DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   22 / 39

63K to 66K   out of 116.4K words

kika ɓoye ainihin wace ce ga Anty, me yasa kike da fuska biyu? Ki na nuna wa kamar ke ɗin mace ce mai nutsuwa da hankali bayan zahirinki ba hakan kike ba, karuwa ce ke wacce take rayuwa a cikin gidan karuwa da masu zaman kansu. Tun ranar da Anty ta kawo ki cikin gidan nan na sa a yi min bincike akan ki kuma an kawo min cikakken labarin rayuwarki, me yasa kika ɓoye wa matar da ta yarda da ke gaskiyar wace ce ke? Me yasa kika ɓoye wa matar da ta aikata miki a lokaci da kike tsananin buƙatar taimako ainihin kalarki? Ta yarda ta ke wannan dalili shi ya ba ta ƙwarin gwiwar kawo ki cikin gidanta, ka sakar miki tagarman kula da cikin gidanta da kuma ƴaƴanta. A wasu lokutan har su na shafe tsawon awanni tare da ke wanda ba sa yin rabin sa tare da ita sa boda yanayin aikinta da yake tursasa mata fita a cikin ko wani irin yanayi". Ya ɗan tsagaita kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya.

"Me yasa kika shigo cikin rayuwarmu? Waye ya aiko ki kuma nawa suka ba ki? Aikin tsawon wani lokaci za ki yi musu?".

Ban san sa'ilin da hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na buɗe lumshashshun idanuna da suka rikiɗe suka sauya launi zuwa launin ja, suka yi jajir da su har wani zafi da zogi suke yi mini. Ba tare da na sani ba bokatin da yake hannuna ya faɗi ƙasa ruwan da yake cikin ya malale a waje.
A karo na farko da na yi jarumta jefa ƙwayoyin idanuna cikin nasa sai dai na kasa magana sa boda rawan jiki da kuma nauyin da bakina ya yi mini, su suka haɗu suka yi mini taron dangi na gaza aiwatar da komai.

Ya cije leɓɓansa kafin ya furta"ba za ki iya cewa komai ba to ma ina karuwa take da kalaman kare kanta ko kuma ta wanke kanta? Amma tabbas ki tanadi kalaman da za ki wanke kanki da shi a gaban Allah don ba ki da wani hujjan zuwa bariki face son zuciyarki da kike biye wa har ya kai ki zuwa cikin halaka". Zafin da kalamansa suka yi mini ya sanya ni toshe kunnuwana da tafukan hannayena.

"Ya isa haka na ce ya isa". Na yi zancen cikin sarƙafewar harshe da rawar murya.
"Bai isa ba na ce bai isa ba. Kin cutar da rayuwarki a shekarunki har kin san ki iya zuwa cikin otel".

"Ya ishe ka". Na yi zancen cikin zafin rai da ɗaga amo, tar na buɗe idanuna tare da nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata, jikina har izuwa lokaci bai bar rawa haka nan hawayen da suke kwaranya daga koramar idanuna ba su daina gudana ba.
"Ka na tunanin Bawa yana da damar tsarawa kansa irin rayuwar da ta dace da shi ne? Ka na zaton cewa akwai wanda zai zo rayuwarsa ta lalace tun daga tushe sannan duhu ya mamaye hasken da ya zamo masa sandan jagora? Na san ka na da ilmi don ba ba ka yi zubin jahilai ba sai dai ilmin bai yi maka amfan tun da ya kasa samar maka da amshoshin mungayen kalaman da kake jifa na da su, ilminka bai tsinana maka komai tun da bai hana ka zartar da hukunci akan abin da ba ka da tabbacin akan sa ba. Ka sa an yi maka bincike akaina sai me ye na ce sai me ye? Me ye haka ya tsinana maka sannan ta ina hakan ya amfane ka?".

