DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   33 / 39

96K to 99K   out of 116.4K words

taɓa sonka ba Saifullah, me yasa ba ka duba matsayina da na ka ba da suka yi hannun riga. Ƙwarya ta bi ƙwarya idan ta bi alwashi ai fashe wa za ta yi".
"Na ji na yarda ba za ki so ni, amma ni dai ki ba ni dama ki saurare ni".
Hannayena na saka na toshe kunnuwana da shi yayin da hawaye suke zuba daga idanuna kamar bakin indararo, ganin ba zan iya jimirin sauraron zantukansa da suke barazanar raba ni da nutsuwata ba, hakan ya tilasta mini juya wa na shige cikin gida da gudu.
Na ci karo da Anty Sawwama ta na fito wa daga banɗakin ina jin ta tana tambayata ko lafiya na shigo gida da kuka, amma ban iya amsa mata ba. Kai tsaye ɗakin kwanana na nufa na kwanta ina kuka, babu irin tambayoyin da ba ta yi mini ba amma na dage ina ce mata babu komai ba don ta yarda ba haka ta haƙura ta ƙyale ni.

Daren ranar ban iya runtsa wa sai da dare ta raba cikin baccin na ji ana ƙiran sunana na tashi na zauna ina ƙara kasa kunne na ji dai tabbas sunana ake ƙira a tsakar gidan. Zumbur na yi na miƙe ina murtsike idanuna na buɗe ƙofar ɗakin na fito waje inda nake jin sautin ƙiran yana tashi.
Ina fito wa na ga tsakar gidan ya yi haske sosai tamkar ba dare ba, na kai dubana inda nake ji sautin yana tashi idanuna suka sauƙa akan fuskan Hajiya Babba. Take ilahirin jikina ya soma rawa tamkar ana jona mini wutan lantarki na nuna da yar manuniyar yatsana bakina ya na rawa na ce"Hajiya Babba ke ce ki ka biyo ni nan?". Lu na ji na yi baya na zube a ƙasa yayin da kaina ya bugu da dutse, tun idanuna suna gano mini fuskarta dishi-dishi har sai da suka rufe gabaɗaya, daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba balle fahimtar abubuwan da suke wanzuwa.
[12/24, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 7️⃣8️⃣

A hankali na soma buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske kaina ya yi dum tamkar wacce aka yi wa ajiya dutse, hankalina yana dawowa jikina abin da ya faru ya dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan, take na zabure ina rafka salati tare da runtse idanuna da matuƙar ƙarfi ina ta batutuwa mara sa kan gado.
"Hajiya Babba me ye na yi miki za ki biyo ni har cikin gidan nan? A zamana da ke ko da wasa ban cutar da ke ba don Allah ke ma kar ki cutar da ni ko da kwantankwacin misƙala zarratin ne". Ji da na yi an dafo kafaɗana shi ya dawo da ni cikin hyayancina na buɗe runtsatstsun idanuna na kafe Anty Sawwama da su da take zaune kusa da ni, ganinta kusa da ni ya sani ƙanƙame ta a jikina tsaf ina zubar da hawaye tamkar an kunna burɗaɗɗan fanfo.
"Uwata ki nutsu ki kwantar da hankali, babu wani abun da zai faru face alkhairi da iznin Allah. Babu wanda ya isa ya cutar da ke duk abin da kika ga ya faru da ke to daman haka Allah ya ƙaddara zai faru". Luf na yi a jikinta ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin wahala, mun daɗe a haka kafin ta ɗago ni daga cikinta ta tambaye ni abin da yake faru na kwashe komai na sanar da ita, haƙiƙa na hangi tashin hankali da tsoro kwance a cikin ƙwayan idanunta sai dai ta dannan duk yanayin da take ciki.

