Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
A tsakar gidan suka tsaya suna maida mgnr Ummi kuwa gefe ta koma tasa tagumi, bayan
Innawo ta gama musu bayani Alhaji Umar yace, " yanzun Ina Aliyu?"
Rufeshi mukayi tunda yaki sauraron kowa.
Mikewa mazan guda biyu sukayi suka bude kofar suna kallon yadda Aliyu ke huci"
Alhaji Umar ne yace sannu da karfin hali.
Sunkuyar da kanshi yayi kasa tare da gyara wuyan rigar sa.
Alhaji Sani ne yace wai toni abun dake daure min kai, karattun dole ne?, itama yariyar yar
iskace bata da tarbiya.
Ummi ce tace ai ni yanzun ma Aliyu shi babba me laifi, kwata kwata indo bata wuce shekara
14 , Ina za'a hada shi"
Alhaji Sani ne yace, au 14 aini na dauka ma ko budurwa ce.
Ina fa sa'ar Husna ce fah, nan suka shiga masa fada tare da Haddad masa bashi ba Aysha,
sosai suka masa fada tare da daura duk laifin akanshi, sannan suka wuce gidan su Aysha suka
Kara bada hakuri, yayin da Innawo da amsa da sharadi. Baruwan Aliyu da Ayaha.
Koda suka dawo gida, Sun Kara zaunar da Aliyu tare da gargadin sa sosai akan Aysha,
Ummi ko sabo da nuna tsananin bacin ran da tayi aka sashi ya bata hakuri.
Tuni unguwa ta dauka ko Ina labarin ake yayin da hakan ke Kara tada hankalin Ummi.
***
Har akayi kwana biyu da faruwan abun fuskar Aliyu bata dawo daidai ba hama fuskar Aysha
da kannen uwar ta suka taro suka zane, yau ta fara zuwa isalamiya, koda tazo wuce gidan su
Aliyu rage sauri tayi tana me kallon kofar gida.
Misalin karfe 6 Aliyu ne zaune saman motar sa akofar gidan su, tun daga nesa ya
hangota dan haka ya maida hankalin sa gareta, lokacin da tazo saitin shi murmumai daga nesa
yayin daya mayar mata, sannan yace.
An bigeki ranar?
Batare data tsaya ba tace, eh
Wace ta bigeki?
Sakkowa yayi yafara takawa abayanta"
Gaba dayan su saida suka dakeni.
Allah ya isa ya fada, sannan ya sake cewa, kwa biyu ban gankiba banajin dadi.
Nima haka.
Zaki fito anjima gun idi?
Kila, ta fada tare da hawa gadan gidan su.
Zan jira ki awajen ya fada tare da wuce gidan nasu.
08:00pm
Umma sauro sun hanani bacci baki da maganin sauro ne.
Buda cikin kwanon nan ki dauka.
Bude kwanon Aysha tayi bakomai aciki Umma.
Babu?, miko min ingani.
Mika mata tayi, ganin babu ta dauko kudi ta mikawa Aysha amsa maza kije ki sawo.................
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 15- 16
Agogon dake daure a hannun sa yake kalla tare da waigawa ya kalli kofar gidan su Aysha.
Har cikin ransa yake son ganin ta, yayi da ya kafe gidan nasu da ido yana daga karkashin
wata katuwar fishiya gefen shagon idi cikin duhu.
Akan idon sa ta fito daga cikin gida, murmushi yayi wadda yasa zuciyarsa yin fari Kar
sannan ya zuba mata ido harta karaso gaban shagon idi"
Hasken fitulun unguwar ne ya haske fuskar Ayaha, itako har ta Isa shagon idi raba idon take
yayin da yaita murmushi.
Ganin harta amsa maganin sauro din tana ta waigen bayanta yasashi tausasa murya tare
da mata dan Kira, Indo!!!
Cikin sauri ta kalli cikin duhun tare da dan karasawa gurin ta dan tsaya nesa dashi,yaya
Kaine anan?
Eh shigo mana Indo"
Nidai gaskiya ka fito sarari.
Murmushi yayi kadan, kina nufin nan asako nake?
A'a kam Yaya, amman duk fadin layin nan mu rasa inda zamu zauna sai a mattarar aljanu"
Dariya yayi har ya fitar da sauti sannan yace, kice tsoro gareki kenan?
Nidai banson bishiya.
Waigawa ya fara yi to Ina zamu tsaya nan yafi sirri ai"
Nidai ka fito nan gurin.
Takowa ya farayi hannun sa cikin aljihun sa yana me binta da kallo, Yaya akayi kika fito?
Wayau nama Umma, cemata nayi sauro ya hanani bacci.
Ke!!! nine sauro?
Cikin matsancin murmushi tace, " Kai!! Yaya ta yaya zance maka sauro?
