DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   32 / 39

93K to 96K   out of 116.4K words

ƙofar ɗakin ya furta"sun gama ke yake jira".

"To ka ce masa gani nan fitowa". Kansa ya gyaɗa tare da juyawa ya fita don iskar da saƙon, muka miƙe ni da ita mu na kallon junanmu tamkar yau muka fara tozali da junanmu.

"To Amira sai kuma na zo ni in sha Allah, ki ci gaba da haƙuri akan wanda kika yi sannan ki ci gaba da addu'a Allah ya ƙara shirya sa ya kuma ƙara rufa asiri".

Cike da gamsuwa ta ce"wallahi na yi kewar shawarwarinki a gare ni, na tabbatar da ki na a kusa da ni da abubuwa da yawa sun zo min da sauƙi". Murmushi muka sakar wa juna hannunmu riƙe cikin na juna ta yi sallama a Anty Sawwama da ta haɗa mata turaren wuta taf a leda ta bata a matsayin tsaraba. Har ƙofan gida na rako ta muka hango Mansur tsaye a jikin adaidatan tana waya da wata ƙaramar wayar da yake kunnensa ƙiran kamfanin tecno.
Yana hango mu ya katse ƙiran ya ɗan faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"Amatullah kun fito ke nan?". Na gyaɗa masa kaina na lura sai wani ƙasa-ƙasa yake yi da kansa kafin na yi magana ya riga ni cewa"wallahi Amatullah kunyar haɗa ido nake yi da ke, tabbas na cutar da ƙawarki na ci amanar yarda da amanar da ta ba ni. Amma duk da hakan ta yi min halaccin da har ƙasa ya rufe idanuna ba zan taɓa manta wa ba, ki taya ni ba ta haƙuri ta yafe min tarin laifukan da na yi mata, amma duk da hakan soyayyar da take yi min ko kaɗan bai sauya domin ina ganin hakan a cikin idanunta". A raunane ya ƙare zancen tamkar wanda yake shirin fashewa da kuka.
"Mun riga da mun yi magana da ita in sha Allah komai ya wuce da yardan Allah. Ina fata da addu'ar Allah ya dawwamar da zaman lafiya a cikin gidan aurenki, ya albarkace ku da zuri'a ɗayyaba".

"Amin ya hayyu ya ƙayyum".

Suka haɗe baki wajen amsa wa cike da jin daɗin addu'ar, haka muka yi sallama da Amira ba don raina ya so ba ina tsaye a wajen har sai da na ga sun ɓace wa ganina kana na koma ciki.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana gudu yayin da kwanakinmu na duniya yake ƙarewa, wasa-wasa muna ƙara kusantar mutuwarmu ba tare da mun farga ba balle mu tanadin kuzurin tafiya. A cikin wannan yanayin har Umma ta cika kwanaki arba'in da barin duniya, a kullum kwanan duniya Anty Sawwama da ƴaƴanta ba su da wani burin da ya wuce su faranta mini ta hanyar samar mini da duk wasu abubuwan da zan buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci suka sauya mini rayuwata daga duhu zuwa bayyanan nan haske. Na sama dukkan wani kulawan da nake buƙata tare da tattali. Ranar da na cika wata uku a cikin gidan a wani rana bayan sallan isha'i na shirya na je ɗakin Yaya Alhassan, a ranar na yi yunƙurin sanar da shi komai dangane da dalilin zuwa na otel a wannan ranar da suke je nemana.
Yana zaune aka kujerar zaman mutum ɗaya da yake cikin ɗakin na yi sallama ya amsa mini na shigo sai kuma na tsaya a ƙofar ɗakin ya ɗago ido muka haɗa ido hakan ya sanya sa fahimtar dalilin da ya hana ni ƙarisowa. Ya tashi ya ɗauki rigarsa ya saka a jikinsa kafin na shigo cikin ɗakin.

"To yanzu kam sai ki shigo ko".

