Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
mabuɗin ilmi ce. Sai dai a wannan gaɓar zan iya ce miki ba ni da amsar ko guda ɗaya daga cikin tambayoyin da kika yi min hasalima yadda kike gan sa a cikin gidan nan ya zo, ni ma haka nake ganinsa tun yana yaro ban taɓa damuwa da na san mene ne alaƙarsa da masu gidan ba don wannan ba hurumina ba ne kuma bai shafe ni ba". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da zantukansa da dukkan suke kan gwadaben gaskiya.
"Haka ne kam Baba to Allah ya kyauta".
"Amin ya Allah".
"Zan nem takarda da biro na zo ana ɗaura mini darasi. Ko gaisuwa ya kamata na koya daga cikin yaren nan tun da ban iya furta ko kalma guda a ciki ba". Ya dara sosai kafin ya ce"ba girin-girin ba dai ta yi maiƙo, kullum haka kike ce har na gaji da gafara sa ba tare da na ga ƙaho ba". Kafin na kai ga cewa wani abu Aryan ya iso wajen.
"Wai ki zo in ji Umminmu". Haka kawai na ji gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi. Jikina a sanyaye na ce"lafiya?". Ya ɗage mini kafaɗunsa alamar bai sa ni ba daga haka ya dura da gudu ya koma ciki.
"Tashi ki je ƴar nan kar ki yi sanya don ba a bori da sanyin jiki". Kaina kawai na gyaɗa masa na tashi na nufi cikin gidan ba tare da na san abin da zan je na tarar a ciki ba.
Ina doso cikin falon idanuna suka soma sauƙa aka fuskar Altine da take zaune kusa da ƙafafun Hajiya Muhibbat gefe guda kuma Aryan da Ayan ne suke wasan mota. Na durƙusa kana na ce"Barka da hutawa Hajiya, ga ni an ce ki na nema na".
Ta ɗau lokacin kafin ta ce"me ya kai ki wajen mai gadi?".
"Hajiya gaisawa kawai muke yi da shi, sai kuma yaren kanuranci da na roƙi ya dinga koya mini kasance yarena ne kuma nan yi ba". Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to ba na son na ƙara ganin kin ce wajensa ko da wasa ne kuwa, ki yi aikinki shi ma ya yi nasa".
"In sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa za a kiyaye".
"Good". Ta amsa da shi a taƙaice, jikina ya yi sanyi ƙalau don na kasa gano inda maganganun natan suka dosa da kuma abin da take nufi da kar na ƙara zuwa wajensa ko da kuwa da wasa ne.
"Hajiya rana tana yi me ye za a girka ne?". Furucin da Altine ta yi kenan da ya tilasta mini cira kai na yi mata kallo guda tare da janye idanuna daga gare ta.
"Fita ni zan yi zuwa anjima can da yamma. Ku dafa abin da za ku ji don ba na jin ma su Saif za su dawo nan kusa". Tana dasa aya ta tashi ta bar cikin falon sa boda ƙirar wyarta da aka yi ta hau sama zuwa ɗakin da kallo na raka ta har ta ɓace wa ganina daidai lokacin da sautin Altine ya sauƙa a masarrafar naɗar sautina.
"Idan kunne ya ji jiki ya tsira". Duk yanayin da nake ciki hakan bai hana ni sakar mata da murmushin ba duk da kuwa bai kai har cikin ƙasan zuciyata ba. Ta tashi ta bar ni a gantale a cikin falon ba tare da ta sanar da ni abin da zan yi ba, zafafan iska na fesar daga bakina ina ɗan lumshe idanuna da nake jin har wani zafi-zafi suke yi mini.
Jin an fado kafaɗuna ya sa ni buɗe lumshashshun idanuna ina tsayar da su akan Ayan da yake tsaye a gabana yana rungume da dokin wasa a hannunsa.
