Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
a cikin gidan nan".
"To".
Kawai na amsa mata da shi a taƙaice, ta juya ta bi ta tare da wuƙar da yake hannunta. Kallon-kallo muka yi wa juna ni da Sha'awanatu kafin na wuce zuwa makwancina na kwanta raina a jagule. Ina ta jiran na ji ko za ta kunna sautin da ta yi ikirarin cewar ba ta iya bacci ba tare da ta kunna sa ba, sai na ji shuru kamar Malam ya haɗiye shirya. Na yi ƙwafa ina gyara kwanciyata tare da ƙara tabbatar da cewar wargi ma waje ya samu, kuma maganin biri karen maguzawa.
[12/5, 5:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 6️⃣2️⃣
Ban iya runtsawa ba har sai da dare ta raba sosai, sai faman juyi nake yi na kasa yin baccin. Gabaɗaya ba na jin daɗin komai raina ya gama ragulewa yayin da zuciyata ta lalace ainun. Ƙwafa na yi ina tashi na zauna duk da kuwa duhun da ya mamaye cikin ɗakin nan sai dai hasken farin wata yana hasko cikin ɗakin daga tagar da yake a buɗe.
Karatun alƙur'ani na soma yi tun sautina ba ya fita har sai ya soma fita na ɗau tsawon lokaci ina karatun har sai da na ji wani sanyi ta ratsa sashin ruhina, sai da na yi sallan asubahi kana na kwantar da haƙarƙarina wani bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, sosai na yi baccin ban farka ba sai da hantsi ya fito.
Ina buɗe idanuna na ga ranar ral ta galle, na yi zumbur ina miƙewa tare da murtsike idanuna don tabbatar da sahihancin abin da nake gani. Tabbas rana ta yi saboda yadda ta galle haske da zafinta ya mamaye ko'ina. Kallabina na za ra na ɗaura akaina na saka hijabina na ɗauki buta na fito na wanke fuska da bakina na mayar da ita cikin ɗaki, kana na fito ina fitowa muka haɗu da Zinariya. Muka sakarwa juna murmushi kafin na ce"ranki shi daɗe kin tashi ke nan? Sai yanzu na ki safiyar ta yi ke nan?". Ta yi miƙa kafin ta ce"wallahi ke dai bari daren jiya ban samu na yi bacci da wuri ba ne, na tsaya yin waya ban yi aune ba har sai da lokaci ya ja kin gan ni nan sai yanzu na sama daman tashi da ƙyar".
"To Allah dai ya sa kin yi salla?".
Ta taɓe baki"so nake yi yanzu idan na yi wanka, inna ci abinci sai na samu na yi sallan. Don ina jin sallan daren jiya ma ban yi ta ba na ɓige da yin waya".
"Sallan kike haɗa wa a kanki haka?".
"To ya ya zan yi Amatullah ayyuka su yi min yawa, dole wani abun sai ana ajiye shi a gefe idan aka sama sarari sai a ɗago shi".
Shuru na yi don mamaki da al'ajabi ya hana ni furta ko da kalma guda, sai da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na sama lasisin faɗin"ya dai kamata kam ki samu ki yi sallan, ni na fita wajen aiki".
"In kin dawo za mu yi magana". Ta murmusa"akwai zancen bakinki na ga alama sai na dawo ɗin dai kawai sai mu tattaunawa". Dariya ta fashe da shi har ta tafa hannu, ban tsaya jiran abin da za ta faɗa ba na fice don ko ban tambaya ba na san cewa na makara.
Gudu-gudu sauri-sauri nake tafiyar ƙafafuna har suna sarƙewa tsabar sautin da nake zuba wa tamkar za tashi sama, kamar daga sama na ji an danna mini horn lamarin da ya yi matuƙar gigita ni. Na ɗaura hannuna aka tare da runtse idanuna ina jiran na ji ta inda motar za ta doke ni da yadda Allah zai yi da ni.
Ji na yi motar ba ta dake ni ba hakan ya ba ni ƙwarin gwiwan buɗe idanuna don ganin abin da yake wakana, take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da yake tsaye a gabana ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon suit ɗin da yake jikinsa, idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin janye nawa gefe guda.
"Amatullah ko?".
Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar da yake kamar an yi masa dole ko kuma mai ciwon baki.
"Da kin daina wahalar da kanki ki na yin sammakon zuwa wajen aikin da ba zai amfane ki da komai ba, da zan ba ki shawara ki ɗaura da na ce da ke tun wuri da kin ɗauke ƙafarki daga cikin wannan gidan".
Na cira kaina ina kallonsa sai dai kwarjininsa da cika ido ya hana ni ba ni damar yi masa dogon kallo.
"Me ye yake nufi da waɗannan maganganun nakan?".
