DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   13 / 39

36K to 39K   out of 116.4K words

jigum da ita kamar majinyaciya.

"Ba ki tambaye ni gidan aikina ba?".

Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin sa a cikin kunnuwana kafin ta furta"ina kuwa zan iya tambayanki bayan kin gama shayar da ni giyan mamaki. Ba ni labari me ya faru don na ga kin ma dawo da wuri ai". Na fesar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na juye mata duk abin da ya faru.
"To yanzu wani shawara kika yanke barin aikin ke nan za ki yi, ko kuma ya ya za ki yi?".

"Da farko na yi tunanin na haƙura da aikin amma tun daga lokacin da Baba Mai gari ya sanar da ni wace ce Altine, da kuma salon nau'in munafurcinta sai na ji na ƙara son aikin a cikin raina, zan shiga cikin Hajiya sosai har sai na fahimtar da ita wace ce Altine na kuma fito da ainihin halinta kowa ya gani. To daga wannan ranar zan bar aikin".

"Tabbas kin yi tunani mai kyau".

Kafin na ba ta amsa wata budurwa ta shigo cikin ɗakin ta jefo miji baƙin ledar dake hannunta.
"Ga shi in ji Hajiya kayan sakawa ne ta ce ki saka su. Don baƙonki yana hanya". Na tsaki wani murmushin da ba shi da haɗi da nishaɗi kafin na ce"to ina godiya saƙo ya iso. Tabbas Hajiya tana ƙoƙarin sangarta ni a cikin gidan nan, har kaya take saya mini". Na ƙare zancen ina bin budurwar da kallo da take ta cika ta na batsewa da tun a tashin farko na fahimci a cikin biyu dole akwai ɗaya. Ko dai baƙon da zai zo musamman domin ni take baƙin ciki da zuwansa ko kuma kayan da Hajiya ta ba ni ne ya baƙanta mata rai.
Tsaki ta tsirtar mai dogon zango tare da faɗin"har ina abin yake wai maye ya ci jajiri? Ke kar kin sa ki shiga sahun matan da Hajiya take ji da su a cikin gidan nan? Ko da yake ai an ce na kwance bai ga gari ba". Ta na gama zancen ta juya ta fice na taka ta da dariya da ina da tabbacin hakan ya ƙara ƙular da ita matuƙa. Na ɗaga muryata na ce"a sauƙa lafiya".

"Ke Amatullah wai ke ce kuwa?". Furucin La'aniyatu ya sa ni waigo wa ina kallonta.
"Me ye kika gani?"
"Na ga kin tsiri wasu ɗabi'un da ba na ki ba kin lafawa kanki".

"Yanayi ne yake sauya wasu abubuwan La'aniyatu. Wani lokacin mutum ya kan sauya na tare da shi kansa ya fahimci hakan ba". A raunane na yi zancen ina jin ruwan hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata.
"Bari na bar ki ki shirya". Tana zancen tana miƙe wa ta bar cikin ɗakin a ƙalla na ɓata mintuna talatin zaune a wajen ban motsa ba, kafin na zazzage ledar ina kallon kayan ciki. Doguwar riga ce irin da aka watsa mata duwatsu masu ƙyalla da haske sai kuma mayafinta da ba shi da girma wanda bai zarce girman kallabin da yake kaina ba. Sai kuma turare su kenan a cikin ledar na ɗaga rigar ina kallo tare da sauƙe tagwayen ajiyan numfashi.
Na saka rigar na ga ya kama mini jikina sosai har da ƙyar nake numfashi, duk wata surar jikina ta bayyana musamman ƙirjina. Na ɗaura kyallen a kaina na saka hijabina don na ba zan iya fita haka ba, feshi biyu na yi a turaren na ajiye don ya yi ƙarfi da yawa har yana hawa kai.

