Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
ya ja su limanci suka gabatar da sallan raka'a biyu na
nafila suka miƙa ƙoƙon baran su zuwa ga sarkin da ba shi da abokin tarayya, Sarkin da ba ya ce a roƙo zai amsa.
Ba su bar cikin ɗakin ba har sai da bacci ya ɗauke ta suka kunna karatun alƙur'ani a waya suka ajiye a cikin ɗakin. Yaya Alhassan ya tisa ta a gaba yana kallon ta tamkar bai taɓa ganin ta ba. Umar ya dafo kafaɗarsa cike da kulawa yake faɗin"Yaya Alhassan ka kwantar da hankalinka komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba. Watarana sai dai labari".
"Umar idan na ce ba na cikin damuwa haƙiƙa ma yi ƙarya mai girma, tun ranar da Amatullah ta ɓace ban ƙara samun kwanciyar hankali ba, ban ƙasa kasancewa cikin daidaitacciyar nutsuwa ba. Kullum a cikin fargana nake da fatan Allah ya sa tana cikin hannu mai aminci".
"In Sha Allah za ta dawo gare mu cikin aminci. Ina ji a jikina Amatullah ba za ta taɓa sauƙa daga kan turban da muka san sa ta ba".
"Allah ya amsa".
"Amin ya Allah yaya Alhassan".
Kashe wutar ɗakin suka yi suka koma nasu ɗakin cikin jimami da tarin damuwar da yake danƙare a cikin zuciyoyinsu.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 5️⃣7️⃣
Haka kawai na wayi gari ina ji na cikin wani irin karsashi a jikina, wanda na danganta hakan da karatun alƙur'anin da na yi ta yi bayan na yi sallan asubahi. Na tisa haddan da yake kaina sosai har sai da na ji wani nutsuwa ya lulluɓe mini rai da ruhina. Sai da na ɗebo ruwa na yi wanka na mayar da kayan da yake jikina na duba ko'ina na rasa abin da zan tauna a cikin ɗakin, na gama cinye duk siyayyar da Hajiya Muhibbat ta yi mini kat. Numfashi na ja na fesar kafin na yi shirin tafiya wajen aikin zan fita na ji sautin da ya tirsasa mini tsayawa.
"Madam fita za ki yi ne?".
Na waigo na yi mata kallo guda tana kwance akan katifarta da ban ma san sa'ilin da ta dawo ba daren jiya sai wayen gari na yi na gan ta cikin ɗakin.
"E ko na tsaya za ki aike ni ne?".
"To ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Abin ai bai kai haka ba, dama na ga muna zaune a ɗaki ɗaya ne akwai haƙƙin maƙwabta a kanmu ai ko?". Na bi ta da wani kallo don har yanzu ban manta zafafan kalaman da ta yaɓa mini ba ranar farko da ta zo cikin ɗakin.
"Tambaya kike yi ko neman sani?".
"Duk wanda kika ɗauka daga cikin biyun daidai ne". Ban amsa mata ba na ja tsaki na fice daga cikin ɗakin ina jin haushin abin da ta yi mini har yanzu a cikin raina. Ina fitowa na yi kiciɓus da zinariya tana ƙoƙarin shiga ɗakin na ƙirƙiri murmushin dole na aza a bisa fuskana.
"Barka da safiya ranki ya daɗe".
"Ai ke ce ranki ya daɗe, dama na zo na ƙara duba jikin nakin ne. Ban saman shigowa ba".
"Ai na je na iske ki na waya sai kuma daga nan ban dawo ba. Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi....". Kafin na rufe bakina na ji ta rumgume ni tsam a jikinta kafin na yi aune na ji hannayenta a gadon bayana tana shafa wa har zuwa ƙunguna. Jikina na mutu murus na kasa cewa da ita komai kamar yadda na gaza hana ta yawo da hannunta da take yi a cikin jikina.