To danwa kika fito?
Dan kai.
Kinga kenan nine sauro.
A'a Yaya kafi karfin sauro, ni kawai wayau nayi dan in fito.
Toh naji me wayau, yanzun Ina kudina kodan ban miki karatu kwana biyu ba shikenan
bazaki bani ba wannan karon?
Cikin dariya sosai tace wlh yaya kacika son kudi.
Kinga laifina?
Tana dariya tace a'a.
To gaya min Ina kudina, suna jakata Ina Tara maka ai.
Toh kin kauta, yanzun ki koma gida sai gobe ko?
Kaita daga alamar eh.
Hannunsa dake cikin aljihun ya murza sannan ya fito da kudi ya mika mata.
Yaya daman kana da kudi ne?
Au kin dauka kasuwan da nake zuwa gantali ne kawai?
A'a Yaya ni bance ba, amman ni ka barso, yanzun fa ka gama tambayana kudi.
Eh naki nafiso.
Toh zan baka nawan wannan ma ka barshi.
A'a ya fada yana waigen layin tare da fadin kona sawo miki nama ne?
Itama?, waigawa tayi ta kalli me naman tare da fadin, ni banson Naman mutumin nan dama
dai me kuli ne.
Me kuli?, Hanyar ya kallah Ina zuwa to barin nemo miki me kulin.
Mikewa yayi yabi saman layin yayin da Aysha ta fara raba idon kar wani ya ganta, Aliyu
be wani jima ba ya dawo ya mika mata ledan sannan ta nufi gida.
Shima fitowa yayi yana me bin bayan ta bayan tahau gadan gidan su ya daga mata Hannu
itama ta daga masa.
Maida hankalin sa yayi kofar gidan su, yayin da ya hangi Innawo zaune kan takalin
dake kofar gidan.
Kallonta yayi sosai sannan ya karasa
Yana fadin Innawo me kike nan?
Karaso ta fada ahankali.
Karasawa yayi tare da zama gefenta, sai dai ya kula akwai damuwa akan fuskarta dan haka
yace Innawo meke damun ki ne.
Kallon shi tayi sosai sannan tace, Aliyu Kaine, Aliyu me kake nema ne gurin Aysha, yanzun
ranar nan yadda aka tara maka jama'a bakaji kunya ba? Abun da ya faro ranar ko yaro na goye
da yana da baki saiyace wani abu domin ko yagaji da Jin sunanka bakin uwarshi da ubanshi
wajen maida mgnr, kuma duk wadda yaji wannan lbrn dole saiya zarke ka, yanzun wannan
besa kai hankali ka rabu da Aysha ba, to yanzun daga Ina kuke??.
Zancen kauce kauce be taso ba, Aliyu ya fada azuciyar sa, afili kuwa cewa yayi, ni naje
wajen idine kawai muka hadu.
Kuka hadu Aliyyu?, Yanzun Aliyu bazaka guji wani abu ya sake faruwa ba?, karka bari a
buga maka tanbari fah.
Innawo nifa, abun da wasu zasuce baya damuna fah, tunda nina San ba wani mugun abu
neke ba, Allah ma yasani, toh Innawo idan duk duniya zata dauka bani da kirki ni dan iskane
suje suyi tayi, ai zargi haramun ne, Kuma ni ba dan iska bane, ko Ina iskanci bazan tsaya a
jaririyar yariya kamar Aysha ba, taimakonta kawai nake ni.
Wanni irin kallo Innawo ta masa na tuhuma sannan tace Amman kuwa idan har haka kake
da kafiyan tsiya baka dauko abun arziki ba, Kuma matsawar baka rabu da itaba toni nabar bin
bayan ka, kuma zan gayawa uwarka domin baxan bari abun yai nisa ba, mikewa tayi ta shige
gida yayin daya bita da kallo.
****
Ganin duk suna bacci ta lallaba ta wuce bayan Umma ta kwanta, kusan minti 20 da
kwanciyarta sannan ta fara laluban namanta tana turawa abaki, tas ta cinye sannan ta saka
agadon tasha ruwa tare da fita tasa ledan abola tare da wanko hannunta ta koma dakin.
Washegari da Safe Umma ta fito ta nufin shara, gidan tashare tsaf sannan ta kwashe ta
nufi bola, ledan datagani saman bolan ne ranta be kwanta dashi ba dan haka ta dauko ta bude.
Nama me kuli ta hanga aciki guda biyu tare da yankan albasa, cike da mamaki ta juya ta
kalli dakin tare da kwalawa mamakira.
Fitowa mama tayi yayin da Umma tace, waye ne yaci nama da tsohon dare dan munafunci.
Nama?, Umma.
Nama kuwa gashi nan dan keta har zubarwa akayi, idan bake bace to yarki ce.