Sai da na yarce hawayen da yake tsintiri a bisa kuncina kafin na sama zarafin ci gaba da maganar cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata.
"Na ji na yarda binciken da ka yi a kaina ya kawo maka shi daidai, a cikin gidan karuwai nake rayuwa amma shin ka damu da binciko dalilin da ya yi silar zuwa na cikin gidan har nake rayuwa a cikinsa?. Na yarda zaman kaina nake yi ba na tare da iyayena, ƴan uwa balle kuma dangi. Babu wani wanda zai ƙwabe ni idan na yi ba daidai ba balle kuma wanda zai dawo da ni kan turba a sanda nake ƙoƙarin kauce hanya, amma shin ka binciko dalilin da ya sa na zaɓi na yi irin wannan rayuwar? Me yasa ba ka sa an binciko mana yadda na gudanar da rayuwata ta baya ba?. Ka taso a cikin gata ka sama duk wani kulawa, tattani tare da riritawar da ko wani ɗa yake samu a zamanin ƙuruciyarsa, ka ci abinci mai kyau, ka sha abin sha mai kyau, ka kwanta a waje mai kyau sannan ka sama ilmin addini da na zamani a makarantar da kulawa ya wadata. Ka rayu da kulawar iyaye da kuma dangi waɗanda da ka ce wash za su tambaye dalili, sannan ba sa bari hawaye ya zuba daga idanunka kafin ka nema an tanada maka shi ta ina hankali da tunaninka zai sarrafa mata cewar akwai waɗanda ba su sama kwatankwacin irin gatan da ka samu ba. Ban taso da irin wannan gatan ba ranka ya daɗe amma mahaifina bai bar ni na taso cikin rashin tarbiyya ba, haƙiƙa ya wadata ni da ilmin addini da ya kai matakin har na hadda alƙur'ani mafi girma da daraja a cikin dukkan littattafan da Ubangiji ya sauƙe wa Annabawansa".

Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin ci gaba da amayar da zancen, idanuna suna hasko mini abubuwan daki-daki tamkar yanzu suke wanzuwa.
"A zamanin rayuwata ta baya na yi shura na ɗaukaka ta yadda duk wata uwar da za ta yi ɗiyarta faɗa da nusar da ita akan ta guji ruɗi da ƙyale-ƙyalen cikin duniya da ni Amatullah take buga mata misali. Na rayuwa a matsayin kamilar mace, mai nutsuwa, mai tarbiya, wacce hankali ya ratsa jini da jijiyoyin jikinta, mace wacce ta san kanta. Wacce babu wani abun duniya zai ruɗe ta ko kuma ya sauya mata tunaninta da yadda takr hango abubuwa, ana tinƙaho da ni a cikin unguwa yayin malamaina a makaranta su na alfahari da ni kafin guguwar ƙaddarar dake sarrafa rayuwata ya jijjige kyakykyawan tarihin da na kafa tun daga tushe. Lokaci guda ya shafe duk wani aikin alkhairin da na rayu a kansa ya shafa miji baƙin fentin da zai bibiyi rayuwata har ranar da numfashi zai yi ban kwana da gangar jikina. Na ja wa dangina abin kunya na tozarta iyayena mussamman mahaifina ya kai munzalin da har wasu suke tantama tare da sanya shakku akan tarbiyyar da ya ba ni. Idan ka san mafari ba ka san ƙarshe ba don haka kar ka ƙalubalence kowa a bisa rayuwar da ka ga yana yi ba tare da ka zurfafa bincike ka kuma ji ta bakinsa ba. Danganta ni da kalmar karuwa da ka yi kuma za mu yi hisabi da kai a ranar da ake wa tare da Yaumul tagabum ranar da Allah zai haɗa Bayinsa tun daga zamanin kakanmu Annabin Adamu har zuwa zamanin ƙarshe".

Ina dasa aya a zantukana na sunkuya na ɗauki bokati da moppern na yi shigewa ta cikin kicin na bar shi tsaye a wajen. Ina shiga cikin kicin ɗin na mayar da ƙofar na rufe tare da jingina jikina a jikin ƙofar, sannu a hankali na soma sulale wa ƙasa har sai da na yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa.