A hankali na tako na shigo na zauna ina gaishe shi ya amsa tare da zarce wa da faɗin"akwai wani matsala ne?".
"A'a daman na zo mu yi wani magana". Ya gyara zamansa yana fuskanta da kyau kafin ya ce"ina sauraronki".

"Ka bar sauraron wannan tukunna". Na yi zancen ina kunna masa sautin muryar da muka naɗa, ya amsa wayar ya na saurara sai da ya gama ji tsaf ya ga hotunan nan kana ya ɗago kai yana duba na cikin wani irin mungun yanayin muryarsa a ƙashe ya ce"waɗannan hotunan fa?". Jikina ya ɗauki rawa sa boda yanayin da ya furzo zancen take tsoro ya mamaye mini raunananniyar ƙalbina sai dai hakan bai hana bakina sanar da shi ragowar bayanin ba. Ban ƙarisa ba na ji ya ɗauke ni da wani irin mungun mari duk da ina zaune sai da na ji wani irin yana ɗauka na, marin da ya sauƙe mini har sai da bakina ya fashe ya soma zubar da jini. Cikin zafin rai ya miƙe tsaye yana nuna ni da ɗan yatsansa idanunsa sun yi jajir tamkar wanda aka watsa wa tsakin barkono, sai dai bakinsa ya gaza cewa komai.
[12/23, 2:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 7️⃣7️⃣

Mun ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya furzo takaicin da na yi silar cusa masa"me ye ya kai ki aikata wannan ɗanyen aikin Amatullah? Me yasa za ki jefa kanki cikin bala'in, fitina da kuma tashin hankali da zai zama ruwan dafa kanki wataƙila har ya ƙona ki? Kin san girma da martaba wannan mutumin kuwa a idanuna jama'a?".
Cikin ƙarajin kukan da sautinsa ba ya fita na furta"Yaya Alhassan mutumin ba mutumin kirki ba ne kamar yadda yake nuna hakan a idanun jama'a, ka na jin abin da yake furta wa ba. Ya yi silan lalata rayuwar ƴaƴa mata masu yawan gaske ta hanyar amfani da ƙarfin ikon da yake da shi a cikin jama'arsa". Bai bar ni dire zancen ba ya doka mini wani gigitaccen tsawan da ya tursasa mini haɗiye ragowar zancen har ina ƙoƙarin datse harshena.
"Ban taɓa tantama akan tabbacin cikar hankali da tunaninki har ma da ƙalubalantan ilminki ba sai yau Amatullah, me yasa hankalinki ya gushe har kika kai kanki cikin wannan bala'in? Har da bayyana fuskarki ki ɗauki hoto da shi, dole sai ta wannan hanyar za ki fallasa asirinsa ga duniya kowa ya san halin da yake ciki? Ai idan ba kya iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka kuma ka rasa hanyar da za ka kuɓutar da kanka". Tun da ya soma zancen na yi shuru tare da sadda kaina ƙasa ina sharar ƙwalla tare da ci gaba da sauraron zancen da ya ɗago da shi cikin zafin rai.
"Yanzu idan wannan hotunan suka fita suka watso a dunia ki na tunanin mutumci kika ja wa kanki ko kuwa rashinsa?" Ya dafa kansa cike da damuwar da ta bayyana ƙarara a fuskarsa har zuwa cikin muryarsa ya koma mazauninsa ya zauna ya sassauta amon muryarsa kafin ya soma faɗin"yanzu me ke kike so a yi da kika zo min da wannan zancen?".