Jimmmm Mama tayi sannan ta fito tana leka takardan sannan ta kwalawa Aysha Kira"
Ganin takardan Naman jiya hannun mama gaban Aysha yai mugun faduwa.
Ina kika samu wannan Mama ta tambayeta.
Tsintan kanta tayi da fadin, idi me shago ne yabani.
Ke kiji masharraciyar yariya, ni Zaki rainawa hankali, shi idin me yaci bare yaba wani, duk
yadda akayi kin hadu da wannan dan iskan yaron, shine kawai duk nan duniya yake da wannan
karfin halin, dauka yake kamar shidin babu wadda yake shayi, kana masa mgn yana wani
rurrufe idon sa na rashin d'a'a.
Kallon tuhuma Mama tabi Aysha dashi sannan tace, fita kikayi da daddare??
Sunkuyar da kanta tayi Umma ce tace na sawo mata maganin sauro.
Zaro ido Umma tayi, nace ki sawo min maganin sauro koko ke kikace min sauro ya hanaki
bacci?
Ke kika aikeni, Aysha tafada batare data kalli inda Umma take ba.
Cikin tsabar mamaki Umma tace, eh lallai Aysha baki da kirki, zuciyarki bata dakyau Sam,
Kuma idan ba da gaske aka miki ba mgn Zaki dauko mana akwai alamun hakan.
Mama dakin ta dawo yayin da Aysha ta zauna abakin gado cikin tagumi.
Itama mama cikin damuwa tace, " Jiya kinje gurin Aliyun ne?"
Nifa Idi ne fa ya rage daidai naje Sayan maganin sauron ya miko min.
Shikenan Mama ta fada sannan ta juya ta fita tsakar gida, yanajin tashin hirarsu sai dai
bayajin me suke cewa.
*****
Indai nice uwarka dana tsuguna na haifeka toh nagaya maka ka rabo da Aysha, wai wanni irin
masifane haka, me kake nema wajenta Aliyu?, aita mgn daya ko kunya bakaji, wlh bantaba
maka shedan rashinji ba, Kuma bantaba tunanin haka daga gareka ba, nasanka dai da fushi
kamar kuturo amman baka da rashin ji sai wannan karon, ni daga gau bazan sake maka mgn
akan Aysha ba, Amman kasani, nafada Kuma zan Kara fada maka ayau, tunda nake a duniya
bantabajin natsana wani mutum ba kamar yadda na tsana Aysha, Aysha karamar yariya ce
amman tanada naci, tun tana zuwa karatu yanzun gashi wai har Kai kebinta kofar gidan su, duk
da irin kashedin da aka maka. Ninayi Innawo tayi, su Yaya ba irin mgnr da basu makaba rana
duk akan ka rabu da ita amman Ina, to yau nace maka indai nice uwarka ban amince ko sake
kallon Aysha ba bare har kayi mgn da ita.
Jikin sa amatukar sanyaye yace shikenan naji, kiyi hakuri.
Dauke idonta tayi yayin daya mike yana ma Innawo wani irin kallo.
*****
Misalin 8:30pm Aliyu ne ke juyi kan gadon sa, duk cikin son hana kansa fita, fuskar Aysha
yake tunanawa tana wannan dariyar tata dake sashi nishadi.
Tashi yayi ya zauna, har ga Allah yana son bin umarmin Ummi sai dai wani abun da yakeji
yanai masa yawo balakin son ganin Aysha yake yake dan haka ya Mike kawai ya fito hannun sa
cikin aljihun sa.
Yana dafda fita falon Innawo ta fito tana fadin, " Ina zuwa?,
Gadina kike ne?, Wucewa yayi batare daya jira amsanta ba.
Kallo ta bishi dashi har ya kule ko tantama batayi gurin Aysha zashi dan ada daya
dawo sallah baya sake fita.
Wani irin yanayi ta shiga na damuwa ko Yaya karshen abun zai kasance oho, tunda Aliyu
ya fita har kusan minti 15 da fitansa Innawo ta kasa sukuni tashin hankali ne da damuwa me
tsanani cikin zuciyar Innawo.
Innawo!!!
Na'am Fatima.
Ina Aliyu, Ummi tafada alokacin data fito daga dakin Aliyun.
Cikin tsananin damuwa tare da takaici tace ya fita.
Jimmmm Ummi tayi zuwa can ta koma ta zauna tare da fadin, Innawo mun shiga uku, wani
irin al'amari ne wannan.
Waigowa Innawo tayi tana fadin, wlh kuwa tunanin da nake kenan, zance duk ya wade
unguwa amman shiko ajikin shi, Kuma ni abun dake daure min Kai ita yariyar ba aure ta Isa ba
bare ace sonta yake.
Innawo kibar wannan mgnr, ni yanzun