DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   36 / 39

105K to 108K   out of 116.4K words

ta yi saƙayau nauyin da ƙirjina ya yi mini na ji tamkar ana warware mini shi, ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba.
"Idan har hakan ya tabbata ni kuma na yi maka alƙawarin babu abin da zai hana ni aurenka, na tare a cikin gidanka a matsayin matarta". Da gaggawa ya katse ni"wannan abun da kike faɗa har cikin zuciyanki haka yake?".
Jikina a sanyaye na ce"ƙwarai kuwa".

"Alhamdulillah! Alhamdulillah Ya Allah".

Kit! Na kashe wayar ba tare da saurari ragowar zancen ba, na kwanta na yi ruf da ciki ina hawaye. Ina jin wayar tana ruri wanda ina da tabbacin Saif ne yake ƙira amma ban ɗauka ba.
[12/26, 8:27 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 8️⃣0️⃣

Haka na raya tsawon daren da sallan dare sai bayan sallan asubahi na samu na kwantar da haƙarƙarina take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awun gaba da ni, cikin baccin na ji ana ƙiran sunana cikin sanyin amo tare da bubbuga matashin da nake kwance akan sa. A hankali na soma buɗe idanuna har na buɗe su tar akan fuskar Anty Sawwama da take zaune kusa da ni. Na murtsike idanuna yayin da nake ƙoƙarin tashi na zauna ina faɗin"har gari ya waye?".
"Wani irin gari ya waye kin san yanzu ƙarfe nawa kuwa? To yanzu kusa ƙarfe sha ɗaya ake nema na rana duba fa ki ga yadda rana ta take haskenta ya mamaye ko'ina". Zumbur na yi na tashi tsaye ina leƙa taga na ga hasken rana ya dalle tar.
"Innalillahi har rana ta fito haka Anty? Da kin tashe ni na yi aikin cikin gidan ai". Taƙaitaccen murmushi ta yi kafin ta ce"kwantar da hankali ai na gama duk wasu aikace-aikacen da ya kamata, hatta girki na yi ke dai abin da nake so da ke ki tashi ki je ki wanka ki zo ki ci abincinki ga shi can a cikin kicin". Daɗin zantukanta da yadda suka faranta mini ruhina ya sanya ni sakar mata da murmushi ina zuwa na rumgume ta ina ta jeranta mata godiya wani na bin wani. Albarka ta din ga sanya mini tamkar za ta yi aron baki.

Haka na fito na yi wanka na shirya sannan na ɗauko abincin na tisa kwanon gabana kafin na saka hannuna wayata ta soma ruri, na ɗauko wayar ƙiran Saif ya shigo cikin wayar ban ɗaga ba har sai da ya katse ya ƙara ƙira a karo na biyu kafin na ɗaga, cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa mini cike da kulawa.
"Har kin tashi ke nan?".

"E".

"To ina miki fata da addu'ar Allah ya sanya wannan ranar ta zama rana mafi daraja da alkhairi a gare ki". Cike da jin daɗin addu'ar tasan na amsa da faɗin"amin ya Allah tare da kai gabaɗaya".
"Jiya kin yi min wani furuci wanda nake son ki tabbatar min da shi a yanzu ido yana ganin ido, don na sai na gama sakankancewa akan hakan ashe kuma gigin bacci ne yake ɗeban ki san da kika yi zancen".

"Wani zance ke nan?".

"Alƙawarin amincewa da aure na da kika yi mana". Sai da na ja dogon numfashi na fesar da shi daga bakina kafin na sama zarafin cewa"a cikin hayyacina na yi wannan zancen kuma ba a iya fatan bakina ya sanya ya ratsa har cikin zuciyata". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kana ya ce"ni kuma in sha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe kafin can ya kuma cewa"to bari na bar ki ki huta, in sha Allah a yau ba sai gobe ba zan yi duk yadda zan yi na ga sautin muryan nan ya shiga hannun Sultan. Na san duk yadda zan yi memory card ɗin nan ya je hare sa duk da yanzu ba ma tare da shi a gari guda".

"Fatan nasara". Na furta masa a taƙaice da hakan muka yi sallama da shi na ajiye wayar tare da jingina bayana jikin bango na ɗan lumshe idanuna ina sauraron yadda zuciyata take buga wa a hankali hankali. Yayin da wasu tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyata tabbas izuwa yanzu na ji zuciyata ta nutsu da Saif ban san ko hakan ake ƙira da soyayya ba don ban taɓa tsintar kaina cikin irin makamancin wannan yanayin ba.
Haka na gama cin abincin cikin rashin daɗin yanayi na fito na wanke kwanun, na leƙa ɗakin su Yaya Alhassan na ga ba ya nan Umar ne kawai a ciki yana karantu wani littafin turanci.