"Kuka kike yi?". Na girgiza masa kaina ina kai hannuna ina share hawayena da ya zubo daga idanunta don ban san lokacin da suka zubo ba.
"Ummi ce ta yi miki faɗa shi ne kike kuka ko?".
Na riƙo hannuna ina jinjina kaifin tunanin yaron na furta"Ummi ai duk ta fi mu shi yasa idan muka yi ba daidai ba za yi mana faɗa, sa boda rayuwarmu ta gyaru ba don ba ta son mu ba". Kallon da ya tsare ni da shi ya sa ni fahimtar kalaman da na yi amfani da su sun yi girme wa shekarun da har ya hana sa fahimtar saƙon da nake son a isar masa a cikin zancen.
Na kai hannuna na shafo sumar kansa"ba faɗa Ummi ta yi mini ba ka ji?" Ya gyaɗa mini kansa alamar ya ji, daidai lokacin da Aryan ya iso wajen ya zo ya tsaya kawai yana kallona.
Na ƙirƙiro murmushin dole na dasa a bisa fuskana kafin na kai ga furta"lafiya ka tsaya haka?". Ya yi rau-rau da ido yana ta faman dube-dube ya matso saitin kunnena kamar mai raɗa ya ce"Anti don Allah ki yi mana wanka jikinmu gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mana".
"Wanka kuma? Ba a yi muku ba ne?". Da sauri Ayan ya janye Aryan daga kusa da ni yana faɗin"Aryan Uncle Saif ba ya hana ka yawan magana ba, ka zo mu yi wasan mu". Na cafko hannayensu gabaɗayan su ina kallon Ayan da gaba ɗaya ya bi ya firgice na lura ya fi Ayan tsoro nisa ba kusa ba.
"Me yasa za ka ce ya yi shuru?".
"Uncle Saif ya ce babu kyau yawan suturu". Ya ba ni amsa ba tare da ya yarda mun haɗa ido da shi ba.
"Ba irin wannan maganar yake nufi ba. Yanzu dai ku zo mu je na yi muku wankan sai ku dawo ku yi wasan".
"A'a yanka mu za ta yi". Ayan ya yi zancen hawaye suna ciko masa idanunsa ga jikinsa da ya soma rawa sosai.
Cikin mamaki na ce"waye? Waye zai yanka ku kuma?". Duk su biyun suka sadda kawunansu ƙasa ba tare da sun ba ni amsa ba. Take na ji kifiyar tausayinsu ta ratsa zuciyata tare yin pieces da ita, jikina ya yi la'asar na rasa ta inda zan fara shawo kansu, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi amfani da dabarar da ta faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu.
"Ku zo mu je na yi muku wanka na shirya ku babu wanda zai ji". A tare duk su biyun suka ɗago kai suna kallona kamar za su miƙa wuya sai kuma Ayan ya jan hannun Aryan tana faɗin"ka zo mu tafi mu yi wasan mu". Daga haka ya janye shi suka koma inda suka wasan na bi su da kallo ina tunanin mafitar da ta dace.
[12/3, 7:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 6️⃣0️⃣
Na yi ɗam jim ina ta tunanin ta yadda zan ɓullowa lamarin, can na ji wani dabara ta faɗo mini a cikin kaina tamkar faɗuwar aradu, na tashi na je inda suke wasan na zauna ina faɗin"ina ma zan yi wasan ku biyu ni kuma ni ɗaya". Duk suka ɗago ido suna kallona kafin can Aryan ya ce"kin iya ne?". Na gyaɗa masa kaina alamar e, ya miƙo mini motar guda ɗaya yayin da su ma suka dauki guda-guda, muka soma yin wasan ba mu yi nisa ba suka cinye ni lamarin da ya faranta musu rai da ruhi suka daka tsalle tare da ƙyalƙyalewa da dariya kamar za su shiɗe.
"Mun ci mun cinye ki Anti".