"Bari na bar ki haka tun da na ga kamar fita za ki yi ko?".
Zallar ruwan mamakin da ta shayar da ni ya hana ni amsa mata cikin kalmomin da bakin kan iya furta wa illa gyaɗa mata kaina da na yi.
"To sai kin dawo idan kin dawo sai ki shigo mu yi hira". Na kuma gyaɗa mata kaina a karo na biyu ta sakar mini wani shu'umin murmushin yayin da take ɗaukar hanyar koma wa cikin ɗakinta. Na fita da kallo ƙirjina yana buga wa tamkar zai faso allon ƙirjina ya bayyano waje ya taka rawar disko, na daɗe tsaye a wajen kafin na ja sanƙararrun ƙafafuna da nake jin su tamkar ba za jikin gangar jikina na fice daga cikin gidan.
Ina tafiya ina tunani har na isa ƙofar gidan ina jin wani masifaffen yunwa hancin cikina sai kuka suke yi da neman agaji, na ƙwanƙwasa gate ɗin Baba mai gadi ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar auguda.
"Kin iso ko?". Na gyaɗa masa kaina alamar e.
"To madalla Allah ya taimaka ya yi jagora".
"Amin ya Allah". Na amsa da shi yayin da nake shiga cikin gidan ina shiga na hango motoci guda uku a cikin parking space, ɗayan Kam ko a ina na ganta zan gane ta don motar Hajiya Muhibbat ce. Ɗayan kuma motar Saif ne ɗayar ce baƙuwa amma tabbas a gare ni ba baƙuwa ba ce don ba yau ne rana ta farko da na fara ganinta ba. Ƙirjina ya harba da ƙarfin Rabbussamawati da hakan ya tilasta mini runtse idanuna Ina karanton a'uziya a cikin raina.
"Ƴarta lafiya kuma na ga kin tsaya a nan, ba ki shiga cikin gidan ba?".
"Baba wannan motar baƙo aka yi a cikin gidan nan?".
Ya washe bakinsa kafin ya amsa mini cikin faɗin"wannan motar baƙon Saifullahi ne, da ya zo da yammacin jiya. Yaron kirki ne matuƙa ga girmama manya gami da tsantsan tarbiyya daɗin daɗawa kuma ga nutsuwa da kawaici".
"Tabbas ya cika mutumin kirki tun da har ya sama yabo daga bakin uba na gari kamar ka".
Ya washe bakinsa tamkar wanda aka yi wa wani babban kyauta"duk inda ake neman yaron kirki wannan baƙon ya zarce duk tunanin mai tunani. Ni ɗin nan idan ya zo cikin gidan na irin girman da yake ba ni na daman ne, in ya shigo ya ganni ina wani aikin kuwa sai ya karɓa ya yi min babu ruwansa da matsayinsa, matakin karatunsa ko kuma azurkinsa".
Na riƙe haɓata"dole na zo a ba ni labarin wannan baƙo".
"Ai kuwa za ki sha labari, don duk suna makaranta a nan gidan yake hutunsa har sai sun koma".
"In sha Allah zan zo na sha labari". Daga haka na bar wajen na ƙarisa shiga cikin gidan, na tsaya a ƙofar falo ina ta zabga sallama har baki uku ba a amsa ba sai a na huɗun Ayan ya buɗe ƙofar ya fito, na fafaɗaɗa fara'ar fuskarta kafin na ce da shi"ina kwana".
Ya tsaya ya yi sakeke yana kallona kafin can ya ce"ki shigo Ummin tana ciki". Murmushi na sakar masa na riƙo hannunsa muka shiga cikin falon.
Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Hajiya Muhibbat da na iske zaune a falon tana danna wayarta, yayin da Aryan take zaune a kusa da ita yana wasa da motar da yake hannunsa.
"Lafiya ƙalau kin tashi lafiya?".
"Lafiya alhamdulillah ranki ya daɗe".