Na ji shuru tamkar wacce ruwa ya ci ta, sai da ya ƙara maimata mini zancen a karo na biyu kafin na yi ƙarfin halin magana.
"So nake yi a san yadda za a yi a fitar da sautin duniya su ji, ina so asirinsa ya tono duk wani abun da yake ɓoye wa ya fito fili".
"Amatullah wai ina hankalinki ne ya yi aure ya tare ne? Yanzu idan aka ce miki ki fitar da wannan sautin muryar sai ki fitar da shi? Sanin kanki ne fa mutumin yana da ƙarfin iko, yana kusa da Sarakuna, gwamnoni da kuma masu riƙe da madafan iko fitar da wannan sirrin daidai yake da rushewan rayuka da dama da tarwatsewar dukkan ginin da aka yi na rayuwa. Tun da har Allah ya rufa mana asiri bai sama nasara akan ki ba ina so ki goge dukkan hotuna da sautin muryar nan, ki manta da kin ma taɓa sanin wani mai kama da shi a cikin rayuwarki balle har ki tuna wani zancen da ya shiga tsakaninku da shi". Ya ƙare zancen yana miƙo mini wayar cikin sanyin jiki na kai hannuna na amsa ina jin wasu hawaye suna zarya tsananin kuncina da kuma saman haɓata.

"Amatullah ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Alƙawarin Allah cewar dukkan wani azzalumi ba ya tare da shi kuma sai ya kunyata tun a nan cikin duniya a sai an je ga lahira ba. Mussamman ma masu ci da addini ko kuma masu fakewa da sunan addini suka ha'intan bayin Allah. Don Allah ki cire damuwar komai daga cikin ranki, idan halinsa hakan ko ba ka ma ki ba daɗe sai asirinsa ya tono a duniya sai Allah ya buɗe sirrinsa ga duniya kowa ya ji kuma ya gani sai ya tozartasa irin tozarcin da bai taɓa zato ba".

Kaina na jinjina da ƙyar na furta"to in sha Allah". Sai da na yi masa sai da safe kafin na tashi na tafi ɗakina ina shiga na zube akan katifar ina kuka mai ci rai, gabaɗaya jikina ya yi la'asar na rasa gane abin da yake damuna haka na kwana idanuna biyu ba tare da na runtsa ba. Washe garin ranar na tashi tamkar majinyaci komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar da shi.
Ina zaune a waje na tisa kwanon karin kumallo a gaba na ka sa kai ko da loma guda cikin bakina, Anty Sawwama ta fito har ta tsaya a kaina ban sani ba har sai da ta yi magana kafin na dawo cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da nake yi.
"Amatu lafiya kuwa? Kin tisa abinci a gabanki tun ɗazu kin kasa ci. Ke ba ki ci ba ke ba ki tashi ba". Sai na haɗo jarumta na yaɓawa kaina kafin na iya raba tsakanin leɓena na ce"babu wani damuwa Anty". Daidai lokacin da Yaya Alhassan da Amir suka suka fito daga cikin ɗakin kwanansu duk da kaina ya na ƙasa hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsa suna kaina ni yake kallo har zuwa lokacin da suka durƙusa suka gaishe da Anty Sawwama ta amsa musu cikin sakin fuska da kuma tarin albarka gare su.

"Alhassan ka zo ina son magana da kai". Anty Sawwama ta yi zancen idanunta akan Yaya Alhassan da ya amsa da to yana tashi ya bi ta suka shiga ciki. Zaman da Amir ya yi kusa da ni yana jan kunne abincin gabansa shi ya tursasa mini ɗago kaina ina kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce"abincin ne bai yi miki ba, ko kuma dai yanayin ne kawai?". Sai da na tsame hannuna daga cikin kwanon abincin kafin a taƙaice na furta"na ƙoshi ne".
"Me kika ci da har kika ƙoshi? Za ki zage ki ci abincin nan ko kuma sai na yi ɗura miki da ƙarfin tsiya". Na ɗago kai muka haɗa ido ya kashe mini ido guda yana yalwata fuskarsa da kyakykyawan murmushin da har sai da dake tsakanin haƙwaransa suka bayyana. Murmushin dole na sakar masa ina tsoma hannuna a cikin abincin muka soma ci tare da shi mu na ci yana ja na da hirar da amsana ba ya wuce uhm ko hmm haka har muka gama cin abincin na ɗauki kwano na je na wanke na dawo na zauna.
Ina zama Yaya Alhassan ya fito daga ganawan da suka da Anty Sawwama na bi shi da kallo na ga idanunsa gabaɗaya sun haɗa sun yi jajir gabaɗaya yanayinsa ya sauya haka ya fice daga cikin gidan ba tare da ya yi mana kallo azurki ba balle ya ce da mu wani abun.