A cikin daren ta ƙira Yaya Alhassan ya zo ta sanar da shi komai, ina kwance na ɗaura kaina akan cinyarta yayin da na lumshe idanuna tamkar mai bacci sai dai a farke nake don ina sauraron dukkan abin da suke tattaunawa.
Cike da tarin damuwan da yake tattare da furucin bakinta Anty Sawwama take faɗin"tsoro ɗaya kar wannan matar ta sabauta yarinyar nan, ina tsoron har ta juya mata hankalinta ko ma ta raba ta da shi gabaɗaya, don irin waɗannan matan ababen tsoro ne".
"Umma in sha Allah babu abin da ta isa ta yi wa Amatullah, gobe idan Allah ya kai mu zan je har can garin Jafarin mu yi ta ni da ita, in ta kama ma har ƴan sanda zan saka cikin lamarin". Anty Sawwama ta yi hanzarin taran numfashinsa"kar ka sake ka aikata wannan kuskuren Alhassan. Wani hujja kake da shi da za ka je har cikin gidan ka tunkare ta da wannan zancen? Ka san girman irin wannan lamarin kuwa? Hmm! Addu'a ita kaɗai ce mafita a gare mu". Shuru Yaya Alhassan ya yi har ta kai aya bai ce komai ba sai can ya ce"to yanzu Umma mene ne abin yi? Me ya kamata mu yi?". Ta saki sakakken ajiyar zuciyan da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta sama damar furta abin da yake kwance a ƙasan ranta.

"Ina tunanin idan Allah ya kai mu gobe mu ƙira Malamai su zo, a kewaye mana ƙur'ani a cikin gidan nan, sannan mu riƙi addu'o'i da azkar don shi ne kawai mafita".

Cike da gamsuwa ya ce"in sha Allah yadda kika ce Umma hakan za a yi, bari na je na kwanta Allah ya tashe mu lafiya".
"Amin". Ta amsa da shi da hakan ya ba shi damar tashi ya fita, ni kam dole ta sanya Anty Sawwama kwanan a nan tare da ni sa boda yadda duk bayan mintuna nake firgita har sai an riƙe ni. Washe gari da sassafe Yaya Alhassan ya nemo Malamai suka zo suka yi sauƙan alƙur'ani a cikin domin kariya da kuma fin ƙarfin duk wani aljanni ko iska har ma da wani mai mungun nufi, da mummunan ƙuduri. Kwana biyu na jera a jere ba na samun bacci duk da kuwa yadda aka zage da addu'a da roƙon Allah, Yaya Alhassan har yanka ya sa aka yi mini kafi lamarin ya lafa sai dai cikin ɗan kwanaki na rame sosai na fita daga cikin hayyacina.

A ranar wani labara ina kwance a ɗaki ina karanta littafin ƁOYAYYEN MANUFA, labarin zazzafan soyayyar Aishatu da Abdulhamid da ya karo da ƙaddarar da ta yi silar tarwatsa dukkan gini da tubalin da suka gina soyyayarsu a kai, Amir ya shigo ya kawo mini sabuwan waya ƙarama har da layi a cikinta, ya kuma shaida mini cewar Yaya Alhassan ne ya ce ya kawo min don ba son ina amfani da wannan wayar da na zo na ita ya kuma ce ma na ba ta ita. Ban yi musu ba na tashi na ɗauka wayar daman ko layi babu a cikin ta, memory ne kuma shi ma tunin na cire sa tun lokacin da Yaya Alhassan ya umarce ni da na goge wannan sautin muryar, na naɗe sa a cikin takarda na sanya a cikin jaka yayin na ɓoye sa a can ƙasan kayana.
Tare da shi muka fito falo ta juya wayar a hannuna yayin da nake ba shi saƙon godiya ya isarwa Yaya Alhassan kafin ya dawo gidan na yi masa na mussamman, turus muka yi ganin baƙi a cikin falon tare da Anty Sawwama. Muhammad Taufik ne tare da Saifullah da suke gaishe da Anty Sawwama ciki girmamawa ta na amsawa fuskarta kamar gonar auduga. Juya ciki na yi don ko mayafi babu a jikina na fito na zauna a bakin katifa yayin da na faɗa cakwakiyar tunanin dalilin zuwan su gidan a wannan lokacin.