"Lafiya jiya kika tafi babu sanarwa sai aikowa na yi a ƙira ki aka ce ba kya nan?".
"Hajiya ba na jin daɗi ne shi yasa na tafi, amma tuba nake yi".
"Ba damuwa Allah ya ƙara sauƙi. Ki shiga kicin ku ci gaba da aikin don yau mu na da baƙo na musamman a cikin gidan nan". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na yi hanyar kicin ɗin na tarar da Altine a tsaya ta juya wa ƙofa baya tana waya. Na yi gyaran murya da hakan ya ankarar da ita wanzuwa ta a cikin kicin ɗin, a firgice ta waigo tana datse ƙiran.
"Ke kuma me ye kike yi a nan? Yaushe kika shigo?".
Ruɗewan da ta yi lokaci guda shi ya fi komai ba ni mamaki, sai na ƙariso cikin kicin ɗin kafin na ce"yanzu na shigo na tarar ki na waya. Ina kwana mun tashi lafiya?".
"Lafiya". Ta amsa mini a daƙile tamkar wacce aka yi wa dole, ba ta ƙara bi ta kaina ba ta ci gaba da abin da take yi. Dankalin turawa take soya wa da ƙwai gefe guda kuma tana haɗa dafa shayi da ya sha kayan yaji dangin su citta da kananfari ƙamshi ya buɗe ko'ina.
Ina ta tsaye ba ta ce da ni ga abun da zan yi ba har sai da na ji ƙafafuna sun gaji sun yi sanyi ƙalau. Sai da na tabbatar da cewa ba ta tanka mini na half ƙafafuna na isa wajen da ake ajiye kayan abinci na ɗebo fulawa zan tankaɗe ta dakatar da ni"me ye haka kike ƙokarin aikata wa?". Ba tare da na kalle ta ba na amsa da faɗin"wainar fulawa zan soya".
"Wainar fulawa kuma?". Ta maimaita cikin isa da taƙama kafin ta zarce da cewa"wani irin wainar fulawa kuma? Bayan ga abincin karin kumallo nan ina girka wa ko ba kya gani ne?". Ban ce da ita uffan ba hakan bai hana ta ci gaba da maganar ba tamkar mai amayar da wuta.
"Babu wani wainar fulawan da za a yi a cikin gidan nan tun da ga abinci nan na girka. Duk wanda ba zai ci ba sai ya wuni da yunwa ai yunwa ba uwar kowa ba ce kuma ba a fushi da abinci ko ka yi ma kai ne a wahala".
"Ai na ji Hajiya ta ce akwai babban baƙo a cikin gidan kuma ta ba da lasisin a girka duk abin da ya kamata don a faranta masa. Laifi ne don na girka wannan?". Na ƙare zancen da alamar tambaya, lamarin da ya fusata ta ainun ta yi watsi wani kallo tamkar za ta kai mini bugu tana gallo mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa.
"Sai kuma aka ce da ke baƙo irin baƙin da kika saba ji da gani ne ko? To wannan baƙon babban mutum ne da ya fito daga gidan manya, ina mai tabbatar miki da cewar ko kallon wainar fulawan nan ba zai yi ba balle ya sa shi akan harshensa".
"Sanin daga gidan da ya fito ne ya sa zan yi masa wainar fulawa, don ina da yaƙinin wannan dankali da shayin da kika yi abubuwa ne da kullum yake gani kuma yake cinsu. Amma ina da yaƙinin wannan wainar fulawan zai zama sabon abu a wajensa". Kafin na gama kammala zancen kawai na ga ta ɗaga hannu za ta zabga mini mari na yi hanzarin riƙe hannunta tare da jefa idanuna a cikin na ta.
"Kar ki kuskura ki yi gangancin ɗaura hannunki a jikna da sunan mari. Don abin da zai bi yo bayan hakan daga ni har ke ba zai mana daɗi ba". Kafin ta ce wani abu Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin ta iske mu a haka.
