DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   10 / 39

27K to 30K   out of 116.4K words

karin kumallonki nan". Ta faɗa tana wuce wa ta koma gefe ta zauna, na bi ta da kallo na ga ta jawo wani kula da ƙaramin flask ɗin ruwan shayi na hango wannan kofin da ta tsiyaye madarar a ciki ta zuba ruwan shayin da yake cikin flask ɗin a kai tana juya wa da cokali. Ta kurɓa ta ajiye kana ta buɗe kular na ga ta ɗauko doya soyayya da ƙwai tana dangwala da yaji ta kai bakinta.

Lamarin ya ɗaure mini kai don ni dai ban inda aka soya doya ba hasalima ƙosai na zo na iske ta tana tuyawa. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dawo da dubana kan plate ɗin da yake gabana ƙosai ne wanda a lissafina ba su haura guda bakwai ba, gefe guda an ɗan ɗosa na mini yaji.
Kaman ba zan ci ba sai kuma na yi wani tunani na kai hannuna na ɗauki guda ɗaya na sa a bakina, na ɗa kofin kunun na kai bakina. Na kasa haɗiye don ban yi tsammanin jin sa haka ba. Koko ne wanda ko sugarin arzuki babu a cikinsa ga shi ya yi sanyi ƙalau babu daɗi sha, wanda ni kuma dai na gani da idona kunun madara aka dama. Ban. ce da ita komai ba na ci gaba da cin ƙosan ina haɗawa da kokon ba don ina jin daɗinsa ba har sai da na kama tsaf, na tashi zan fitar da plate na ji ta bushe da dariya bai waigo ba kamar yadda ban tambaye dalilin dariyar ba na yi ficewa ta.

A bisa kan dinning table na iske su Hajiya suna yin karin kumallo, na durƙusa na yi musu sannu da hutawa ta amsa mini cike da kulawa. Na tashi zan shige kicin na Saif yana faɗin"Hajiya Anty mu na da baƙo fa a cikin satin nan, da na ce ba zan sanar da ke sai dai kawai na kawo miki shi amma daga baya na sauya shawara".

"To fa! Wane ne haka".

"Abokina ko in ce amina Muhammad Taufik".

Baan lokacin da na saki plate ɗin da ke hannuna zuwa ƙasa ya tarwatsewa ba. Tsabar firgicin da sunan da ya ambata ya jefa ni a ciki.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 5️⃣2️⃣

"Amatullah lafiyarki me ye ya faru?". Na tsinkayo muryar Hajiya Muhibbat sai dai na kasa cewa da ita komai kamar yadda na kasa motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin tattare plate ɗin da ya tarwatse a wajen.
Ban dawo daidai ba sai da na ji hannun mutum a bisa kafaɗuna da hakan ya sanya ni sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina ɗan lumshe idanuna a hankali.
"Me yake faruwa ne?". Ta ƙara jefa mini tambayar a karo na biyu, sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na sama zarafin faɗin"babu komai Anty, kawai ji na yi kaina ya ɗan sarawa". Ta yi shuru tana kallona na tsawon wasu daƙiƙu kafin ta ce da ni"to ki je ki kwanta ki ɗan hutu a ɗakin Altine". Kaina kawai na gyaɗa mata don ba na tunanin ko na yi ƙoƙarin amsawa mata da kalmomin baka bakina zai ba ni haɗin kai waje aiwatar da hakan a aikatace.

Na nufi kicin na ɗauko tsintsiya da faka na zo na share inda plate ɗin ta tarwatse na je na zubar, a hankali na dawo cikin falon ina tafiya a hankali don haka kawai na ji gabaɗaya ƙafafuna sun riƙe ta yadda da ƙyar nake ɗaga su ina sauƙewa.
"To baƙon nakan yaushe zai zo sai mu fara shiri?".
Na ɗago kai ina satan kallonsa na ga idanunsa suna kan plate ɗin ƙosan da yake gabansa sai dai ban ga sa'ilin da ya kai ko guda cikin bakinsa ba.
"Gobe da yamma in sha Allah zai shigo garin nan tare da mahaifinsa".

