DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   12 / 39

33K to 36K   out of 116.4K words

da na yi mata godiya ba.
Ɗakina na wuce na tarar da ita har yanzu tana baccin ga sautin yana tashi sai dai amon bai kai na ɗazu tashi ba.
Na ayi sallan na zauna a wajen ba tare da na tashi har sai da na yi sallan asr kana na fara yin wani irin yunwa yana ƙwalulan hancin cikina, na jawo ledar kayan nan na gama da ragowar sauran lemukan. Sai a lokacin da hankalina ya dawo jikina na tuna da cewar haka na fito daga gidan ba tare da na sanar da Hajiya Muhibbat halin da nake ciki ba.

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina jin har yanzu kunnuwana sun yi mini wani dum tamkar wacce aka ɗurawa wuta a ciki. Na tuna marin da cin mutuncin da Altine ta yi mini take na ji raina yana soyiwa tamkar yadda ake soya gyaɗa marau-marau a cikin toka. Na ja dogon gashin na fesar daga bakina ina jin wani hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata tabbas na yarda rayuwa ba za ta yiyuwa a haka ba dole ni ma sai na tashi na soma nema wa kaina ƴanci, na fara tsaya wa kaina a cikin ko wani irin yanayi don tabbatar da zaman lafiya da jin daɗina.

Dafo kafaɗana da na ji an yi shi ya dawo sa ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, na ɗago kaina ina kallon La'aniyatu da take tsaye a kaina tana kallona.
"Ki zo Hajiya tana ƙiranki". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na bi ta a baya har zuwa cikin ɗakin Hajiyar ta shige cikin uwar ɗaka yayin da ni kuma na zube a falo ina na iske Hajiya Babba da kuma Aminu zaune. Cikin girmamawa na gaishe da su sai dai cikin su babu wanda ya tanka mini illa bi na da kallo suke yi kamar yau suka fara tozali da ni.

"Amatullah".

"Na'am ranki ya daɗe".

"Ɗaga idonki ki kalle ni da kyau kuma ki saurara abin da zan faɗa miki da kunnen basira". Na cira kaina a hankali ina kallon ta da hakan ya ba ta damar ci gaba da zancen da take yi.
"Gidan nan da kike gani ba wajen sauƙan baƙi ba ne. Gidana gidan gudanar da kasuwanci ne da za ki iya gudanar da su ko kina daga kwance akan katifarki, ba zai yiyuwa ki zauna ki miƙe ƙafa da sunan ki na fita aikin bautan da sai wata ya ƙare kafin a ba ki kuɗi ba, don waɗannan kuɗaɗen ba za su ishe ki ɗaukar ɗawainiyyar kanki ba ma balle har ki biya kuɗin hayan ɗakin da kike zaune a cikinsa har ki yi sauran buƙatunki. Ki kama sana'ar da ƴan matan gidan nan suke yi ko kuma ki shirya barin cikin gidan nan. Tun da kika zo cikin gidan nan ba ki sauya ba kullum jiya i yau ko takalmin takawa ba ki da fitacce balle kuma suturar kirki". Tun da ta fara yin maganan na ji zuffa ya jiƙa jikina sharaf ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau tara, daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin akuya ai kuwa tunin na soma sakin hawaye.

"Don Allah Hajiya ki taimake ni ki taimaki rayuwata ki yi mini rai, kar ki ce na bar cikin gidan nan. Don wallahi ban san inda zan cusa kaina ba inda na bar nan ki tausaya mini.......".Tun kafin na dire zancen ta dakatar da ni.
"Dakata ki ji ni yarinya nan gidan ba tausayi ko kuma jin ƙai nake yi ba, gidan na zo kin zo ne ki baje hajarki ki kwashe ƴan sulallanki. Ki yi hidimar kanki har ma ki yi kyauta ki yi sadaka, idan tausayi kike buƙata sai ki bari sai ranar juma'a ki tafi ƙofar babban masallaci na gidan mai martaba wataƙila ki yi dace ki sama masu taimaka miki bila adadin. Amma a cikin gidan nan dai kam jikinki ne da ƙoƙarinki zai ƙwace ki har ya yi miki riga da wando har da singileti". Ta juya tana kallon Aminu"daman ba ka sanar da ita dokoki da ƙa'idodin cikin gidan nan ba ne?".

"Aradu na sanar da ita komai in detail in ji ƴan boko. Ita ɗin ce akwai ta da daurin kai yadda kika san jinjirin haihuwar jaki, babu irin bayanin da ban yi mata ba amma kanta ya ƙi ɗauka ta dage akan ba za ta aikata zina ba. Na sanar da ita cewar akwai hanyoyi da yawa da za ta sama ƴan kuɗaɗenta ba ma tare da sun yi ido huɗu da na mijin ba amma ta ƙi amincewa".
Da alama bayyanin da Amimu ya yi mata ya taimaka wajen rura wutar takaicin halina da yake ci a cikin ranta.