Na ɗaga ido na kalla Aryan da ya yi zancen na ce"ai gobe ma za mu ƙara gwadawa, yanzu dai tun da mun kama wasan ku zo mu je na yi muku wanka ku sauya wani kaya ku ji sanyi a jikinki". Kamar an yi ruwa an ɗauke lokaci guda fara'a da annurin fuskarsu ya ɗauke, duk su biyun suka yi shigo har sai da na kawar da shurun ta hanyar faɗin"idan ba kya so shi kenan bari na tashi na shiga ciki". Na yi zancen ina yunƙirin miƙe wa suka riƙo hannuna.
"Anti mu je ki yi mana wankan". Murmushi kawai na yi musu muka wuce ɗakin nasun, na cire musu kayan jikinsu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin na yi musu wanka da ruwan ɗumin da na tara a cikin bokati. Na wanke musu sumansu da mayuka da sabule gyaran gashin, na ɗauko musu towel ɗin muka fito na ɗaura su akan gadon suna ta jijjiga kansu yayin da ruwan da yake cikin sumarsu yake watso wa a jikinsa, suna ta kyalƙyala dariya.
Na ke jikin wadrode ɗin kayansu na buɗe na ɗauko musu wata jamfa launin ruwan ƙasa. Ina juyawa Aryan ya ce"Anti ni kam ba zan kayan nan ba". Ina rufe bakinsa ya diro daga kan gadon ya zo ya zaro wani wandon jeans ya ce shi zai saka, yayin da Ayan shi kuma ya dage akan ba sai saka wannan wandon ba.
"To shi kenan Anti kowa ya saka kayan da yake so kawai ko?". Aryan ya yi magana ina tsayar da idanunsa a kaina, na durƙusa a gabansa kafin na furta"ai ba zai yiyu ku saka kaya daban-daban ba, tare aka haife ku tare aka raine ku tare ku ka girma komai tare ake yi muku. Kun ga Ummi ba za ta ji daɗi ba idan aka saka muku kaya daban-daban".
Ina rufe bakina Ayan ya ce"shi kenan Anti a saka wanda Aryan ɗin yake so kawai. Ni na haƙura ba na son Ummi ta ji ba daɗi". Sosai na ji yaron ya ƙara shige mini can ƙasan ƙalbina yaro ne mai matuƙar nutsuwa ga shi sam ba shi da hayaniya balle ƙiriniya irin na yara masu shekarunsa, a ɗan saman da na yi a cikin gidan nan a lura ya fi Aryan maƙon ɗan uwansa.
Take Ayan ma ya tadae rigima ya ce shi ma ya haƙura a saka kayan da Aryan ɗin yake so, haka suka din ga yi har sai da na kawo ƙarshen muhawarar ta hanyan ɗauko musu wani kayan.
Farin riga t-shirt na saka musu mai gajeren hannu gaban rigar an yi rubutu da jan kala, na saka musu wandon jeans da tsayinsa ya tsaya daidai gwiwansu.
Na gyara musu sumar kansu ya sha musu mai tare da taje musu shi, ya yi kyau tare da ƙara yin sheƙi gami da ƙyalle, sosai kayan ya amshi jikinsu da hakan ya taimaka wajen fito da ainihin sihirtaccen kyawunsu.
Na lura su ma kansu sun san cewar kayan ya yi musu kyau don gaban madubi suka tsaya suna kallon kansu suna dariya. Na zo na tsaya a bayansu Aryan ya yi wuf ya ce"Anti ni da shi waye ya fi wani kyau? Ai na fi shi kyau ko?".
"Ƙarya ne ai Uncle Saif ma ya ce ni ne wanda ya fi kama da shi". Ayan ya mayar masa da martani cikin gaggawa, duk suka juyo gare ni suna rige-rigen yin magana.
"Waye ya fi kama da Uncle Saif a cikinmu Anti?". Aryan ya koma jefo mini tambayar a karo na biyu, kafin na amsa masa Ayan ya amshe zancen cikin faɗin"ai ni Ummi ta ce da Abbinmu nake kama".
