DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Tknovels

Chapter   26 / 39

75K to 78K   out of 116.4K words

ido kamar zai cinye ni ɗanya kana ya ce"bayyanar ciki a tare da ke mana da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinki, sannan mahaifiyarki ta yi ikirarin ta sallamaki ga duniya ba ta buƙatar ƙara sanya ki a cikin idanunta. Wannnan dalilin ne ya sanya ki shigo harkar bariki gadan-gadan tun daga lokacin da na tabbatar da cewar kin bar gida kuma har cikin da yake jikinki ya zube tun daga sa'ilin na sauya akalar manufata akan ki don a tsarina ba na taɓa haɗa shimfiɗa da wacce wani ya taɓa kwantawa da ita ko da kuwa bisa tsautsayi ne balle wacce take da ƙarfin halin da bushewar zuciyar shigo wa bariki, a tarihin balaɗala sai yarinyar da ba ta san ko wani ɗa na miji ba nake mu'amala da ita sai kuma wacce ta ƙoshi da tarbiyya aka yi mata shaidar nutsuwa da kamala ni kuma na zo cikin daren guda na wargaza dukkan shiri da tanadin iyayenta akan ta na bar su su na cizon ɗan ƴatsa, watan har mun gama komai na yi cinikinta a kawo min ita ba za ta taɓa jin muryarta ba balle ta mu yi ido huɗu da ita sannan ba na amfani da komai wajen kawar da hankalinsu ko shaƙa musu abin da zai sa su fita daga hayyacinsu, ki na cikin hankalinki kuma ki na ji ki na gani za mu yi komai sai dai na ri ga da na rufe bakin kuma na goge komai na cikin ƙwalƙwalwar".

Jikina ya soma rawa tamkar mazari haƙwarana suka datse harshena wasu hawayen suka ciko kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar kwaranya, sai da na haɗo jarumta kafin na iya faɗin" wani buri daman kake da shi a kaina?".
Bai amsa mini ba illa dariyar da ya saka mai sauti ya na ƙoƙarin kai hannunsa jikina daga inda yake zaune na zame wa ina tashi tsaye na tsaya
"Burin da nake da shi akan kowacce yarinyar da na ƙyalla idanuna akanta".

"Wane ne Muhammad Taukif ake yi wa alaƙabi da Sultan, shin shi ɗin jininka?".
Ya ɗan yi jim yana ɗan bubbuga goshinsa a ƙoƙarin hana idanunsa rufe wa kafin ya furta"Sultan yaron kirki ne ba, shi ɗin jinina ne kuma ɗa miji ɗaya tal a gare ni tamkar rai, ina son shi har cikin raina musamman yadda na lura ya na hazaƙa da basira a bangarorin da suka shafi addininsa. Yaro ne mai nutsuwa da sanin ya kamata haka nan akwai shi da girmamawa duk wani wanda yake gaba da shi uwa uba ga tausayi da jin ƙai. Sai dai na ɓoye ainihin wane ne shi a gare a duniya mutane ƙalilan ne suka san hakan yayin da wasu suke ɗaukar sa a matsayin ɗan ɗan uwana, wasu ma su kan ce ma yaran nan ne kawai da nake taimakawa wajen inganta rayuwarsu. Sai dai shi ɗin ɗana ne jinina yake yawo a cikin jikinsa sai dai ba ta hanyar aure aka haife ba ma'ana shege ko kuma na ce ɗan gaba da fatiha".