Ɗakin Hajiya Babba na nufa na shaida mata na shirya ta bi ni da wani irin kallo har na zauna.
"Wannan hijabin fa?".
"Hajiya ba zan iya fita da wannan kayan ba ne, shi yasa na sanya hijabin". Za ta yi magana wayarta ta soma ruri ta ɗaga na ji ta tana ba da umarnin shigowa. Tana ajiye wayar wani mutum ya shigo cikin falon ya sha manyan kaya shadda fara tas mai ɗaukar hankali ya murza hula zanna bukar ga ƙamshin da yake tashi a jikinsa tamkar an yi ɓarin durum ɗin turare a jikinsa. Ya zauna a kujerar da yake kusa da wanda Hajiya take zaune a kansa suka gaisha kafin ya ce"Hajiya Allah ya sa wannan ce wacce aka ajiye min ɗin. Don tun da na shigo na ji ta sama matsuguni a cikin raina".

Ta saki shewa"me kake ci na baka na zuba Alhaji Manga? Ai dai duk saurin ungozama za ta jira a haihu".

"Fara ba ni amsar tambayata tukunnan ita ce ko ba ita ba ce?".

"Ita ce sai aka yi ya ya?".

Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe su yana cewa"ba ki taɓa zaɓo min wacce ta dace kamar wannan ba dole na ninka abin da na saba biya sau biyar. Sai dai kuma yanzu akwai meeting ɗin da za mu yi da abokan sana'ata a cikin daren nan. Don haka gobe zan dawo sai na ɗauke ta hakan ya yi?".

"Ai duk yadda ka ce haka za a yi ranka ya daɗe, ina godiya".

"Da kin gaya min irin wannan surar zan zo na tarar ai da na aika wani ya wakilce ni a wajen meeting ɗin. Amma yanzu ma dai bai ɓaci ba zan dawo ko na aiko a zo a ɗauke ta, yarinya ya ya sunanki?".

Muryata a shaƙe na ce"sunana Amatullah".

"Amatullah Amatullahi baiwar Allah. Ni kuma sunana Alhaji Manga, yanzu za mu je da ke waje ki karɓo saƙo ki kawo wa Hajiya".
Na gyaɗa masa kaina ina satan kallon Hajiya na ga ta ɗage mini gira alamar na bi shi. Suka yi sallama ya fita na bi shi a baya, tun da muka fito daga ɗakin ƴan matan gidan suke ta kai masa gaisuwa yana ɗaga musu hannu. Muka fita waje inda ya ajiye motarsa ya buɗe gidan baya ya ɗauko wasu baƙaƙen ledodi guda biyu ya miƙo mini.
"Wannan ta ki ce ɗayar kuma na Hajiya ne sai ki kai mata. Kafin na zo goben ko ban zo ba ma zan yi aike".

"Mun gode". Na furta a gajarce.
"Ki saki jikinki da yarinya kin ji ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar shiga cikin motar ya ja ya tafi. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina bin ledar da ya ba shi da kallo.

"Har kin sallame shi kenan?".

Na yi figigi na ɗago kaina don gani mamallakin muryar, sai da na firgita don ban yi tsammanin ganinsa a nan kuma a irin wannan lokacin ba.
"Saifullah kuma?". Na furta a cikin zuciyata ina jin ƙirjina yana tsananta bugu ba tare da na san dalili ba
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________________

Page 5️⃣6️⃣

Duk yadda na so na furzar da zallan mamakin da ya ganin sa ya ƙunsa mini bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace, da ɗago idona ina kallonsa na ga ya watsa mini wani mummunan kallo da ban san sa'ilin da na rusunar da idanuna ƙasa ba. Sa boda cika ido da kwarjinin da yake da shi.
"Zan jira ki a wajen motata ba zan iya tsayiwa a nan wajen ba". Yana gama maganar ya bar wajen ya nufi inda ya ajiye motar da yake can farkon layin na bi shi a baya zaƙwai-zaƙwai har muka isa ya jingina bayansa jikin motar tare da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa idanunsa a kaina ya furta"Anty ce ta ce a zo a duba ko lafiya kika tafi ba tare da kin yi mata sallama ba. Sai dai zuwan da na yi da kuma abin da idanuna suka gane min ya tabbatar min da cewar lafiya kike tun da har za iya fitowa ki gana da saurayi cikin wannan daren har da guzurin saƙo niƙi-niƙi a leda".

