Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 34

24K to 27K   out of 101.2K words


Kusa da innawo ya zauna domin ya kula hankalin Innawo ya tashi sosai, dan tafadata
yayi, Innawo menene wai?, Naga duk kin damu ne.

Ba dole in damu ba Aliyu, bamu ankara ba har ka canza hali Aliyu, me zai kaika ka dauki
yariya mace budurwa kasata cikin dakin ka ka rufe kofa ka rufe window babu me ganin ku sai
Allah.

Wani irin kallo yai mata, Innawo wannan ce budurwa?, Aysha ai karama ce.

Himmmm Aliyu ka gyara tunanin ka, mace mace ce, ba iyayenta ba harni bazan amince da
haka ba, hakika nashiga tashin hankali, ga manya manyan 'yan mata can awaje me zakayi da
Ayaha dahar za'a ce maka ka rabu da ita ka kasa rabuwa da ita.

Innawo ki fahimceni, ni kina bani dariya idan kina nuna wai son ta nake, haba Innawo kallini
fa, babban yaro ne fa, Aysha fa ko nono bata dashi, me zanso a ita?, wlh karatu take so kuma
nasan bazaku bari ta dinga zuwa ba sabo da kakarta, niko ban tsoron kakarta.

Baka tsoron kakarta?, amman kasan duk wanda yaga wannan al'amarin zai kawo wani
tunani daban ko?

Innawo dan Allah kibar wannan mgnr, toh waini ce miki akayi dan iskane ni?, alkawari na
dauka zanbawa Aysha gudunmawata dari bisa dari akan karatun ta, kuma kome wani zaice
bazan janye ba daga abun da nai niya, Innawo ai daman mutum baka iya mishi, dan haka kawai
mutum yayi abun da yake ganin ya dace karya kula da me mutane zasu ce.
Zuwa wannan likacin innawo ta kasa mgn damin ta lura lamarin nashirin girmama, daker ta
iya fadin, " kenan Aysha zata cigaba da shigowa gidan nan, Kuma acikin dakin ka batare da
kowa ya sani ba??

Zanso ki ki rufe min wannan sirrin Innawo, ki yadda dani, wallahi daidai da rana daya banta
bataba ji cikin raina wai zanyi wani abu da ita ba, ina mata kallon kankanuwar yariya ce
yayayyiya, ina jinta acikin zuciyata kwatan kwacin yadda nakejin Husna, sai dai nashaku da ita
sosai fiye da Husna, ni kaina ina son yi mata karatun innawo.
Wani irin yawo Innawo ta hadiye sannan tace, Mahaifiyar ka bazata yadda da wannan
tsarin ba?

Karki gaya mata dan Allah"

Waigowa Innawo tayi ta kalle shi sannan tace shikenan.

****

Karfe 6 Aysha ta taso islamiya tun daga nesa ta hango motar Aliyu akofar gida, dan haka ta
labe wani zaure tare da kiran wani yaro, dan Allah kaje can gidan kace ana kiran Aliyu.

Juyawa yayi yayi Ayaha ta sake kiran sa idan an tambaye ka inji waye kace inji wani ne.

Tafiya yaron yayi ba jimawa sai gashi sun fito tare da Aliyu, lekawa tayi ta hango su dan
haka ta fito"

Tun daga nesa Aliyu ke murmushi, Aysha ma cikin jin kunyarsa take murmushin.

Karasowa yayi gabanta lallai ma yariyar nan kin rainani,towai kece har zaki tsaya kice akira
miki ni?

Dana sani nashigo???

Kishigo kimin me? ba dazon maka rabu ba?

Lumshe ido tayi sannan tace na dame ka ko?

Ni bance ba, amman dai kinsan yanzun gida ya dace ki isa ko?, ogogo ya kalla yazun za'a
kira mangariba kije gida.

Jikinta babu wani karfi ta wuce dan haka yace, nagode da kika leko na ganki.

Gani yayi ta juyo tayi mgn, tana kifkifta ido tare da jujuya bakinta, sai dai tayi nisa dashi
bayajin me take cewa dan haka ya zuba hannun sa cikin aljihu ya bi bayanta, tana gaba yana
binta abaya yake fadin.

Ni kike murgudawa baki?

Tana gaban sa da tazara tsakanin su sosai tace, ni ban murguda maka baki ba.

Takawa take cigaba dayi yayin da shima yake cigaba da takawa, yadda suke da tazara ko
mutum kusa dasu yake baya iya gane magana suke yace, " nagani ai, kenan kema kin iya
murguda baki.

Ya nifa ban murguda maka baki ba, ka koma kar wani ya ganmu.

A'a aike kika aika har gidan mu a kirani dan haka duk inda kika shiga saina biki"

Dariya tasa tare da dan juyowa ta kalleshi, yaya wallahi ka shiko gidan mu zaka hadu da
Umma.

Toh bake bace daga nace yanzun muka rabo kin hau fushi, da bakiyi dariya ba har ciki zan
biki.

Ton naiyi ai kaje kaji.

Korata kikeyi?

A'a tsoro nake kar wani ya gan mu.

Ko an gamu ai baza'a gane tare muke ba.