"To ni ai yanzu ban san Abbin nakun ba haka shi ma Uncle Saif ɗin ban san shi sosai, ina dai ganin sa ne kawai. Kun ga kenan ba zan iya bambamce da waye suke kama ba a cikinsu".
Ina rufe bakina Aryan ya juya ya je ya ɗauko mini wani hoton da yake ajiye akan dirowar dake gefen gadon baccinsu ya kawo mini.
"To kin ga wannan shi ne Abbin namun". Ya yi zancen yana miƙo mini hoton na karɓa tare da zuba idanu, hoton Hajiya ce zaune ta sha wani uban leshi launin hoda da ya amshi jikinta kuma ya hau da zubin jikinta, an yi mata kwalliya a fuskarta da ta zauna a fuskar ta yi ɗas da ita tamkar da shi aka halicce ta. Wuya da kunnenta har da hannayenta sun sha ado sarƙa, ɗan kunne da kuma awarwaro. Gefenta na hagu Ayan ne zaune yayin da gefenta na dama Aryan yake zaune. Wani mutum ne fari sol tsaye a bayansu ya ɗan ranƙwafo ya dafo kadaɗun Hajiya da hannunsa guda ɗaya yayin da ɗayan hannun ya ɗaura akan Aryan, dukkansu fuskokinsu washe da maɗaukakin annuri da ya gauraye da nishaɗi, sai dai na lura hoton kaman tsoho ne don a hoton su Aryan ba za su wuce shekaru ɗaya da wasu watanni da haihuwa ba.
Sai da na saka ido sosai na gano Aryan da Ayan sam ba sa kama da mahaifinsu, duk kamannin mahaifiyarsu Hajiya Muhibbat suka kwaso kwabo da kwabo babu abin da suka bar mata, sai dai hasken ubansu da suka ɗauko. Ban yi aune ba na ji an fizge hoton tamkar za haɗa da hannuna, babu shiri na ɗago kai don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, idanuna suka sauƙa akan fuskar Altine ta take tsaye tana ta cika ta batse wa.
Me ye kike yi a cikin ɗakin nan sannan me ye wannan hoton yake yi a hannunki?".
Ba ta jira na ba ta amsa ba ta ci gaba da balbalin wutar ba'lain da take yi tamkar za ta yi aron baki.
"Watau kin ɗauko hoto kin sa a gaba ki na ta kallo, kin zuba wa mijin mata idanuna kamar mayya kin shagala da kallonsa har ma ba ki san sa'ilin da na shigo cikin ɗakin ba balle tsayuwar da na yi a kanki. Irin ku ne wanda ake ɗaukowa daga rana a shigo da ku cikin inuwa daga ƙarshe ku ku tura mutum cikin ranar, daman ni tun ranar farko da na gan ki nake kokonto a game da ke. Tukunnan ma me ye dalilin da ya kawo ki cikin ɗakin nan?".
Murmushi kawai na yi tare da miƙe wa tsaye, na kai duba na ga su Aryan da suke tsaye da na lura jikinsu gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau har sun kasa motsawa daga inda suke.
Sai da na yi dogon tunanin kafin na ce"daman an iyakance mini inda zan shiga ne a cikin gidan ban sa ni ba?".
"Tambaya kike yi ko kuma neman sani?".
"Duk wanda kika ɗauka a ciki daidai ne ranki ya daɗe". Na yi zancen ina ɗage kafaɗana alamar babu abin da ya sha mini kai ko ya ɗaɗa ni da ƙasa.
Na sa kai zan fice daga cikin ɗakin ta jawo gefen hijabina har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi Allah ya kiyaye.
"Ke har kin isa ina miki magana za ki tashi ki tafi ki bar ni? Wace ce ke kuma da me ye kike taƙama, sannan wa ye ya tsaya miki a cikin gidan da har kike jin cewar za ki iya yin duk abin da kika ga dama?".
