Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Tknovels
son na sanar da ke wani abun da ba ki sani ba. Kamar yadda rayuwata take cikin hatsari haka ke ma ta ki rayuwar da ta ƴaƴanki take cikin hatsari sanadin yarda da amincin da kika ɗaura akan mutane guda biyu da kike ganin sun fi kowa kusanci da ke a cikin wannan duniyar".
Na ƙara taku uku na matso kusa da ita sosai da tun da na soma maganar take bi na da kallo cike da maɗaukakin mamaki da ya haɗu da al'ajabi. Kafin na yi magana ta ri ga ni.
"Wasu mutane biyu kike magana a kai?".
Na saki wani bushashshiyan dariyar da ba ta da alaƙa ta kusa ko ta nisa da nishaɗi kafin na furta"mutum na farko shi ne mijinki wanda a tsakanin gobe da jibi zai shigo cikin ƙasar nan ba tare da saninki ba, kuma ina da tabbacin har ya zo ya koma ba zai nema inda kike ke da ƴaƴanki ba. Sannan mutum na biyu ba kowa ba ne face Altine ƴar aikin da kika riƙe tamkar ƴar uwa kika busa mata iskar ƴancin yayin da ita kuma take amfani da yardar da kika yi mata take cutar da ke, ke da ƴaƴanki". Na ƙare zancen ina yi mata nuni da Altine da ƴar manuniyar ƴatsata.
Ban gama rufe bakina na ji sauƙar wani gigitaccen mari a bisa kuncina har sai da na soma ganin gilmawar baƙin duhu a cikin idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi da ƙyar na iya sarrafa kaina na tsaya akan ƙafafuna. Ta cakomo wuyar hijabina ta riƙe tamau.
"Ke har me ye kika sani akan mijina da za ki faɗa wannan maganar akan sa? Sannan yaushe kika zo cikin gidan nan da za ki gaya min wace ce Altine? Babu wani halinta wanda ban sani ba ta kai ta kawo ko ba ta furta magana da bakinta ba ina ya fahimtar abin da take nufin. Ina kika sama ƙwarin gwiwar nan?".
"Tabbas ban san mijinki amma a yanzu na san abubuwan da ke ma kanki ba ka sani ba game da halinsa. Idan ba ki yarda da abin da nake faɗa ba za ki iya samunsa ranar juma'a a babbn otel ɗin da ke cikin garin Abuja. Batun Altine kuma za ki iya tambayar ƴaƴan idan tsoro bai hana su faɗa ba".
Mamakin furucina ya sanya sakar mini hijabina da ta riƙe.
"Saifullah ka kawar min da yarinyar daga gabana, tun kafin zuciya ta ɗebe ni na lahanta ta na kashe banza na kashe wofi. Ba na son na buɗe idona na gan ta a gabana".
Sai a lokacin Saif ya yi magana da tun ɗazu yake tsaye a wajen yana bin mu da kallo ba tare da ya ce uffan ba.
"Anty don Allah ki kwantar da hankali, mu saurare abin da za ta ce wataƙila mu dace da wani ilmin da mu kanmu ba mu san shi ba".
"Saif babu wani mahalukin da zai tsaya a gabana ya sanar da ni wani hali na Saddam wanda zai Muhibba ban san shi ba, a cikin tsawon zaman da muka yi da shi. Balle kuma Altine duk ranar duniya take muke kwana mu tashi a cikin gidan nan, ka fitar min da yarinyar nan daga cikin gida".
Cikin in-i-na Altine ta ce"wallahi ƙarya ma take yi min ba ni da wani mummunan halin da na ke ɓoye miki shi".
Cikin ba da umarni Saif ya ce"Altine ɗauki su Aryan ki shiga ciki da su".
"To ranka ya daɗe". Ta amsa da shi cikin bin umarni da girmamawa, ta kwashe su Aryan suka yi cikin gida. Zai yi magana na tar numfashinsa.
