DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   2 / 39

3K to 6K   out of 116.4K words

kike don na ga alamar ke ba ƴar cikin garin nan ba ne, tun daga yanayin Hausarki na ga ne haka. Sannan me ya rabo ki da gidan iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi jarumtar faɗin"sannu a hankali za ki san komai game da ni. Amma kafin zuwan wannan lokacin ina son ki yi mini wani alfarma guda ɗaga".
Ta gyara zamanta alamar tana ji da saurarona hakan ya ba ni damar ci gaba da maganan cikin ƙwarin gwiwa.
"Ina son na san wasu abubuwa dangane da tsarin gidan nan, wanda za su taimaka mini wajen gudanar da rayuwata a cikin gidan nan ba tare da wani matsala ta faru ba". Ta ɗan jim tana ta kallona kafin can ta furta"da farko dai kowa da kika gani a cikin gidan nan zaman kanta take yi, mafi akasarinsu iyayensu ne suka kore su ko kuma suka aikata wani mummunan abin kunyan da ya hana su zama a gaban iyayen ala dole suka haɗo kayansu suka baro iyaye da danginsu. Wasu kuma sun gagari iyayen ne shi ne suka sallama su suka shigo duniya, da yawan matan da za ki gani a cikin gidan akwai bakin uwa akan su wannan dalilin ya sanya ba sa kunya ko shakkan aikata komai. Abu na biyu shi ne komai na gidan nan na sayarwa hatta ruwan da za ki wanke idanunki da shi, in har ki na son zamanki cikin gidan nan ya yi tsawon rai dole sai kin zama fitsararriya ta buga wa a jarida wacce ba ta bari ko ta kwana, sai kin zama wacce ba ta raina ruwan shuka wacce duk wanda ya ɗaga mata ɗan ƴatsa sai ta karya shi komai tsufa ko kuma furfuransa".

Babu shiri na dafe ƙirjina"na shiga uku! Wani irin zama ne wannan? Sannan wani irin sana'a matan gidan nan suke yi da suke iya ɗaukan nauyin kansu, tun da komai na sayarwa ne a cikin gidan?".
Ta murmusa kafin ta furta"kowacce da kike gani tana da hanyar da yake kawo mata kuɗin shiga sai dai mafi akasarinsu jikinsu ne jarin su. Jikinsu suke bayarwa domin biyan buƙatan ransu. Suna hulɗa da manyan mutanen masu madarar kuɗi a hannunsu da masu riƙe da madafun iko. Ummata tana da ɗaurin gindi a garin nan don ta san manyan mutane da suke da ikon juya lamarin jahar nan shi ya sa take cin karenta babu babbaka babu wanda ya isa ya taɓa ta ya kwana lafiya".

"Jikinsu fa kika ce suke bayarwa domin biyan buƙatansu. Zina kenan fa?".
"Ƙwarai kuwa kuma ke ma ina mai tabbatar miki idan har ki na zaune a cikin gidan nan, a kwana a tashi wataran sai kin bi layin da suka bi. Don shi kaɗai ne hanyar rayuwa a cikin gidan nan shi kaɗai ne mafita ga duk wata macen da take zaune a cikin gidan nan".
Na zabga tagumi da hannu bibbiyu ina sauƙe numfashi wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai, ta dafa kafaɗuna"ba ki da wani mafita da ya wuce wannan, in kuma ba haka ba sai dai yunwa da ƙishirwa su yi ajalinki. Don ko mutuwa za ki yi babu mai kawo miki agaji a cikin gidan nan, kowa harkan gabanta take yi babu ruwan wani da wani. Kin ga rayuwar cikin gidan nan rayuwa ce da babu imani a cikin ta balle tausayi don haka tun wuri ma gwara ki yi ɗamara".

Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"babu wani mafita sai wannan? Ni wallahi ko aikatau ne zan yi don na ciyar da kaina". Na yi ƙuri tana kallona tamkar ba da yaren Hausa na yi maganar ba.
"Ba na ce babu ba amma dai na sanar da ke abin da yake a zahiri ne. Idan tun farko kin ga ba za ki iya ba ina mai ba ki shawarar tun kafin tafiyar ta yi nisa gwada ki koma gaban iyayenki don na ji ana cewa mutumcin kowacce mace a iske ta a gaban iyayenta komai talaucinsu. Ina takaicin ganin yadda kullum a cikin gidan nan sai an yi baƙin mata wasu sa'annina wasu ma na fi su a shekaru".

