Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
amarya kuma uwar ango. Ranar da za a kai ni tare muka wuni da Anty Zulaihatu da kuma Amira ranar mun sha kuka sosai har sai idanuna suka kumbura har ya kai jallin da ba na iya buɗe su. Gidan a cike yake da mutane maƙota, ƴan uwa da kuma abokan azurki. Dangin mahaifin su Yaya Alhassan ba su nuna mini tsana ko ƙyama ba sai ma ja na a jiki da suke yi da yi wa iyayen addu'ar samun rahamar Ubangiji.
Ban gaskata cewar da gaske an ɗaura mini aure ba sai da aka fito ni aka saka ni a cikin mota domin kai ni ɗakin miji, tun da motar ta soma tafiya ƙirjina yake dakan lugudai taka birkin da aka yi ya yi daidai da lokacin da hawaye suka zubo daga idanuna sai dai mayafin aka rufe mini fuskana da shi ya hana mutane fahimtar kuka nake yi, haka aka fito da ni daga cikin motar aka shigar da ni cikin gidan. Bayan wata dattijuwar mata ta yi mini umarnin na shiga da ƙafar dama tare da addu'ar Allah ya sa na shiga ke nan sai dai a fito da gawa ba.
Anty Zulaihatu ne ta kai ni har cikin ɗakin miji ta kuma jira har aka yi rakiyar ango ta damƙa amanata a hannun Yaya Alhassan tare da yi nasihar idan ya cutar da ni ko ya wulaƙata ni, to ba ni ya wulaƙanta ba kansa ya tozarta. Haka suka tafi suka bar ni ni ɗaya ƙwal don na kai ga roƙon Amira ta kwana murzawa idanunta toka ta yi, da na matsa mata sai ce wa da ni ta yi to ita kuma na ta mijin ta yi ya ya da shi? Haka ina ji ina gani duk aka watsa aka bar ni ni ɗaya tamkar mayya.
Ina zaune a cikin ɗakin ina kuka na ji an buɗe ƙofa an shigo ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya tabbatar mini da wanzuwar Yaya Alhassan kusa da inda nake, kafin na ji ya kai hannu ya yaye mayafin da yake kaina ya sanya hannunsa ya tallafo haɓana yana kallon fuskana da ta kumbura ta yi tsimtim tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis.
"Kukan nan ya isa haka Amatullah. Ki tausayawa kanki haka mana tun yaushe kike wannan kukan. Ya kamata kin san cewa kuka fa ba ya magani".
Shuru na yi ban amsa masa ba don ina da yaƙinin ko na buɗe bakina sautina ba zai fita ba.
"Amatullah". Na ɗaga kai na kalle shi da hakan ya ba shi tabbacin cewa ina sauraronsa.
"Aurena da ke ya ƙara tabbatar min da cewar duk abin da kasance rabonka ne to fa ba ya taɓa wuce ka, na kuma ƙara tabbatar da sahihancin wannan karin maganan ta Malam Bahaushe da yake cewa zakaran da Allah ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi. Allah ya ƙaddara cewa ke ce matar da zan aura a duniya ga shi kuma hakan a tabbata a lokacin da dukkanmu ba mu yi tsammani ba balle zato. Ina so ki cire komai a cikin ranki ki manta da duk wasu abubuwan da suka faru a baya domin yanzu sabon shafi ne ya buɗe a cikin rayuwarki. Na yi miki alƙawarin zame miki mijin marainiya wanda zai share miki hawayenki a duk sa'ilin da zuba kwanrayo. Zan kasance mai yi miki hidima har zuwa ƙarshen rayuwata, zan hidimta miki da karfina, lokacin da kuma aljihuna. Na yi ɗamarar sauya rayuwarki daga duhu zuwa bayyanannen hasken da zai haskaka miki hanya".
Take na ji kalamansa sun samar mini da nutsuwa a sashin ruhina, na ɗau lokacin kafin na yi magana cikin dushashewan amo.
"Ina fatan na kasace mace ta gari kuma saliha a gare ka kamar yadda Annabinmu ya ƙira mace ta gari da mafi ƙololuwan jin daɗin duniya ga raywuar ko wani ɗa na miji, ina addu'ar Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya akan komai matuƙar komai ɗin bai hauce wa hanyar Allah da koyarwan manzonsa ba".
Cike da jin daɗin kalamaina yake amsa wa da Amin, ya dafa kaina ya yi mini addu'a kamar yanda yake a addinance kana muka je muka yi alwala muka gabatar da salla raka'a biyu mu ka yi godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar a cikin rayuwarmu, sannan muka roƙe shi albarkar da yake cikin auren da kuma zuri'a ɗayyaba. Sai da ya haɗa mini da magiya da lallashi kafin na iya cin kazar amarcin da ya shigo da ita, jikina gau ya ɗau zafi sa boda zazzaɓin da ya rufe ni ga shi dare ya yi balle ya je ya sayo mini magana, amma duk da hakan bai saduda ba ya ɗaga waya wai zai ƙira wani abokinsa mai chemist in bai rufe ba ya je ya karɓo mini magana.