"Zan fita ba sai ka fitar da ni ba, Hajiya ko ba ki ce da ni kar na ƙara zuwa cikin gidanki ba ni ma daman ina da niyyar sallamar kaina daga wannan aikin, sai dai ina mai ba ki shawara da ki nutsu ki yi nazarin abubuwan da na sanar dake yanzu. Ko ba daɗe ko ba jima watarana za ki neme ni ki kuma gode mini". Tas na ji ta kuma ɗauke ni da wani marin mai matuƙar sauti a karo na biyu.
Na kai hannuna na dafe kuncina ina cije leɓena sa boda zafin marin da ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina ya kuma raunana ƙarfin jiki da zuciyata.
"Na gode ranki ya daɗe, na gode bisa halin girma da karamcin da kika nuna mini". Ina dasa aya a nan na sunkuya na kwashe kuɗin da ta watsa mini don na san su ɗin haƙƙina, na raba biyu na ɗauki ɗaya na damƙa mata ɗayan.
"Na ɗauki iya haƙƙina ga ragowar dukiyarki".
Ban jira abin da za ta ce mini ba na fi tafiyata ina tafe hawaye duk yadda na so sarrafa kaina wajen ganin na tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga kurmin idanuna lamarin ya gagare ni. Na buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin zan fita muryar Baba Mai Gadi ta tilasta mini dakatawa.
"Ƴar nan kar ki tafi ba tare da kin warware min ƙullin zantukan da na ji ku na musayarsu ba. Shin da gaske ne abin da Altine ta faɗa akan ki? Da gaske ke ɗin karuwa ce kuma zaman kanki kike yi?".
Sai da ya yarce hawaye da suke tsare-tsare a kuncina kana na ce"e Baba duk abin da ka ji haka yake, zaman kaina nake yi a garin nan sannan a cikin gidan karuwai nake rayuwata". Ina gama faɗin haka na fice daga cikin gida fita irin wacce ba na fatan ko a cikin mafarki na dawo, fita irin wacce babu waiwaye har abada balle dawowa. Fita ita wacce take datse ko wani irin alaƙa da mu'amalar da aka ƙulla komai ƙarko da daɗewansa.
Sai da na yi nisa na nema ƙasan wani bishiya na zauna na ci kuka na yi kuka na zubda ƙwalla tamkar raina zai fita. Komai ya fita daga cikin kaina na rasa inda zan nufa na ji daɗi da sanyi a cikin raina. Duniyar da abubuwan da suke cikinta gabaɗayansu suka daina burge ni balle su ba ni sha'awa. Ba don ilmin addini da nake da shi wanda ya yi matuƙar tasiri a gare ni har yake bayyana kansa cikin aikina ba, da kuma hukunci da azabar da na san Ubangiji ya tanada ga duk Bawan da ya kashe kansa ba da babu abin da hana ni shan guba ko kuma na rataye kaina, na huta ba.
Zafin ranar da yake duka na shi ya tursasa mini tashi daga wajen ba domin na gaji da kukan da nake yi ɗin ba. A tashi na ci gaba da tafiya ina tafe ina haɗa hanya tamkar ƴar mayen ta sha abubuwan gusar da hankali ta bugu ta yi tatil.
Ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida ba domin na san inda kaina yake ba, balle ina nake cilla ƙafata a buɗe na tarar da ƙofar ɗakin da hakan ya tabbatar mini da cewar Sha'awanatu tana ciki, ina shiga na gan ta zaune tana latsa waya ta kuna kiɗa tamkar za ta ɗaga ɗakin, mu na haɗa ido da ita ta kashe kiɗa ta soma bi na da kallo har na je kwanta akan tabarmata. Na dafe kaina ina ta murtsukuku sa boda tsananin azabar ciwon kan da ya rufe ni lokaci guda ko buɗe idona ba na ƙaunar yi balle na ga haske, ina jin Sha'awanatu na tambayata ko lafiya na yi banza da ita ba tare da na tanka mata ba har ta yi ta gaji ta koma ta ci gaba da harkokinta.
