DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   28 / 39

81K to 84K   out of 116.4K words

da wani kuka da ni ma ya tursasa hawaye kwaranya daga idanuna. Ban iya ce mata ko kanzil ba har zuwa lokacin da Yaya Alhassan suka dawo cikin ɗakin tare da Likitan ya duba ni ya kuma tabbatar da cewar jikina ya yi sauƙi ya rubuta mana sallama tare da wasu magungunan da ya ce lalle a saye su, kuma na fara amfani da su da gaggawa.

Haka muka fito har cikin haraban asibitin hannuna saƙale cikin na Zinariya, da Yaya Alhassan yake ta yi mata nasihar ta tuba da koma zuwa ga Allah da ya kasance gafurul rahim. Kanta kawai take gyaɗa masa don da ni da ita mun an cewa akwai ɓoyayyan matsalan da bala'in da yake tattare da hakan.
Ko da muka zo rabuwa da ita ji na yi tamkar raina zai bar gangar jikina. Haka muka sha kukanmu Amir ya din ga ba mu haƙuri da ƙyar muka saki hannun juna, haka muka rabu muka hau adaidaita muka nufi tasha, muna isa muka saka motar garinmu ba mu yi mintuna goma ba ta shiga muka soma tafiya.
Tun da muka soma tafiya ƙirjina yake bugawa har muka isa cikin garin, ina fitowa daga cikin motar na ji gabana ya faɗi da har sai da na runtse idanuna, muka tara adaidaita muka shiga na lura har zuwa wanna lokacin Yaya Alhassan fushi yake yi da ni hatta magana ma sama-sama yake yi mini shi ma sai ya zama dole ne. Mu na iso ƙofar gidan Anty Sawwama na ji wani zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe wajen gabaɗaya ya sauya miki tamkar wacce ta yi shekaru goma cur da barin cikin gidan, da ƙyar nake ɗaga ƙafata da na ke jin ta tamkar ba ta kasance ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikina ba yayin da wani jiri yake kwasa ta da barazanar buga Ni da ƙasa haka muka ƙarisa cikin gidan da Anty Zulaihatu da ta fito daga banɗaki na fara tozali.

Mamakin ganina ya sanya ta sakin butar da ke hannunta ya faɗi zuwa ƙasa, ta murtsuke idanunta don tabbatar da cewa ni ɗin ce dai ko kuma gizo nake yi mata, sai da ta tabbatar da cewa ni ce tsaye a gabanta kuma a zahiri ba mafarki kana ta kurm salati ta bi bayansa da hamdala tana faɗin"Umma Umma fito ki ga wallahi ga Amatullah ta dawo". Ta ƙare zancen tana isowa inda nake ta rungume ni, ni kam na kasa yin komai illa hawayen da suke ta zuba daga idanuna har izuwa lokacin da Umar da Anty Sawwama suka fito, mu na haɗa ido da ita ta ja ta tsaya a wajen guda kawai ta kafe ni da ido ba tare da ta ce da ni komai haka nan ba ta ƙariso inda nake ba.
Na sa ƙarfi na ɓanɓare Anty Zulaihatu daga jikina na isa gaban Anty Sawwama na durƙusa akan gwiwoyina sai dai na gaza cewa komai na tsawon mintuna illa kukan da na ci gaba yin sa da dukkanin ƙarfin da Ubangiji ya azurta ni da shi.
[12/19, 1:20 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________________

