Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
da ido, dole na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa sa boda kwarjini da cika idon da yake da shi.
"Za ki iya tafiya". Kalaman da ya saka mini da su kenan bayan sautin maganarsa ya fita raɗau, na saci kallonsa na ga ya mayar da idanunsa ya lumshe su, sai dai har yanzu numfashinsa bai daidata.
"Allah ya ƙara sauƙi".
Na furta yayin da nake tashi na fice daga cikin falon ina goge fuskana da hawaye ya damalmala mini shi. Ƙarar rufe ƙofar da ta yi shi ya sanya Saif buɗe lumshashshun idanunsa yana bin ƙofar da kallo daidai sa'ilin da wayarsa ta soma ruri. Sunan Sultan ya bayyana cikin screen ɗin wayar. Sai da ƙiran ya kusa tsinkewa kana ya ɗaga bai sanya a kunnensa ba maimakon hakan sai ya sanya ta a amsa-kuwwa.
"Saif".
"Ina jinka".
"Ya jikin nakan? Wallahi hankalina ya tashi sosai da na ji halin da kake ciki". Sai da ya cije naman leɓansa kafin ya ba shi da faɗin"da sauƙi fa yanzu yadda nake ji na ma zan iya wasan polo da ingarman doki, sa boda ƙarfin da nake ji a jikina".
Murmusawa Sultan ya yi kafin ya ce"daman har yanzu ka na fama da wannan lalular Saif? Na yi tunanin zuwa lokacin abubuwan sun yi sauƙi ba kamar da ba".
"Babu abin da ya sauya daga abin da ka sa ni Sultan". Shuru ya biyo bayan zancen Saif na ƙarshe. Sai can ya ce"wace ce yarinyar da ta ɗauki wayarka muka yi waya da ita? Don na san gidanku babu ɗiya mace".
A dake ya furta"ni ma ban san ta ba".
"Mu bar maganar wasa mana Saif, wace ce?".
"Ka riga da ba wa kanka amsa tun da tun farkon zancenka kai ma ka ce gidanmu babu ɗiya mace".
Dariya sosai Sultan ya yi sai da ya tsagaita ya furta"any way ko ma dai wace ce, tabbas ta shiga cikin firgici ganin halin da kake ciki ka ji yadda take kuka kuwa tsakanin da Allah. Tambaya kuwa ta yi min ya kai sau ashirin akan za ka tashi kuwa? Na ce da ita in sha Allah, ba don ta zo akan lokaci ba Saif wataƙila da yanzu wani labarin ake yi ba wannan ba. Ko wace ce wannan yarinyar haƙiƙa ta ceto rayuwarka kuma ta ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da numfashin da kake yi yanzu a cikin duniya, ka gode mata don ta cancanci hakan sosai".
Kit! Saif ya datse ƙiran ba tare ya ba wa Sultani damar amayar da sauran zancen da suke cikin bakisa ba. Ya zame daga zaunen da yake ya kwanta akan bayansa yana jan bargon ya lulluɓe rabin jikinsa, numfashi mai zafi ya furta daga bakinsa yana ɗan lumshe idanunsa sa boda ciwon kan da yake ji yana damun sa kaɗan kaɗan.
Ya daɗe kwance a wajen yana saƙa da warwara cikin ransa kafin ya tashi ya haura sama zuwa cikin ɗakinsa, wanka ya yi ya ɗauro alwala ya fito ya sanya farar doguwar jallabiya da aka yi wa ado da zare launin ruwan zuma mai ƙyalli da ɗaukar ido, ƙaramar hula ya sanya a kansa ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallan zuhur tare na sallan asr yana iddarwa ya ɗauko alƙur'ani ya soma karantawa.
Dole ne ya tursasa masa rufe alƙur'anin ya ajiye a gefe sa boda rawar da jikinsa yake yi tamkar mazari. Ya kunna ƙira'an Sheikh Ahmad Suleiman a cikin wayarsa ya ajiye, a nan kan sallayan ya kwanta take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya wa hakan ba.