A daddafe na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan zuhur ina shafa addu'ar da na yi na tsinkayo muryar Zinariya ta na faman ɗura ashariya a tsakar gidan, wanda ban zan da wanda take yi ba. Na yi wuf na tashi na fito daidai lokacin da ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga na bi bayanta, ta waigo tana kallona.
"Har kin dawo ke nan yau da wuri haka?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta saki ledodin siyayyar da ta yi a kasuwa suka faɗi ƙasa ta riƙo hannuna muka zauna.
"Kukan me ye kike yi Amatullah? Sanar da ni abin da yake faruwa?".
Ban yi ƙasa a gwiwa ba na kwashe duk abin da ya faru na sanar da ita. Sai dai ban fayyace mata cewar Hajiya Muhibbat ita ce matar Saddam wanda take yi wa take da Oganta ba.
"Kan bala'i bura uban can. Yau ina ga ni wani zallan rainin wayo da ɗiban albarka. Kuma ke sai kika tsaya kika zuba musu ido su na jifanki da waɗannan kalaman? Ai fito na fito za ki yi da su ki nuna musu ainihin kalar taki salon barikin. Na rantse sai na dira a cikin gidan matar nan tamkar sauƙar aradu na yi wasan kura da ita sai na nuna mata cewar lalle da ruwa ake dafa shayi kuma bakin rijiya bai kasance wajen wasan makaho ba, tashi mu je ki kai ni gidan". Ta yi zancen yayin da take miƙe wa tsaye.
"A'a Zinariya ba za a yi haka na ƙudurce a cikin raina cewar ba zan ƙara wuce wa ko da ta ƙofar gidan ba ne balle na shiga cikinsa. Na ri ga na yi musu bayannin komai".
A kufule ta ce"waya gaya miki yanzu bayani yana tasiri ga mutane? Ai duk yadda kika ƙware wajen iya tsara kalaman da gogewarki wajen furta su daki-daki, wasu mutanen ba sa fahimta sai kin haɗa musu da akuyanci a cikin lamarin. Ki yi wa girman Allah ki tashi mu je gidan matar nan na ƙaddamar mata".
Na tashi tsayi na riƙo hannunta"don Allah ki taushi zuciyarki ki yayyafa mata ruwan sanyi, mu bar maganar nan ta wuce. Na sanar da ke kawai don na ji sanyi a ciki raina ba don wani abun ba". Ba ta ce da ni komai ba illa zare hannunta da ta yi daga cikin na wa ta koma mazauninta ta zauna, ta yi ƙwafa kana ta ce"billahillazi don kawai zan yi tafiya ne shi yasa zan lafa bayan hakan ban dalilin da za ki ce kin bar wannan maganar ba".
Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya tare da faɗin"gobe za ki tafi Abujan ko?".
"Da sassafe ma kuma Ogana kuma jibi da yamma zai diro najeriya, a ƙalla za mu iya yin sati guda tare".
Na waro idanuna waje"kika ce hutun ƙarshen mako kawai za ku yi tare ki dawo?".
Ta yi fari da idanunta"e amma yanzu lissafin ta sauya kai tsaye ba zan iya ce miki ga ranar dawowa ta ba, sai dai ranar da Allah ya nufa kawai za ki ganni. Zan bar miki makulin ɗakina akwai ragowar kayan abinci ki yi amfani da su. Sannan don Allah ina son kafin na dawo ki sauya daga wannan Amatullah ɗin da take zaune a gabana yanzu, ina son duk wanda ya ɗaga miki ƴatsa ki tabbatar kafin ya sauƙe ta kin karya ɗan tsayan, kin ga harkar bariki fa babu wanda zai zo don ya taimake, ya kawo miki agaji ko kuma ya ƙwata miki haƙƙinki. Yaƙi ne da babu wanda zai tallafa miki ke za ki tashi ki yi wa kanki yaƙin neman ƴancin kai".