Page 7️⃣3️⃣

Na salwantar da wasu mintuna masu tsayin gaske ba tare da na iya cewa komai ba illa kukan da har izuwa lokacin bai yanke daga idanuna ba, haka nan babu wanda ya ba ni haƙuri balle kalman lallashina Anty Zulaihatu ma kukan da take yi yayin da har nake jin sautinta.
Sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙahon ƙirjina kafin na sama lasisin fesar da zantukan da suke bisa kan harshena cikin raunin da kai tsaye yake fitowa daga can ƙasan zuciyata da ta yi nauyin gaske.
"Anty don Allah ki yi haƙuri ki yafe mini. Na san da cewan na aika muku ba daidai ba ina roƙonku da ku yafe muni dukkan kurakuren da na aikata a gare ku, ko hakan zai haifar mini da salama a cikin ruhina har ya yi silar wanzar da kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin ƙirjina". Shuru ta yi ba tare da ta ce komai na tsawon wasu mintuna har sai da na yanke tsammani na kuma cire rai daga cewar za ta amsa mini, kafin na ji ta soma magana cikin rawar murya da ya taimaka wajen fallasa sirrin da yake taskace a cikin tsokar zuciyarta, na tarin damuwar da take ciki.

"Amatullah ba ki yi mana laifin komai ba. Kuma ba mu riƙe ki a cikin zuciyoyinmu ba". Ta ƙare zancen hawaye yana zuba daga idanunta, da hakan ya ƙara gigita ragowar nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina. Na cira kai na kalle ta na ga dai lalle hawayen da take yi, ban san sa'ilin da na ja jikina na riƙo ƙafafunta na rungume tare da jingina kaina a jikinsu ba.

"Don Allah Anty ki yi haƙuri ki sassauta mini wannan halin da nake ciki. Duba fa ki ga kuka ki ke yi sa boda baƙin ciki da takaicin da na yi silar cusa muku a cikin zuciyoyinku. Wallahi ba zan taɓa yafewa kaina ba akan halin da na yi dalilin faɗawarku cikinsa". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda numfashi da yake ta sama da ƙasa yana maƙale mini a ƙirji, ta sa hannu ta ɗago ni tsaye daga durƙushewan da na yi yayin da take goge mini ruwan ƙwallan da ya gama damalmala mini fuskana.
Sai dai ita ma ta kasa magana sai da ta runtse idanunta kafin ta iya faɗin"kamar yadda na sanar da ke tun farko duk cikin mun nan babu wanda ya ƙullace ki a cikin ransa. Kullum fata da burin da muke kwana mu tashi da shi a cikin zuƙatanmu shi ne Allah ya amintar da ke a duk inda kike a cikin faɗin duniyar nan, kuma Allah ya karkato da hankali da tunanin zuwa gida sai kuma ga shi Allah ma ji roƙan Bayinsa ya amsa mana addu'armu a lokacin da duk ba mu yi tsammani ba. Amatullah yadda nake jin su Alhassan a cikin raina kuma na jin babu wani abun da za su aikata a gare ni wanda idan suka tuba suka yi nadama Ba zan iya yafe musu ba, haka nan ke ma babu abin da za ki yi wanda ba zan iya yafe miki shi ba. Sa boda kamar ƴata nake jinki". Ta riƙo hannuna"ta ku mu je ciki". Daga haka ta ja hannuna muka shiga cikin falonta haka ta sa Anty Zulaihatu ta tafasa mini ruwan zafi ta kai mini banɗaki na je na yi wanka haka nan na iske suturuna a gyare tamkar an san da dawowa ta cikin gidan, ɗakin ko'ina tsaf da shi babu alamar datti balle ƙazanta. Kayan sawana kuwa har da waɗanda aka goge su sai tashin ƙamshi suke tamkar mun haɗa iri da ƴan maiduguri. Haka na durƙushe akan kayan na ci kukana tamkar raina zai fi ta tabbas na so na butulcewa rahama da ni'iman da Ubangijina ya lulluɓe rayuwata da ita kamar yadda Yaya Alhassan ya furta hakan a gare ni, na ja dogon numfashi na fesar yayin da nake ƙara shaƙan ƙamshin da ya buɗaɗe cikin ɗakin ina tuno tarin ƙarni sa ƙazantan da yake tattare a cikin ɗakin da na dawo, hatta banɗakin ɗaya muke amfani da shi duk yawan jama'ar da suke rayuwa a cikin gida, mata da kuma matan ƴan gida da kuma baƙi, kafin ka tsuguna ka sauƙe buƙatanta wajibi ne sai ka kora ruwa. Sai da na ci kukana kamar babu gobe kana na tashi na gabatar da sallan zuhur da kuma Asr nan inda na yi sallan na zauna na haɗa kaina da gwiwa yayin da na faɗa cikin cakwalkwalin tunanin da yake barazanar tarwatsa ƙalbina.

