DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   35 / 39

102K to 105K   out of 116.4K words

bayan sallan magrib zai zo ya ɗauke ni mu koma gida.
"Matar mijinta ki na sha'aninki a cikin gidan nan". Na yi zancen cikin sigar zolaya yayin da nake cire hijabina. Murmushin ta yi kafin ta ce"duk da tun da kika shigo annuri bai gushe daga kan fuskarki ba, amma hakan bai hana ni fahimtar cewar akwai abin da kike ɓoye wa a cikin ranki ba, Amatullah shin akwai wata matsalar ne?". Numfashi mai nisan zango na ja na fesar daga bakina kafin na cira kai ina kallonta na ce"Amira ke ma kin sa matsaloli ai ba ya ƙare wa, in dai da rayuwa to tabbas akwai jarabawa". Ta shimfiɗa masa tabarma a waje muka zauna kana na kwashe komai na sanar da ni don na yarda abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa haka nan abokin cin mushe ba ya ɓoye masa wuƙa.

Ta jajanta mini sosai kafin ta ce"ni fa Amatullah ina ganin kamar ki amince masa kawai, inda gaske yake sonki ya zo a yi auren a wuce wajen. Don kin gan ni nan wallahi yanzu ba na goyan bayan dogon soyayyan nan da ake yi a waje da za a shafe shekaru ana buga wa, gwara a yi auren duk soyayya da kulawan da za a ba wa juna ku yi shi a cikin gidanku".
Bushashshiyan murmushi na saka da ba shi da alaƙa da nishaɗi kafin na yi ƙarfin halin faɗin" ba na jin zan iya soyayya a yanzu haka, sai dai zan amshe shi ne kawai don cikar wani burina wanda a yanzu shi kaɗai zai iya taimaka mini". Babu shiri ta waro idanunta"wani buri ke nan?".
"Me ye abin da tada hankali haka? Sanin kanki ne dai ba zan aikata abin da yake na haramci ba ko?". Kanta ta jinjina cikin sanyin jiki ta soma cewa"haka ne kam to Allah ya shige mana gaba".
"Amin ya Allah" Na amsa da shi yayin da muka ci gaba hirar mu cike da kewar rayuwar da muka yi a gaba da takaicin yadda rayuwa ta yi mana atishawan tsakin barkono. Mun ba wa juna shawara akan abubuwa da yawa na rayuwar yau da kullum.Tare muka wuni da Amira da hakan ya yi mini matuƙar daɗi har na manta da tari damuwar da nake cikinsa sai da aka yi sallan magrib kafin ƙiran Yaya Alhassan ya shigo cikin wayata na ɗaga ya shaida mini cewar yana ƙofar gida, na tashi na miƙe tsaye ina faɗin"kin ga ni kam bari na wuce Yaya Alhassan yana waje yana jira na".

Cikin rashin jin daɗi ta furta" ga shi har za ki tafi Mansur bai dawo ba, na so a ce ya zo ya same ki wallahi".
"Ba komai kar ki wani damu ai zan dawo wataran. Yarinya ta Mansur sai na tuna irin zumuɗin da kike a da idan ya ƙira ki ya ce miki yana hanyar zuwa gida, ranar walwala da farin cikinki na daban ne. Haka ranan in muka je talle za ki ta zuba masa kamar kyauta".
Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"rayuwa fa ke nan ga shi yanzu komai ya wuce har ya zama labari".

"Watarana mu ma haka za a tuna mu, a lokaci da muka gushe daga cikin duniyar".
"Allah ya yi mana mai kyau". Ta furta yayin da take ɗaukar hijabinta ta saka muka fito, a ƙofar gidan muka iske Yaya Alhassan take ya soma faɗan me yasa zan jawo Amira ta fito raka ni alhalin na san ita ta matar aure, sai da na ba shi haƙuri kafin ya saduda ya yi sanyi. Haka muka yi sallama da Amira ba don ranmu ya so ba muka tafi bayan na yi mata alƙawarin ƙara zuwa nan ba da jima wa ba.
Bayan mun koma gida har na yi shirin kwanciya na ji wayata ta soma ruri na yi caraf na ɗaga ƙiran tare da amsa sallamar da ya yi mini na ɗaura da faɗin"ko ba ka ƙira ni ba dama ina da burin ƙiranka yau".

