Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
faru da ita?". Ganin yadda na birkice ya sanya ta sanyaya muryarta tana faɗin"ki kwantar da hankalinki babu abin da ya faru da ita. Za kuma ki je ki gan ta a yau ba sai gobe ba". Kaina kawai na yi ƙarfin halin gyaɗa mata don jikina ya gama ba ni tabbacin cewa akwai wani abu a ƙasa.
Muna yin sallan asubahi ko abincin ban tsaya ci ba muka nufi gidan ni da Anty Zulaihatu har izuwa lokacin ƙirjina bai daina harbawa haka yana dakan lugudan-lugudan tara-tara. Muna sauƙa a ƙofan gidan na ji wasu tulin hawaye sun ciko mini idanuna rayuwata ta baya ya soma dawo mjni cikin kwanyata, yayin da wani haske ya ratsa idanuna tamkar majigin da yake hasko mini jiya ta zuwa yau. Babu abin da na fi tuna illa lokacin zaman makokin Abba yadda aka cika a ƙofar gidan. Sai da ta riƙo hannuna muka shiga cikin gidan yayin da yaran gidan da na maƙwabta suna cika a kaina suka mamaye ni kowa burinsa ya ɗaura hannunsa a jikina don kawai ya tabbatar da cewa ni ɗin ce na dawo ba wata ba.
Muna shiga filin tsakar gidan da Umman Amira na fara cin karo ta saki kwanon wainar da yake hannunta ya faɗi ƙasa.
"Amatullah ke ce? Jama'a ku fito ku fito ga Amatullahi ta dawo gida. Allah alhamdulillah". Ta yi zancen cikin ɗaga murya yayin da take rugowa da gudu ta zo ta ƙanƙame ni ƙam a jikinta. Kamar an kaɗa ƙararrawa haka ragowar matan gidan suka soma fitowa ƙwansu da ƙwarƙwatansu.
"Allah buwayi gagara misali. Amatullah ke ce tsaye a gabanmu? Ko da yake daman masu iya magana ai sun ce giji lahira ce". Maman Adnan da na gan ta da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe a jikinta, kaina kawai na jinjina cikin ƙarfin hali na kallo Umman Amira na ce"ina Ummata take?".
Ta yi mini nuni da hanyar ɗakinmu"tana cikin ɗakin". Da gudu na nufi ɗakin ina ƙwalla mata ƙira cikin muryata da ta gama dushashewa sa boda kukan da na ɗauki tsawon lokaci ina yin sa, turus na yi na tsaya lokacin da na yi ido huɗu da ita yashe a falon a bisa kan tabarma na bi ta da kallon tsaf yayin da ƙirjina yake buga wa kamar zai bayyano waje.
Daga ita sai zani ɗaurin ƙirji a jikinta sai kuma wani ɗan ƙyallen da ta lulluɓe kanta da shi, ƙafafunta na yi da kallo da wani wari da ɗoyi yake tashi daga gare su, ƙafarta ɗaya na ga an yanke har zuwa gwiwar ƙafar yayin da ɗayar kuma ta kumbura ta yi tsimtim kamar za ta fashe.
"Um-um-um-umma ke ce haka me ye ya same ƙafafunki?". Na furta zancen cikin tsintsinkewar zance numfashina yana sama yana ƙasa tamkar ceron da yake bugan sa a cikin turmi. Ta kasa cewa da ni komai illa kallon da ta kafe ni da shi hawaye suna tsiyaya a bisa baƙin fuskarta da ta yi duhun gaske tamkar bayan tukunya, ta ƙanjame kamar mai cutar ƙanjamau duk ta lalace kamar kamun mayu. Na duƙufa a gefenta ina kuka yayin da ita ma take taya ni babu ji babu gani kamar waɗannan aka yi wa mutuwar ƙare dangi.