"Ina nufin ba za ki taɓa samun gurbi a cikin zuciyoyin mutanen da suke rayuwa a cikin wannan gidan nan, ba ki da tarbiyya da nagartar da ya dace ki kasance a kusa da mu kasancewarki mai zaman kanta kuma a cikin gidan magajiya cikin tsakiyar karuwai da ƴan daudu. Da babu abin da suka sanya a gabansu face saɓon Allah da kaucewa koyar wa Annabinsa".
Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sa boda zafin kalamansa da na ji, kaina na ƙasa da hakan ya ba wa hawayen damar kwaranya na kuma gaza samun ikon tsayar da su.
"Amma ka san cewar ko wani bawa da irin na shi salon ƙaddarar da Ubangiji yake ƙaddara masa ko....?". Tun kafin na gama zancen ya ɗaga mini hannu alamar ba ya ƙaunar sauraron raguwar zantukan nawan.
"Allah ba ya taɓa ɗaura wa Bawa abin da ba zai iya ba. Kuma duk wani abin alkhairin da kika ga ya sama Bawa to daga Allah ne akasin hakan kuma daga mu ƴan adam ne".
Jinjina kaina na yi ina haɗiya kukan da yake ƙoƙarin kufce mini, na kai hannu na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana kana na furta"duk kalamanka babu kuskure a cikinsu, amma ka roƙi Allah kar ya jarabce ka da abin da ba za ka iya ba kuma ba ka taɓa tsammanin tsintar kanka a cikin irin rayuwar ba". Ina dasa aya a nan na juya na bar shi tsaye a wajen, na karya kwanar da za ta sada ni da gidan. Baba Mai gadi na iske zaune a bakin gare ɗin na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini cike da kulawa, ban bari mun yi wani dogon zance da shi ba na tashi na shiga cikin gidan.
Babu kowa a falon don hakan kaina tsaye na wuce ɗakin Altine na shiga cikin banɗaki na kulle kaina na jingina jikin ƙofar banɗakin yayin da wasu hawaye masu ɗumi suke gudun famfalaƙi a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa saman haɓata.
Tabbas juyi-juyi ce in ji kwaɗo ya ce wash! Da ya tsinci kansa tsumgum a cikin ruwan zafi. Haƙiƙa ta kan zo a ko wacce irin siga ba tare da ta yi raunin mutumin da za ta faɗa kansa ba. A zamanin baya idan wani ya kalle ni ya ce wannan yarinyar za ta iya sanya ƙafa ta bar cikin gidan mahaifinta ta shiga duniya ta yi zaman kanta, ilahirin mutanen da suka sanni kuma su ka san wace ce ni, sai sun yi haɗaka sun yi taron dangi sun ƙaryata abin da ya furta cikin babbar murya. Sai ga shi ƙaddara ta jefo ni cikin duniyar da babu kulawar uwa balle uba, babu mai tsawartawa balle ƙwaba, babu mai hana ki balle ya saka ki duk abin da kika ga damar aikatawa shi za ki yi babu mai tambayarki dalili balle har ki sama tagomashin shawara. Babu tswatarwa iyaye balle dangi babu mai tanƙwara ka balle ya tursasa ka ka yi abin da ba kya yi niyya ba.
Ko a cikin mungayen mafarkan da na yi sheiɗan bai taɓa kimtsa mini cewar wata rana zan yi zaman kaina ba, balle har na kwana na tashi a cikin gidan karuwa. Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina ina sulale ƙasa na yi zaman dirsham ina wani irin kuka mai rauna zuciyar mai saurare.
Haƙiƙa sai yanzu na ƙara yarda cewar babu abin da ya kai mutuwa tonon silili da ban kaɗo rufaffun sirrukanta ta sanya a faifayi ta raba a duniya. Ina da yaƙinin da Abbana yana raye a cikin wannan duniyar da ban tsinci kaina a cikin wannan rayuwar ba, ko da kuwa ƙaddara ta jawo ni to tabbas ba zan yi nisan zango a cikinsa ba. Tun ina kukan hawaye suna zuba har sai na na koma yin kukan zuci sa boda hawayen sun tsaya sun kafe tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe na tsawon shekaru masu nisan zango.
Jin da na ji ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin shi ya fargar da ni na dawo cikin hayyacina daga na tunanin da na yi nitso a cikinsa. Da ƙyar na iya miƙewa akan ƙafafuna sa boda ciwon kan da lokaci guda ya rufe har ya sauƙar da mini da zazzaɓi mai zafi a cikin jikina. Sai da na wanke fuskana kafin na buɗe ƙofar muka haɗa ido da Altine na yi saurin kasar da nawa idon daga gare ta ina ƙoƙarin fitowa daga cikin banɗakin na ce"ina kwananmu mun tashi lafiya?".