"Me yake faruwa na gan ku kun tsaya cirko-cirko?".
"Babu komai Hajiya, da inna fere dankalin nan ne na kuskure hannuna shi ne take so ta ɗauke min wajen".
Altine ta kora mata bayanin da ta ƙirƙire shi a take a wajen, ban ce da ita komai hasalima ko hannun ta ban yi ba.
"To Allah ya kiyaye gaba. Wannan fulawar fa?".
Na yi caraf na amshe zancen kamar ji nake yi ta ce kule na ce cas.
"Hajiya wainar fulawa ne zan soya wa baƙo?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"watau a baƙo kawai ban da mu ƴan gidan ko Amatu?". Na murmusa kafin na ce" har da kowa da kowa ma ranki ya daɗe. Amma Anty Altine ta riƙa da ta shirya abin karin kumallo shi yasa na taƙaita wainar fulawan ga baƙon kawai".
"Ai kuwa ni ma dai ina ga wainar fulawan nan zan ci, don dankalin nan gabaɗaya ya gama fita daga kaina zan dai sha shayin. Amma fa sai ki hanzarta don sun kusa fitowa kuma fita za su yi".
Cike da jin daɗin kalamanta na ce"in sha Allah Hajiya ba zan ɓa ta lokaci ba". Murmushi kawai ta sakar mini ta juya ta bar cikin kicin ɗin, ko ido ban ɗaga na ga Altine ba balle na tanka mata sai dai ina jiyo sautin ƙwafan da ta dunga sake wa wani na bin bayan wani na tsawon mintuna.
Har na yi ƙare suyar wainar fulawan ba ta ce da ni da komai ba. Na ɗauko hula na zuba a ciki, can na hango cabbage na ɗauko na yanka na wanke na zuba a gefen a wani plate na rufe shi. Na waiga na kalle ta.
"Ranki ya daɗe na gama sai kuma me ye ya rage?".
Ban yi mamaki ko na haɗu ba da na ga ta gallo mini wata uwar harara kafin ta ce"a tambayi kaza hanyar zuwa tafi?".
"Tabbas kam ba za a tambaye ta tun da ba zuwa take yi ba"
Daga haka ban ƙara ce mata komai na ɗauko tray na jere su a kai na fita ina jin tsakin da take dokawa yayin da nake ƙoƙarin ficewa daga cikin kicin ɗin.
Ban iske kowa a falon ba sai ƙarar iskan AC da yake aiki a cikin falon na jere su akan dinning table, Ina tsaye a wajen Aryan da Ayan sun rugo a guje suka shigo cikin falon suka nufo inda nake tsaye.
"Wai in ji Uncle Saif an gama abinci? Za su fita da abokinsa".
Kafin na yi magana Hajiya ta sauƙo ta karɓe zancen"babu inda za a kai musu abinci idan ba za su zo nan su ci ba, sai dai su haƙura". Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta ƙira shi ina jin ta abin da take faɗi cikin tsare gida babu alamar wasa a tattare da ita.
"Ku shigo an kammala abincin". Tana gama faɗin haka ta katse wayar ta ƙariso ta zauna, ban bar cikin falon ba ya shigo take na ji ƙirjina ya buga da ƙarfi ta gabana ya zo ya wuce na gaishe shi ya yi banza da ni wanda kuma ina da tabbacin ya ji gaisuwar da na yi masa sarai.
"Hajiya Antynmu tun ɗazu fa abincin nan muke jira, idan ba za a ba mu ba ne sai a gaya mana mu san inda dare ya yi mana". Ya ƙare zancen cikin sigar zolaya yana ɗan sosa ƙeyarsa.
"Ina shi baƙon nakan?"
"Yana can sashina".
"To sai ku fito ku zo mu ci abincin".
"Hajiya Anty kin san Taufik fa da kunya ba zai taɓa iya nan gabanki ya sha ko da ruwa ne ba balle har ya saki jiki ya ci abinci".