Eh amman nakusan shigewa gida in barka awaje.

Ba komai, ana aiken kine da daddare?

Wata rana dai ana aike na gurin idi sawu maganin sauro ko wanni abun.

Zaki fito anjima injira ki a wajen ?

Eh amman kuma ni idan ba'a aikoni ba fah?

Sai in koma gida inta kuka.

Dariya ta kuma yi tare da dan juyowa ta kalleshi toh ai bana wajen bare inyi dariya.

Lallai ma yariyar nan, wato har kukana ma idan inayi dariya zaki min?

Toh daman babba kamar ka yana kuka ne?

Yanayi mana, amman ni bazakiga kukana ba insha Allahu, danni bana kuka, amman
anjima idan baki fito ba zan kasa bacci.

Zanzo tafada adaidai lokacin data dafa kofar gidan su dare da fakan idon mutane ta
daga masa hannu cikin fara'a.

Da kansa ya amsa, tare da daga mata gira, tana shigewa gida shiko cigaba da tafiya yayi
saida yai nisa da gidan nasu sannan ya dawo ya nufi masallaci.

******

Da daddare kamar yadda Aliyu yace ya Isa gurin idi me shago Ana fitowa sallan Isha,'i saidai
har ya karaci zaman sa Aysha bata fito ba, dan haka ya nufi gida, tashi yayi ya nufi gida cikin
sanyin jiki sosai domin ba haka ransa yaso ba, Koda ya kwanta gadon sa yata tuna Aysha yana
dariya daga can bacci me nauyi ya dauke shi.

Misalin karfe 03:15pm, Aliyu ne kwance bakin katifar sa, runtse idon sa yayi da karfi
ayanzun jiran zuwanta kawai yake yi, zuwa can yaji ana kwankwasa kofar ahankali.

Sakowa yayi ya Isa ya leka window Aisha ce dawowa yayi ya bude kofar ya leka ya mata
nuni da tashigo sannan suka shiga dakin tare da maida kofar ya rufe.

Ina wuni Yaya Aliyu?

Lafiya Lau, ya fada tare da mika masa hannu ta bashi litrafinta.

Littafin ta fito dashi sannan ta mika masa cikin daure fuska ya amasa.

Satan kallon idon sa take yadda yake daure fuska saita tunashi acan da kafin ya fara

sakar mata fuska.

Karutun yake mata, Amman kwata kwata hankalinta baya gun karatun tunanin ta kawai
be wuce tasan me yake damun sa ba dan haka ahankali tace, ' yau baka da lafiya ne?

Lafiya ta Lau, bacci ne kawai ban samu ba jiya, kaina ciwo yake min.

Littafin ta mika hannunta ta dauka ta maida cikin jaka adaidai lokacin da yake cewa kawo
Mana.

A'a baka da lafiya gobe sai muyi,

Ki kawo nace.

Yaya ka bari gobe sai muyi.

Idan gobema na tashi da rashin lafiyar fa, ni haka nake idan banyi bacci ba saina kwana biyu
Banda lafiya.

Lumshe ido tayi sannan tace, jiya bakayi bacin bane?

Banyi ba ya bata amsa yana me kawar da kansa.

Yi hakuri, naso fitowa ba'a barni bane, amman yau insha Allahu zan fito.

Sakin ransa yayi kadan dan kaha Aysha ta sake cewa kayi hakuri kaji?

Naji, kawo littafin to.

Kabarshi sai gobe.

Komawa yayi ya kwanta saman katifar, yayin da Aysha take zaune kujerar dake gefen gadon
tana me karewa sumar kansa ido ahankali ta kira sunan sa, Yaya Aliyu?

Na'am indo.

Bakayin aski ne??

Dago kansa yayi yana kallonta tare da fadin, me kika gani?

Naga gashin ka yayi tsayo kamar na mace.

Murmushi yayi, macen da bata da gashi ko?, Inayi kawai yana saurin taruwa ne.

Sumar ta Kara kallo sannan tace, Yaya Aliyu?

Na'am indo, ya sake fada akaro na biyu.

Inma kitso?

Kitso kuma Ayaha?, Kin iya kitson ne?

Eh na iya.

Murmushi yayi bayan ya kalli fuskarta ya tabbatar da gaske take sannan yace yi min to.

Hannunta ta daura kansa tare da diban gashin kamar yadda makitsa keyi ta fara kitsawa.

Duk abun da take Sadiq najinta, aciki zuciyar sa yasan babu wani kitson da zata iya dan
haka ya barta ta masa din, yanajin yadda take ta cikuikuye masa gashi, ita ko Aysha yi take
tana cigaba da surutu yayin da yake amsa mata, saidai zuwa can taita magana tajishi shiru dan
haka ta leka fuskarsa, baccin sa yake merai da lafiya dan haka ta fashe da dariya wadda
dariyar ta tadashi.

Ke baki wuce ba.

Nagama maka kana bacci.

Tashi yayi zaune, tashi ki wuce gida, saukowa yayi ya leka tsakar gidan yana fadin, yi maza
insaki ta window Innawo da Ummi suna kitchen.