Ban damu da sai ta amsa mini ba na sa kai zan yi wuce ta ta jawo ni na koma da baya.
"Me ye kika aikatawa a cikin banɗakin da kika shiga kika ƙulle ƙofa?".
"Har abun da na aikata a cikin banɗakin ma zai na sanar da ke ranki ya daɗe?". Ban tsaya na ji amsar da za ta ba ni ba na yi ficewa ta daga cikin ɗakin na bar ta tsaye a wajen tana cizon ƴatsa.
Na iske Hajiya Muhibbat zaune a cikin falon tare da Saif da alama wata muhimmiyar tattaunawa suke yi ganin yadda gabaɗayan su suka tattara hankulansu waje guda.
"Anty lokaci ya yi fa za mu gaya wa Yaya gaskiya abin da yake yi sam bai dace ba. Ta ya ya mutum mai iyali sai tafi can wata uwa duniya ya tare shi kaɗai har ya shafe tsawon wani lokaci mai tsayi ba tare da ys waiwayi amanar da yake kansa ba balle har ya yi ƙoƙarin sauƙe nauyin da Ubangiji ya ɗaura masa ba. Anty idan ma har yanzu wannan abun da ya faru ne a cikin ransa ai ina tunanin za ki ci albarkacin waɗannan ƴaƴan da kika haifa masa ya sauƙo. Ya rumgumi ƙaddara kamar yadda ke ma kika manta da duk abin da ya afku kika amshi a matsayin miji a gare ki kuma uba ga tagwayen ƴaƴanki".
Cike da gajiya da sauraronsa Hajiya ta ɗaga masa hannu muryarta tana rawa ta ce"Saifullah ya isa haka ba na son ana tuna min da abin da ya riga ya wuce hakan ya kan jefa ni cikin wani irin hali. Ina yi wa Saddam uzuri akan komai da yake aikata ba wai don ba na jin zafin abin da yake aikata wa sai don kawai ɗaurewar zaman lafiya a tsakaninmu da shi tun da ka fi kowa sanin halaye da ɗab'iun ɗan uwanka. Babu abin da Saddam zai aikata a gare ni da hakan zai sauya matsayin da yake da shi a cikin zuciyata".
"Anty wai har sai yaushe ne za ki daina yi wa Yaya Saddam uzuri akan rashin adalcin da yake yi a gare ki? Na yarda ki na son mijinki amma don Allah na roƙe ki kar ki ba fi wannan soyayyar ta rufe miki ido, ta ki kasa faɗa masa gaskiya idan ya aikata ba daidai ba. Shi fa zaman aure na mutum biyu ba na mutum ɗaya ba dole sai kowa ya ba da na shi gudumawar kafin abubuwa su tafi yadda ya kamata. Anty ba ni da kowa a duniyar nan da ya rage min face Yaya Saddam shi ne komai na wa, shin ki na tunanin ba na jin zafin abin da yake aikata wa ne? Waɗannan fa ƴaƴansa ne ke kuma matarsa ce wacce ta sadaukar da komai sa bosa shi, ki zaɓi shi sama da kowa. Ki zaɓi ki yi rayuwa da shi har izuwa lokacin da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinki".
"Ya isa haka Saif na ce ya isa haka".
Hajiya ta yi zancen cikin ɗaga sauti tana sa hannayenta ta toshe kunnuwanta da su.
"Ka tashi ka fita ka ba ni waje ko kuma ka yi wata maganar amma ba wannan ba. Don ba zan iya juran hakan ba".
Miƙewa tsaye ya yi jikinsa gabaɗaya ya mutu murus kamar wanda aka zare wa laka. A hankali yake motsa leɓansa yana faɗin"shi kenan Anty ba zan ƙara yi miki wannan maganar ba. Daman na shigo na sanar da ke cewar ɗazu na kai Muhammad Sultan filin jirgi, mun zo tare zai yi miki sallama kuma na ga ba ku buɗe ƙofa na ƙira wayarki ba ki ɗaga ba, ya ce a yi miki godiyar irin ɗawainiyyar da kuka yi da shi a tsawon kwanakin da ya yi a cikin wannan gidan". Yana dasa aya a zancen ya juya ya fice daga cikin falon, da hakan ya sanya Hajiya dafe kanta cike da damuwar da ya gauraye da tsananin tashin hankali.
Saɗal-saɗal na ja ƙafafuna na bar cikin falon na wuce cikin kicin na tarar da babu wani alamar an ɗaura girki, na nema waje na tsaya na rumgume hannayena a ƙirjina kafin na soma safa da marwa a cikin kicin ɗin.
"Saddam".