Kafin na yi magana aka ɗago labulen ƙofar ɗakin babu neman izni Aminu ya faɗo cikin ɗakin ya bi mu da kallo kafin ya ƙariso ya zauna.
"La'aniyatutu manyan gari wannan ɗin ma kin zo ki hure mata kunne ne kamar yadda kika saba? To ina so kin san wani abu guda ɗaya duk abin da kika ga ya sa ɓera fitowa daga raminsa ya faɗa wuta to haƙiƙa ya fi wutan zafi da ƙona a gare sa". Ta banka masa harara tana cuno baki ta ce"ni fa ka daina ɓata min suna, sannan ni ba wani hure mata kunne da na zo na yi na dai faɗa mata gaskiya ne kawai sannan ban mata dole ba in ta ga dama ta yi amfani da abin da na ce da ita in ta ga dama ta watsar da shi a nan da muka yi maganar". Tana gama faɗin haka ta tashi ta fita tana ƙananun magana.

"Ina kwana an tashi lafiya". Na gaishe shi cikin girmamawa maimakon ya amsa sai ya jefo mini wata tambayar ta daban.
"Ba wannan ba ne ya kawo ni na zo na ji hukuncin da kika yanke ne?". Na sadda kaina ƙasa ina sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ce"zan zauna".

"Za ki zauna?". Ya maimaita abin da na ce na gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi damar ci gaba da zancen daga inda ya tsaya.
"Kin yi kyan kai kuma ina mai tabbatar miki da cewar ba za ki yi dana sanin zamanki a cikin gidan nan. Tun da na fara ganinki na hango wani a tattare da ke bariki za ta yi miki riga da wando". Na yi hanzarin katse shi"ni ba bariki na zo yi ba, zan nema sana'an da zan riƙe kaina da shi".

Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya har yana riƙe ciki sai da ya yi mai isars kafin ya ce"ba yau na saba jin irin wannan kalaman ba hasalima duk wacce kika gani a bariki da irin wannan kalaman take farawa, amma idan tafiya ta yi tafiya sai zancen ya sauya. Da ƙafarki za ki zo ki na neman wanda zai kwana da ke......".
Na runtse idanuna tare da kai hannuna na toshe ƙofofin kunnuwana"ba zan taɓa aikata zina ba".

"Lokaci ne zai tabbatar da hakan ƴan mata. Yanzu dai akwai wani abun da kike buƙata ne?".

"Babu wani abun da nake buƙata, don wanda ka kawo jiya ma ban yi amfani da shi. Sama ko ƙasa na neme shi na rasa".

"Ai mantawa na yi ban gaya miki ko filin tsakar gidan nan za ki fita ki ja ƙofar ɗakinki ki rufe shi da makulli. Don akwai ɓerane masu suffa mutane a cikin gidan nan da kuma masu dogon hannu, zan karɓo miki makulin ɗakin a wajen Hajiya Babba sannan zan taho miki da abin kari". Bai jira abin da zan ce ba ya tashi ya fice ya bar ni zaune a cikin ɗakin mamaki ya hana yin ƙwaƙwƙwaran motsi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma ban ga alamar zan sama littafin alƙur'ani mai girma a cikin gidan ba, don haka na kifa kai da gwiwana ina karato abin da yake haddace a cikin kaina.
"Da kin bar karatun nan tukunnan kin sa wani abu a cikin cikinki ƴan mata". Na tsinkayo muryar Aminu a tsakiyar kaina, na ɗago kaina ina duban sa yayin da yake ajiye wani baƙin leda a gabana kana ya miƙo mini wani ɗan makuli na kai hannu na amsa.

"Wannan shi ne makullin ɗakin duk inda za ki motsa ki ja ƙofarki ki rufe ta, in ba haka ba kuwa an dinga yi miki sakiyan da babu ruwa, wataran hatta tabarman da kike kwance akanta sai an ɗaga ki an ajiye a gefen an ɗauke ta".

"In sha Allah zan na rufewa".

"Da kin yi kyan kai kuwa, ga abincin nan ki samu ki ci. Zan ciyar da ke na tsawon sati guda kafin ki waye da wasu abubuwan daga nan kuma zan bar ki da halinki ke za ki fita ki nemo ki ciyar da kanki har ni ma na raɓe a jikinki". Jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har ya fita daga cikin ɗakin na ɗade zaune a inda ya bar ni ina ta saƙa da warwara a cikin raina. Ganin yunwa tana neman yi mini lakani ya tursasa mini jawo ledan na buɗe awara ne da buredi sai pure water guda biyu, na soma ci don maganin yunwa ba don ina jin daɗi ko ɗanɗanonsa a bisa harshena ba. Sai da na cinye tas na shanye ruwan guda ɗaya na bar ɗaya a waje na yi bacci ban san adadin awannin da na kwashe ina baccin ba sai hayaniyar da na ji kamar a cikin mafarki ne ya tashe ni.