Na waro idanuna waje cike da son tabbatar da sahihancin abin da kunnuwana suke ji yo mini. Cikin ruɗani na ce"shege kuma?". Kamar jira yake yi na yi tambayar ya yi caraf ya ba ni cikakken amsa"e shege don ba ta hanyar aure aka same shi ba sai dai wannan wani sirri ne da duk duniya babu wanda ya san shi cikin kuwa har da iyalina da shi kansa Sultan ɗin. Mahaifiyarsa ba musulma ba ce sai dai kin sa ko a cikin ƙabilan ma kawai masu tarbiyya da ilmin sanin addininsu, ƴar asalin ƙasar Ghana mun haɗu da ita lokacin da muka je gabatar da wa'azi muka keɓe ta ita a wannan lokacin Allahu Mulƙussamawati ya ƙaddara samuwar Sultan a cikin cikinta, bayan na dawo ƙasa Najeriya na sa a ci gaba da bibiyanta har zuwa lokacin da ta haihu ko da na ji ɗa na miji ta haifa sai na saka aka sato min shi ta ɓoyayyar hanyar da har abada ba za ta taɓa tunanin ni na yi wannan aikin ba. Na kai shi cikin gidan na damƙa sa a hannun mai ɗakina Hajiya Halima wanda a lokacin ita ta haihu amma yarinyar ba ta zo da rai da ba, ita ta shayar da shi ta kuma raine shi har ya zama mutum ta nuna masa ƙauna da kulawa don na ce da ita tsintar sa aka yi a cikin bola an yasar da shi shi ne dalilin da ya sa na ɗauke. Kusancin da yake da shi da ni da iyalina da kuma ƴancin da yake da shi a cikin gidan nan babu wanda za a gaya wa cewar ba ni na haife shi ba ya yarda".
Take jikina gabaɗaya ya soma rawa sa boda ban taɓa tunanin amsar da zai furta ba ke nan, tabbas sai yanzu na ƙara tabbatar da cewar sanin ainihin halin mutum sai Ubangijin da ya halicce sa, muryarsa ce ta dawo da ni cikin duniyar zahiri daga na tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa.

"Zo ki zauna a nan gefena mana ƴan mata". Rawan da jikina yake ya ƙara tsananta ba ni da wani mafita illa na yi abin da ya ce mussamman da na lura babu wani ƙarfi a jikinsa hatta maganar da yake yi ƙarfin hali ne kawai da taurin rai gami da kaifin da linzamin bakinsa yake da shi.
A hankali na soma tako wa ina ɗaga ƙafata har na iso inda yake zaune zan zauna ke nan ya damƙo tulin gashin kaina da na tufke shi ta bayan wuyana ya riƙe tamau tamkar zai cire su.

"Me ye kika sa min a cikin shayin da na sha?".

Ya jefa mini tambayar da ta haifar mini da rawan jiki da harbawan zuciya fiye da kima a kimiyyance. Na yi ƙarfin halin faɗin"ni babu abin da na saka maka, ka sakar mini gashina".
Ya riƙe mini gashi tamau har sai da na ji kaina kamar kaina zai faɗo ƙasa, duk jijiyoyin kaina na ci sun riƙe har sai da idanuna suka soma rufe ba, numfashi yana ta sama da ƙasa sai da ya yi yin sa ya hankaɗa ni gefe na faɗi sai a lokacin na samu na kwace kaina, na tashi na koma can ƙarshen ɗakin ina kallonsa, yayin da ya zame ya kwanta akan kujerar ƙafafunsa suna reto ya soma wani nauyayyen bacci da hakan ya haifar mini da sauƙe wasu wahalallun ajiyan zuciya masu nauyin gaske.

Na ɗan matso inda yake a tsorace na tabbatar da cewar ya yi nisa a baccin da ya yi. Na durƙushe akan gwiwoyina yayin da wani kuka mai ƙarfi yake kufɓe mini ji nake yi raina gabaɗaya yana tugunzuma, sai a lokacin na raruma wayar na kashe naɗar sautin da nake yi. Sosai nake kukan kamar raina zai fita daga cikin gangar jikina yayin da kalaman da Sheik suke yi mini amsa-kuwwa a cikin naƙurar naɗar sautina ji nake yi tamkar a lokacin yake furzo zantukan. Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi mini ajiyar dutsen dala ba gammo haka na kwana ina kuka wajajen ƙarfe uku da rabi na daren na ji an buɗo ƙofar ɗakin na yi zumbur na tashi tsaye.
Deeno ne da Zinariya suka shigo cikin ɗakin muna haɗa ido da ita na tafi da hanzarina na je na rumgume ta tsam a jikina ban san sa'ilin da wani kukan ya kuma ƙwace mini a karo na barkatai.