[12/20, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 7️⃣4️⃣
Mun ɗauki lokaci muna kukan daga ni har ita babu mai lallashin wani haka Anty Zulaihatu da Umman Amira suka shigo ciki suka iske mu, yayin da ragowar sauran matan suka tsaya a ƙofar ɗakin ba tare da sun shigo. Sai faman ƙorafin wari da ɗoyin da take tashi daga cikin ɗakin suke yi.
"Haƙuri za ki yi Amatullah ai yanzu jikin natan ma da sauƙi sosai, tun da har ta na iya gane wanda yake tsaye a kanta". Muryar Umma Amira ya ratsa cikin ƙoƙon kaina da ya tursasa mini cira kaina ina dubansa bakina yana rawa yayin da haƙwarana suke karafɗiya da juna na furta"yanzu hakan ne jikin da sauƙi? Don Allah ku sanar da ni me ye ne abin da ya same ta har ta koma haka?".
"Wallahi wani azzalumin mai mota ne ya buge ta kuma don tsabar tsagwaron rashin mutumci ya yi tafiyarsa ba tare da ko waiwayanta ya yi ba, haka ta zo nan ta yi ta jinyar ƙafar bayan an yi mata ɗaurin gargajiya abin ya ci tura dole aka dangana da asibiti, shi ma ɗin da ƙyar da suɗin goshi ta amince aka je har aka sanar da Gwaggonki Sawwama. Nan Likitoci suka ce wai wani abu shi infection ya riga da ya kama ƙafar dole sai an yanke ta haka kuma aka yi mu na ji muna gani ana yanke ƙafar, bayan wasu kwanakin ɗayan ƙafan ma ya harbu ya soma fitar da wani ruwa mai ɗoyi da wari tare da ƙarni kamar jinin haihuwa. Kin gan ta nan yadda take jaɓe a nan ko ƙofar ɗaki ba ta iya fitowa ba ta iya taimakon kanta da komai, a nan za ta yi fitsari ta sauƙe duk wani buƙatunta babu mai shigo wa ya yi mata sannu balle ya taimaka mata da ko da abin da za ta saka a bakinta ne, tun da ke ma sanin kanki ne ba halin ƙwarai ba ne da ita haka nan ba ta zauna da kowa zaman lafiya a cikin gidan nan ba. Ni ce kawai ta zame min dole ni ma ɗin kuma na fara gajiya tun da daman Ubangijinmu ne ai kawai ya ba ya gajiya da mu Bayinsa".
Ji na yi kaina ya yi mini dum jikina gabaɗaya ya ƙara sake wa, wani baƙin duhu da babu ko da ɗigon haske a cikinsa ya gilma ta cikin idanuna. Duk da idan zaune ji na yi kamar ina shirin faɗuwa ƙasa, hakan ya sanya ni yin zaman ƴar bori dirshan a ƙasa. Na juyo da kaina ina kallon fuskar Umma da tun da Umman Amira ta soma zancen ta yi ƙasa da idanunta hawaye su na ci gaba da zuba daga gare su.
"Umma me yasa kika zauna haka har jinyar nan ta yi nisa, ba tare da kin nema maganinta ba"?". Kafin ta ba ni amsa Umma Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin faɗin"to ke kuwa Amatullah jinya ba dole sai da kuɗi ba, to haka kawai ake tashi a nema maganin ba tare da ko sisi ba?. Ko wancan aikin yanke ƙafan da aka yi Alhassan ɗan Gwaggonki da yake su ma ƴaƴan kirki ne irin albarka da suka kwankwaɗi tarbiyya a cikin kofin girmamawa shi ne ya yi ƙundunbala ya biya kuɗin aikin da na magungunan da aka rubuta haka nan ya yi mata siyayyar kayan abinci ya kawo, shi nake ɗan tsakura ina dafa mata har zuwa wannan lokacin da kika zo kika iske ta tana numfashi".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta cikin wani iriyar muryar mai tattare da tarin rauni saka kaina tsakanin tafukan hannayena tare da rushewa da wani matsanancin kuka mai tsanani.