Ban yi nisa cikin tunanin ba Amir ya ɗago labulen ɗakin fuskarsa a sake ya ce"ki fito ku gaisa".
Na murtuƙe fuskana"Mu gaisa kuma Yaya Amir? Ni fa ina tunanin lokaci ya yi da za du dakatar da mutanen nan daga zuwa cikin gidan nan". Jijjiga kansa ya yi yana ɗan murmushi ya ce"yanzu dai ki yi haƙuri ki fito ku gaisa". Ya na dasa aya a zancen ya saki labulen ya juya ya fita, ina ta ƙunƙunai na ɗauko hijabi na saka na fito falon lokacin da na fito na iske Anty Sawwama ma ta tashi daga cikin falon. Can gefe na zauna kaina a ƙasa na gaishe su suka haɗa baki wajen amsawa kafin shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe. Har sai da na ƙosa da zaman kafin na tsinkayo muryar Muhammad Taufik yana faɗin"Amatullah mun zo gaisuwa ne tare da neman iri, na san ba ki manta zancen da Saifullah ya zo miki da shi ba kwanakin baya ya sanar da ni cewar har yanzu ba ki ba shi amsa ba hasalima ba ki saurare shi ba. Ina mai tabbatar miki da cewar Saif mutumin kirki ne duk inda ake neman mutum na ƙwara to ya kai wannan matakin a iya tsawon zamana da shi ban taɓa jin ya buɗe baki ya furta yana son wata mace har ya yi burin aurenta ba sai ke, ke ce mace ta farko a cikin labarin rayuwarsa ke ce mace ta farko da ta fara karya alƙadarinsa. Don Allah ki ba shi dama ko da sau ɗaya ne ki ba shi damar ya yi yaƙi domin tabbatar miki da ƙarfin soyyaya da ƙaunar da yake gwada miki". Tun da ya soma zancen nake kallonsa da wutsiyar idanuna ina jin wani abu yana tasowa tun daga cikin zuciyata yana tokare mini ƙirjina.

Take! Ranar kuwa fara ganin lokacin zan tafi islamiyya ya soma dawo mini cikin kwanyata, na yi saurin tare da hawayen da suke shirin ɓalle mini.
"Mun yi tunanin ko akwai wanda kike magana da shi ko kuma an riga da an yi miki miji shi yasa ba ki saurare shi, amma yanzu da muka zuwa Anty da maganan ta tabbatar babu ko ɗaya, kuma ta ba shi damar ya nema amincewanki idan har kin amince shi kenan". Ban san dalili ba haka kawai tun ya ci gaba da maganan na ji hawayen da nake ta ƙoƙarin riƙe wa sun ɓalle suka fara kwaranya.

"Ka ga ne Sultan ba ri na je waje ba zan iya jure ganin zuban hawaye daga idanunta ba". Saif ya yi furucin cikin sanyin jiki da na murya bai jira amsar da zai ba shi ba ya tashi ya fita. Daga ni har Muhammad Taufik muka yi shuru na tsawon mintuna kafin can ya kawar da shurun ta hnayar cewa"Amatullah in dai ba ni damuwa kuma ba za ki takura ba. Don Allah ki ba wa Saifullah dama ina yaƙinin ba za ki taɓa yin dana sanin zaɓinsa ba, ba zai taɓa yin gangancin jefa ki a cikin wani halin da za ki yi tir da kasancewarki da shi a cikin inuwa ɗaya ba".

"Me yasa ka gaza fahimtar cewa ban dace da shi? Ba na so na gurɓata masa tarihi ta hanyar haɗa jini da shi. Na yarda aure bautar Ubangiji sai Allah bai kallabafawa Bawansa yin sa dole ba hasalima akwai hanyoyin neman aljanna bila adadin. Zan rayu kuma na tsayu akan hanyar bautar Allah da neman yardansa ba dole sai na yi aure ba".