"In sha Allah ba zan dawwama a haka ba ni ma, dole akwai lokaci ya na zuwa wanda zan sauya".
Ta murmusawa"yauwa ƴar gari yanzu na ji batu". Daga haka ta ɗauki ledodin siyayyar da ta yi ta soma nuna mini, magungunan mata ne da na matsi birjik iya ganin mai gani. Daga na turare sai na tsuguna da na sha da kuma na ci da kaza. Ta sayo mini wasu dogayen riguna da mayafai ta ba ni, bakina har kunne na din ga doka mata godiya tamkar zan yi aron baki.
A nan ɗakinta na yi sallan isha'i muka ci abinci, ita take gulmata mini cewar Hajiya Babba ta tura La'aniyatu can ƙasar nijer wajen wata aminiyarta don a ba ta horo a kuma koyar da ita kwasa-kwasan bariki don a cewarta so take yi ta gaje ta ta ɗaura daga inda ta ja birki. Ba kaɗan ba lamarin ya taɓa ni tausayin La'aniyatu ya mamaye zuciyata ni shaida ce akan cewar ba ta ƙaunar irin rayuwar da mahaifiyata take yi, balle daidai da rana guda ta ji sha'awarsa a cikin ranta.
Ba ni na baro ɗakin Zinariya ba sai ƙarfe sha ɗaya dare, lokacin ta gama haɗa kayanta tsaf domin tafiyar gobe. Ta rako ni har ƙofar ɗakinmu muka yi sallama don ta tabbatar mini da cewar ƙarfe ukun dare za a zo ɗaukarta za su wuce garin Kano inda daga nan za ta kai jirgin safe da zai tashi daga cikin filin tashin jiragen sama na cikin jihar Kano zuwa garin Abuja, ta ɗauki makulin ɗakin ta damƙa mini na yi mata fatan sauƙa lafiya kana na shige ɗakin.
Washe gari da ƙyar na tashi sa boda daren jiya ban iya runtsawa da wuri, a makare na gabatar da sallan asubahi na zauna inda na yi sallan na yi shuru ina tunanin ta yadda ta fara gudanar da rayuwata a wannan gaɓar, sai dai kamar yadda Zinariya ta faɗa ne dole na tashi na yi yaƙin nema wa kaina ƴancin kai. Haka kuwa haka ba ta cika sati guda da tafiya ba sai da na zama babu wanda bai
sanni ba a kaf cikin gidan, hatta baƙin da suke zuwa san sunana ko da kuwa ba su taɓa ganin fuskata ba.
Na yi ƙaurin suna fiye da tunanin mai tunani ta yadda duk wani rashin mutunci da tijara na san farillai da sunnoninsu, har na kai munzalin da babu wanda yake rayuwa a cikin gidan da za a ƙira sunana ba tare da ya sha jinin jikinsa. Babu wanda ya isa ya nuna mini ɗan ƴatsa rashin mutuncin da nake yi ina sa yaƙinin ko Zinariya ce ta dawo ba za ta yi rabinsa.
Faɗa da jagwal babu wanda ba na shiga, rigima kuwa ko ba da ni ake yi ba zan shiga na amshe balle kuma da ni ake yi. Yo wani ma ya yi rawa balle ɗan makiɗi. Duk tijara da kwashe-kwashen Aminu sai da ya zubar da makamansa ya duƙa a gabana ya sara mini.
Har na kai lokacin da duk sa'ilin da aka kawo wata sabuwar yarinyar cikin gida waje na ake fara kawo ta na yi mata darasi. Sai dai duk barikin da nake bugawa babu wani na mijin da nake sake wa fuska balle na ba shi gangar jikina, haka nan duk shagalata ba na wasa da addini ko kaɗan du abin nake yi kuma a duk inda nake da na ji an yi ƙiran sallan zan bar abin da nake yi salla, haka nan azumin Litinin da alhamis ba ya taɓa wuce ni. Hakan nan ba a yin cikakkun kwanaki goma sha biyar ba tare da na sauƙe alƙur'ani ba, sadaka kuwa sai dai in ban sama taro da sisi ba.