Takalmanta ta diba yayin da Aliyu ya dauketa cak ya zurata batare daya lekaba kamar yadda
yasaba kowacce rana.

Gaban sa ya yaji ya fadin adaidai lokacin da yaji muryar wata na fadin, Innalillahi wa inna
ilaihir raju'un, toh kuzo ku gani.

Jin wannan kalamin yayi matukar daga hankalin Aliyu, dan haka ya taho da sauri ya leka.

Wata mata ce take tafa hannuwa cikin tsabar mamaki da tashin hankali akan fuskar ta, yayin
da Ayaha ke rungume da jakar makarantar ta tare da takalmanta a kirjinta.

Innawo da Ummi ne suka karaso gurin yayin da matar ke fadin kunce bata shigo ba?, Gata
adaki. Katon namiji balagagge.

Ummi ce ta kalli Aliyu dake tsaye ta window, cikin tsananin mamaki ta juya ta kalli matar

tana fadin, " Murja daga Ina kikaga Ayaha ta fito?

Gashi kina gani kuwa ga wadda ya daukata nan cak daga cikin dakin ya dareta anan, akan
idona ba wani ne ya gaya min ba, nifa daman jiya da idona naga shigowan Ayaha gidan nan
Amman kukace bata shigoba sabo da da hadin bakin ku ake sata adaki.

Wani irin kallo Ummi taiwa Aliyu na tuhuma sannan tace, Aliyu kaika sako Aysha ta
window?

Fuskarsa daure sosai yace eh.

Eh?, Aliyu eh fa kace min?

Lumshe idon sa yayi cikin yanayin dake nuna beji dadi ba, yace Ummi karatu tazo"

Karatu?, Hannunta ta daga cikin zafin rai ta rafka masa mari wadda har saida yasa
hannunsa ya dafe.

Murja kuwa juyawa tayi ta fice agidan tabar Aysha tsaye agurin"

Innawo kuwa bata da bakin mgn, rasa abun yi yasa Ummi fashewa da kuka, cikin kukan take
zagin Aliyu mgn ta ciki bacin rai babu irin wadda bata fada masa ba.

Idon sa ne ya kada yai jawur, tare da fadin, Ummi tsaya kiji, amman Ina ta inda take shiga
batanan take fita ba, cikin wannan yanayin Umma da Murja suka samu Ummi, nan umma ta
shiga surfawa Aliyu zagi tare da fadin, ya lalata mata jika"

Idan hankalin Ummi da Innawo yakai dubu toh yau duk sun baci, cin mutunci sosai Umma
kewa Aliyu yayin da yake kallonta ido cikin ido tana me nuna shi da yatsa, wannan lokacin
Innawo hakuri ta shiga bawa Umma yayi da Umma ke ture Innawo tana zagin Aliyu.

Cikin wata irin murya me cike da karadi da hargowa yake kadawa Umma Hannu tare da
fadin karki Kara zagina ya isheki haka

Eh lallai, ke Murja kiga min dan iska mara mutunci, wadda besan darajan manya ba.

Juyowa Aliyu yayi afusace ya fito daga dakin, ganin barin sa dakin Innawo da Ummi sukayi
cikin gida aguje, ganin sa sukayi da masifar gudu ya fito daga kitchen dauke da bakin wuta ya
nufusu, tara tara suka masa daker suka samu suka rike shi yayin da Umma ke fadin, kubarshi
ya kawo dan uban shi.
Zafgegen itace ne ahannun sa, yayi da Ummi da Innawo suke kokarin kwacewa, duk yadda
suke son hakan ya gagara kokarin nufar Umma yake yayin da Umma ke tsalle tana surfa masa

zagi,

Daker Ummi da innawu suka tura Aliyu cikin daki suka maida kofar suka rufe.

Zuwa wannan lokacin jama'ar unguwa sun fara cika gidan, mutane ne tun daga ciki har
kofar gida, ganin yadda aketa gutsura mgnr ya dagawa Ummi hankali yasata daukan gyale
bashiri tabar gidan.

Innawo ko da mutanen unguwa daker suka fitar da Umma da iyalenta, har gida Innawo ta
bita tana me bata hakuri, hakama kwakota hakurin suke bawa Umma domin dai babu wadda ya
taba ganin abokin fadan Aliyu Kuma ba'a sanshi da wani mugun hali ba, asali ma be cika sakin
fuska ba, sai dai kowa yasan shi mutum ne meson yara, daker Umma ta lafa sannan suka baro
gidan, ganin yadda hankalin Innawo yake atashe mutane sukaita kokarin kwantar mata da
hankali, har cikin gida wata makociyarta ta rakata yayin da har wannan lokacin Aliyu na rufe
adaki.

Innawo ce atsakar gida tare da inna talatu makociyar su, inna talatu ce tace toh abudeshi
Mana.

Kofar falon Innawo ta kalla, a'a rabu dashi aciki, fadan karfin hali yake yi, mutumin da bashi
da gaskiya wai shi ke tada jijiyoyin wuya.

Ummi ce ta dawo ita da Alhaji Umar da wani yayanta Alhaji sani, ganin su Inna talatu ta
tashi ta fita.

9 / 34