Jikina ya yi sanyi ƙalau wasu hawaye suka kuma ciko mini idanuna sauran ƙiris su zubo na kai hannu na tare su.
"Lafiya ƙalau kawai ba na jin daɗin jikina ne shi yasa na dawo. Amma ina sha Allah gobe sammako zan yi na zo.....". Tun kafin na kammala ƙarshen zancen ya tari numfashina.
"Ba ma buƙatarki don haka ki yi zamanki. Idan ma ya zama dole to za a nema wata".

"Ba kai ka ɗauke ni aiki ba ranka ya daɗe don haka ba ka da hurumin dakatar da ni, Hajiya ce kawai take da wannan ikon".

Tabbas na hango mamakin zancena kwance a cikin idanunsa ya sauƙe numfashi da har sai da na ji sautin fitarsa.
"Repeat yourself please".
Duk da na fahimci abun da ya furta amma sai na sauya akalar zancen"a gaishe ta kuma a isar mata da saƙona". Ina gama furta haka na juya zan tafi na ji wata murya ta sauƙa a ƙofofin kunnuwana, muryar da ba zan taɓa manta tasirinta a cikin rayuwata ba. Muryar da ko ina gangaran mutuwa in na ji ta haƙiƙa zan gane amonta. Muryar da ta sama matsuguni ta zauna a cikin kwanyata ba tare da biyan tara ko haraji ba. Cak na tsaya jikina yana wani irin rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki haƙwarana suka datse harshena wanda ina da tabbacin har sai da ya fitar da jini.
"Saif wai me ye yake faruwa ne? Ina ne nan wajen kuma?".

"Ba komai Taukif shiga motar mu tafi kawai".

"Wannan yarinyarta fa me ye haɗinka da ita? Na dai san ba ka zuwa ire-iren wajajen nan. Ke zo nan".
Take ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau goma sha tara, zuffa ya soma tsantsafo mini sa'ilin da na ji takun tafiya ana kusanto inda nake tsaye har ƙamshin turaren jikinsa ya riga sa isowa gare ni.

"Ke yarinya me ye kike yi a nan wajen?".

"Ba-ba-ba-ba-ba babu". Na amsa masa a gajarce ina ɗaukar hanyar barin wajen cikin matuƙar sauti kamar zan tashi sama, har ƙafafuna suna haɗewa cikin doguwar rigan da ta gama jikina tsam tamkar tare aka halicce mu.
Kaina tsaye na wuce ɗakina na zubu akan tabarma ko kukan na kasa yi illa kawai soyar da zuciyata take yi mini. Ƙirjina yana yi mini wani irin zafi tamkar ana watsa wa mini garwashin wuta ta yadda nake jin zafin yana ratsa wa har ta cikin nama da jijiyoyin jikina. Kan ka ce kabo gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi har wani kakkarwa nake yi.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!".

Shi kaɗai na yi nasarar furta wa kafin zuciyata ta antaya cikin cakwakiyar tunani. Tabbas ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan muryar Muhammad Taukif ne. Mutumin da ba zan iya mance da ranar da na far tozali da shi akan hanyata ta zuwa islamiyya da kuma kalamansa ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi a cikin rayuwata da zuciyata ta sama
nutsuwa da kalamansa tun kafin na san halayensa da ɗabi'un balle har na kai ga sanin haƙiƙanin wane ne shi.
In dai ta tabbata shi ne baƙon da na ji Saif yana batun zuwansa to ina cikin lukutin yanayi. Na yarce zuffan da ya kwanta a saman goshina kana na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba domin kai mata saƙon da aka bayar da sunanta.