Hawayen da suke gudana a idanuna suka ci gaba da zuba tamkar da bakin ƙwarya duk yadda na so na yi karanto wani yanki daga cikin addu'o'in da na haddace a cikin kwanyata, lamarin ya faskara komai ya gagare ni aikatawa. Haka na cigaba da kukan mara sauti illa zafi, radaɗi da kuma zogi a cikin raina. Da ƙyar na tashi na je na ɗauko mopper da tsumma kana na ɗaukin bokatin na buɗe ƙofar kicin ɗin na fito da zummar gyara inda ruwan ya zube.
Ina fitowa idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yana zaune akan kujerar zaman mutum biyu ya kwantar da bayansa a jikin kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci. Sai dai tun daga kallon farko da na yi masa na fahimci cewa ba bacci yake yi ba a farke yake.

Ban b ta kansa ba na soma yin aikin da yake gabana na saka tsumman ina tsame ruwan wajen ina matse wa a cikin bokati sai da na tsame ruwan tas, na sama mopper na goge wajen. Na ji wani jiri ya na ɗiba na tare da ƙoƙarin kayar da ni ƙasa sai da na dafe jikin kujera kafin na iya tsaya wa akan ƙafafuna da suke rawa alamar sun gaza ga ɗaukar nauyin gangar jikina. Numfashina ya soma harɗewa waje guda jikina ya ɗauki zafi gau tamkar garwashin dake ƙasa tukuban tsire.
Duk wani karatun da ya fara ziyartar ƙwaƙwalwata shi bakina ya soma karantawa ban gushe ina yi ba har sai da na ji wani sanyin nutsuwa ya ziyarci sashin ruhina, ƙarfi ya ziyarci sakakken gangar jikina da ya sake tamkar ƙanƙarar da aka jefa a cikin ruwa.

Na cije leɓena yayin da nake ƙoƙarin tashi sai dai na kasa hakan sa boda nauyin da gangar jikina ya yi mini.

"Ki na lafiya kuwa?".

Na tsinkayo amon muryarsa tamkar daga sama ya sauƙa na'urar naɗan sautina, lamarin da ya sauƙar mini da wani karsashi a ciki jikina. Ban san lokacin da na tashi na tsaya tsam akan ƙafafuna ba, ban ko kalla inda yake ba balle na tanka masa na ɗauki abubuwan da na yi amfani da su na koma kicin ɗin na fita ta ƙofar baya na shanya tsumman akan igiya kana na dawo na fito. Idanuna har wani baƙin duhu suke gano mini da ƙyar na kai kaina cikin ɗakin Altine ina tura ƙofa na hange ta tsaye ta riƙe ƙugu tana fuskantar ƙofar shigo wa.
Ban bi ta kan ta na ɗauki sallaya zan shimfiɗa don na kwantar sa boda ciwon kai da jirin da nake ji, ta yi wuf ta wafce sallayan daga hannuna.

"Allah ya kiyaye Karuwa wacce take zaman kanta ta ɗaura wani sashin jikinta, akan sallayan da nake yin ibada a kansa".

Na yi ƙuri da ido ina kallonta sai dai bai ko kaɗan ban yi mamakin furucinta ba, don ina da tabbacin in dai tana cikin gidan ɗazun dole ta ji kuma ta san abin da ya faru.
Waje na nema zan zauna a ƙasa na ji an ture ni har sai da kaina ya bugu da jikin ginin ɗakin, wani zafi ya ratsa har cikin kwanyata. Na cira kai ina duban ta tare da sauraron zantukan da ta ɗaura da faɗinsu.

"Kin yi asara kin ji kunyar duniya da kuma lahira. Ashe duk kallon da ake yi miki kura ce lulluɓe da fatar akuya, ashe lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi. Wallahi kin yi asara har yawon otel-otel kike yi da ƙartin maza, in sha Allah daga rana mai kamar ta yau zamanki a cikin gidan nan ya zo ƙarshe don sai na tone asirin da kika haƙa rami kika burne shi a gaban Hajiya da kowa da kowa a cikin gidan nan".