"Ba kuka za ki yi mata ba Amatullah addu'a za ki yi mata Allah ya kawo mata sauƙi da mafitan halin da take ciki. Idan kuma wannan jinyar ba na tashi ba ne to Allah ya sauƙaƙa mata tafiyar ya sa can ya fi mata nan kasancewa alkhairi a gare ta. Ki tashi ki fito waje ki ɗan sha iska don warin cikin ɗakin nan babu makawa sai ya kumbura miki ciki, ko kuma ya haifar miki da wani cutar mai zaman kanta".
Umma Amira ta yi zancen ta na kai hannunta ta rufe hancinta tare da juya wa ta fice daga cikin ɗakin.
Na tsinkayo amon Anty Zulaihatu cikin rarrashi ta na cewa"ba kuka za ki yi ba Amatullah addu'a za ki yi mata, sannan kuma a fara neman mafitan nema mata lafiya. Wanda daman akan hakan ki ka zo ki ka same mu, akwai wasu gidauniyar da suke ɗaukan nauyin majinya mussamman masu irin lalurarta a yi musu aiki kyauta, magani ma kuma kyauta. Tunin Yaya Alhassan ya saka sunanta kuma in sha Allah akwai cikakken yaƙinin cewar za a dace don haka ki kwantar da hankali komai ya yi farko zai yi ƙarshe da iznin Allah". Ban iya cewa da ita komai sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni ainun, rurin da wayarta ya yi shi ya tilasta mata tashi ta fita daga cikin ɗakin don ta amsa ƙiran, ban ga laifinta don ta fita ba don tabbas zama ciki ɗakin sai ka kai zuciyarka nisa kuma sai hakan ya zama dole a gare ka watau ba ka da wani zaɓi.
"Amatullah".
Umma ta ƙira sunana da hakan ya sanya ni ɗaga kai ina kallon fuskarta, ta riƙo hannuna ta sanya cikin na ta. Hawaye suna gudu a bisa kuncinta ta ce"Amatullah kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Tun bayan rasuwar Manniru nake ta haɗuwa da jarabawa kala-kala daga wannan sai wannan kamar wacce aka saka wa hannu a cikin lamarin. A da na yi zaton barin sa cikin duniya zai ba ni wani dama ne da zan ci duniyata da tsinke sakace ta yadda zan sakata na kuma wala sai dai ashe kallon tsire nake yi wa rogo, na wofantar da ke sosai na ƙunsawa dangin Manniru ƙunci da baƙin ciki ba wai don ba na ƙaunar ki ba. Duk abin da na yi na yi sa da nufin ƙuntatawa Sawwama da kuma ƴaƴanta sai dai ban sani ba ashe wuƙa na ɗauka na daɓa wa kaina ba tare da na sani ba rashin Manniru ya sa ni fahimci komai isa, izza da taƙamar mace dole ta na buƙatar jagorancin na miji a cikin rayuwarta. Rashin Manniru ya sa ni na fahimci dole akwai wasu buƙatun da komai gata da azurkinki a cikin duniya ba za ki taɓa iya biya wa kanki su ba, rashin Manniru ya sa ni na fahimci duk macen da take zaune ba tare da wani tsayayyen na miji a cikin rayuwarta ba walau uba, miji ko kuma ƴaƴa to ita da hanyar Zamfara ɗaya suke a ɓangaren rashin tsaro. Amatullahi tun da wannan jinyar ta same ni babu ranar da garin Allah zai waye ba tare da na yi kukan rashinki ba lokuta da yawa na kan zauna na yi tunanin a wani irin hali na jefa rayuwarki a cikin yanzu? Tabbas Manniru ya yi gaskiya da ya ce DAFIN HARSHE ya fi dafin da ke tattare da bakin maciji da duk wani dabba mai cutarwa ga lafiyan ɗan Adam, mussamman kuwa bakin uwa don kamar yadda duk addu'ar da ta yi wa ƴaƴanta Allah yake amsar sa haka nan idan ta furta mummunan kalma gare su, sai hakan ya yi tasiri akan su ko ba daɗe ko ba jima ƙarshe kuwa ita za a bari da cizon ɗan yatsa. Kowa ya juya min baya a cikin gidan sai dai daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin laifinsu bisa hakan ba tun da ni ma a lokutan baya ban rangwanta musu. Idan na ga yadda ƴaƴansu suke yi musu hidima ko da kowa hidimar aikace-aikacen cikin gida ne sai na ji hawaye su na zubo wa daga cikin idanuna tunaninki da na halin da na je da rayuwarki a ciki sai ya dawo min sabo dal a cikin raina".