Na fito ƙofar ɗakin na tsaya domin ganewa idanuna abin da yake faruwa, kowa tana tsaye cirko-cirko a filin tsakar gidan. Yayin da wata matashiyar budurwa ta sha ɗamara tamkar mai shirin zuwa filin gwabzawa sai bala'i take yi kamar za ta yi aron baki.
"Daman na daɗe da fahimtar don ƴan gidan nan hassada suke yi min sun ƙi jinin su ga na yi wani babban kamu. Tun da na haɗo da Alhaji Bashiru yake yi min ruwan sulalla ake yada min da magana, shi ne yau don an ga ba na nan aka haɗa baki za a yi min sakiyar da babu ruwa, shi ne aka ja shi har cikin ɗaki akan tsegumta masa cewar wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba. To kwarankwatsa dubu ba zan laminta ba ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa, ko a fito min da munafukar ko kuma na bankawo gidan nan wuta kowa ya ƙone".

Kamar wacce aka jefo ta haka Hajiya Babba ta fito daga cikin ɗakinta tana bala'i.
"Wacce shegiyar ce mai tsinin baki nake jin tana ambata ƙona min gida?".

"Hajiya ni ce munafurci aka haɗa min. Don an ga bana nan shi ne da Alhajina ya zo aka ja shi ɗaki ake tsegumta masa wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba".

"Ke Farida ƴar mutan gabas sa idonki a cikin nawa ki kalle ni da kyau. Idan ba ki shiryawa bariki ba kika shigo cikinta to ki kuma ki je ki nema ilminta sannan ki dawo. Ke yanzu akan wannan abun ne za ki zo ki na tada jijiyar wuya har da ikirarin ƙona min gida, ke yanzu sai na zaunar da ke na fassara miki ma'anar wannan karatun da ake faɗin duk wanda ya yi maka kan kara ka yi masa na rodi? Ke ma ai ware rana za ki yi ki je ki tare Alhajin wata ki fanshe abin da aka yi miki. Yo ai daman bariki alelen gero ne duk wanda bai iya ba kwaɓe masa take yi, don haka kowacce ta gama harkokin gabanta a watse na kashe wannan case ɗin".

Tsimi-tsimi na ga kowacce ta ja jikinta ta koma ɗakinta bayan an gama jefawa juna harara da kallon uku saura kwata. Ni ma koma ciki na zauna ina ta jiran na ji an yi ƙiran sallan zuhur amma shuru kamar an aike Bawa garinsu. Ganin wankin hula yana neman kai ni dare na dauki ɗayan pure watern da na ajiye na fito na yi alwala da shi na shiga na yi sallan zuhur ina zaune inda na yi sallan La'aniyatu ta shigo, muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"har ya tafi kenan?".

"Waye fa?"

"Aminu mana tauraro mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba". Na saki taƙaitaccen murmushi ba tare da na ce da ita komai ba.
"Kin ga mutumin kusan rabi da kwatan matan gidan nan shi ya kawo su, kuma duk wanda suka kwanta da shi ya biya su sai an cire masa nasa kason mai tsoka a ciki. Wani zubin har ɗaukan su yake yi ya kai su wajen manyan mutane su yi haramtacciyar mu'amala, akan kuɗi babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Kuma ke ma ina tabbatar miki da cewar duk wannan rawan ƙafa da ɗawainiyyar da yake yi a kanki zzi fanshe su tsaf har da riba". Na yi shuru na kasa cewa komai sai can na furta"Allah ya kyauta shi kuma Allah ya ganar da shi". Ba ta amsa ba illa taɓe bakin da ta yi tana ɗauke kanta gefe guda.

"Tun ɗazu ina ta zaune a nan ina jiran ƙiran salla amma shuru".

"Ƙiran salla dai? To ai ko za ki shekara a nan ba za ki taɓa jin ƙiran salla ba. Tun daga farkon layin nan har ƙarshenta babu masallaci, islamiyya ko kuma wani majalasin da ake koyar da faɗin Allah da Manzonsa. Ke in taƙaice miki bayani babu wani ɗan arzikin da yake biyo wa a layin nan don duk mutumci da kimarka idan aka ganka a layin daga ranar ba za a ƙara yi maka kallon mutumci ba. Idan kin ji ana faɗin layin jahannama to layin nan kenan".
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________

Page 4️⃣3️⃣

Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya bugawa tamkar zai faso nama da fatana ya bayyano waje, ta kalle ni ta saki murmushi"mamaki kike yi ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta daman zarcewa da faɗin"indai mamaki kike yi to yanzu kika fara don sai an wayi gari watarana kin daina ma jin mamakin wasu abubuwan".
"Allah ya kyauta". Na furta a taƙaice ba ta amsa mini ba har sai da na ƙara cewa"don Allah yanzu ƙarfe nawa ne?".