"Allah ya ba ki sa'a".

Na furta a taƙaice sa boda ba zan iya dogon magana ba balle na sama ƙwarin gwiwa, nutsuwa da kuma kuzarin yi mata bayani sala-sala.
Na zauna tare da kifa kaina da gwiwa ina sauƙe ajiyar numfashi akai-akai, ban yi aune ba na ji a finciko hannuna tamkar za ta tsinke sa daga jikin gangar jikina. Cak ta miƙa da ni akan ƙafafuna ta finciko ni zuwa waje ja na take yi tamkar dabba duk da ina cijewa tare da turjewa lamarin ya fi ƙarfina.

Ba ta sake ni ba har sai da ta fito da ni harabar gidan ta yi jifa da ni gefe guda na faɗi ƙasa akan gwiwan hannuna. Daidai lokacin da motar Hajiya Muhibbat ta shigo cikin gidan, har ta gama daidaita parking ban ɗago kaina ba sa boda azabar zafin buguwar da na yi a hannuna har na ji hannun ya sake sosai, ina jin shi tamkar bai kasance ɗaya daga cikin wani ɓangaren gaɓoɓin jikina ba.

"Altine lafiya na gan ku a nan?". Muryar Hajiya ya ratsa ƙofofin kunnuwana da hakan ya ba ni damar ɗago kaina, kafin Altine ta ba ta amsa Saif ya iso wajen a hanzarce.

"Me ye yake faru wa?".

"Ina ka ga yanzu shigo wa ta na tarar da su a haka. Me yake faru wa Altine ki yi mana bayani me ye Amatullah ɗin ta yi na ga kin jawo ta waje haka? Wani abun ta ɗauka ko kuma kama ta kika yi laifin ha'inci?".

"Hajiya ai gwara sata akan munin abin da ta aika".

"Me ye ta aikata?".

"Hajiya ashe wannan yarinar karuwa ce, a cikin gidan karuwai da ƴan daudu tambaɗaɗɗun mutane da suka kwashe kayansu daga zauren Ma'aiki take rayuwa".
Cike da mamaki Hajiya ta ce"Karuwa kuma Amatullah ɗin?".
"Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe, ai ba a ƙarya kusa da gida ga ta nan ki tambaye ta idan ƙarya nake yi mata ko kuma na yi kuskure cikin maganganuna". Altine ta yi furucin cike da ƙwarin gwiwar da ya gauraye da karfin hali da zumuɗin bankaɗo sirrina.
[12/13, 12:57 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 6️⃣8️⃣

Cike da ruɗu Hajiya Muhibbat ta ce"wani irin magana kike faɗa haka Altine? Anya ki na cikin hankali da hayyacinki kuwa? A ina kika ji wannan maganar?".
"Hajiya ina cikin hayyacina sannan hankalina ma yana nan tare da ni har ki yi imanin cewar wai ba na cikin hayyacina. Da kunnena na ji Yallaɓai Saif yana tuhumarta akan wannan zancen, kuma shi ma ya san da wannan zancen ga shi a tsaya ki na da damar da za ki tambaye shi idan har ba ki yarda ba".

"Saifullah me ye gaskiyar abin da Altine take faɗa? Shin da gaske ne Amatullah karuwa ce kuma zaman kanta take yi a cikin gidan karuwai da ƴan daudu?". Runtse idanunsa ya yi yana cije leɓansa tare da zuba hannayensa cikin ajihun wandon farin shaddan da yake jikinsa.

"Kai nake sauraro Saif". Maganar da ta yi a karo na biyu ya sanya shi buɗe lumshashshun idanunsa muryarsa can ƙasan maƙoshinsa ya soma maganar a hankali.
"Anty haka ne a cikin gidan karuwai take rayuwa amma akwai wani abu guda wanda ba mu san da shi ba......". Ban bar shi ya ƙarisa ba ta yi wuf na amshe zancen yayin da nake tashi tsaye daga faɗuwar da na yi akan hannuna.