Na maimaita sunan a bayyane ina sauƙe wani gwauron ajiyar zuciya mai nauyin kilo ɗari da ɗoriya da ƴan kai. In dai ta tabbata cewar wanda na ga a fuskar wayar Zinariya shi ne Saddam mijin Hajiya Muhibbat ya yi wa Zinariya alƙawarin durowa cikin ƙasar nan a yammacin ranar juma'a.
"Kai kawon me ye kike yi? Ba ki fara haramar ɗauka abin kari ba?".
Na tsinkayo muryar Altine ya sauƙa a cikin ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu. A ɗaga kai ina dubanta cike da son ƙarin bayyani, fahimtar abin da nake nufi ya sanya ta faɗin"ƙwarai ai kin ji abin da na faɗa, da can waye kike ajiye da kike tunanin zai ɗaura miki girkin ki zo ki ɗiba ki je ki baje akan katifa?".
Ban ce da ita komai ba na wuce na soma kici-kicin ɗaura girkin, ɗan wake na yi mai rai da motsi. Na yanda kabeji, tumatur da kokanba na soya mai ya soyu rafai. Na haɗa komai na jere su akan dinning table kana na zo na durƙusa a gaban Hajiya.
"Hajiya ga abin karin kumallo a gama".
"Amatullah ba na jin zan iya cin komai, ba na jin sha'awar cin dankalin nan a dai kawo min ruwan shayin na sha kawai".
"Ba dankali ba ne ranki ya daɗe, ɗan wanke ne".
"Ɗan wake?". Ta maimaita na gyaɗa mata kaina alamar e.
"Ai kuwa na kwana biyu ban ci ɗan wake ba. Tun wani lokacin da muka je gidan Hajiyata ta sa aka yi mana rabona da cin ɗan wake. Kawo min nan mu ci tare da su Ayan sai ki kai wa Saif na shi don na san yanayin da ya bar nan ba lalle ya shigo yanzu ba".
"To".
Na amsa da shi a taƙaice tare da tashi na je na kawo mata komai gabanta, na haɗa na Saif kamar yadda ya faɗa na fita zan kai masa, ina ta jeranta sallama a ƙofar falon amma ba a amsa ba kamar yadda ba a fito an buɗe ƙofar ba. Sai can aka zo aka buɗe ƙofar na tura ƙofar na shiga cikin bakina ɗauke da guntun sallama.
Yana kwance akan doguwar kujerar zaman mutum uku ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman ƙirjinsa yayin da hannu ɗayan ya dafe goshinsa da shi, idanunsa suna lumshe amma na tabbatar da cewar ba bacci yake yi ba. Na ajiye tray ɗin abincin akan teburin da yake gabansa na juya zan fita.
[12/6, 1:28 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 6️⃣3️⃣
Har na kai ƙofar ficewa daga cikin falon na tsinkayo muryarsa a dake yana faɗin"dawo ki ɗauke abin da ya kika ajiye".
"Me yasa?". Ya yi banza da ni ba tare da ya ce da ni ci kanki ba, shurun sa bai hana ni ƙarisa zancen da na ɗauko ba"Hajiya ce ta ce a kawo maka idan ba za ka ci ba ita ya kamata ka ƙira ka sanar da ita, faɗa nata ne ni kuma ci kawa nawa".
Ina dasa aya anan na juya na fita daga cikin falon a hankali nake taka ƙasa ina ɗaga ƙafafuna da ƙyar na koma cikin sashin Hajiya suna zaune tare da su Ayan suna cin abinci sai dai ita juya cokalin kawai take yi ban ga ta kai ko da loma guda cikin bakinta ba.
Na rusuna na yi mata sannu ta amsa mini tare da cewa"ki dafa min shayi ba na jin daɗin jikina ba zan iya cin komai ba".
"To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice cikin bin umarni da girmamawa. Na wuce cikin kicin ɗin na dafa mata shayin da ta buƙata babu ɓata lokaci na kammala na kawo mata. Tana zaune akan kujera ta jingina bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanunta ta dafe goshinta da hannayenta da hakan ya taimaka wajen fito da damuwar da take cikinsa ƙarara.
"Hajiya lafiya kuwa kike?".
Sai a lokacin ta buɗe lumshashshun idanunta na kuma fahimci lumshe su da ta yi ashe kuka take yi.
"Subhanallahi! Kuka ku ma Hajiya me ya yi zafi haka?".
Ta kawar da guntun hawayen da suke idanunta ta kai hannu ta amshi kofin shayin da nake miƙa mata, ta kai bakina ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye a gefenta.
Cikina a sanyaye na furta"ban san me yake dsmunki a cikin zuciyarki don sanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciya haƙiƙa wannan sai mahaliccinta, amma don Allah ku yi ƙoƙarin ki cire komai daga cikin ranki in sha Allah watarana komai zai wuce har ma ya zama labari".
Sai da ta