"Ko dai sakamakon jiran da aka ce na yi za a sanar min? Yanzu na tashi na je na yi alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu na roƙi Allah ya ba ni juriyar ɗaukar duk irin amsan da zan ji ya fito daga bakinki".
Na ɗan lumshe idanuna kafin na buɗe ina faɗin"ba abin da kake tunani ba ne, daman ina son ganinka ne gobe akwai maganar da nake son mu tattaunawa da kai".
"Faɗa naki cika wa nawa. In sha Allah goben zan zo ni da wuri ma kuwa".

"Na gode Allah ya kai mu".
"Amin". Ya amsa da shi daga muka yi shuru dukkanmu sai can na ji ya ce"Aryan da Ayan su na tambayarki". Na yi firgitit na buɗe idanuna da na lumshe su"wai kana nufin har yanzu ba su manta da ni ba?".
"Ƙwarai kuwa don kusan kullum sai sun yi maganarki, tun bayan gano gaskiyan da muka yi game da Altine wanda hakan ya faru ne ta dalilinki. Amatullah kin zama silar bayyanar haske a cikin rayuwarmu kin cuce rayuwar su Ayan daga zalunci, cutarwa da kuma ha'incin da Atline ta daɗe tana aikatawa gare su ta ƙarƙashin ƙasa. Tabbas idan abubuwa ya daidaita ma Anty Muhibbat za ta zo da kanta ta yi miki godiya har gida sai dai a yanzu ta ce kunyarki take yi".

"Wani irin kunya ke nan?".

"Kunyan abubuwan da ta yi miki mana".
Na saki taƙaitaccen murmushin da ya tsaya iya kan leɓena kafin na ce"don Allah ka sanar da ita cewar tarin alkhairan ta gare ni sun shafe komai. Ta riƙe n bisa gaskiya da kuma zuciya ɗaya ba ta taɓa yi mini wani abun cutarwa ba don haka bai kamata ta ji kunyata ba". Da alama ya ji daɗin zantukan da na jero don ina jin yadda yake ta sauƙe ajiyan zuciya wani na bin wani.

"In sha Allah zan sanar da saƙonki a kumnuwanta".

"Amma da san da cewa ka na zuwa gidanmu?".
Cike da ƙwarin gwiwa ya mai do mini da amsa"ƙwarai kuwa hasalima ita ta ba ni ƙwarin gwiwan tunkaranki don ita ma kanta ta yaba da nutsuwa, hankali da kuma riƙon amananki". Lamau na yi tamkar mai bacci har sai da na ji ya ci gaba da maganan"amma ko zan iya sanin dalilin ƙiran da ake yi min na gaggawa kafin goben?".
"Me kake ci na ba ka na zuba? Allah dai kawai ya kai mu goben ko ma mene ne ai za ka ji".

"Haka ne kam".

Mun ɗan taɓa hira kafin muka yi sallama da wuri na kwanta, don ina so na tashi na yi sallan dare kamar yadda na saba. Washe gari ban sanar da kowa zancen zuwan Saifullah sai dai kawai ina zaune a ɗaki Anty Sawwama ta ɗago labulen ɗakin.
"Sai ki fito ki na baƙi". Gabaɗaya na manta da cewar mun yi magana da Saifullah mussamman da na ji ta ce baƙi maimakon ta ce baƙo.

"Wasu baƙi kuwa? Ba wasu baƙin da muka yi da su za su waje na yau".