Tun da na fito daga sashinsa na nufi hanyar gate ina tafiya a hankali tamkar babu laka a jikina, ina dab da fita na tsinkayo muryar Baba Mai gadi.
"Ƴar nan lafiya kuwa na ga kamar kuka kike yi?". Na yi saurin goge fuskana da ban san lokacin da wasu sabbin hawayen suka fito ba, na waigo tare da duƙawa na gaishe shi, ya amsa yana bi na da kallon tuhumar son gano abin da yake faruwa da ni. Ya zauna akan bencin da yake wajen ni ma na je na zauna.
"Ko dai cikin gidan ne babu lafiya? Don ɗazu na ga Saifullahi ya fito daga cikin gidan ya nufi sashinsa cikin wani irin yanayi, wanda har ina tsoron har hakan ya tasar masa da ciwon da yake damunsa".
Na sauri na ce"wani irin ciwo ke nan Baba?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"tun yana ƙarami yake fama da wani irin ciwo ga shi nan dai kamar aikin aljanu ko iskokai. A duk lokacin da ransa ya ɓaci ko kuma ya yi cacar baki da wani ke wani lokacin ma ko dogon zancen ya yi sai ki ga kawai ya yanke jiki ya faɗi jikinsa ya sanƙare haka zai koma ba shi da maraba da gawar da rai ya yi bankwana da gangar jikinsa, sai ta yi masa karatun alƙur'ani kafin yake dawowa daidai kuma da zaran ya tashi zai koma kamar ba shi ba".
Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina jin ƙaran da ƙirjina yake yi tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawar disko. Sai da na harhaɗo kalaman kafin na yi nasarar cewa"Allah ya na shi lafiya, Baba bari na je gida na dawo".
"Amin ya Allah, to ƴar nan a gaishe da mutanan gidan".
"Za su ji in sha Allah". Na amsa da shi yayin da nake tashi daga kan bencin, tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda nake cilla ƙafafuna ba ina tafe ina tunani tare da nazarin kalaman Baba mai gadi. Saura ƙiris wani mai napep ya kwashe ni Allah a rufa asiri, ai kuwa ya fito ya balbale ni da bala'i da masifa tamkar zai yi aron baki da ƙyar ya haƙura ya ja napep ɗinsa ya tafi bayan ya gama wurwurga mini ashariya tamkar ya hana jini da dangin maguzawa. Sai yamma lilis na iso gida lokacin ko wacce budurwar dake cikin gidan ta ci ƙwaras tana ƙoƙarin fice wa wajen harkanta. Gidan ya yi shuru sosai ina shigowa na kai duba na ƙofar ɗakin Hajiya Babba na ga ƙofar ɗakin a rufe an buga masa kwaɗo. Na lura cikin kwanakin nan ba na ganin La'aniyatu a cikin gidan nan kuma na rasa wanda zan tambaya.
Har na ɗauki hanyar ɗakinmu sai kuma na fasa don har cikin raina ba na ƙaunar haɗa ido da Sha'awanatu don har yanzu ban huce daga abin da ya faru ba. Ganin ƙofar ɗakin Zinariya a buɗe ya ba ni ƙwarin gwiwar faɗa wa cikin ɗakin.
Na iske ta tana kwance akan katifarta tana bacci na zauna a gefen tana dukan ƙafarta har sai da ta shi, ganin ni ce ya hana ta ƙarisa ashariyar da ta danno.
"Au wai ke ce?".
"Da waye kike yi tunani?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta tashi ta zauna ta ce"kin dawo daga aikin wahalar ke nan?". Na yi murmushi har sai da haƙwarana suka bayyana"aikin rufa wa kai asiri dai ko?". Ta taɓe baki ba tare da ta ce da ni ko kanzil ba sai ma sauya akalar zancen da ta yi
"Ki na da lokaci ki raka ni kasuwa?".