Ya ɗago kai ya na kallona kafin ya ce"ke kuma me ye kin wani tsare ni da idanuna kamar za ki cinye ni? Mai sunan tsofaffi kawai". Murmusawa na yi kafin na furta"za ka ji da shi dai, ai sai an kula kare sannan yake haushi". Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin"yanzu ni ne karen ke nan? Ai wallahi in da ni kare ne da tunin na daɗe da cinye namanki har na taune ƙasussuwanki yarinya". Dariya na aka mai sauti ina jijjiga kaina na juya na fice daga cikin ɗakin na koma ɗakina, karatun Alkur'ani na ɗan yi kafin na fito na haɗa girkin rana. Haka na wuni cikin tsammanin ganin ƙiran Saif ya sanar da ni yadda ake ciki amma shuru tamkar an shuka dusa har na kwanta ƙiransa bai shigo cikin wayata. Ni kuma ina kunyar ƙiransa haka na daure safiya ta yi ko ƙaran shigowar saƙon kamfanin layin MTN na ji ya shigo cikin wayata sai na yi zumbur na tashi na duba ko zan ci karo da saƙon Saif amma wayam, haka na ƙarar da wunin wannan ranar komai cikin sanyin jiki nake aiwatar da shi tamkar majinyaciya. Har dare ta yi bai ƙira ni ba muna tsaka da cin abinci na ji wayata ta yi ruri na kusa bazama da sauti na je na ɗauko ta da yake ajiye a saman firijin da yake cikin falon

Ina duba wa na ga baƙuwar lamba ce take na ji raina ya ɓaci don ba wannan nake tsammani ba, ban yi ƙasa a gwiwa ba na katse ƙiran tare da ajiye wayar na dawo na zauna ina zama wani ƙiran ya ƙara shigowa a karo na biyu na yi biris da shi tamkar ban ji ba.

"Wai ba wayanki ake ƙira ba ne Amatullah?". Yaya Alhassan ya jefa mini tambaya cikin kakkauran murya.
"Baƙuwar lamba ce ban san wanda yake ƙira ba".
"Ɗauko min wayar na gani". Ya furta cikin ba da umarni, hakan ya tilasta mini tashi na je na ɗauko wayar na miƙa masa daidai sa'ilin da wani ƙiran yake ƙara
shigowa a karo na barkatai. Ya ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa aka yi sallama ya amsa.

"Mansur ne mijin Amira". Aka furta daga ɗayan ɓangaren sai a lokacin da na ji muryarsa na tuna cewar lokacin da na je gidansu ta amshi lambana a fefa da nufin idan Mansur ya dawo za ta ƙira ni da wayarsa. Miƙo mini wayar da Yaya Alhassan ya yi bayan sun gama gaisa wa da Mansur shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na amsa wayar muka gaisa da shi kafin ya miƙa wa Amira ita muka gaisa.

"Ya na ji muryarki haka ba ki da lafiya ne ko kuma dai akwai wani abun da yake damunki?". Sai da na saci kallon Anty Sawwama kafin na mai da wa Amira amsar tambayar da ta yi mini.
"Lafiya ƙalau me kika ji da ya sa ki faɗin haka?".
"Haba! Amatullah ki na nufin ban san halinki ba ne ko kuma mene ne?". Da hanzari na taka mata burki ganin ta na ƙoƙarin wuce mini zani a cikin tsakiyar kasuwa.

"Mu na cin abincin bari inna gama zan ƙara ƙira". Ina gama maganan na katse ƙiran tare da ajiye wayan, na ci gaba da cin abincin sai dai duk a tsarge nake. Har muka gama cin abincin ban ɗago kaina ba muna gama wa na tattare kwanukan na je na wanke su kaina a ƙasa na zo na wuce zuwa ɗaki sai da na yi shirin kwanciya sannan na danna wa Amira ƙira, bugun farko ta ɗaga.
"Wai Amatullah ki na lafiya ƙalau kuwa? Na ji a jikina akwai matsala ga shi kwanakin sai mafarkinki nake yi da zaran na kwanta bacci wannan ya ƙara tabbatar min da cewar akwai wani damuwa. Don Allah mene ne yake faruwa?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kukan da ya yi matuƙar gigita mata tunaninta ta din ga jeranta mini tambayo ɗaya bayan ɗaya.
"Subhanallahi! Hashashen zuciyata ya tabbata ke nan wai me yake faruwa ne sanar da ni idan akwai wani matsalan?".

"Amira ina cikin matsala shi kenan na jefa kaina da wanda bai ji ba bai gani ba cikin matsalar da ni na yi silar ruruwanta".