"Allah Sarki! Muhammad Taufik ina jin daɗin ganin yadda yake bayar da hankali wajen ba wa addini gudunmawa kamar yadda mahaifinsa yake yi, duk da irin yanayin aikinsa. Shi fa yanzu lokacin kansa ma bai da shi balle kuma na mace daga kai har shi ɗin shi yasa har yanzu kun kasa fito da matayen aure. Ga shi kullum ƙara girma kuke yi shekarunku suna ƙara tafiya".

"Hajiya Antynmu ai komai lokaci ne, idan lokacin mu ya yi babu makawa za mu yi auren nan. Ko kika sa ni ma ba mu daga cikin wanda Allah ya ƙaddarawa za mu yi aure a cikin duniya". Ya ƙare zancen yana miƙe wa tsaye daidai sanda zan shige ɗaki na ji Hajiya Muhibbat tana tambayar sa ya ta ga ya tashi? Ya ce da ita ya ƙoshi ban san yanda suka ƙare ba na shige ɗakin. Ina shiga muka haɗa ido da Altine ta banko mini wata uwar harara tamkar wacce ta yi arba da kashi, na yi hanzarin janye idanuna ina ƙariso na zauna a ƙasa. Mun shafe a ƙalla mintuna talatin ni da ita babu wanda ya ce da wani ko kanzil ina waige-waigena na hango alƙur'ani ajiye a saman akwati.

"Anty Altine don Allah ina ba damuwa zan yi amfani da alƙur'anin nan". Ta ɗago ido ta yi mini wani banzan kallo kafin ta ce"ai ba a kaina kika gan shi, da za ki ce sai kin jira na sauƙe kafin ki yi amfani da shi". Ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauko alƙur'nin na soma karanta suratul Maryam cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi ɗaya bayan ɗaya.

"Malama ki rage muryarki don bacci nake so na yi". Na yi mata wani kallo ta wutsiyar idona na ci gaba da karatun da nake yi ba tare da na bi ta kanta ba. Ban yi aune ba kawai na ji an zagbaw mini wani gigitaccen mari a kuncina babu shiri na dafe kuncina tare da ɗago idanuna na sauƙe shi akan fuskar Altine da take tsaye a kaina ta riƙe ƙugu tana huci tamkar saniyar da take shirin kai bugu.
"Me ye na yi miki da za ki mare ni?".

"Bari ki ji in gaya miki wani abun da ba ki sani ba shi ne duk wata ƴar aikin da aka kawo cikin gidan nan dole ta bi umarnina. Sannan wajibi ne a gare ta ta yi mini biyayya don a gaba nake da ita. Na lura tun ranar ki ta farko kanki yana rawa ki na ta wani ƙoƙarin shige wa jikin Hajiya da wani kinibibin jan su Aryan a jikinki, to billahillazi tun wuri gwara ki kama kanki kafin na haɗa miki sharri da tuggun da ba za ki iya fitar da kanki ba". Na ji zuciyata tana wani irin harzuƙa ta zo mini har wuya tabbas na yi sanyi don da zamani da nake gida ne ba ta isa ta ɗaga mini ƴatsa ban karya shi ba duk da kuwa ina da haƙuri matuƙa da kai zuciya nisa.