Muka taka shi da kallo daga ni har Amir har ya fice kafin Amir ya furta"an ya lafiya kuwa? Na ga ya fito duk yanayinsa ya sauya". Na ɗage kafaɗuna alamar ban sani ba.
"Bari ki ga na bi shi na ji ko lafiya". Ya yi zancen yana miƙe wa ya bi bayan Yaya Alhassan, numfashi mai nauyi na sauƙe ina ɗan lumshe idanuna. Haka aka yi sati biyu a jere ba ranar da za ta fito ta faɗi Yaya Alhassan bai tambaye ni akan na goge sautin murya da hotunan nan ba, na kan ce da shi na yi hakan duk da kuwa har zuwa wannan lokacin na gaza goge su.
Ba na manta wata ranar juma'a wanda daga wannan ranar tubalin baƙin ƙaddarar rayuwata ta soma, da yammacin ranar Anty Zulaihatu ta zo ta gidan tare da mijinta Mu'azzam domin duba Anty Sawwama kasancewar ba ta ji daɗi a cikin kwanaki, ina ɗaki na ji shigowarsu na fito na gaishe su. Tun da na fito na lura da wani kallon ƙyaman da Yaya Mu'azzam yake yi mini har wani taɓe baki yake yi tamkar wanda ya yi arba da kashi, haka kawai na ji gabaɗaya jikina ya mutu murus har ya tashi ya fita akan zai je da dare ya dawo ya ɗauki Anty Zulaihatu na kasa ɗaga kaina. Zuwan Anty Zulaihatu ya ɗebe mini kewan da nake cikinsa sa boda ba na fita ko nan da can kullum ina cikin ɗakin.

Bayan sallan magrib Yaya Mu'azzam ya ƙira ta yana sanar da ita ba zai sama daman zuwa ya ɗauke ta ba, ta hau adaidaita kawai ta koma gida. Ƙarfe takwas saura na dare na fito na raka ta domin ta hau adaidaita muna tafe muna ɗan taɓa hira har sai da muka iso bakin titi kana ta sama abin hawa, muka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zuwa gidanta cikin kwanan nan.
Sai da na ga wucewan mai adaidaitan kafin na juyo domin komawa gida. A hankali nake tafiyar kaina a ƙasa tamkar wacce take neman wani abu a ƙasan haka har na iso ƙofar gida ina ɗago kaina na ga an dalle mini ido da hasken mota har sai da ya kai munzalin da na kai tafukan hannuna na kafe idanuna. Sai da aka kashe hasken na ga motar ta nufo inda nake na cira kaina ina kallonta sai dai na kasa gane inda na san motar.

Hakan ya sa ni soma tafiya zan shiga cikin gida na ji an ambaci sunana cikin sakakkiyar murya.
"Amatullah". Da hanzari na juya don tabbatar da mamallakin muryar take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saifullah da yake tsaye jikin motan yana kallo na kamar yadda ni ma na zuba masa idanuna. Ya tako ya iso inda nake tsaye.
"Kin wuni lafiya?". Bambarakwai na ji tambayar tasan wai na miji da suna Hajara, na ja dogon numfashi na fesar a ƙoƙarin daidaita nutsuwata kafin na ce"idan wajen Yaya Alhassan ka zo to bai dawo gida ba tun da ya fita sallan isha'i". Tun kafin na dire zancen ya katse ni"wajen ki na zo".

"Waje na kuma?". Na maimaita zancen ina yi masa nuni da kaina.
"Ƙwarai kuwa wajenki na zo ni Amatullah, idan da hali ma magana nake so mu yi mai matuƙar muhimmanci. So samu ma mu nema waje mu zauna".