"Wani irin matsala ke nan?".
Take na kwashe komai na yadda muka yi da Saif har da alƙawarin da na yi masa da kuma yadda ya daina ƙira na na tsawon kwanaki biyu, sannan na ƙara da faɗin"jikina ya na ba ni tabbas akwai wani matsalan tun da har na ji shi shuru na tsawon wannan lokacin, sai dai ban san abin da yake faruwa. Idan ma matsalar ce ba na fatan ta shafi kowa mussamman Saifullah da shi ne mutum na farko da ya fara ba n goyon baya kuma ya tsaya mini tsayin daka wajen ganin na cika wannan burin da ya daɗe a cikin rai. Daman sai da Yaya Alhassan ya gargaɗe ni amma na ƙi amfani da abin da ya faɗa mini har umartana ya yi akan na karya memory ɗin amma na yi kunnen uwar shegu".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me yasa za ki aikata haka? Me yasa ke ba kya jin magana ne sannan ki na da kafiya akan abu. Na yi tunanin kin daɗe da mance wa da babin wannan mutumin a cikin rayuwarki ashe har yanzu ki na nan akan bakanki. Me yasa kike ƙoƙarin butulcewa rahamar da Ubangiji ya yi miki? Kike ta ƙoƙarin ganin kin bankaɗo sirrinki da Ubangiji ya lulluɓe ta a idon duniya?. Allah ya rufa miki asiri ya ceto ki daga rayuwar halakan da kika faɗa ya karkarto da hankalinki zuwa gida ki ka dawo rayuwa cikin ƴan uwanki, su ka rufa miki asiri suka yi miki gata suka ɗauke dukkan ɗawainiyyarki ta hanyar killace ki a cikin gida suna wadata ki da dukkanin abin buƙatun rayuwa. Daga ƙarshe Allah ya ɗaga kimarki ta hanyar yi miki tagomashi da samun mijin da yake shirye ya aure ki, duk wannan tarin ni'iman da Ubangiji ya lulluɓe ki da ita amma kike ƙoƙarin butulcewa". Izuwa yanzu kuka nake yi sosai wiwi don jikina ya gama mutuwa murus na kuma tabbatar wa cewar matsala ce ta hana Saifullah ƙira na ya sanar da ni halin da ake ciki.

Sai da ta sallawantar da wasu mintuna kafin ta furta"yanzu dai ki yi haƙuri ki kwantar da hankali, ki yi addu'a Allah ya sa komai lafiya kuma shi ma yana cikin ƙoshin lafiya. Idan kin ga abun ya ci tura to ina mai ba ki shawara da ke ki ɗaga waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki domin hakan ba laifi ba ne, masu iya magana su na cewa gaida mai gaishe ka ko da kuwa ba zai amsa ba". Sai da na zurfar da zafafan iska daga bakina kafin na ce da ita"na ƙira shi kuma?".
Ta katse ni"to hakan laifi ne ko kuma haramun ne aikata hakan? Kin ga wannan jan ajin babu inda zai kai ki sai dai ya sauƙe ki a tashar nadama. Ki ɗauki waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki alama ce ta nuna kin damu dashi, ko ke da nan ki na tunanin shi da yake ɗaga waya kullu yaumin ya ƙira ki shi bai san ciwon kansa da darajan kansa ba ne?". Luƙus jikina ya yi sanyi ƙalau har na kasa motsa wa daga inda nake zaune.

"In sha Allah inna ga shurun ya yi yawa zan ƙira shi". Ban ƙari sa zancen ba ta katse mini hanzari"kamar ya ya? Ai yanzu ya kamata ki ƙira shi son samu m, mu na gama wayar nan ki ƙira shi".
"Ki na ganin hakan ne mafita?". A kufule ta ce"ban sa ni ba, tun da ke nan zama kika yi kika miƙe ƙafa ki na jiran ƙiransa, to sai ki yi ta jira daga nan har zuwa ranar da mahadi zai bayyana". Ta gama furzar da zancen kit ta katse ƙiran ta bar ni da sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin ƙarfi. Rumgume wayar na yi a ƙirjina tare da lumshe idanuna da ruwan hawaye yake zuba daga cikinsu ina yin zantukan na Amira suna yi mini amsa-kuwwa a cikin na'urar naɗan sautina tamkar a lokacin take furta mini su daki-daki.
Wani sashin zuciyata ta gaskata abun da Amira ta ce da ni, don haka na ɗauki wayar na lalumo lambarsa na dannan masa ƙira sai dai ƙiran ba ya tafiya, a jere a jere sai da na yi masa ƙira uku amma duk ba ya tafiya. Dole ƙanwar na ƙi na haƙura na ajiye wayar na kwanta ina ta fama da tunani kala daban-daban bacci sai da ya cika cikakken ɓarawo kafin ya iya ɗauka na sai da na makara tashi sallan asubahi, ko da na iddar da sallan sai da na ƙara gwada layin Saif amma har yanzu ba ya tafi, ganin tunanin yana neman ya yi rikita mini kwanyata ya sanya ni ɗauko alƙur'ani na buɗe na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai da na ji zuciyata ta sama nutsuwa wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko da na gama karatun zama na yi a wajen na zabga wani uban tagumi.