Da ƙyar na hana sa fita ta hanyar muna masa cewa na ji sauƙi haka muka kwanta washe gari shi ya tashe ni sallan asubahi nan inda na yi sallan na kwanta baccin huce gajiyan da na kwasa ban tashi ba har sai da gari ya yi haske wannan ɗin ma shi ya tashi ni ya ce na je na wanka na zo na ci abinci sai na sha magani don har ya fita ya amso mini.
Kunya ya mamaye ni matuƙar don ni gabaɗaya ma na mance da cewar yanzu ni matar aure ce shi yasa na kwanta na sha baccina hankali kwance. Tashi na yi na wanka da ruwan zafin da ya sanya mini na zo muka ci abincin da ya girka kana na sha maganin bai fita har sai da dangi da ƴan uwa suka fara zuwa gidan nan ma sai da ya Amira da Anty Zulaihatu sun zo kana ya fita bayan ya shaida musu cewar ku kula da ni don ba na jin daɗi. Nan fa suka haɗe kai suka din ga yi mini tsiya zolaya kam babu irin wanda ba su yi mini ba.
Sai da suka yi sallan magrib suka tafi bayan sun yi mini nasiha mai ratsa jiki da kashe zuciya, shawarwari kuwa sun ba ni shi daidai gwargwado sun kuma ɗaura ni akan hanyar da ta dace. Haka har na cika sati a cikin gidan aure Yaya Alhassan ne yake yi mana girkin safe duk yadda zan tashi da wuri don na yi aikina to fa sai ya riga ni, sai dai mu yi aikin tare, haka tun ina jin kunyarsa har na saki jikina mussamman da na ga yadda yake ta faɗi tashi wajen ganin ya kyautata mini ba dare ba rana, dole ni ma na yi azaman faranta masa na watsar da komai na rumgumi mijina da kuma laluman hanyar da zan bi in faranta masa rai.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kwanciyar hankali da nutsuwa suka tabbata a gare ni, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na yi ƙiba na murmure fatana ta yi kyau har wani sheƙi nake yi kamar bayan kifi. Duk da ba nida haske amma fatata ta yi farau ta washe. Zuciya babu wani damuwa haka nan raina fari ƙal tamkar zaiba. Ranar da na cika sati huɗu muka yi baƙi Saifullah da Muhammad Taufik suka zo wani abun mamakin har da Sheik Dawood sun wuni suna tattaunawa da Yaya Alhassan, ni kam kunya ta hana ni sakat tun da na fito muka gaisa ban ƙara koda wullagawa ta cikin falon sai da za su tafi Yaya Alhassan ya zo ƙira ni. Tabbas ba na buƙatar sai an faɗa mini da kalmomin baki idanuna kawai sun nuna mini cewar Sheik ya sauya don mun sha ruwan addu'o'i da albarka daga gare sa, ya ɗauki Naira dubu asiri ya ba ni da za su tafi.
Haƙiƙa Yaya Alhassan ya cika mijin marainiyan da ya ambata kuma ya cika dukkanin alƙawarin da ya yi mini a darenmu na farko, ya inganta rayuwata matuƙa da kuɗin sadakina na shiga harkan kasuwanci atamfofi nake sayar wa da duk wasu nau'in kayan sawan mata, likkafa ta ci gaba don har lefe nake haɗawa mai rai da motsi na fita kunya. Kan ka ce kwabo rayuwa ta sauya jin daɗi ya zauna mana ni da mijina ba mu da wani burin da ya wuce faranta wa juna, na ƙara waye wa da samun ilmin zaman duniya da kuma mu'amala mutanen cikinta. Ranar ina zaune kwatsam sai ga Hajiya Muhibbat a cikin gidana tsabar farin ciki sai da na rasa inda zan tsoma ta mun sha hiran yaushe gamo da ita, tare da ba wa juna labarin bayan rabuwa nan take shaida mini cewar mijinta Saddam zai ƙara aure kuma Zinariya ce matar da zai aura, don ita da kanta ma ta shige masa gaba wajen neman auren, don ta fahimci suna don junansu kuma ba za su iya rabu wa, sannan Saifullah ma zai angwance da babbar jika a gun Sheik Dawood, na yi musu murna matuƙa da lokacin auren ya yi Yaya Alhassan da su Amir suka je su domin shaida ɗaurin auren. Sati ɗaya tsakani Amira ta haihu sai dai ɗiyar ba ta zo da raina ba.
Ni kam haihuwar ta yi jinkiri don sai na shekara ɗaya da rabi a gidan aure kafin na haifi ɗa na miji santalele da shi, da sati ya gayayo ya ci sunan Abbana ana yi masa alkunya da Abul-khair watansa biyar a duniya aka yi bikin Amir da ya angwance da ƙanwar mijin Anty Zulaihatu mun sha biki don tare wa na yi a gidan Anty Sawwama, haka Yaya Alhassan ya gama fushinsa har ya sauƙo don kansa, a rage saura Umar kawai wanda kullum nake yi masa tsiya da cewar sai mun daina ba shi abinci.