Na zauna a ƙasa ina yi mata sannu da hutawa ta amsa tare da zarce wa da faɗin"to ya ya kika gan shi ina fatan ya yi miki?".
Na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ga wannan ya ce a ba ki". Na miƙa ledodin dukka biyu ta amsa tana faɗaɗa annurin fuskarta bakinta har kunne.
"Dukka wannan nawa? Amma mun yi waya da shi kafin shigowar ki ya ce ɗayan saƙon na ki ne. Don haka ga shi ke ma sai ki je ki fantama ki more wa ranki, don na san waɗanda zai ba ki gobe sai sun ci uban waɗannan".

Na girgiza kaina"Hajiya ba zan ci ko naira ɗaya daga cikin kuɗinsa ba. Don bai kwanta mini a raina ba, Hajiya kamar yadda kuka sa na yi abin da kuke so ni ma ina da nawa sharaɗin da dokoki. Ba zan fara mu'amala da kowa ba sai wani mutum guda".

"Wane ne wannan mutumin?".

Na ɗan yi jim kafin can na ce"Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe".

Ta dafe ƙirjinta tare da waro idanunta waje"Sheikh Dawood dai da na sani mai tafsirin Alkur'ani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e.
Ta kallo ni da wutsiyar idonta tana faɗin"ke yarinyar nan watau bayan taurin kai da kafiyar tsiya tamkar kafiran farko har da hauka ma akwai a cikin kanki. Yo in ba hauka ba ta yaya kike tunanin za a iya jawo hankalin irin wannan mutumin da addini da tsoron Allah ya ratsa jini da jijiyarsa".
"Ba zai yi wahalar shiga hannu ba Hajiya. Ni ko hanya ayi mini na gan shi ni kuma na yi miki alƙawarin sai na jawo hankalinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci"

Ta yi mini wani irin kallo irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce ta ja tsaki ta tofar tana mayar da hankalinta kan abin da take yi ta furta"bari Aminu ya damu mu yi magana tabbas akwai wani abu da yake yawo a cikin wannan kan nakin". Na cira kai na kalle cike da ƙwarin gwiwa na ce"babu komai a cikin kaina Hajiya, ki ba dama ni kuma na yi miki alƙawarin zan jawo shi har ya shigo hannu. Idan na gaza aikata abin da na furta na yarda ki haɗa mini kayana ki ɗaura mini a kaina ki kora ni daga cikin gidan nan sannan ki haɗa mini da ko wani irin wulaƙancin da kika yi niyya".
"Kin san me ye kika faɗa kuwa?".

"Ƙwarai kuwa Hajiya".

Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"shi kenan na ba ki dama amma idan kika kasa jan hankalinsa tabbas zan yaga miki rigar rashin mutumcin a bainar nasi, zan wulaƙanki irin wulaƙancin da ko kare ba zai ci ba. Zan tozarta ki irin tozarcin da za ki ƙwammace ina ma uwarki ba ta haifo ki kin zo cikin duniyar na ba. Zan muzanta ki irin muzancin da za ki zaɓi mutuwarki sau dubu akan rayuwarki. Zan jefa rayuwarki cikin ƙunci da takura da har sai kin daina jin daɗin rayuwar duniya sai kin ji a cikin ranki wanda yake kwance a cikin kabari ma ya fi ki ƴanci da walwala".

Ba tare da wani tunani ko dogon nazari ba na amsa da faɗin"ma yarda da duk wasu sharruɗan da za ki gindaya mini. In sha Allah sai na jawo hankalinsa".
"Kuma babu wanda zai taimaka miki ke kaɗai za ki yi wannan yaƙin. In ma ki ci in ma ki sha ƙasa". Na haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe tamkar ƙasar sahara a lokacin zafi.
"Na yarda da dukkan sharruɗanki Hajiya".