Tsam na miƙe jikina har wani rawa yake yi kamar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna suna ba da wani sautin ɗas ɗas. Ta matso dab da ni ta ce"ko za ki rama ne na ga kin miƙe ina wani jijjiga?". Ta saki wani bushashshiyar dariyar da ba ta da haɗi da nishaɗi, jin daɗi ko kuma walwala kana na furta"ai ko dukana kika yi da itacen bishiya ba zan rama ba Anty, sa boda na ƙoshi da tarbiyya kuma an koyar da ni yadda zan girmama na gaba da ni ko da kuwa da sankan ɗaya ya riga ni zuwa duniya balle ke da kin kusa haifa ta. Bari na je na duba Hajiya ko sun gama na tattare kwanukan". Da alama ba ta ji daɗin zancena na ƙarshe ba don sakeke ta yi tana bi na da kallo tamkar ta sama majigi har na fice daga cikin ɗakin ba ta ce da ni komai ba.
Da sallama na ƙariso ciki falon na ga har sun gama cin abincin sun koma kan kujeru sun zauna, na tsuguna na yi wa Hajiya sannu da hutawa kana na isa wajen dinning table ɗin na tattare kwanunkan na kai kicin na wanke su tas na mayar da su majiyarsu.

Ina kicin ɗin Ayan ya shigo wai na zo in ji Umminsu, muka fito tare da shi na zauna a ƙasa cikin girmama wa na ce"Hajiya ga ni".
"Jiya Saif ya kai ki gidan nakun?". Ƙirjina ya buga da ƙarfi na ɗago ido ina satan kallonsa na ga shi kam ko a jikinsa wai an muntsini kakkarauna yana zaune yana latsa wayar da yake hannunsa.
Sai da na daidaita nutsuwata kafin na iya furta"e Hajiya ya kai ni". Ta mayar da dubanta gare shi"ka ga gidan na sun?".

Ba tare da ya ɗago kansa ba ya ce"e Hajiya Antynmu ko yanzu ma in ki na so zan iya kai ki".
"To alhamdulillah tun da ka ga gidan, ka ba ta makullin sashinka ta share maka kafin ka fita. Don ni yau sai around 5:pm zan fita". Sai a lokacin ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake yi"Anty ni fa sashina a gyare yake. Ke ma kin san ko wata macen ba za ta nuna min tsafta ba balle kuma wannan". Ta murmusa kafin ta ce"ai duk tsaftan namiji Saif a bayan mace yale komai ƙanƙantan ta kuwa. Ka ba ta makullan kawai ta je ta gyara maka, kar wani gyara ka iya kai da yaushe ma ka zauna a cikin gidan". Kamar na yi magana na ce ta ita ta bar shi kawai tun da ba ya so sai kuma na yi shuru.
Muryarsa a cushe ya ce"a buɗe yake".

"To Amatullah tashi ki je sashin nasan ma a buɗe yake, ki gyara masa shi tsaf irin gyaran da shi da kanki sai ya sa an nemo ki gobe. Idan hakan ya faru kuma ni da kaina zan tsaya miki ki gara shi kamar ƙwallon ƙafa kafin ki je ki ƙara gyara masa".

"To Hajiya". Na amsa da shi a taƙaice jikina gabaɗaya ya mutu murus, na tashi na fita zuwa sashin nasan ƙirjina yana tsananta bugu kamar zai fito waje. Sai da na isa ƙofar sashin na ja dogon numfashi na fesar kafin na turo ƙofar na shiga ciki na tsaya ina ƙarewa zubi da tsarin falon kallo. Ba shi da girma sosai don bai kai na Hajiya Muhibbat ba ya tsaru sosai da dukkan abubuwan more rayuwa da ƙawata waje, komai na falon fari ne tun daga kan labulaye, kujeru, tayis da kuma kafet ɗin hatta abin da aka ɗaura tv a kai fari ne. Na cire hijabina na ɗaura a ƙuguna na soma tattare takardun da na gani a barbaze akan kujerar kan teburin kofi ne da goran ruwan da aka sha ba a ɗauke ba.
Na tattare takardun na kimtsa su na saka a cikin jakar da na gani a gefe, na ɗauke kofi da goran ruwan na shiga ɗaya daga cikin ƙofofi biyu da na gani. Ƙofan farko da na shiga na ga kicin ne na ajiye kofi da goran, kicin babu ƙazanta a cikinsa amma komai a birkice yake komai ba ya muhallinsa.