Ji da na yi an dafa kafaɗuna shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa, na cira kaina ina bin Anty Zulaihatu da kallo har ta iso gabana ta zauna tana kallona tamkar mai son gano wani gaskiyar da na haƙa rami na burne.
"Amatullah".
"Na'am" Na amsa da shi cikin sanyin amo da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganar da take.
"Mun yi kukan rashinki irin wanda baki ba zai iya furtawa ba, mun yi baƙin cikin kasancewarki a kusa da mu mussamman idan muka tuna amanarki da Kawu ya ɗauka ya damƙawa Umma lokacin da rai yake ƙoƙarin sallama da gangar jikinsa. Babu inda ba mu neme ki ba Amatullah sai dai tunaninmu bai taɓa ayyana mana cewa za ki iya zuwa ki yi rayuwa a cikin karuwai ba har ma ki ɗabi'antu da irin rayuwar da suke yi".

Kalamanta na ƙarshe suka zaunana zuciyata tare da baƙanta mini rai da ruhina take wani kuka mai matuƙar sauti ya tsinke mini. Na kifa kaina a kan cinyoyinta ina ta fama rera kukan jikina har wani rawa yake ye yi ga wani zafin da nake ji yana ratsa har cikin jijiya da ɓargona.
"Wallahi Anty ko daidai da rana guda ban taɓa aikata abin da kike zargina da shi ba. Ko karuwan da muka zauna da su cikin gida ɗaya za su ba da wannan shaidan a kaina cewar ban taɓa keɓewa da wani ɗa na miji ba". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"Amatullah Amir fa ya sanar da mu duk yadda aka yi da kuma irin dambarwan da aka yi da Magajiyar gidan Karuwan da kike zaune a ciki, kafin har suka iya samun daman tahowa da ke. Babban abin baƙin cikinmu ma shi ne a ranar da suke je neman ki a ba ka kwana a cikin gidan ba hasalima a ɗakin otel kika kwana". Cikin ƙarfin halin ta ƙare zancen sa boda kukan da ita ma ya karyo mata, kasa magana na yi illa jijjiga kaina da kawai nake yi yayin da zuciyata ta yi mini nauyin gaske yayin da na kasa samun damar harhaɗa kalaman da zan kare kaina a gare ta. Haka muka ci gaba da kukan ni da ita har izuwa lokacin da Umar ya shigo ya ce wai mu fito mu ci abinci sai da ta taimaka mini kafin na iya miƙe wa akan ƙafana muka fito falon, muka iske kowa yana zauna da Yaya Alhassan muka fara haɗa ido na ga ya wurga mini wani mungun hararan da ya hautsina kayan cikina, muka zauna tare da Anty Zulaihatu ta soma zuba abincin ga kowa yayin da dukkanmu muka yi shuru kowa da irin tunanin da yake saƙawa a cikin ruhinsa, juya cokalin kawai nake yi a cikin abincin don ni kam ba na tunanin ko na saka abincin akan harshena zan iya haɗiye wa har ya wuce ta cikin maƙoƙarona da ya bushe tamkar ƙasar sahara a cikin tsananin zafin rana.