"Duk a cikin shirin tarban Yallaɓai ɗin ne?". Ta yi fari da idonta"ƙwarai kuwa". Na gyaɗa kaina"Allah ya bar ƙauna Madam ta gaban goshin Saddam". Caraf bakina ya yi furucin ba tare ta yi shawari da zuciyata ba.
"Saddam kuma? Ina kika san sunansa?".
Cike da dabara na wayince"kar ki daina basirar duk wata macen da kika ga ni a cikin harkan bariki".
[12/9, 6:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 6️⃣5️⃣
Tun da na yi zancen take bi na da kallo da mamakin zancen ya tilasta mata wartsakewa daga baccin da take yi. Ta rarumo hannuna ta riƙe gam"sanar da ni inda kika san sunansa don Allah". Na saki wani shu'umin murmushin gefen baki kafin na furta"ki fa kwantar da hankalinki na canza ne kawai. Sai kuma aka yi dace sunan ya zo daidai". Ta yi jim tana ta bi na da kallo kafin can ta ce"kin tabbata?".
Na yi fari da idona kafin na amsa mata da faɗin"ki yarda da ni wallahi ki ji rantsuwar ɗan musulmi ke nan ko? Ban taɓa ganin sa to ina ma za mu haɗu da shi mutumin da kika ce ba ya cikin ƙasar nan".
Da alama ta sama nutsuwa da kalaman da na furzar don ina jin sautin sauƙar numfashin da ta sauƙe.
"Na yarda da ke".
"To ba ta labarin abin da ake shiryawa yallaɓai ɗin namun?". Washe baki ta yi tamkar gonar auduga don na ga alamar tamkar babu maganar da yake sanya ta cikin tsananin farin ciki kamar batun Saddan da ta yi masa laƙabi da Oganta.
"So nake yi na je na sayo abubuwan gyaran jiki da kayan ƙamshi. Don so nake yi na shirya kaina kafin mu haɗu da shi, ina so wannan haɗuwar tamun ta zama abar tunawa a gare shi ta yadda ban bar shi masa tabon a cikin kwayansa".
Sai da na musguta kafin na ce"irin wannan kulawan da kuke ba wa junanku to me ye zai hana ku auri junanku?".
Ta taɓe baki"ai aure lokaci ne kuma ni ban shirya yin aure a wannan shekarun nawan ba. Kin gan ni nan sai na gama cin duniyarta da tsinken sakacen sannan na yi aure, mu yi rayuwar farin ciki da shi mu farantawa juna rai da zaran mun yi aure duk wannan soyayyar neman ta za mu yi mu rasa, duk marmarin junan da muke yi za mu koma jin haushin juna. Kin ga zaman auren nan zaman takura ne da rashin samun cikakken ƴancin kai mussamman aure a yanki arewacin ƙasar nan da za su san darajar mace ba sun mayar da matayensu tamkar bayin da ba su da ƴancin kansu, komai sai an ba ki izini za ki yi shi".
"To ai wannan abubuwan da kika lissafo ba ɗabi'ar ba ce, koyar wa addini ne cewar miji yana gaba da matarsa. Kuma ko fita za ki yi ƙofar gida sai da iznininsa".
Taɓe bakinta ta yi tana gyara ƙarin gashin doki da yake kanta kana ta ce"yanzu dai me ye kike so ki ce da ni?".
"Ku yi aure ya fi wannan rayuwar da kuke ciki. Ku ma kanki sai kun fi girmamawa da mutunta junanku".