"Zan ba ki zaɓi biyu wanda a ciki dole ki zaɓa ɗaya kafin nan zuwa ƙarfe goma sha biyun daren yau. Ko dai ki bi hanyar da ko wacce yarinya take bi ko kuma ki haɗa komatsanki ki setawa kanki hanya".

Gabaɗaya na ji jikina ya yi sany tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na kasa cewa komai na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin faɗin"Hajiya kafin wa'adin lokacin da kika ɗauka mini in sha Allah zan zo miki da abin da na yanke cikin zaɓin da kika ba ni".
"Da kuwa kin yi wa kanki adalci yarinya. Yadda kike da suran nan ai za ki ci abinci sosai a harkan nan".

"Amatullah ki nutsu ki yanke shawarar da za ta fishshe ki kar ki yi wa kanki baƙin ciki. Ki na da sura da dirin da ko wani ɗa na miji in ya ganki sai kin tafi da hankalinsa. Ke ɗin matar manya ce kalar shiga gaban mota irin matan da suke ba za taro su tashi kan kowa".

Galla masa harara na yi sa boda haushi da takaicin da kalamansa suka cusa mini na miƙe da nufin barin cikin ɗakin na ji ya furta"tabbas Allah ya yi halitta a nan wajen. Irin wannan zubin kamar kika zama surarki".
Ban tanka masa ba na fice daga ɗakin na faɗa cikin ɗakinmu na zube akan tabarman kwanciyata, duk yadda zuciyata take suya da raɗaɗi idanuna sun daina zubar da hawaye sai sa'ilin na yarda wani tashin hankali ya fi ƙarfin a yi masa kuka sai da kukan zuciya wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi.

Na yi shuru ina sauraran bugawan zuciyata da yake ɓat ɓat. Na koma sauƙe numfarfashi mai ɗumi ina lumshe idanun yayin da zantukan Hajiya Babba da na Aminu suka dawowa mini cikin kaina tiryan-tiryan.
Tabbas rayuwa za ta yi mini matuƙar wahala har ma sai na gwammace wataƙila gwara mutuwa akan rayuwa, sai dai duk rintsin da na yi wa kaina alƙawarin cewar ba zan ƙara aikata wani aikin zunubi da zai sanya Ubangiji ya yi fushi da ni ina cikin sani da hankalina ba. Sai dai in ban bi hanyar da suke so ba ina zan sama kuɗin da zan nema wa kaina matsuguni?.Na cire leɓena ina ci gaba da tunanin zucin da nake yi yayin da na sama salamar zubda da hawaye a daidai lokacin.

"To fa! Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ke kuma kukan me ye kike yi? Ai tun da kika sako ƙafarki kika shigo duniyar bariki duk daga lokacin za ki sabar wa zuciyarki dakiya, juriya da kuma shan duk irin yanayin da kika tsinci kanki. In ki ka ce kuka za ki dinga yi ina mai tabbatar miki da cewar sai an wayi gari watarana kin rasa hawayen da za ki tsiyayar, ni na fita sai kuma Allah ya yi dawowata zan je na kafa na tsare a bakin manyan ma'aikatu har sai na samu nawa rabon".

Na ɗaga kai ina bin ta da kallo ta shirya tsaf cikin shirgar ƙananan kayan da suka kama jikinta tamau kamar fatanta. Da wani uban gashin kantin da ta watsa wa kanta ta sha kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar tantance sarauniyar kyau.
"Ki yi rayuwarki na tawa babu ruwan biri da gada. Zaman kanki kike yi haka ni ma shi nake yi". Na mayar mata da zancen muryata a dake.

"To Allah ya kyauta".

"Amin". Na amsa da shi a taƙaice da hakan ya ba ta lasisin fita ta tafi gararambana. Haka na ci gaba da zama a haka har na tashi na yi fita na yi alwala na dawo cikin ɗakin na yi sallan magrib, ban tashi daga inda na yi sallan ba har sai da na yi sallan isha'i. Na bi kayan jikina da kallo tun da na zo garin jafari ban sauya wasu kayan ba, balle hijabi da takalmin da wannan mai gadin ya taimaka mini da su. Jikina ya soma rawa ina jin wani zafi yana ratsa wa har cikin naman jikina.

"Allah na tuba ka yafe mini sannan ka kawo mini ɗauki da mafita akan halin da nake ciki".