"In ki ka fito ai za ki gan su, a nan ne za ki gane kin san da zuwansu ko akasin haka". Ta dasa aya a nan ta saki labulen ta yi ficewar ta, ta bar ni saƙa da warwara a cikin raina. Haka na tashi na saka hijabina na fito ina saka ƙafana a cikin falon Ayan da Aryan suka rugo da gudu har suna karo da juna suka rungume ƙafafuna. Tsugunawa na yi a gabansu ina shafa fuskokinsu don tabbas Allah ya jarabce ni da wani irin zafafan ƙaunar yaran wanda hakan ya samu asali daga soyayyar da nake yi wa duk wasu ƴan biyu musamman masu kama iri kwabo da kwabo ɗin nan.
"Yaushe ku ka zo?".

"Ba mu daɗe da zuwa ba, tare da Uncle Saif muka zo mu. Kuma Umminma ta ce in mun zo mu gaishe da ke sosai sosai". Aryan ya yi zancen har yana kwaikwayon muryar Umminsu.
"Ina amsa wa ni ma in kun koma ku ce ina gaishe ta". Kansu suka gyaɗa mini alamar sun ji da hakan ya sa ni tashi tsaye na riƙon hannunsu muka ƙarisa cikin falon, Yaya Alhassan ne da Umar sai kuma Anty Sawwama yayin da gefe guda kuma Saif ne zaune Muhammad Taufik yana kusa da shi suke ke nan a cikin falon. Sai da na zauna na gaishe su suka amsa take na ji tausayi da tunanin halin da Muhammad Taufik zai shirga bayan na aikata abin da zuciyata take ingiza ni na yi. A zahiri hankalina yana kan su Ayan da suke ta zuba mini suturu sai dai hankalina yana kan hirar da su Yaya Alhassan suke yi, har zuwa lokacin da Saif ya ce zai je ya kai Muhammad Taukif filin jirgi don jirgin ƙarfe goma sha ɗayan rana zai bi zuwa cikin Abuja.
Ya yi sallama da Anty Sawwama yayin take ta sa masa albarka da yi masa addu'ar Allah ya sauƙe shi lafiya.

A nutse muyarta can ƙasan maƙoshina na furta"Allah ya sauƙe ku lafiya mun gode da ziyara". Caraf idanuna suka sauƙa cikin na Muhammad Taukif, shi ya fara janye na sa idanun ya na amsa da kalmar Amir yayin da suke fice wa daga cikin falon.
Na kwashe su Ayan muka shige cikin ɗakin har muka fito na ɗaura girkin rana na gama na yi alwalan sallan zuhur na yi sallan, ina zaune kan sallayan yayin da su Ayan suke gefe na suka cin abincin da na saka musu. Na ji wayata ta soma ruri na yi hanzarin ɗauka tare da ɗaga ƙiran, maimakon amsa sallamar da na yi sai ji na yi an sauƙe ajiyar numfashi mai ƙarfin sauti.

"Ina ga dai matar nan kin manta da cewar ki na da baƙo ko?". Na dafe goshina kafin na ce"afuwan na ji tunanin ba ka dawo ba ne ai".
"Na dawo ina ƙofan gida ina jiranki za ki fito ne ko kuma na shigo?". Da sauri na ce"A'a ka tsaya a nan zan fito". Sai da na yi maganan sai kuma ni da kaina na ji kunya na katse ƙiran na tashi na je wajen ajiye kayana na ɗauko jakar da na sanya memory card ɗin nan a cikin na ɗauka.
"Ku zauna a nan ba ri yanzu na je na dawo kun ji".

"To". Suka haɗe baki wajen amsa wa da hakan ya ba ni damar fita, ban iske kowa a falo ba hakan ya ba ni salama da nutsuwar fice wa wajen kaina tsaye. Ina fitowa na hango shi tsaye a jikin motarsa yana latsa wayarsa. Da sallama ɗauke a bakina ya amsa mini yana ɗago kai tare da kafe ni da ido bayan ya mayar da wayan cikin aljihunsa.

"Ki bar Bawan Allah Saifullahi marayan Allah yana ta jiranki a cikin rana".

Na sadda kaina ƙasa"ai ka dawo da ka shigo ciki".
"Kayya! Wallahi kunyar Anty nake yi shi yasa kawai na tsaya a nan, yanzu dai ina sauraronki don jiya na kwana cikin zaƙuwa". Na ɗan tsagaita kafin na miƙa masa memory card ɗin da yake hannuna ya karɓa yana jujjuya shi a hannunsa.
"Wannan fa na mene ne?".