"Ni fa yanzu ba aure ba ne a gabana Amatullah, kuma ke ki na tunanin aure a cikin wannan lokacin abu ne mai sauƙin da kike ta faman faɗinsa haka? Duk wacce ta sako ƙafarta ta tako cikin gidan nan da zummar shigowa harkan bariki to kafe ta ake yi, su shanye ta ta yadda ko ta so fita daga harkar ba za ta iya ba, wannan dalilin ne ya sanya da yawa daga cikinmu ko mafarkin fitan ma ba sa ya yi balle su yi wani yunƙurin ganin hakan ya faru. Wasu ma da suka riƙa a cikin harkan har ƙungiya ne da su da zaran kin yi yunƙurin fita za su sanya miki wani cutar da za ki yi ta fama da shi har sai kin gwammace mutuwarki akan ci gaba da rayuwa. ko ma su haukata ki gabaɗaya wasu ma idan kika yi karo da masu rangwamen imani sai sun yin sanadin rayuwarki. Kin ga duk wacce ta yi gangancin barin cikn gidan iyayenta ta bijire musu ta zaɓi ta yi nisa da su har tsautsayi ya sanya ta sako ƙafafunta cikin harkar bariki sai dai a fitar da gawarta ba daidai ta sauya sheƙa ba".
Kalamanta suka sanya ni faɗa cikin tunani mai zurfin haske sai na ɗau wasu mintuna kafin na magana a hankali.
"Ki na nufin matan cikin gidan nan ma duk Hajiya Babba ta kafe su ke nan? Ko suna son barin wannan harkar ba za su i ya ba?".
Maimakon ta amsa mini sai kawai ta fashe da dariya mai matuƙar sauti har tana shiɗewa ta kwanta akan katifar tana dariyar. Na tsaya kawai ina ta kallonta cikin al'ajabi da mamaki.
"Ki gwada ƙoƙarin fita ki ga ni sai ki zo ki ba wasu labari". Ganin ta mayar da abin shiririta ya tursasa mini yi wa bakina linzami sai dai giyar mamaki da al'ajabin da zantukanta suka shayar da ni bai sake ni har yanzu wannan lokacin.
Jiya ina jin hayaniyarku da Shaaqana ikon Allah. Kin yi min daidai don tun kallon farko da na yi wa yarintar na ji ba ta kwanta min a cikin rai ba, ita ba kyau ba, ita ba kyakykyawan sura balle giri haka nan babu murya mai daɗin sauraro uwa uba ga duhun fata tamkar bayan tukunya".
"Ta kai ni maƙura ne amma ni ma hakan ba halina ba ne".
"Ai babu abin da bariki ba ta saka mutum ya yi duk wani halin da bai kasance naka ba dalilin bariki da rayuwar jikinta, za ta sanya ki fara ɗabi'antuwa da shi ba tare da ita ma kanta ta sani ba. Kin ga bariki da kike gani kike raina wa awwbillahillazi babu abin da ba zai sa mutum ya yi ba, take za ki rikiɗe ki soma sauya launi tamkar hawainiyya".
"To Allah ya kyauta".
"Amin". Ta amsa da shi a taƙaice tana tashi ta zauna daga kwanciyar da dariyar da take yi ya tursasa mata yin sa.
"Yanzu dai za ki raka ni kasuwar ne ko ƙaƙa?".
Ta ɗan yi shuru kafin na yi tunanin abin da zan faɗa"sai dai mu yi wani abu ki ba ni gishiri na ba ki manda".
Ta bi ni da ido"yi min yadda zan ga ne".
"Zan raka har sai kin gama duk siyayyar da za ki yi ko da kuwa za mu kai dare a can. Amma ni ma fa za ki taimaka mini ta wani fannin don cimma wani daɗaɗɗan burin raina".
"Wani buri ne wannan haka? Kuma ta wani hanya zan iya taimaka miki?".
Na gyara zamana kafin na hau zazzago mata bayani ina zuba tamkar bishiyar magarya.
"Akwai wani mutumin da nake son ko ta wani hali ne na gan shi ya ganni ko da kuwa na minti guda ne. Sai dai kasancewarsa babban mutum kuma mai kima da daraja a idanun mutane hakan yana neman ya gagare, idan har kika taimaka mini ki ka yi mini hanyar ganinsa kin gama yi mini komai a cikin rayuwar nan". Cike da zaƙuwa ta ce"wane mutum ne haka?".