Dole ta tsagaita sa boda tari mai ƙarfi da ya sarƙafe ta, lokaci guda ya fitar da ita daga cikin hayyacinta. Na ɗauki kofin da yake na zaba ma da gudu waje da nufin ɗebo mata ruwa, har na buɗe rangan zan ɗebo ruwan na ji an riƙe mini hannuna.
"Kar ki sake ki haramta min ruwan da nake sha kuma nake ibada da shi, ta hanyar soma min wannan ƙazamin kofin marar tsafta da ya fito daga cikin ɗakin wulaƙantacciyar matan can da ba ta san mutuncin ɗan Adam ba".
Cak! Na tsaya ina bin matar da kallo don a tsawon zamana a cikin gidan ban taɓa ganin fuskarta a cikin gidan ba, ko da kuwa a zuwan baƙunta ne.
Muryata ta na rawa na ce"don Allah ki yi haƙuri ki ba ni ruwan nan ko kaɗan ne, na kai mata ta sha tari ya sarƙafe ta ga shi nan ma ki na jin sautinta". Na ƙare zancen wasu hawayen su na gudu a fuskana. Tsaki ta buga mini tare da sa dukkannin ƙarfinta ta ture ni Allah ya rufa mini asiri ban kai ƙasa ba ta rufe rangan kirif, ta tsaya a wajen tare da riƙe ƙugu tana jijiigawa.
Numfashi mai ƙarfi na ja fesar ina rarraba idanuna ko zan hango Anty Zulaihatu amma ban gan ta a cikin filin tsakar gidan, da hakan ya ba ni tabbacin in ba ta cikin zaure to tabbas ta fita.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta can ƙasan maƙoshina tare da runtse idanuna sa boda sautin da tarin da Umma take yi har yanzu babu ƙauƙautawa tamkar za ta shiɗe. Duniya ke nan juyi-juyi in ji kwaɗo da ya ji sa a cikin ruwan zafi tsamo-tsamo. Wai yau ruwan da Umma za ta ji ƙa maƙoshinta da shi ne yake neman gagararta, a lokutan bayan ko don gudun rigima da tijararta dole mutum ya kamfata ya ba ta ko da kuwa babu cikakken niyya sai ga shi yau reshe yana neman juyewa da mujiya.
"Amatullahi mu je na ba ki ruwan sai ki kai mata ta sha". Idanuna cike da hawaye na ɗago kai ina kallon matar Ustazu Abdulwahab da take tsaye a gabana, ta amshi kofin hannuna ta je ta ciko mini shi da ruwa taf ta kawo mini na amsa, motsa leɓena nake yi da zummar son furzar da kalaman godiya gare ta sai dai na kasa. Fahimtar hakan ya sanya ta faɗin"ba damu ba sai kin gode min ba Amatullah, ki yi maza ki kai mata ta sha ga shi har yanzu tarin bai lafa ba". Kaina kawai na jinjina mata na juya da sauri na koma cikin ɗakinmu na ba wa Umma ruwa ta ɗan sha amma duk da haka tarin bai lafa ba.
Jikina yana rawa na soma karanto wani yanki daga cikin yankokin Alqur'ani mai girma tofawa a cikin ruwan kana na ba ta sha. Kamar yankan wuƙa take tarin ya tsaya kamar an yi ruwa an ɗauke, na din ga jeranta mata sannu wani na bin wani tare da gyara mata zamanta tare da sanya mata matashi a bayanta ta yadda za ta ji daɗin zaman.