"Tashi ki je na sallame ki"

Ban ce da ita komai ba na tashi na bar cikin ɗakin na koma ɗakinmu, na zauna na buga wani uban tagumi ina jin gabaɗaya duniyar ta yi mini zafi na ja numfashi na furzar ya fi sau shurin masaƙi. Hawayen idanuna sun kafe ƙaf tamkar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe na tsawon shekaru masu yawan gaske, sai yanzu ma yarda tabbas wani tashin hankalin ya wuce a yi masa hawaye sai dai kukan zuci wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi.

A firgice Anty Sawwama ta farka daga baccin da ya cikakken ɓarawo har ya yi nasarar sace ta duk da girman tashin hankali da damuwar da yake cikin ƙalbinta da ta gama raunana. A tare Yaya Alhassan da Umar suka shigo cikin ɗakin, Umar ya kunna wutan lantarki take haske ya gauraye ko'ina.
"Umma lafiya kuwa me ye yake faruwa?". Kasa magana ta yi illa zuffan da ta ci gaba da haɗa wa tamkar wacce aka sheƙa wa ruwa ya yi mata jilif.
"Umar samu ruwa yanzu-yanzu". Da sauri Umar ya fita ya je ya ɗebo ruwan ya dawo ya miƙa wa Yaya Alhassan ya karɓa ya yi tufin wasu addu'o'i a cikin ya ba ta ta sha sannan ya shafa mata ragowar a fuskarta, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani. Umar ya riƙo hannunta ya sanya cikin nasa yana murza wa a hankali.

"Umma lafiya kike? Ki na jin abin da muke faɗa?".

Kanta ta gyaɗa alamar e tana zarce wa da faɗin"lafiya ƙalau wani mafarki kawai na yi da ya tsora ni ainun".
"Wani irin mafarki ne haka Umma?".
"Umar mafarkin nan dai da na saba yi a duk sa'ilin da na kwantar da haƙarƙarina da sunan bacci".

Cike da damuwa Yaya Alhassan ya ce"mafarki kike yi da Kawu Manniru ya zo yana tambayarki amanar Amatullah da ya ba ki ko?". Cikin sanyin jiki ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa har ta kai ta kawo ba na ƙaunar na kwanta bacci ko da kuwa na minti ɗaya ne. Ban san ina zan je da girman alƙawarin da Manniru ya bar min ba, Amatullah ina kika shiga ne a cikin duniyar?".

"Umma don Allah ki rufa mana asiri ki cire wannan damuwar daga cikin ranki kar wani jinyar ya same ki a dalilin hakan. In Sha Allah Amatullah za ta dawo gare mu cikin aminci da yardan Allah, ina ji a jikina duk inda take tana hannu mai kyau kuma ba za ta taɓa aikata abin da Allah zai yi fushi da ita ba, don duk cikinmu babu wanda bai yarda da tarbiyyan Amatullah ba. Ƙaddarar ta ce kawai ta zo a irin wannan sigar wanda babu yanda muka iya ba za mu iya guje mata ba balle mu sauya mata fasali. Har yau ba mu fasa neman ta ba ina da yaƙinin duk wani mai nema watarana zai dace Umma don haka ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe".
Numfashi mai zafi ya ja ta furzar daga bakinta kafin ta sama lasisin faɗin"hakan nake fata da buri Alhassan. Allah ya yi muku albarka ya jiɓanci lamuranku yadda kuke ƙoƙarin yi min biyayya ku ma Allah ya azurta ku da ƴaƴan da za su yi muku fiye da haka". Cike da jin daɗin furucinta suka amsa da amin, Yaya Alhassan ya sa Umar ya zuba mata ruwa a cikin buta ta je ta yi alwala kana su ma suka je duk suka yi alwalan, Yaya Alhassan

13 / 39