Ban san lokacin da Yaya Alhassan ya shigo cikin ɗakin ba har sai da saurin muryarsa ta ratsa dodon kunnuwana.
"Tunanin me ye kike yi haka?". Na yi figigi na dawo cikin hayyacina"na'am ka ce me ye?". Ya kafe ni da ido kafin ya furta"tunanin me ye kike yi?".
Na sadda kaina ƙasa"babu komai".
"Koma dai mene ne tabbas kawai abin da yake damun ki, ki yi ƙoƙarin yaƙar duk damuwar da yake damunki a cikin ranki".

"In sha Allah Yaya na gode sosai".

Naira duhu uku ya zaro daga cikin aljihunsa ya ajiye mini a gabana tare da faɗin"ga wannan ki rage wani buƙatunki da shi, babu yawa ki yi maneji da shi".
Wani daɗi na ji ya cika mini rai da ruhina har sai da ya haddasa mini tsiyayar da ƙwalla zan yi magana ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga nuni hannu alamar ba ya son jin komai daga gare ni.
"Ki yi abin da na ce miki kawai".

Na buɗe baki zan yi godiya ya kuma katse ni"ba na son wannan godiyan nakin da ba shi da iyaka. Duk abin da na yi miki ki sa a ranki cewar haka daman wani nauyi ne da ya rataya a kaina na sauƙe shi". Kaina kawai na jinjina masa kafin na furta"Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da azurki mai amfani".

"Amin" ya Allah ya amsa da shi yayin da yake tashi ya miƙe tsaye haɗe da ƙara faɗin"babu wata matsalar ina fatan dai ko?".

"E babu komai Yaya Alhassan, tabbas a zamana da ku kun wadata ni da komai babu abin da na nema na rasa". Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce mini komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin na raka shi da kallo har ya fice kafin na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyin gaske. Na daɗe zaune a wajen kafin na tashi na je na nuna wa Anty Sawwama kuɗin ta yi ta sanya mana albarka tare da yi mana addu'ar Allah ya haɗa kawunanmu kana na fito na soma rage wasu ayyukan cikin gidan. Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa lokaci yana shuɗawa har aka dosa kwanaki biyar ba tare da Saifullah ya ƙira ni ba hakan nan du ƙiran duniyar nan da zan yi masa layinsa ba ya shiga, duk na bi na damu hankalina ya yi mummunan tashi da na zauna shuru to ba ni da aiki sai tunaninsa da tunanin halin da na jefa sa ba na sanin lokacin da hawaye yake zuba daga idona sai dai kawai na ji ɗumin su a bisa kuncina.
Duk wanda ya ganni ya san inda cikin matsanancin damuwa da ƙololuwan tashin hankali amma haka na yi ta ɓoye wa duk tambayar da za a yi miki cewa nake yi ba komai idan aka matsa mini ba sai na fashe da kuka ala dole suke haƙura su bar ni ba don sun sama abin da suke so ba.
Ranar da aka cika sati da faruwan lamarin a wata safiyar ranar lahadi ƙiran Saif ya shigo cikin wayata kafin na ɗauka ƙiran ya tsinke ina ƙoƙarin bin ƙiran ya ƙara ƙira a karo na biyu.

Jikina yana rawa na ɗaga ƙiran na soma amayar da tulin damuwar da yake kwance ƙasan raina.
"Lafiya kuwa kwana da yawa inna ƙira layinka ba ya shiga, sannan ba na ji daga gare ka ina fatan dai lafiya babu wani matsalar ko?".
Sai da ya numfasa kafin na ce da ni"ki na gida ne?".
"E". Na amsa da shi har zuwa lokacin jikina yana rawa tamkar mazari.
"Nan da awa ɗaya mu na zuwa, ki sanar da mutanen gidan".

"Ku na zuwa kai da waye ke nan? Sannan lafiya zuwa haka bakatatan ba tsammani?". Na yi zancen jikina yana tsananta rawan da har sai da ya tilasta mini yin zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ina sauraron amsar da ya dawo mini da ita muryarsa cike da rashin walwala.
"Idan mun zo za ki ga wanda za mu tare da shi, sannan za ki ji dalilin zuwan mu". Daga haka ya katse ƙiran ya bar ni da faman faɗin"hello! Hello". Har

36 / 39