Ta ɗago ni daga jikinta ta na share mini hawayen fuskana"Ina fatan komai ya tafi yadda muka tsara ko?". Na gyaɗa mata kaina alamar e yayin da wasu hawayen suke ta ambaliya a bisa dandamalin fuskana. Ta riƙo hannuna muka tattare kayan da na shigo da shi muka mayar cikin jakar muka fice daga cikin ɗakin, na shiga banɗaki na wanko fuskana na zo na gyara ta na zauna akan hannun kujerar da yake kwance a kai na ɗan ranƙwafo kaina daidai fuskarsa Zinariya ta kafta mana hoto, sai da na sauya wurare aƙalla sau uku ta na ɗauka mana hoton kana muka fita daga cikin ɗakin. Sai da muka sauƙa ƙasa muka shiga wani ɗan madaidaicin ɗaki da ki rabin wancan bai kai a girma ba balle kuma a zo batun kayan alatun da suke jibge a cikinsa, muna shiga ciki na zube akan gadon tamkar wacce ba ta san ciwon jikinta ba na ci gaba da reron kukan.
Ɗaukar wayar Zinariya ta yi ta kunna sautin da na naɗa tana sauraro ita da Deen yayin da duk suka tattara hankulansu a wajen guda, ba su tsagaita ba har sai da suka saurara tsaf.

"Tabbas wannan abun babban lamari ne. Hakiƙa kin yi abin da ya dace a yaba miki". Deeno ya yi zancen cikin jinjin girman ƙoƙarin da na yi. Zinariya ta ɗago ni daga kwancen da nake na zauna kana ta zuba mini ido muryarta cike da rauni ta ce"Amatullah da gaske a rayuwarki ta baya kin taɓa zubar da ciki? Sannan baƙin cikinki ne ya yi sanadiyyar rayuwar mahaifinki? Mahaifiyarki kuma ta sallamaki ga duniya?". Ta watsa miji tambayoyin a dunƙule kuma a lokaci guda, sai da na ja dogon numfashi mai nisan zangon kafin na sama zarafin warware mata tsakanin zare da abawa, babu abin da na ɓoye mata game da gurɓataccen tarihin rayuwata na sanar da ita komai ba tare da na rufe wani abun ko na kwaskware shi ba.

Tun da na soma ba ta labarin take zubar da hawaye har na kai aya ina ƙarewa da faɗin"to yau dai kin sauraru tarihin rayuwata kin san wace ce ni...". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta rumgume ni duk mu biyu muka tuntsire da wani irin kuka mai matuƙar cin rai da azabtar da ruhi.
"Tabbas bakin uwa masifa ne ga ƴaƴanta abin da da yawa-yawan iyaye matan wannan zamanin ba su fahimta ba ke nan. Kaifin harshen Ummanki akan ki shi ne abin da yake bibiyar rayuwarki Amatullah, shi yasa ake ce wa DAFIN HARSHE ya zarce dafin maciji cutar wa da gurɓata duk wani abun da ya soma baki a ciki". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba sa boda nauyin da bakina ya yi mini, harshena ya cika mini bakina da hakan ya taka rawar ganin wajen hana maganata fita. Deeno ne ke ta ba mu haƙuri har muka tsagaita da kukan da muke yi lokacin har ƙarfe biyar ɗin asubahi ya yi har an fara haramar ƙiran sallan asubahi.