Wasa-wasa sai da Zinariya ta ci satikai biyar cur ba ta dawo ba, tun abin ba ya damu na har ya soma damuna. A duk lokacin da zan ce Aminu ya ƙira mini layinta a kashe yake lamarin ya yi matuƙar ɗaga mini hankali da jefa ni cikin cakwakiyar tunanin an ya kuwa lafiya?.
[12/14, 12:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 6️⃣9️⃣
Haka nake kwana na tashi da tunanin halin da Zinariya take ciki, tabbas da na san garin Abuja ko kuma na taɓa zuwa cikinsa babu abin da zai hana ni tashi takanas na je neman Zinariya. Sai dai na ji an ce mini babban gari da ya tara manya da hamshaƙan mutane neman mutum a cikin irin wannan garin ba ƙaramin aiki ba ne.
Ina ƙwance a ɗaki ina ta saƙa da warwara a cikin raina yayin da wani sashin zuciyata yake hasko mini rayuwarta ta baya mussamman yadda muka rayu da Abba, ta tabbata a gare ni ba ni da wani masoyin da ya wuce shi haka nan babu wani wanda zai nuna mini ƙauna kwatankwacin irin wanda ya gwada mini. Murmushi kawai na yi ina jinjina kaina don izuwa yanzu a zo bijiren da zuciyata ta bushe ta zama tamkar dutse wajen dake wa, babu abin da yake sani fargaba balle tsoro ko kuma tausayi haka nan hawaye ba za zuba daga idanuna. Maimaikon lokacin da suka shuɗe da ba na sanin sa'ilin da suke cin gashin kansu.
Babu shiri na tashi daga kwanciyar da na yi sa boda hayaniyar da na ji yana tashi a tsakar gidan ana ta ruwan shariya tamkar dangin maguzawa. Diro wa na yi daga kan katifar Zinariya da nake kwance na bayyano waje.
"To ƴaƴan kaji dangin karnuka wani gurmin kuma aka haɗo da sanyin safiyar nan?". Na yi zancen yayin da nake iso wa inda na ga su a tsaye cirko-cirko tamkar sun haɗiyi taɓarma.
"Wai don tsabar iskanci da rainin wayon mutanen cikin gidan nan, na ɗaura girki daga na fito na shiga banɗaki na dawo na samu an sace tukunyar gabaɗaya, sa boda rashin ta kunya da tsiya. Wallahi a fito mini
Sabuwar yarinyar da aka kawo da na bi ya mata littafin sirrin zaman bariki babi-babi, kuma aka yi karati yarinyar kanta yana ɗauka uwa uba kuma a wayenta ta shigo harkar.
"Ke Kyawawa shi ne kika hargitsa gidan haka da sassafen nan? Ko da yake ban ga laifinki ba a ɗauke tukunya sukutum ai dole ki tada jijiyoyin wuya. Yarinya ci gaba da masifa har sai an fito miki da kayanki ai bala'i da masifa babu uwar wacce ta kashe".
Ina rufe bakina Aminu da shigowar sa ke nan ya amshe zancen"ina gaida uwar haɗa gurmi, yarinyar nan kin san kan tsiya kuma kin san wassulanta. Kin san har yanzu kaina ya ƙasa yarda cewar ki na da haddar alƙur'ani a cikin wannan kan nakin".
Na saki shewa har da tafa hannu kana na ce"ai kuwa ya kamata ka yarda don yadda nake murza wulaƙanci na tofar. Haka nake sarrafa ayoyin cin alƙur'ani yayin rera su". Ya kwashe da dariya mai sauti"Mahaddaciya ga sani