"Fitowa na daga ɗaki dai ƙarfe huɗu saura". Na yi zumbur na miƙe ina tada iƙaman sallan asr, har na iddar da sallan tana zaune tana kallona na shafa addu'ar da na yi kana na fuskanto ta.
"Don Allah ina neman wani taimako".

"Faɗi kanki tsaye, matuƙar zan iya to kin same shi kin huta".
"Ina so na zagaya cikin unguwan nan don kafin wa'adin da Aminu ya ɗebar mini na ciyar da ni ya cika. Ina so na tsaya da ƙafafuna ba tare da na bi hanyar da ragowar sauran mutanen gidan nan suka bi ba".
"Za ki sha wahala ne kawai don a kaf unguwan ba na tunanin za ki sama aikin da za ki kare mutumcinki da shi. Idan har kin san cewar ba bariki kika fito yi ba me yasa tun farko kika baro gaban iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na furta"wannan wani labari ne mai zaman kansa watarana zan ba ki labarina. Yanzu dai ina so na fita don na lura zama bai kama ni ba".

"Bari na duba idan Ummanta ta yi bacci sai mu fita na raka ki". Ba ta jira abin da zancen ba ta tashi ta fita da sauri, babu jimawa ta dawo" mu yi sauri mu fita, ta yi bacci na san kuma ba za ta tashi ba wataƙila sai nan da zuwa dare. Don ta shawo ta yi tatil". Na yi sakeke ina kallonta ganin ba ni da niyyan motsawa ya sa ta jan hannuna ta jijjiga ni na dawo cikin hayyacina daga kogin mamakin da na faɗa, ta ɗauki ɗan makullin ta muka fito ta ja ƙofan ɗakin ta rufe da makulin muka fita a zaure muka yi kiciɓus da wasu samari su biyu suna shigowa. Kamar za mu gogi juna da su amma duk da hakan sun ƙi matsawa sai ma ƙara matso mu da suke yi.

"Gambo ka ba ni hanya na wuce tun kafin na yi maka rashi mutumci mai wasali".
Ya fashe da dariya"to ki yi mana wani dare ne jamage mai gani ba La'aniyatu? Ni fa babu wani nau'in rashin mutumcin da ban ga ni ba, to don kin yi na ki a matsayinki na ƙaramar ƴar bariki ma ai ba zai yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba".
Ɗayan ya saki tsaki yana banka mana harara"ni wallahi na rasa abin da ka gani a jikin wannan ƙwailan yarinyar da ka ji ka nace mata. Na rantse da Sarkin dake busan numfashi ko a yau na yi niyyan kwanciya da yarinyar nan babu makawa sai na yi ko da amincewarta ko babu. Bar ganin wai uwarki tana ba ki tsaro da kariya yarinya".

"Kanku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wanka na nake yi". La'aniyatu ta yi zancen cikin matsanancin ɓacin ran tana jan hannuna muak raɓa ta gefensu muka wuce tun da muka fito ba ta ce da ni komai kuma ba mu fasa tafiya ba kamar yadda ba ta sanar da ni inda muka nufa ba. Sai da muka yi nisa kafin na ce"na ga kaman ranki ya ɓaci bisa abin da samarin can suka yi miki ko?".

"Kar ki damu zan koya musu hankali ɗaya bayan ɗaya". Na saci kallonta kafin na ce"su waye ne su ɗin? Sannan me yasa suke cin irin wannan alwashin a kanki?". Ta ja dogon numfashi ta fesar sai da ta shafe wasu mintuna ba ta yi magana ba.
"Ki yi haƙuri idan abin da na faɗa ya sosa miki rai ko kuma ba ki ji daɗinsa ba".

"Kar ki damu babu komai. Ba kowa ba ne su ɗin face irin ƴan iskan garin da suke taruwa a cikin gidanmu, gani suke yi don kasancewata ƴar magajiyar karuwai da ƴan daudu shikenan ni ma ƴar iska ce ba su san cewar baƙar tukunya ta kan iya fitar da farin tuwo ba". Na jinjina kaina alamar gamsuwa da dukkan zantukanta"haka ne kam kin san lamarin mutane sai haƙuri".
"Kin gan ni nan tun da na yi wayau na iya bambamce tsakanin launin fari da baƙi daidai da rana guda ban taɓa jin rayuwar da mahaifiyata take yi yana burge ni ba. Tun ina ƙarama na tashi da tsana da ƙyaman irin rayuwar da take yi, tun kafin san haramcin abun a addinance nake jin tsanarsa a cikin raina. Mutane da

2 / 39