Ban san sa'ilin da na saki tsakin takaici ba ina kwakwayon muryarsa na ce"ni ko'ina a sashina a gyare ya ke ko wata macen ba za ta nuna mini tsafta ba". Na tattare kicin ɗin na share kana yi mopping na fito na shiga ɗayan ƙofan ɗaki ne mai ɗauke da kayan ɗaki tsaf sai dai da alama ba wanda yake kwana a cikinsa saboda yadda ya yi ƙora na karkaɗe na sauya zanin gadon na shiga banɗaki na wanke na fito na hau benin ya sada ni da wani ɗan madaidaicin falo nan komai a gyare yake sai ɗan abin da ba za a rasa ba, na kashe tvn da na gani a kunne kana na rufe tagogin da suke buɗe.
Ƙofa ɗaya na gani na shiga na tarar da ɗakin kwana ne shi ma komai na cikinsa launin fari ne hatta zanin dake kan gadon.

Sauya zanin gadon na fara yi na gyara gaban madubin da komai ya ke warwartse kana na wanke banɗaki. Na hango wani air freshener akan dirowar da ke jikin gadon na je da nufin ɗauka na feshe ɗakin da shi, sai dai mummunan ganin da na yi ya tursasa mini tsayawa cak na kasa motsawa na tsawon wasu dakiƙu.

Jikina yana rawa tamkar mazari na kai hannu na ɗauko hoton da na gani ajiye a saman dirowar ina ƙara ware idanuna akan sa. In dai ba idanuna ba ne suka sama matsala tabbas hoton Muhammad Taufik da Saif na gani tare cikin shiga irin ɗaya kowa hannunsa riƙe da sallaya da alama masallaci za su je, ko kuma ranar bikin salla aka yi hoton. Duk su biyun fuskokinsu yana ɗauke da maɗaukakin annurin.

"Muhammad Taufik".

Na furta cikin rawan jiki da na murya yayin da wasu hawaye suke gangarowa daga idanuna suna wanke mini fuskana. Jin an turo ƙofan ɗakin an buɗe ya sani na firgita da har ban san lokacin da hoton ya zame daga hannuna zuwa ƙasa ba, gilashin dake jiki ya yi kwasa-kwasa. Runtse idanuna na yi ina kai hannayena dukka biyu na toshe kunnuwana da ƙaran fashewan gilashin da ya gigita ni har ya na barazanar juyar mini da ƙaramar curin ƙwaƙwalwata.

"Me ye kike yi a nan?".

Na yi muryarsa tamkar daga sama ban iya cewa da shi komai har ya iso inda nake tsaye daidai lokacin da nake buɗe lumshashshun idanuna har na gama buɗe su tar akan gilashin da ya tarwatse a wajen.
Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi ya yi mini wani matsaiyacin kallo kafin ya tsuguna ya ɗauki frame ɗin bai ce da ni komai ba ya fita daga cikin ɗakin. Wani kuka ne mai ƙarfi ya kuɓuce mini na sulale ƙasa na yi zaman dirshan ina jin yadda dunduniyar ƙafana ya cashi gilashin yana fitar da jini amma ban damu ba na ci gaba da kukan da nake, tare da jefa wa kaina jerin gwanon tambayoyin da na gaza cimma amshoshinsu.

Me ye alaƙar Saif da Muhammad Taukif da har na ga hotonsu tare? Shin da gaske yadda kunnuwana suka ji yo mini shi ne baƙon da zai zo cikin gidan nan da yammacin gobe?. Tagwayen ajiyan zuciya mai ƙarfi na ja na fesar kafin na yi ƙarfin halin tashi tsaye ina ɗan ɗingisa ƙafata na ɗauko tsintsiya na share wajen na fesa air freshener ɗin da na yi niyya kana na ja ƙofar ɗakin na fito. Babu kowa a falon saman amma an kunna sautin karatun alƙur'ani cikin wata muryar da na kasa tuna inda na taɓa jin ta, na sauƙo ƙasa na iske shi zaune a falon ƙasa yana zaune ya yi shuru kamar wanda yake nazarin wani abu. Na zo na durƙusa a gabansa.