"Ki ci abincin mana". Na tsinkayo muryar Anty Sawwama ta sauƙa a cikin kunnuwana. Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina ɗan gyara zama na buɗe bakina zan yi magana kenan na ji wani kuka ya ƙwace mini mai matuƙar sauti, da ya jawo hankulansu gare ni na kifa kaina akan gwiwoyina ina rera kukan daga can ƙasan zuciyata.
"Wannan kukan kuma na mene ne Amatullah?". Anty Sawwama ta jefo mini tambayar cikin tsananin kulawa yayin da take ɗago kaina da na kifa shi tana share mini hawayen fuskana.
"Ya kamata ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi tun da sanda kika shigo cikin gidan nan fa, kuka kawai kike yi ko daidai da minti guda ba ki bar idanunkin sun huta ba. Ya kamata ki tausaya wa kanki". Numfashi mai zafi na ja na fesar daga baki kafin na sama damar cewar"Anty don Allah ku yarda da ni wallahi tun da sa ƙafata na fita daga cikin gidan nan, ban taɓa aikata wani abun da na san cewa Allah ya haramta sa da gangan ba, na yi iya ƙoƙarin kiyaye kaina daga faɗawa cikin halaka da fushin Ubangijina". Ta ɗaga mini hannu alamar maganar ya isa haka dole na ja bakina na yi masa linzami.

"Mu gama cin abincin sai mu yi magana".
Ban iya ce mata komai ba illa jinjina kaina da na yi, haka aka ci gaba da cin abincin sai dai ni kam ina ci ne kawai ba wai don ina jin ɗanɗanon abincin a bisa harshena ba, haka nan ba don ina son cin abincin haka na ci gaba da tuttura abin cin har muka gama ci. Muka tattare wajen tare da Anty Zulaihatu muka wanke kwanukan, na dawo na zauna a ɗaki ina ta tsammanin ko Anty Sawwama za ta aiko a ƙira ni ta ba ni damar fayyace musu komai amma ba ta yi hakan ba, haka muka kwana ba tare da wani ya ce mini ci kanki ba na yanki dare na yi kuka mai tsanani har sai da na ji numfashina yana cushewa waje guda kafin na tsagaita, na tashi na fita na ɗauro alwala na zo na fuskanci alƙibla na tada kabbara. Raka'a biyu na yi a fashe wa Ubangiji da kuka a cikin sujjadata na ƙarshe.
Daren ranar ban iya runtsawa ba hakan ya sa ni washe gari na tashi da wani irin matsanancin zazzaɓi mai dafa jiki. Ina kwance a ɗakin Umar ya shigo ya iske ni a haka ya ruga ya je ya sanar da Anty Sawwama ta zo ta ɗago ni ta ji jikina ya ɗauki zafi gau. Ta sa Umar ya riƙa Yaya Alhassan ya zo shi ta ce ya kai ni asibiti yayin da ta umarce Anty Zulaihatu ta raka ni sa boda a gidan ta kwana, don a daren jiya na ji tana waya da mijinta yana shaida mata yau zai dawo daga tafiyar da ya yi.

Hijabina na saka na tashi tsaye yayin da Anty Zulaihatu ta riƙe mini hannuna sa boda yadda jiri yake ta faman kai ni ƙasa.
"Alhassan idan kun je ayi mata dukkanin gwaje-gwajen da suka kamata". Ciken rashin fahimtar inda zantukan natan suka nufo ya ce"wasu irin gwaje-gwaje ke nan Umma? Na yi tunanin ai zazzaɓi ne kawai".

"A yi mata gwajin dukkanin cututtuka ciki har da na cuta mai karya garkuwan jiki da kuma gwajin ciki".