"Umma haka tarin yake yi miki haka kamar zai raba ki da numfashinki?". Ta gyaɗa mini kanta ta na ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushin ƙarfin hali.
"Umma dole mu tafi asibiti a duba ki, don a gano ainihin abin da yake damun ki. Zama haka ba zai yiyu ba bari na je na dubo Anty Zulaihatu ta zo ta". Na yi zancen ina miƙe wa tsaye zan fice ta riƙo hannuna hakan ya sa na waigo ina kallonta da ido ta yi mini alama akan na dawo na zauna na kuma yi kamar ta buƙata.
"Amatullah ina ji a jikina wannan jinyar ba na tashi ba ne abokin tafiya ne, ki yafe min duk abubuwan da na yi miki, na san da cewar duk halin da kika faɗa ni ce sila DAFIN HARSHEna ne sila. Kaicona! Ba na tunanin akwai wani maganin da zan sha na sama sauƙi ko da kuwa na sama sauƙin ma to iya na gangar jikina ne, amma ciwon da yake cikin zuciyata yafiyarki gare ni kawai zai warkar da wannan gyambon".
"Umma kin wuce komai a wajena haka zalika kin fin ƙarfin komai. Wallahi wani ne ya yi mini ba daidai ba ki ka ce na yafe masa to an gama maganar ke nan balle kuma ke da kanki. Umma na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki ɗaya amma don Allah ki bari a kai ki asibiti, a nema miki magani".
Ina gama maganan na tashi na fita ina fitowa na hango Anty Zulaihatu tana shigo hannunta riƙe da baƙin leda. Na yi hanzarin isa gare ta"Anty Zulaihatu don Allah ki zo mu kai Umma asibiti". Da sauri muka isa cikin ɗakin, muka haɗa muka rawa mu tafi asibiti Umma ta ce ba za ta je ba har Yaya Alhassan muka ƙira a waya ya zo ya saka baki amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda.
Yaya Alhassan ya ce a bar ta zuwa gobe ko za ta sauƙo ko kuma a ƙira likitan ya duba ta a gida, tare da Anty Zulaihatu muka share ɗakin muka tsaftace ko'ina. Muka yi wa Umma wanka muka sauya mata kaya.
Sai dab da magrib Anty Zulaihatu ta koma gida sa boda a ranar mijinta zai dawo. Haka na zauna na Umma na tisa ta a gaba na din ga karato mata karatun Alkur'ani da nufin ko za ta sama nutsuwa a cikin ranta.
"Amatullah Allah ya miki albarka".
Babu shiri na tsaya daga karatun da nake yi ba tare da na zo gaɓar da ya dace na tsaya a ƙa'idance ba.
"Umma me ye ki ka ce?".
"Ce wa na yi Allah ya yi miki albarka".
Ban iya amsa wa da kalaman baki ba, illa jan jikin da na yi na isa kusa da ita, hawayen farin ciki da murna su na zuba daga idanuna, ba zan iya tuna ranar da Umma ta taɓa sa mini albarka a kaf cikin rayuwata ba.
"Umma na gode, ke ma don Allah ki yafe mini kura-kuren da na yi miki". Ta sa hannu ta shafo kaina"ba ki taɓa ɓata min ba Amatullah, Allah ya raya ki".
"Amin ya Allah". Na amsa da shi ina kwantar da kaina a bisa kafaɗunta ina ta sauƙe ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Sanadin albarkan da Umma ta sanya mini na ji na manta da dukkan damuwata har na ji wani nutsuwa ya mamaye mini ruhina. Ina zaune a haka ban san lokacin da bacci ya sace ni ba. Muryar Umma shi ya yi silar farkar da ni daga baccin da ya ci idona.
"Ki tashi ki rufe mana ƙofa, sanyi ya fara sauƙa".
Firgitit! Na buɗe idanuna ina kallon cikin ɗakin da