"Ina so idan ka je gida ka nutsu ka saurare abin da yake cikinsa da zaran ka gama saurara sai ka ƙira ni mu yi magana".

Shuru ya yi kallona kamar mai nazari ko kuma son gano wani abu, sai can ya ce"to shi ke nan ba matsala". Ya ƙare zancen yana cira wa a cikin aljihunsa.

"Yanzu za ku wuce ne?".

Ya waro idanununsa tar a kaina"to fa! Kora da hali ake yi mana ke nan? To shiga ki kwaso min su mu wuce". Kunya ya lulluɓe ni har sai da na rufe fuskana da tafukan hannayena.
"Ba fa haka nake nufi ba, na ga su Ayan abinci suke ci ne shi yasa na tambaya".

"Su sun sama karramawa ke nan tun da har girki aka yi musu. Saɓanin ni ɗan marayan Allah da aka shanya ni a tsakiyar rana aka manta da kashi na".

"Wallahi Yaya Saif ba haka ba ne ban san ka dawo ba ne.....". Ban ƙarisa zancen ba sa boda yadda ya tsare ni da idanunsa har sai da na ɗan tsorita na ce"lafiya kuwa?".
Ya ja dogon numfashi mai nisan zango kana ya furta"don Allah ƙara ƙiran sunan na ji, sai na ji kamar babu wanda ya kai ki iya furta sunan daidai. Ban taɓa jin an ƙira sunan da na ji daɗinsa irin haka ba, don Allah ki ƙara faɗa ko sau ɗaya ne".

Na ɗaga ido na saci kallonsa daidai lokacin da yake ƙara faɗin"Please mana".
"Cewa na yi Yaya Saif". Ina furtawa na juya da sauri na shige cikin gida muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana ƙoƙarin fitowa da mashin ɗinsa na yi saurin ja da baya na ba shi hanya yayin da kunya ya gama mamaye ni har na kasa ɗago idanuna, sai da ya gama fito da mashin ɗin na sama hanyar shiga ciki.
Na koma wajen su Ayan na iske su har sun gama cin abincin, ina zama ƙiran Saif ya shigo cikin wayata na ɗaga ƙiran na ba wa Aryan na ce ya yi magana.

Sai da suka gama na tambaye shi yadda suka yi ya shaida mini cewa ya yi in su gama su fito su tafi yana jiransu a waje. Kimtsa su na yi na kamo hannunsu muka je wajen Anty Sawwama suka yi mata sallama yayin da take musu leda taf da tarkacen abubuwa dangin su bushashshan kuɓewa, zogale, kanwa da kuwa yajin ƙuli ta ce su kai wa Umminsu. Har bakin ƙofa na rako su sai da na fitan su har suka isa wajensa kafin na jawo ƙofar na koma ciki.

Haka na ƙarar da wunin cikin tsinkewar zuciya da faɗuwan gaba. Bayan na yi sallan isha'i na ɗauko alƙur'ani na soma karantawa sai da na yi izu biyu daga suratul Naba'i zuwa suratul Nasi. Ban jin sha'awan cin komai hakan ya sa ni yin shirin kwanciya na kwanta ina ta saƙe-saƙe a cikin raina. Har bacci ya fara ɗauka ta na jiyo rurin wayata na zabura na tashi na ɗauko ta tare da ɗaga ƙiran don dama shi nake jira har bacci ya sace ni.

"Amatullah ina kika sama sautin muryan nan? Idan ban yi ƙarya ba fa muryanki ne me ya kai ki wajen mutumin nan? Me yasa kika naɗi sautin nan?".