Take na ji ƙirjina ya buga kwatankwacin irin bugun da maƙeri yake yi wa ƙarfi da dukkan ƙarfinsa. Kalaman Anty Sawwama suka karyar mini da zuciya tare da haifar da wasi-wasi a cikin zuciyata, mamaki ya cika mini raina sai dai na gaza juyowa na kalle ta kamar yadda na kasa ɗaga ƙafana na bar wajen. Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna muka bar wajen kafin na dawo cikin hayyacina haka muka fita muka nema adaidaita muka shiga zuwa asibitin.
Mu na zuwa aka ƙarbe ni aka yi mini duk wasu gwaje-gwajen da suka dace ciki kuwa har ta waɗanda Anty Sawwama ta lissafa. Tunin magunguna aka rubuta mini cikin har da ƙarin ruwa sun so su ba ni gado Yaya Alhassan ya ce su rubuta mini magani kawai. Haka muka saya magungunan jimgim muka koma gida a yadda muka iske Anty Sawwama ta na ta faman safa da marwa a tsakar gidan ya tabbatar mini da cewar duk da muka fita daga cikin gidan ruhinta bai huta ba hakan nan zuciyanta bai daina saƙa mata abubuwa ba. Sai da muka shiga cikin falo muka zauna sannan Yaya Alhassan ya tabbatar mata da cewar babu ciki a jikina kuma likitoci sun tabbatar da cewar ko cutar sanyi ba na ɗauke da ita balle cuta mai karya garkuwa jiki watau siga.
Silalewa daga kan kujerar da take Anty Sawwama ta yi ta yi sujudul shukur tana gode wa Ubangijnta Sarkin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Ta daɗe kafin ta ɗago ta koma mazauninta ta yi alama da idon akan na zo kusa da ita na zauna.

Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je kusa da ita na zauna na sadda kaina ƙasa yayin da ta riƙo hannayena ta sanya cikin nata ta na murzawa a hankali ta ce"Uwata ɗago idanunki ki kalle ni" a hankali na ɗago idona ina kallon fuskarta da ta washe da annuri.
"Ba wai ina tantama akan tarbiyyanki ba ne amma shin da gaske ne tun da kika saka ƙafa kika fita daga cikin gidan nan ba ki aika wani abun ashsha ba, balle kuma wanda Allah ya haramta aikata sa?". Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina na furta"wallahi Anty ban aika ko ɗaya daga ciki ba, na kiyaye mutunci da kuma kimar kaina". Daga haka na zarce da ba su lamarin duk abin da ya wakana tun daga ranar farko da na sa ƙafata na fita daga cikin gidan har zuwa lokacin da muka yi ido huɗu da Yaya Alhassan da Amir a ɗakin Hajiya, sai dai na ɓoyeH musu haƙiƙanin gaskiyan abin da ya kai ni otel a cikin wannan daren. Haƙiƙa na ga zallan tausayawa kwance a cikin idanunsu yayin da Anty Zulaihatu da Umar suka zubar mini da hawaye tausayi sosai, Amir da Yaya Alhassan kuwa duk jikkunansu ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Anty Sawwama kuwa baƙinta ya ƙi rufewa sai godiya take ta faman jeranta wa Allah na yi ta ƙara gode masa, tare da addu'ar Allah ya ba ta ikon kulawa da rayuwata daga yanzu har zuwa fitar numfashinta na ƙarshe.

"Ga Amatullah nan na ba ku amanarta da ragamar kula da ita duk wani a cikin ku da yake son faranta min, to ya faranta mata. Haka zalika duk wani da yake
son ganin ɓacin raina to ya musguna mat yy yh h yh hmy a, ko bayan raina ban yarda ku wulaƙanta ba ko kuma ku bari ta yi kukan maraincin mahaifinta". Jikinmu gabaɗaya ya kuma yin sanyi na kwantar da kaina a bisa cinyar Anty Sawwama ina faɗin"Anty ina Ummata tun da na zo babu wanda ya yi mini maganarta, ina so na je na gan ta ita ma na nema yafiyarta".

"Ummanki tana nan Amatullah. Kuma sa boda ita ne ma ya sa muka saya kai da fata wajen ganin mun dawo da ke gida". Babu shiri na ɗago kaina ina kallonta"sa boda ita kuma? Wani abun ne ya

28 / 39