"Kar ki tsawaita bincike a kaina Hajiya don ina da tabbacin binciken ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba, babu komai a cikin tarihin rayuwata face ƙunci, tashin hankali da kuma ruɗani. Ƙaddarar rayuwata ta bambanta da na ko wacce yarinya mai irin shekaruna. Tun kafin na yi girman bambamce tsakanin fari da baƙi na san mene ne baƙin ciki kuma na san ɗanɗanonsa, babu kuskure a cikin dukkan abin da Altine ta faɗa tabbas haka ne a cikin gidan karuwai nake rayuwa kuma zaman kaina nake yi ba a gaban iyayena, ƴan uwa ko dangi nake ba gashin kaina nake ji babu kwaɓa babu mai tsawartawa balle wanda zai kama hannuna ya ɗaura ni a hanyan da take daidai. Sai dai tun da nake ban taɓa aikata zina ban taɓa kusantarsa sai dai na yi imanin cewa dukkanin wani Bawa ba ta taɓa wuce ƙaddararsa".

"Babu wani mai hankalin da za ki faɗa wa wannan maganganun ƙanzon kuregen nakin ya yarda da ke. Ta ya ya za a ce kin rayu a cikin tsakiyar karuwai ba tare da ki na aikata abin da suke yin ado da shi ba, to in ma haka ne ba ki aikata ba ɗin me ye kike zaman kanki?".

Na runtse idanuna da hakan ya ba wa hawaye. Da sur ciki mini kurmin idaniyata damar kwaranya, ina jin wani zafi a cikin raina tamkar ana watsa mini tafashashshen ruwan dalman da ba sirka shi da komai ba a cikin farfajiyar ƙirjina.
"Ban faɗa don neman yardarki ba sannan ban damu da ko wani irin kallo za ki yi mini, Abu ɗaya na sani kuma a kansa zan tsaya har ƙarshen rayuwata shi ne iya gaskiya ta na faɗa muku. Hajiya ina mai ba ki haƙuri akan ɓoye miki gaskiyar wace ce ni da na yi har tsawon wannan lokacin, haƙiƙa a ɗan zaman da na yi da ke na ga zallar ƙauna da tausayinki a gare kwance a cikin idanunki. Ban yi hakan da wani nufi ba kuma Allah shi ne shaida ta akan hakan.....".

"Ya isa haka ya isa Amatullah".

Hajiya Muhibbat ta dakatar da ni ba tare da na gama amaryar da zancen da yake kan harshena ba.
"Mai zaman kanta? Kin san ma'anar wannan kalmar kuwa Amatullah? Kin ba ni mamaki matuƙar ina miki kallon mai hankali da nutsuwa wacce ba ruwanta ashe kallon biri nake yi miki ki na yi min na ayaba. A ƙananun shekarunki har kin san ki sanya ƙafa ki baro cikin gidan iyayenki ki zo inda ba ki san kowa ba kuma ba wanda ya san ki ki fara zaman kanki. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wace iriyar rayuwa ce muke rayuwa a cikin ta haka? Me yasa masifu da bala'i kala-kala ba za su baibaiye al'ummar mu ba?". Ta tsagaita tare da yarce ruwan ƙwalla da ya zubo daga idanunta kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya.

"Daga yau ba na son na ƙara ganin ki a kusa a gidan nan balle kuma ki tsaya a jikin gidan nan, na sallame ki ki ƙara gaba niyyar da taimakon da na yi Allah ya ba ni ladan niyya ke kuma idan mai shiryuwa ce Allah ya shirya ki. Ga kuɗin aikinki". Ta ƙare zancen tana zige jakarta ta ciro wasu kuɗaɗen da ko tsaya wa ƙidaya su ba ta yi ba, ta watso mini su a fuskana.
Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina na cira kai na dube ta sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na sama zarafin magana.
"Duk magangunin akan turban gaskiya kike amma ke ma ina

22 / 39