"Ko da kuwa aure bai kasance dole ba amma shi ne cikar mutunci da kimar duk wata mace. Aure rufin asiri ne ga ƴaƴan mata, ko ba Saifullah ba ina tabbatar miki da in lokaci ya yi dole ne ki yi aure". A sanyaye ya ƙare zancen muryarsa har ta na riƙe wa, alamar akwai wani abun a ƙunshe a ƙasan zuciyarsa da yake ɓoye wa.
"Me yasa kake yin duk wannan ƙoƙarin akan kawai na amince da Abokinka?". Kamar jira yake yi na yi masa tambayar ya yi hanzarin ba ni amsa.
"Sa boda na tabbatar da soyayyar da yake yi miki babu yaudara a cikinta, kuma zai riƙe ki amana tare da ƙoƙarin faranta miki har ƙarshen rayuwarsa".

Na jinjina kaina tare da ƙarfin halin cilla ƙwayoyin idanuna cikin na sa kafin na furta"ka na nufin ke nan kai ba so na kake yi ba?". Babu shiri ya ɗago idanunsa da suke bayyanar da maɗaukakin mamaki ya kafe ni da su. Hakan ya ba ni ƙarfin gwiwan ci gaba da furzo da magana"kar ka musa abin da ya riga ya bayyana a cikin idanunka. Muhammad tun ranar da Allah ya haɗa mu kana so ka ce mini ba sona kake yi ba? Idan ba so na kake yi ba me yasa ka shigo rayuwata ka yi tsamo-tsamo a cikinta a wancan lokacin". Ya yi saurin katse mini hanzari"Amatullah ni ban so ki ba, na san dai tabbas akwai tausayinki da yake maƙale a ƙasan raina". Yana ƙare zancen ya miƙe tsaye ni ma na tashi na je na tsaya a gabansa.

"Ka kalla cikin idanuna Muhammad Taufik sai ka sanar da ni cewar ba ka taɓa jin soyayyata a cikin ranka ba, ta hakan ne kawai zan yarda da kai. Har na iya amincewa abokinka".

"Ya isa haka Amatullah ya isa mana". Ya yi zancen cikin wani iriyar sarƙarƙiyar amo mai bayyanar da tarin damuwar da yake tattare da shi, ya kai hannu ya shafo suman fuskarsa yana saki ajiyar zuciya mai nauyi.
"Na ji Amatullah a lokacin na ji soyayyarki a cikin raina, na ji a raina cewan zan iya rayuwa da ke a cikin ko wani hali kika tsinci kanki a cikinsa. Wannan dalilin ne ya sanya na dage tsayin daka wajen ganin na nemo ki har kin dawo cikin ƴan uwanki. Na yarda har yanzu akwai soyyayarki a cikin raina sai dai tun lokacin da Saifullah ya zo min da batun yana sonki tun daga lokacin na shiga ba wa zuciyata haƙuri, don ba zan iya gasa da Saif akan komai ba ko ya kuwa nake tsananin so da ƙaunar abun ya kai ƙololuwa. Zan iya sadaukar da komai akan Saifullah raina ne kawai ba zan iya zarewa na ba shi ba shi ma ɗin don ba ni da iko akan hakan ne".
Ya yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin ya matso dab da ni idanunsa akaina ya ci gaba da furzo da sirrin take taskace cikin tsokar zuciyarsa.