"Ka faɗi duk abin da za ka faɗa, ina sauraronka".

"Ki yi haƙuri mu shiga cikin mota sai mu yi maganar". Na ɗaga masa hannuna"ka gaggauta faɗin abin da ya kawo ka, idan kuma ba ka shirya to ni zan koma ciki don ina da abin yi". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kafin ya ce"Amatullah ban san yanda za ki ɗauki maganar da zan furta miki a yanzu ba, amma ina so ki sani duk abin da zai fito a bakina a yanzu to daga ƙasan zuciyata yake fitowa kai tsaye kuma iya tsagwaron gaskiyata nake sanar da ke. Tun ranar da na san wace ce ina nufin asalinki da kuma tarihin rayuwarki tausayinki ya maƙale a cikin raina, a duk san da na zauna ba na komai to tunaninki ne da irin abubuwan da na aikata miki yake addaban raina. Yau na zo ne don na furta miki kalmar da ban taɓa furtawa wata ƴa mace ba tun da nake a rayuwata".

Cike da ƙosawa da sauraronsa na ce"ka tafi kai tsaye ga zancen da kake son furta wa".
Ya ɗan yi jim tare da sadda kansa ƙasa yana murza zoben azurfan da yake saƙale a ɗan yatsan hannunsa kafin can ya ce"Amatullah ina sonki, ina fata da burin ki kasance mata a gare ni sannan uwa ga ƴaƴana". Tun da ya soma maganar na kafe shi da idanuna ina ganin tamkar mafarki nake yi ba a farke nake ba.
"An ya ka san abin da bakinka yake furtawa kuwa? Ko kuwa dai ka mance wacce take tsaye a gabanka ne?". Ban jira amsar da zai ba ni ba na ci gaba da zancena cikin ƙonar zuciya da tafasan rai.
"Idan ba ka gane ni na yi mata tuni ni ce fa Amatullah wannan ɗiyar da ka zargi tarbiyyarta. Wacce ta yi ciki ba tare da aure ba wacce ta tafi can uwa duniya ta yi rayuwa ba tare da tsawatarwan iyayen ba. Wacce ta yi zaman kanta a cikin tsakiyar gidan karuwai ta ci gashin kanta da kanta. Wannan yarinyar da ta mayar da ɗakin otel tamkar ɗakin kwananta, wannan yarinyar marar tarbiya da nutsuwa. Wannan yarinyar da kake shakku da kokonton kasancewar ta kusa da ahalinka". Na saki murmushin takaici kafin na ci gaba daga inda na tsaya.

"Shin ko ka manta ku rayuwarku a tsaftace take? Ba ku da wani abun aibu a tattare da ku shin ka manta ikirarin da ka yi na cewar Allah a raba ku da kaidina?. Yadda kake mutumin ƙwarai kuma kamili ai da matar ƙwarai ka dace wacce ta fito daga gidan tarbiya da halin girma. Saifullah kar ka yaudari kanka da neman soyayyarta domin bayan rashin dacewan da muka yi da juna ba zan taɓa iya cusa sonka a cikin zuciyata da ka zama silar raunatata ba. Na roƙe ka idan ma ɓatan hanya ka yi ko kuma tuntuɓe harshe ka samu to kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan, babu wani abun da ya rage tsakanina da ku". Na ƙare zancen cikin rauni ina haɗe hannayena wajen guda alamar, zai yi magana na katse masa hanzari.

"Don Allah ka bar ƙofar gidan nan wallahi ba na ƙaunar ganinka. Ka yi wa girman Allah ka bar ƙofan gidan nan".

"Na ji zan tafi amma don Allah ki ba ni ko da mintuna goma daga cikin lokacinki, ki saurare ni ki ji bayanin da zan yi miki. Ban zo wajen da nufin yaudara ko cutar da ke ba hasalima....".
Na datse numfashinsa"ba zan

32 / 39