Na furta a bayyane yayin da nake miƙe wa tsaye na fita daga cikin ɗakin na nufi ɗakin Hajiya Babba tana zaune a falon tana irga wasu tulin kuɗaɗen da suke gabanta, na durƙusa na yi mata sannu ta amsa mini ba tare da ta kalle ni ba.
"Hajiya daman na zo na sanar da ke hukuncin da na yanke akan zaɓin da kika ba ni ne".

"Ina jinki".

Sai da na sauƙe wai gauron ajiyar zuciya kafin na furta"na amince zan bi hanyar da kuke so".
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 5️⃣5️⃣

Tun da na so zancen ta kafe ni da ido har na kai aya, cike da mamaki ta furta"abin da kike faɗa ɗin nan ya kai har cikin zuciyarki kuwa? Sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike ji da gani cikakkiyar ƴar bariki ce mai lasisi babu inda ƙafafuna ɗin nan ba su taka ba a cikin duniyar bariki. Duk wani salon munafukarci, luggu da nurƙufanci na san shi tare da alamominsa. Nan cikin gidan nan kwanakin baya wata yarinya ta zo simi-simi da ita kamar ba za a sanya mata hannu a baki ta ciza ba, mun sha fama da ita kafin ta bi layi mutumin farko da ta fara mu'amala da shi babban mutum ne don duk faɗin garin nan babu inda zan shiga ba a san sunansa ko an san shi a fuska ba. Rimi-rimi ya aiko aka ɗauke ta zuwa otel yarinyar nan ta burma masa wuƙa a cikinsa ta ji ajalinsa har lahira ta kwashe masa maƙudan kudaɗe ta tsallake boda, ta bar ni a cikin masifa da ha'ula'i aka yi mini rufgudu na yi trending a cikin garin nan. Da ƙyar aka same ta a can yankin sudan aka cafke ta kafin na sama salama, ke ma na lura wannan simi-simin da kike yi tsabar tsagwaron munafurci da iya ƙulla luggu".

Ilahirin jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin cikin rauni na furta"Hajiya har cikin raina na yanke wannan hukuncin". Ta ɗan yi jim tana bi na da kallo kafin can cikin wani irin dakakkiyar murya ta ce da ni"ke yarinya sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike gani wargi ce daidai ƙugun ko wacce ƴar bariki da take jin karanta ya kai tsaiko". A hankali na cira kai na sanya idanuna a cikin nata sai dai na kasa jurar jimirin haɗa ido da ita babu shiri na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran zancen da ta ɗaura da shi.
"Ina fatan abin da kika furta su kasance gaskiya don ina mai tabbatar miki da cewar duk abin da kika jangalo a kanki zai ƙare don duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Akwai sharruɗa da nake gindayawa duk wata yarinyar da take cikin gidan nan, duk wani namijin da kuka yi mu'amala da shi ina da kaso ɗaya cikin uku na abin da ya sallame ki ina fatan ki na saurarana?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar cewa"ki na da mutane a ƙasa ko kuma mu nema miki duk yadda kike da suran nan babu wanda zai gan ki ya ji ba ki burge shi ba balle har ya kau da kai".

"Babu wasu a ƙasa".

Na amsa mata muryata can ƙasa kamar an dannen kwaɓo a cikin ruwan zafi.
"To ku shirya da dare bayan misalin ƙarfe takwas za ki yi baƙo". Kaina kawai na jin wani irin abu yana tasowa tun daga ɗan yatsana yana bin dukkan sassan jikina, na tashi cikin rashin kuzari da ƙwarin jiki zan fita na ji an ƙira sunana da hakan ya tilasta mini tsaya wa ba tare da na waigo ba.

"Ke kuma La'aniyatu me ye ya fito da ke daga cikin ɗakin? Ke da kika ce ba ki da lafiya kanki yana yi miki ciwo".
"Umma ni fa na warke. Sai ki yi ta garƙame ni a ɗaki kamar wata ƙaramar yarinya kuma na daɗe da gane manufarki akan hakan. Harkar da kike jawo ƴaƴan wasu cikinta ne ni ba kya so na bi wannan layin, ai an ce duk abin da ka shuka Umma shi za ka girba". Tsam Hajiya Babba ta miƙe"ke La'aniyatu ki san irin maganan da za ki na furta domin ni ɗin uwarki ce. Kuma duk lalacewa ta ba za ki sauya ni a matsayin mahaifiyarki ba kamar yadda duk lalacewar tuwo ba a sauya masa suna".