Na tashi na shiga cikin banɗakin da take cikin ɗakin na yi alwala na zo na gabatar da sallan a zaune sa boda gabaɗaya jikina babu ƙwari, ba na zato da tunanin ƙafafuna za su iya jure ɗaukar nauyin gangar jikina. Ko da na iddar da sallan na yi dogon addu'an kafin na tashi daga wajen lokacin kusan ƙarfe shida saura, muka fara haramar tafiya Deeno ya kawo mana face mask ya ce mu saka haka kuwa muka yi muka saka kafin muka fito muka yi sallama da Deeno muka hau adaidaita zuwa gida, tun da muka shiga ban ce komai ba illa lumshe idanuna da na yi ji na nake yi tamkar majinyanci don ba na iya aikawatar da komai.
Ko da muka iso gida sai da Zinariya ta taɓo kafaɗuna kafin na ankare da cewar mun iso na sauƙa, ta miƙa masa kuɗinsa ya ja napep ɗinsa ya bar wajen, Zinariya ta kallo ni tare da cewa"wannan damuwar duk na mene ne Amatullah? Na yi tunanin tun da yanzu kam kin cika burinki ai komai ya zo ƙarshe babu abin da ya dace da ke face farin ciki da kuma murna cikar muradinki".

"Ni ma kaina hakan na yi tsammani sai dai ban san dalilin da ya sa na tsinci kaina cikin wannan damuwar ba".

Cike da ƙarfafawa ta ce"mu shiga ciki ki huta, da yardan Allah yanzu kam komai ya zo ƙarshe". Ta riƙo hannuna muka shiga ciki kai tsaye ɗakinta muka nufo ta buɗe mana ƙofar muka shiga ciki, a nan ɗin ma kwanciya na yi na rufe jikina ruf sa boda yadda nake jin wani sanyi yana ratsa jini da gaɓoɓin jikina. Ina kwance na ji Zinariya na magana.

"Ki tashi mu je wajen Hajiya Babba ki yi mata wannan babban albishiri ɗin, ina da tabbacin ita da kanta ma sai ta sara miki balle kuma fadawan natan".

Furucinta ya tilasta mini yaye bangon da na lulluɓe har kaina da shi sai a lokacin na ga har rana ta fito ta dalle ko'ina da haskenta. Na yi miƙa haɗe da faɗin"wai har gari ya waye haka?".
"Tun yaushe kuwa, yanzu fa kusan ƙarfe goma ake nema ba". Na waro idanuna waje cike da mamaki na tashi daga kan katifar ta miƙo mini wayar na amsa muka nufi ɗakin Hajiya Babba tare.
Tana kishingiɗe muka iske ta muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin mu ce komai ta tare mu da faɗin"ina fatan dai ki na lissafin ragowar kwanakin da suka rage miki ko?"
Na kaɗa ina murmushi kana na furta"ai in sha Allah ma daga yanzu duk wani lissafi ya ƙare, yau na zo gabanki da cikakkun shaidun da za su tabbatar miki da cewar duk wani alwashin da na yi na cika sa tsaf". Na lallasa wayar na shiga fegin hotunan da muka yi na miƙa wayar ta sa hannu ta amsa tana kallo sai da ta kalle su tsaf kafin ta ce"amma ai satan ɗaukar hoton aka yi tun da gashi ma kwance yake yana bacci, aka yi hoton".

"Hajiya idan kin tuna a cikin yarjejeniyarmu ba ki gindaya mini sharaɗin cewar sai na farke zan yi hoto da shi ba, don haka ko yanzu aka tashi tabbas ni na ci wannan wasan". Ta ɗan yi shuru ta na ta ƙare wa hoton kallo kafin ta ce"wannan hoton anya kuwa ba haɗa wa aka yi ba?".