"Ba zan iya hana zuciyata son ki Amatullah har abada, kuma komai za ki yi ko ki zama hakan ba zai taɓa sanya soyayyar da nake yi miki ta sauya ba. Sai dai dole na danne abin da nake so don wanzuwar farin cikin aminina, zan taya sa yaƙin neman soyayyarki har sai na ga ya yi nasara. Sannan ina roƙonki don Allah kar ki fitar da wannan maganan, ina so yadda muka yi ta a nan mu burne ta a nan".
Yana dasa aya a zancen ya sa kai ya fice yana ɗan lumshe idanunsa da suka cika da ruwan ƙwalla, da ido na raka shi har ya fice daga cikin falon daidai sa'ilin fitarsa daidai lokacin da na durƙushe akan gwiwoyina ina jero wani kuka marar sauti.
Haka Anty Sawwama ta zo ta same ni ta ɗago ni daga inda nake durƙushe ta kwantar da ni a jikinta yayin da take shafa kaina cike da kulawa ta soma faɗin"Uwata ki daina wannan kukan ya isa haka, kuka ba ya magani da yana magani tabbas da yanzu ya kawar miki da dukkan matsalolinki. Kuka ba mafita ba ne sai dai ma ya haddasa miki wani ciwon kamata ya yi ki ɗaga hannu ki gode wa Allah da ya yi miki wannan suturan, har ya kawo miki mai sonki kuma ɗan gidan mutunci da nutsuwa. Ki yi istikara ki nema zaɓin Allah ya yi miki zaɓin da babu nadama, dana sani balle kuma cizon ɗan yatsa a cikinsa. In sha Allah ina ji a jikina rayuwarki ta kusa sauyawa farin ciki zai maye gurbin dukkan wasu baƙaƙen abubuwan da suka wakana a cikin rayuwarki".

Luf! Na kwantar da kaina a jikinta ina cikin gaba da sauraron tarin nasihan da take yi mini, a haka ina kwance a jikinta har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba. Dogon bacci na yi ban tashi ba sai can yamma lilis na tashi na yi wanka na zo na gabatar da salla a makare, na daɗe kan sallayan ina ta tunani kafin na tashi na fito waje na yi wasu ayyukan kana na soma kici-kicin ɗaura girkin dare. Sai dab sallan magrib na gama girkin na sauƙe tare da yin alwala na shiga ciki na yi salla, ban tashi daga inda na yi sallan ba na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi bisa ƙa'ida. Sai da na yi sallan isha'i kana na tashi na fito daga ɗakin lokacin har su Yaya Alhassan sun dawo, na zubo mana abinci tare da Anty Sawwama yayin da Yaya Alhassan, Amir da Umar suka ci nasu tare a kwano ɗaya kamar yadda al'adan gidan yake, bayan mun kama cin abincin na tattare kwanukan na je na wanke su ina doso ƙofan falon na ji Anty Sawwama tana sanar da Yaya Alhassan yadda suka yi da su Saifullah.
Kaina a ƙasa na shigo cikin falon na wuce ɗaki daidai lokacin da nake jiyo muryar Yaya Alhassan yana faɗin"tabbas kam mutumin kirki ne, sai ta ya ta da addu'a in shi ne alkhairi gare ta Allah ya tabbatar...". Bai ƙarisa zancen ba sakamakon wani tarin da ya sarƙafe shi ya fara yin sa tamkar zai shiɗe, da sauri na juyo na fita waje na je na ɗebo masa ruwa na miƙa masa.

Amsa ya yi ya ɗan sha kaɗan kafin tarin ya lafa muka haɗa ido da shi na ga ya yi hanzarin ɗauke na shi. Yana amsa sannun da Amir da Umar suka haɗe bakin wajen yi masa. Ya miƙe da hakan ya sa ni bin shi da kallo sai dai ko kaɗan ya ƙi yarda mu haɗa ido da shi, a taƙaice ya furta"Umma zan je na kwanta gabaɗaya ba na jin daɗin jikina". Bai jira amsar da za mu ba shi ba ya juya ya fice daga cikin falon, ya bar mu da tarin tambayoyi a ƙunshe a cikin ranmu. Ganin hawaye ya na ƙoƙarin ƙwace mini ya sanya ni na yi wuf na shige cikin ɗaki na zube akan katifa

33 / 39