Duk da abin da ta yi mini ya yi mini matuƙar ciwo tare da tusa mini takaici amma ban nuna mata ba ko a fuska, maimakon hakan ma murmushi na sakar mata ina tsayar da idanuna ƙar a kanta.
"Ni ba kowa ba ce a cikin gidan nan face ƴar aiki kamar ki, wacce ta fito aiki domin rufa wa kanta asiri da kuma samun abin da za ta ɗauki nauyin buƙatun rayuwarta". Ina dire zancen na juya na yi ficewa ta ina jin wani gigitaccen tsawan da ta dokawa su Aryan yayin da nake fice wa daga cikin ɗakin ko kanzil ban juyo na ce da ita ba. Kai tsaye ɗakin Altine na nufa wanda kai tsaye zan iya ƙiran da ɗakinmu na shiga banɗaki na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallan zuhur, na ɗaga hannayena sama ina jero kirari ga Ubangiji kana na shafa doguwar addu'ar da na yi wanda dukkaninta addu'ar neman rahama da gafara ne ga Abba. Wanda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da na yi tunanin sa ba ko kuma ya faɗo mini a cikin raina ba.
Hoton da na ɗauko a sashin Saif na tsince ɗaga gefen hijabina da na ƙulle na zura wa hoton idanuna yayin da wasu tambayoyi masu rikitarwa suke yi mini yawo a cikin kwanyata.
Tabbas akwai buƙatar na nemo wata iriyar alaƙa ce tsakanin Muhammad Taufik da kuma Sheikh Dawood ko kuma na ce baƙin Balarabe kamar yadda na laƙanci haka daga wajen Baba Mai gadi.
Numfashi mai nauyi na ja na fesar daga cikin baki sa boda tunawa da na yi da Amira, babu wanda yake saurin gane ina cikin damuwa ko da kuwa ban furta ba sama da ita, babu abin da ta ƙi jini a rayuwarta kamar ta ganni cikin ƙunci. Mun shaƙu da ita sosai ta yarda ba na shakkan sanar da ita dukkan sirrina domin ba ni da kaufi akan ta, ina jin ta tamkar ƴar uwar da muka rayu a mahaifa guda da ita kana muna fito duniya a tare kuma a lokacin ɗaya.
Na san ta yi nemana har ta gaji ta sadadu ta fawwalawa Allah komai, ko har yanzu suna tare da Mansur ko kuma ƙaddara ta raba su, wataƙila izuwa wannan lokacin sun mallakin junansu sun cika burinsu na zama miji da mata oho? Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina zame wa na kwanta sa boda sarawan da kaina yake yi mini tamkar ana buga mini guduma.
Ban yi nisa a cikin baccin ba na ji sauƙar ruwa mai sanyi a fuskana babu shiri na tashi sai dai duk da firgitan da na yi hakan bai hana ni kamo sunayen mahaliccina guda ɗari babu ɗaya ba cikin bakina.
Na cira kai ina duban Altine da take tsaye a kaina babu alamar ranƙwafawa tamkar wacce ta haɗiye taɓarya. Raina ya tuntsura yana tafasa tamkar talgen da yake bisa wuta yana ɓararraka.
"Kin fi kowa sanin cewar ai ba bacci ne ya kawo ki ba, da za ki zo ki yada baki ki na baccin asara wanda babu gaira babu dalili".
Tsam na miƙe akan ƙafafuna"na lura duk yadda na kai ga ƙoƙarin ganin na ba ki girmanki na kuma mutunta ki ba kya ganin hakan. To gwara na fito miki a mutum na fito miki a yadda kike so, Ina so ki sani ni fa baiwarki ba ne a cikin gidan nan hasalima matsayinmu ɗaya. Ki riƙe girmanki ni ma zan tabbatar da cewar na yi miki biyyaya a matsayinki da wacce kike gaba da ni amma