"Hajiya ki dai ƙara duba wa sa kyau". Zinariya ta ba ta amsa, wayarta ta ɗauka ta ƙira Aminu ta ce duk inda yake ya zo yanzu ta na son ganinsa, ya kuma amsa mata da cewar ga shi tafe daman ba nisa ya yi ba. Cikin ƙasa da mintuna ashirin ya bayyana a cikin ɗakin ta miƙa masa wayar ta na faɗin"karɓi ka duba hoton nan ka gane min haɗa wa aka yi ko kuma na gaske ne". Na amshi wayar yana kallon hoton tare da yin zooming ɗinsa ciki da waje, sai da ya gama ƙure basirarsa kafin ya ce"billahillazi Hajiya wannan hoton na gaske ne ba haɗa wa aka yi ba, sannan ba aikin AI ba ne wannan na'urar zamani mai ƙwaƙwalwar nan. Wannan hoton na gaske ne". Ya mayar da idanunsa kaina.
"Tabbas kin cika mai cika duk wata maganar da ta furta kin kuma cancanci a jinjina miki bisa wannan na mijin ƙoƙarin da kika yi, yanzu kam ai sai ki kama harka babu kama hannun yaro ko?".
Na ɗan murmusa kafin na ce"ina buƙatan lokaci na yi tunani akan hakan, kafin na fara aiwatar da komai".

"Duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe. Amatullahi mai abin mamaki ga sani fal ga kuma shagala". Duk mu ukun muka yi dariya ban da Hajiya Babba ta da murtuƙe fuskarta tamkar magribar ɗinya ta soma faɗin"akwai wasu maza biyu da suka zo neman ki jiya cikin gidan nan in taƙaice miki bayani a jiyan kawai sai da suka zo sau kusa biyar. Na shaida musu cewar ba za ki kwana a gida ba jiya ki na can otel don haka su dawo yau da misalin ƙarfe biyu na rana, don haka sai ki shirya tabar baƙi. Duk da ma dai na ga ba wani tsiyar ba ne a tare da su".

Ban kawo komai a cikin raina ba don na ɗauki zantukan natan kamar ƙidan shata don haka na ce"Allah ya kawo su lafiya ina nan ina jiran su". Da haka muka yi mata sallama muka koma ɗakinmu Zinariya ta yi mana girki muka ci na kwanta bayan na sha maganin zazzaɓi da na ciwon kai take bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba ni na tashi ba har sai da aka yi sallan zuhur, Zinariya ta tashe ni na yi salla bayan na iddar ta zo ta zauna da inda nake zaune.
"Yanzu me ya tsarinmu na gaba? A tunanin a waye ya dace mu turawa wannan sautin muryar da kuma hotunan nan?". Na ja dogon numfashi mai nauyi da sauti na fesar kafin na sama lasisin faɗin"tunanin da ni ma nake yi ke nan, amma zuciyata ta fi aminta da cewar mu nema lambar Muhammad Taufik mu tura masa sautin muryar. Hotunan kuma mu goge su tun da daman sa boda mu gamsar da Hajiya muka yi su". Ina rufe bakina Aminu ya ɗago labulen ɗakin ya shigo ya zauna duk muka bi shi da kallo.

"Ga can baƙinki fa sun iso, su na falon Hajiya su na jiranki".

"Wai daman da gaske ne an zo nema na? Ni kuwa waye na sane da zai taso takanas ya zo cikin gidan nemana?". Ya ɗage mini kafaɗarsa alamar shi ma ba shi da masaniya akan hakan.
"Ke kuwa ki tashi mana ki je ki ga su wane ne. Tun da an ce gani ya kori ji". Zinariya ta yi zancen da ya kama hankalina, ba cire hijabina da yake kaina da na yi sallan da shi ba na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba. Na bi takalaman maza da suke ƙofar ɗakin kafin na shiga ciki.

"Hajiya ga ni". Na furta ina daga tsaye tare da tsayar da ƙwayoyin idanuna akan ta.
Ta taɓe baki"ba ni nake nemanki ba. Baƙinki ne ga su can". Ta ƙare zancen tana yi muni nuni da samari biyu da suke zaune a cikin falon da sai a lokacin idanuna suka kai kansu.
Take numfashina ya ɗauke na wuce gadi sakamako tozali da na yi da mutanen da ba na tunanin sake ganin su a nan kusa a cikin rayuwata. Jikina ya na rawa tamkar mazari na nuna su da ƴar manuniyar ƴatsata.

"Yaya Alhassan da Amir ku

26 / 39