ya shigo ciki tare da Yaya Alhassan da ya dawo daga masallaci muka iske su a falo suna gaisawa da Anty Sawwama. Idanuna na tsayar ƙar akan fuskar Mansur tabbas kamanninsa bai sauya ki da da ɗan taƙi ba, amma ya lalace ya rame ya yi baƙi ƙirin da shi tamkar wanda ya yi taimama da garin gawayi.

"Amatullah ke ce wannan?". Ya jefa mini tamnayar yayin da muke ƙarisowa cikin falon muka zauna, kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da maganan.
"Na ji matuƙar daɗi da na sama labarin cewan kin dawo gida, Umma kuma lokaci ya yi Allah ya jiƙanta ya sada ta da Mala'ikun rahama ya kyautata makwancinta".

"Amin".

Duk muka haɗe baki muka amsa da shi, nan ma Anty Sawwama ta ƙara yi musu nasiha sosai don na saurari duk labarin da Amira ya labarta mini, sai ga Mansur har da ƴan guntun hawayensa, tare da su Yaya Alhassan ya tashi suka je masallaci don gabatar da sallan isha'in da ya gabato mu ma muka yi namun sallan, Anty Sawwama ta ce mu zuba musu abinci kafin su dawo, hakan kuwa aka yi muka shirya musu abincin muka ajiye musu a falo yayin da muka koma cikin ɗakin. Muna jin su har suka dawo daga masallacin suka ci abincin suka ɗan taɓa hira kafin Umar ya ɗago labulen ɗakin yana daga tsaye a

31 / 39