"Ni ban ce zan sauya ki a matsayinki ba amma ina gaya miki abin da yake zahiri ne wanda ko ba ji ma ko ba daɗe ko kuma raye ko ba ma ciki rayayyu, babu makawa sai hakan ya faru....". Ba ta ƙarishe zancen ba Hajiya Babba ta zuga mata mari mai matuƙar sauri har sai da hancin cikina ya kaɗa.
"Tsinanniya wacce ba ta san haƙƙin uwa ba, in sha Allahu ke kam ba za ki gama da wannan duniyar salin ƙalin ba. Da ba a cikin ɗakin nan na haife ki ba sai na ce sauya min ke aka yi a asibiti, duk ƙoƙarin da nake yi wajen inganta rayuwarki da ganin ba ki nema komai kin rasa ba La'aniyatu ba kya gani?" Ta ƙarƙare zancen cikin sanyin amon.
Kasa motsawa na yi daga inda nake tsaye munanan kalaman Hajiya Babba suka jirkita mini tunanina, na tuna da Ummanta a lokacin da take jifa na da makamantan irin waɗannan kalaman wanda ina da yaƙinin su suka yi tasiri a kaina har na tsinci kai a cikin gidan karuwai da ƴan daudu. Ji na yi an ja hannun aka fizgo ni muka fice daga cikin ɗakin ba mu tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina. Na fizge hannuna daga cikin riƙon da ta yi mini.

"La'aniyatu me ye haka kike yi?".

A zafafe ta mayar min da tambaya"me ye kika ga na yi?". Na watsa mata wani kallo don ban taɓa raina wayo, hankali da hangen nisanta ba irin na yau.
"Hajiya fa mahaifiyarki ce ko me ye take aikatawa hakan ba shi zai ba ki damar da za ki na faɗa mata duk wani abun da ya zo bakinki, ba tare da kin tauna kalaman ba".

"Ni yanzu ba wannan ba shin da gaske kike za ki bi hanyar da suke so?".

Na harare ta da wutsiyar idanuna kafin na ce"ƙwarai kuwa". Ina dasa aya na wuce zan zauna ta jayo gefen hijabina.
"Me yasa za ki aminci bayan kin yi wa kanki alƙawarin ba za ki aikata ɓarna ba? Ke ma kenan za ki zama ba ki da bambamci da ragowar matan gidan nan? Kin san yadda suke yin wulaƙantaccen ƙarshe kuwa? Wasun su su kamo da jinyar da za ta yi ajalinsu, wasu shaye-shaye ya haukatar da su yayin da wasu kuma tsufa yake cim musu duk waɗanda suke mu'amala da shi su yi ɓatan gado su gudu ko sama ko ƙasa. Idan ba ki yi sa'a ba kuma har da kuzurin cuta za ta jajiɓowa kansu wasu kuma su haifa shegu waɗanda ba su da uba, haka rayuwarsu da ta yaran za ta faɗa garari su zama abin wulaƙantawa da tozarwa a tsakanin al'umma".

Na cire hannunta daga jikina na je na yi zamana ina cire hijabin da yake kaina"duk na san da hakan, me ye zan zauna na yi bayan ga abin da ya kawo ni nan ban yi shi ba. La'aniyatu duk matan cikin gidan nan ƙaryan bariki suke yi yanzu ne zan nuna musu ainihin abin da kalmar ta ƙunsa, domin zan warware musu zare da abawa. Ke dai kawai ki zuba mini ido ki kuma bi ni da fatan alkhairi".
"Mata da yawa da haka suke fara har su zarje su zama jan wuya. Amatullah ina jiye miki tsoron abin da kike shirin aikatawa zai haifar miki a nan gaba, kin ga muranen nan ba su da tausayi balle imami da zarar sun fara nannaɗa garɗin mace to ba sa barin ta haka banza wallahi har malamai da bokaye suna bi, don wasu ba a cin kuɗinsu a zauna lafiya".

Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce da ita"ni kuwa zan ci kuɗin kuma lafiya sumul".

"Amatullah".

Ta ƙira sunana cikin wani irin yanayi da ya fi kama da na zallan mamakin da ba sirka shi da komai. Na ɗage mata idona guda alamar lafiya? Ta zo ta zauna a kusa da ni tare da riƙo hannuna za ta yi magana na dakatar da ita.
"Ki zuba mini ido kawai na ce da ke, na fahimci wani abu guda cewar in dan har ba ka tashi ka nema wa kanka ƴanci ba haka za ka dawwama a cikin ƙasƙanci". Da alama mamaki da al'ajabi ne ya hana ta cewa komai illa kallon da take bi na da shi na sakar mata da murmushi ina miƙe wa tsaye ina ƙoƙarin mayar da hijabina na ce"bari ki ga na yi salla don ina da babban baƙo. Har ya zo ban gama kimtsa wa". Ba ta ce da ni uffan ba har na yi sallan na iddar na shafa dogon addu'ar da na yi, na waigo ina kallonta ta yi

12 / 39