"Na ga ma duk wani gyaran da ya dace na yi. Shi ne na ce bari na tamnaya inda akwai abin da kake so a yi maka".

Sai da na cire rai da samun amsa daga gare sa, don har da ƙafafuna suka gaji na ji kamar na ɗaura hannuna a ka na yi ta kurma ihu tsabar takaicin da ya ƙunsa mini, na tsani na yi wa mutum magana ya yi banza da ni wannan abun ci mini rai yake yi sosai da sosai.
"Za ki iya tafiya kuma kar ki ƙara dawowa sashin nan don ba na buƙatarki a nan. Don haka ki san abin da za ki faɗa wa Anty". Yana gama zancen ya tashi ya ɗauki wayarsa da wasu makullan da suke kan teburin da yake gabansa ya zuba a cikin aljihunsa ya fita, ni ma tashi na yi na fita sanda na fito na gan shi har ya shiga motarsa Baba mai gadi ya buɗe masa gate zai fita na bi motar da kallo har sai da ya fice daidai lokacin da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 5️⃣3️⃣

Ji na yi kamar na koma cikin sashin na binciko dalilin kasancewar hoton Muhammad Taufik a cikin ɗakinsa, gabaɗaya na rasa gane kaina balle fahimtar abin da yake yi mini daɗi. Na tsaya cak a wajen ina ta karatun wasiƙan jaki da saƙa da warwara cikin raina. Kamar daga sama na ji saurar dirin sauti a cikin kunnuwana da ya tursasa mini ɗago idona Ina duban Baba Mai gadi.

"Ƴar nan lafiya? Tun ɗazu na hango ki kin fito kin tsaya a nan kin yi shuru. Ko dai akwai wani damuwar ne?". Na saki taƙaitaccen murmushin da iya kansa kan leɓena bai kar har cikin zuci ba.
"Lafiya ƙalau Baba. Yanzu ma wajenka nake son na je in ba ka wani aikin ka soma koya mini ƙananun kalmomin yaren". Ya yalwata annurin fuskarsa kafin ya furta"ai kuwa ba na komai ina dai zaune ne kawai". Yana dasa aya a zancen ya juya na bi shi a baya har zuwa bakin gate ɗin ya zauna akan wani benci yayin da na zauna a kusa da shi.

"To yanzu ta ina za mu fara?". Na duƙar da kaina ƙasa"ai Baba tun daga gaisuwa za a fara koya mini har a gangaro a zo kan ƙidaya da wasu kalmomin da suka kasance na amfanin kullum-kullum". Ya yi dara kafin ya ce"to kamata ya yi ki nema takarda da biro ina faɗa miki ki na rubutawa, tun da kin yi karatun zamani ai ko?".
Na riƙe haɓa"na yi amma ban yi nisa ba". Kafin ya ce da ni wani abun Altine ta iso wajen kamar mai shirin zuwa filin yaƙi ta ja ta tsaya a gabanmu hannunta riƙe da wani baho ƙiran ghana must go ƙarami.

"Amma kin san akwai aiki a cikin gidan kika zo nan kika tare ko?".

Cike da mamaki na ɗaga ido ina kallonta da ta haɗe girarta na sama da na ƙasa. Ta murtuƙe fuska kamar magribar ɗinya. A hankali na ce"na wanke har kwanukan da aka ci abinci fa kafin Hajiya ta ce na je sashin can na gyara....". Tun kafin na gama ta tari numfashina"don kin wanke kwanuka kuma sai

10 / 39