"Sunansa Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe, amma na ji a garin nan ana ce wa da shi ba baƙin balarabe". Tun kafin na gama zancen ta waro idanu waje tare da dafe ƙirji"anya kanki ɗaya kuwa kin san abin da kike faɗa? Duk da ban cika sauraron wa'azi da halattar inda ake faɗin Allah ya ce Annabi ya ce ba, tabbas wannan sunan ba ɓoyayye ba ne ga kunnuwan kowa da yake cikin garin na babba da yaro. In ban yi ƙarya ba a iya sani na shi ɗin babban Malamin addini ne da aka yi masa shaidar dukkanin halaye da ɗabi'u na ƙwarai. In kin haɗu da shi me ye za ki ce masa ke kuwa?".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na soma kora mata bayani daki-daki ban ɓoye mata komai tun daga farkon haɗuwarmu na kwashe na sanar da ita.
Ta yi shuru tamkar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"to ke yanzu ta ina za ki fara neman sa? Sannan in kin yi dace kin gan san ma me ye za ki ce da shi har ki ja ra'ayinsa? Wallahi da gwamma garin nan kika yi wannan alwashin akan sa sai na ce da ke hakan zai ya fi miki sauƙi n akan wannan da kika yi".
"In dai har na gan sa ɗin to haƙiƙa na yi mai wuyar".
Ta yi shuru tare da zabga tagumi tana kallona kafin ta ce"tabbas ba ki da hankali". Ta yi zancen tana ƙoƙarin tashi ta fita na yi hanzarin cafko hannunta.
"Ina cikin hnakalina sai dai ku da kuke yi mini kallon zautacciya ku ya kamata a bincike ƙwaƙwalwarku. Ke dai inda taimakon da za ki iya yi mini kawai ki yi mini inda babu taimakon da za ki yi mini kuma to ki bi ni da fatan alkhairi".
Sai da ta ƙare mini kallon tsaf irin kallon da mai hnakali yake yi wa zautacce kafin ta ce"ban san me ye zan ce miki ba Amatullah". Ta koma ta zauna kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya.
"Taimako ɗaya zan yi miki shi ne na haɗa ki da wata mata da take ba ta sirrin mallaka da karkato da hankali mutum zuwa gare ka, shi ma kuma fa sai ku na garin ɗaya ta yadda za ku dinga haɗuwa har aikin ya ci".
Na jijjiga kaina"ba na son na jawo hankalinsa ta hanyar asiri. In dai kawai in akwai hanyar da za ki yi ki taimaka mini ki yi amma ba wannan ba". Ta yi shuru na tsawon mintuna har sai da na karaya kafin can ta ce"na san otel ɗin da tawagarsa suke sauƙa idan suka zo gabatar da wa'azi a ciki garin nan, sai dai in daga nan za mu sama ƙarin bayani. Don na taɓa ganinsa sau ɗaya a otel ɗin lokacin da ya zo gabatar da wa'azi a cikin tsakiyar watan Ramadana. A lokacin an ce babu yadda mai martaba Sarki bai yi da shi ba akan ya sauƙa a can masarautar amma ya ƙi a lokacin har Gwamma sai da ya saka ba ki amma bai amince ba, dalilin hakan ranar aka yi kora a otel ɗin babu wanda aka ba wa ɗaki sai shi da tawagarsa".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina hamdala a cikin zuciyata. Farin ciki ƙarara ya bayyana a bisa fuskata da har sai da na kasa magana.
Sai da na yi da gaske na sama zarafin faɗin"to yanzu yaushe za mu je mu tambaya masu otel ɗin?".
"Mu je ina otel? Ce miki aka yi haka siddan ake zuwa otel ɗin a soma tambayan ma'aikatansu bayanan kwastomominsu? Ai hakan ya saɓawa ƙa'idar ko wani irin aiki kawai taɓarɓarewar ƙasar