Ko sallama bai yi mini ba illa jerin tambayoyin nan da ya soma jefo mini a jere wani na bin bayan wani.
"Ka tsaya na yi maka bayani". Na zancen cikin sanyi ganin yadda gabaɗaya lokaci guda ya birkice.
"Wani irin bayani za ki yi min Amatullah bayan abin da na saurara yanzu?. Tambaya ɗaya zan yi miki wanda nake so ki ba ni amsarsa shin da gaske wannan sautin muryan da na ji mallakin Sheik Dawood ne mahaifi ga aminina Muhammad Taufik ko kuma na ce Sultan?".
Cikin ƙwarin gwiwan da ban san ina da shi na furta"ƙwarai kuwa muryarsa ne, kuma duk abin da ya faɗa haka yake babu kuskure a cikinsa. Na ba ka ka saurara ne don ka ceto rayuwar abokinka da har kake ikirarin a zama amini kuma ɗan uwa a gare ka. Na ba ka saurara ne sa boda mu ceto rayuwar ƴaƴan matan da zai iya lalatawa rayuwa a nan gaba" .
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musibati. Ya Allah ta ina zan fara? Kin san yadda nake ganin girma da darajar Malam kuwa? Wallahil azim kallon uba nake yi masa haka nan shi ma ya ɗauke ni tamkar ɗan da ya haifa a cikinsa. Ina da tabbacin Sultan bai taɓa sanin cewa ba shi ya haife sa sa boda ya ba shi dukkanin kulawan da uba zai ba wa ɗansa". A sanyaye ya ƙare zancen cikin yanayin damuwa da ya haɗe da ruɗani.

"Dole ne kuwa sai na ji hakan ko ba daɗe ko ba jima. Ka fi ni sanin hanyar da ya dace ka sanar da shi wannan ɓoyayyan sirrin". Shuru ya yi na tsawon lokaci mai tsayi har sai da na yi zaton ko ƙiran ya katse ne sai da na duba na ga yana tafiya.
"Hello". Na yi furucin cikin sanyayyan amo.
"Amatullah". Ya ƙira sunana muryarsa ba ta fita sosai.

"Na'am Yaya Saif".

"Tabbas kin zo da babban lamarin da na ji kaina ya gaza ɗaukansa, zuciyata ta kasa yarda cewa Sheik ɗin da na sani ne ya rikiɗa ya zama wannan. Tabbas zan bayyana wannan sirrin ga Sultan sai dai ta ya ya kuma ta ina zan fara?".

Daga ni har shi muka yi shuru don ban san amsar da ta dace na ce da shi ba.
"Zan neman wani layin da bai san ni da shi ba na buɗe what's app da shi sai na tura masa, na tabbatar idan ya saurara ni ne mutum na farko da zai fara tunkara da matsalar daga nan sai mu warware matsalar a tare. Amma kai tsaye kam wallahi ba zan iya tunkararsa na sanar da shi cewar ina zargin Sheik da aikata wannan ɗanyen aikin ba". Shuru ina sauraronsa har ya gama ban iya cewa komai ba. Ina jin sa sai faman maimaita kalmar hasbunallahu wa ni'iman wakil yake yi kafin ya ce"amma me yasa kika zaɓi ni ki ka ba ni wannan memory card ɗin?".

"Ba ni na zaɓe ka zuciyata ce ta zaɓe a bisa wannan aiki don a wannan ɓangaren, tabbas ka sama yardanta".

"Amma da farko me ye kika yi niyyan aikatawa da sautin muryan da kika naɗa?".
Babu wani ɓoye-ɓoye balle nuƙu-nuƙu na fito ɓaro-ɓaro na sanar da shi komai har da yadda muka yi da Yaya Alhassan. Ya ɗan yi jim kafin can bayan lokaci mai tsayi ya ce"tabbas kin yi kyan da kai da ba ki bayyana wa duniya wannan sautin muryar ba, Sheikh babban mutum ne a idon jama'a kuma ko ba komai shi ɗin ubana ga ƴayansa, marayu har ma da masu uban. In sha Allah na yi miki alƙawarin shawon kan lamarin nan cikin ruwan sanyi har mu warware komai ba tare da kin shiga cikin wata matsala kamar yadda Alhassan yake tunani ba".
Ji na yi zuciyata

35 / 39