Ta harare shi"mace ne ƙarshen kunya kenan ai ko?". Ya marairaice murya"mu dai yanzu Anty ki yi haƙuri a ba mu abincin. Kin san fa an ce koro da yunwa ba shi da kyau kuma ba shi da daɗi". Dariya ta tuntsire da shi kafin ta waigo tana kallona da har yanzu ina tsaya a inda nake ban motsa ba.
"Amatullahi ɗauki girkin kika jera ki kai musu. Ayan zai biyo ki da flask din tea ɗin".
"To ranki ya daɗe".
Na amsa da shi a taƙaice na ƙara jere su akan tray ɗin na fita na nufi sashinsa, ina jin ƙirjina yana tsananta bugu da ƙarfi da ƙarfi. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sanya ƙafata a cikin falon na yi hamdala sa boda iske falon da na yi
babu kowa a cikinsa sai sautin karatun Alqur'anin da aka kunna yana tashi.
Na ajiye tray ɗin akan table na juya da sauri xan fita na ji an tsayar da ni ta hanyar faɗin"baiwar Allah tsaya mana". Take jikina ya soma rawa mussamman da na ji sautin takunsa yana ƙara nufo inda nake tsaye, ban yi ƙasa a gwiwa ba na yi saurin ci gaba da tafiya sai dai ban yi taku huɗu masu kyau ba.
Aka buɗo ƙofar falon Saif da su Ayan suka shigo yana riƙe da flask ɗin tea, Ayan yana riƙe da sacet ɗin madara da milo yayin da Aryan ya riƙo kofuna. Sanƙarewa na yi a inda nake tsaye, tabbas wannan shi ne gaba kura baya ƙura, na rasa inda zan yi gaba ko gaba.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 5️⃣8️⃣
Ina ɗago kai idanuna suka sauƙa a cikin na Saif kallon da ya watsa mini ya sanya jikina yin la'asar tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi na rusunar da idanuna ƙasa yayin da Aryan da Ayan suka ƙarisa shigowa cikin falon suka je suka ajiye abin da yake hannunsa akan teburin.
"Za ki iya tafiya tun da kin gama abin da ya kawo ki ko". Ya yi zancen cikin tsare gida fuskarsa babu alamar wasa balle ya ɗauki wargi.
"To ranka ya daɗe". Na yi zancen ina ɗaukar hanyar fita daga cikin falon cikin matuƙar sauti tamkar zan tashi sama, har na kai ƙofar fita na ji an dakatar da ni.
"Wace ce wannan ɗin Saif? Ban san ta ba tun da nake zuwa cikin gidan nan".
"Baƙuwa ce".
Ya ba shi amsa a taƙaice da hakan ya ba n damar ficewa da sauri ban sarara ba har sai da na zo ƙofan falon sashin Hajiya Muhibbat na tsaya ina mayar da numfashi tare da daidaita nutsuwata kana na shiga ciki, tana zaune tana shan shayi na iske ta jifa-jifa tana latsa wayarta, na yi mata sannu kana na wuce ɗakin Altine bakina ɗauke da sallamar da ban sama amsa daga gare ta ba illa kallon banzan da ta bi ni da shi har na isa na zauna a bakin katifar.
"Ga can abinci a kula ki ɗauka". Kaina kawai na gyaɗa mata na jawo hular da ta yi mini nuni da shi. Ina buɗe wa na ci karo da farar shinkafa da ta gama shan iska ta bushe ƙararau ga wani ɗan yajin da aka yafa a gefen tamkar wanda aka roƙo daga maƙota.
"Abincin waye wannan ɗin? Ko a karnuka za a ba wa?".
"Tun da kike zuwa gidan nan kin taɓa ganin kare ne?".
"To na sani abu a duhu. Don wannan abincin kam ai ɗan Adam dai mai rai da numfashi ba zai iya cin sa ya kwana lafiya ba sai dai