Lokacin auren Muhammad Taufik gayya muka yi muka je mu bikin iyalan Sheikh suka karrama mu matuƙa har muka je muka dawo mu na jinjina halin girma da dattaku irin na su. Na zamo abar alfahari ga mijina iyayen da kuma ƴan uwa har ma da matan cikin unguwan da nake, a ko a kan hanya nake tafiya na ga uwa tana furta munanan furuci ga ɗanta, sai na dakata na sanar da ita illar hakan a wasu lokatan har na kan yanko wani sashi na cikin tarihi don hakan ya sama iznina a gare su. Don tabbas na ishe kowa misali cewar DAFIN HARSHE mussamman na uwa akan ƴaƴanta ya fi dafin maciji illa don shi kassara rayuwa yake yi gabaɗaya. Har gida Saifullah da Muhammad Taufik suka kawo mini matanyensu, Zinariya ma sa ta rikiɗa ta koma sunanta na yanka watau Maryam ta kawo mini mun sha kuka ni da ita, mussamman da ta labarta mini cikin tsananin da ta fuskata da barazana daga wajen Hajiya Babba a yayin da ta yi ƙoƙarin sauya rayuwa, ta ce da ni har hauka sai da ta sa ta yi hauka tuburan har sai an ɗaure ta da mari don in ta bazama ta fice daga cikin gida to fa sai lokacin da Allah ya nufa. Da taimakon Allah da kuma addu'o'i ta sama sauƙi har hankalinta ya dawo jikinta.
Ranar wata juma'a mun dawo daga gidan Anty Sawwama da muka kai mata wuni, ina gaba Yaya Alhassan yana baya yayin da yake riƙe da Abul-khair a hannunsa, na zaro makullin daga cikin jakata na buɗe ƙofar falon muka shiga ciki a nan cikin falon muka yada zango. Na amshi Abul-khair da ya fara bacci na je na kwantar da shi kana na dawo.
Kusa da shi na zauna na tisa shi a gaba ina kallonsa har sai ya yi magana.
"Ke lafiyanki kuwa wannan kallon kamar za ki cinye ni?".
Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na ce"kawai ina tunanin da wasu kalamai ya dace na gode wa Allah ne, bisa kyautar da ya yi mini da kuma ni'iman da ya lulluɓe rayuwata da ita".
"Ban gane ba".
"Yaya Alhassan ni da kai mun san cewa ban dace da kai ba, amma duk da hakan ka aure ni ka killace ni a cikin gidanka ka ba ni dukkan kulawan da ya dace. A zamanmu da kai kullum cikin neman sabon hanyan da za kyautata mini kake yi......". Ban ƙarisa ba ya ɗaura ɗan yatsansa a saman leɓena.
"Shit! Ba na son na ji wannan kalmar ta ƙara fito wa daga cikin bakinki. Bari na faɗa miki abin da ban taɓa faɗa miki ba, ni fa daman tun da ran Abba ina sonki a cikin zuciyata kawai na rasa ta yadda zan faɗa miki ne, ban san kuma yadda za ki fahimci maganar ba sa boda lokaci da yarinta a tattare da ke".
Hannunsa da yake saman leɓena na ture"wai daman tun lokacin kake so na?".
Ya ɗage mini giransa"ƙwara kuwa kawai ban faɗa miki ba, amma na san da na faɗa miki da yanzu mun haifi ƴaƴan ya kai dozin biyu". Babu shiri na kai masa duka a kafaɗarsa ya yi saurin zame wa.
"Dozin biyu sai ka ce ka sama akuya". Dariya ya ƙyalƙyale da shi sai da ya tsagaita kana ya ce"to me ye a ciki? Ai duk za mu iya kula da su. In kuma ba za ki iya haifa min ƴaƴa ba sai na je na auro wacce za ta iya". Harara na galla masa wanda ya ke yawan cewa a duk lokacin da na yi masa sai ya tsorita.
Zan yi magana ya katse ni"kin ga mayar da wuƙan wasa nake yi miki, Amatu ke ce wacce nake so kuma ba zan taɓa iya haɗa soyayyarki da na wata mace ba, ina fatan ki kasance matata har a cikin gidan aljanna". Ya ƙare zancen ya na jawo ni jikinsa ya rungume a ƙirjinsa, luf na kwantar da kaina tare da lumshe idanuna. Ya kawo bakinsa daidai kunnena kamar mai raɗa ya ce"Ina sonki matar Alhassan".
"Ina sonka mijin Amatullah".
A hankali ya ke shafa kaina kafin na ji ya ɗauke ni cak ya wuce da ni cikin ɗaki, na yi luf abina.
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! A yau Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafin mai suna DAFIN HARSHE . Ina roƙon Allah ya yafe mini kuskuren da na yi a cikinsa abubuwan alkhairin da na yi a ciki kuma Allah ya haɗa mu akan ladan. Ina godiya ga masoyana da suka yi jimirin bibibiyar littafin tun daga farko har ƙarshe ba tare da gajiya wa ba, ina godiya Allah ya bar ƙauna. Ga masu buƙatan littafaina, tambaya, ba da shawara ko wani gyara ƙofa a buɗe take, za a iya tuntuɓa ta ta wannan lambar kamar haka 07038908713.
Sai na ji ku.......