Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 34

36K to 39K   out of 101.2K words

Innawo tace toh Aliko
Allah ya tsare, wani irin kallo yaimata me kama da harara sannan ya kalli Ummin da dake kofar
gida tsaye yace Ummi zantafi , dan Allah ki yafe min.

Cikin kawar dakai tace ni burina kazauna gurin babanka kawai.

Kad'a Kai yayi ya shige motar yayin da Innawo ke daga masa hannu saidai yaki mayar mata
saima dauke kansa da yayi.

Ta kofar gidansu Aysha suka wuce kallo yabi gidan dashi bayan sun wuce gidan ya maida
hankalin sa kan titi.

Abangaren Ummi kuwa tunda Aliyu ya wuce take share hawaye, badan tana ganin
hakan shine kadai mafita ba bazata iya rabowa dashi ba takaishi inda be saba ba, amman
hakan shine kadai mafita dan haka ta shiga damuwa sosai.

Koda Ayaha ta koma gida kuryan gado ta haye yayin da zazzabi me zafi ya rufeta, acikin
gidan su babu wadda yasan da tafiyan Aliyu dan haka babu wadda ya zargi komai.

*******

Aliyu acikin motar, Banda tafarfasa babu abun da zuciyarsa ke masa, adaidai wannan
lakacin yafi tuna Ummin sa fiye da kowa, acikin zuciyarsa yake fadin, yanxun shikenan nabaro
inda Ummi na take, yanzun shikenan a Nigeria zanyi rayuwa, kwalla ya cire tare da kallon
hanyar da suke ketawa.
Har dare ya raba suna sharar hanya yadda yaga rana haka yaga dare idonsa ko gezau ba
yayin da zuciyar sa ke tafarfasa.

Misalin karfe 10 :12am suka iso Kano Nigeria, fitowa yayi cikin tsananin gajiya da
zaman motar, wata motar ya sake dauka wadda zata dauke shi da kayan sa har kofar gidan
mahaifin sa, tafe suke yana kallon garin me cike da ababen hawa, kota Ina motocine tare da
mutane kota ina.
Sannu ahankali suka shigo cikin unguwar gidagene kake gani wannan na wane waccen
masu Dan Karen kau yayin da yake ganin wani gidan tamkar zanashi akayi.

Akofar wani tankasheshen gida yace yayi, tsayawa yayi kamar yadda Aliyu ya dakatar
dashi sannan ya sakko ya biyashi ya taya shi sauke kayan sa ya juya ya wuce.

Aliyu ne ya nufu babban gate din gidan ahankali ya shiga kwankwasawa, bugu biyu wani
dattijo ya taho ya bude masa.

Kurawa juna ido sukayi, tsayon lokaci sannan ya kauce ya bawa Aliyu hanya.

Wucewa Aliyu yayi ciki tare da barin kayansa waje ganin haka mutumin na ya Kira wasu
maza suka shigo da kayan harabar gidan sannan ya kalli Aliyu yace, toh bawan Allah Koda ban
sanka ba Naga kamarka da mai gidan, babu laifi asanarwa hajiya xuwan ka?

Daure fuska Aliyu yayi sosai sannan yasa hannun sa duk biyun cikin aljihu yana fadin, "
gaya mata"

Toh wa za'a ce mata?

Cikin kawar dakai yace Aliyu daga Cameroon.

Cikin sauri tsohon ya wuce ciki yayin da Aliyu ya kalli harabar gidan, filine sosai da aka
kawata shi da shuke shuke na zamani gwanin burgewa, daga can gefe ka wajen adana motoci
inda ya hange zafafan motocin guda 6 jere reras, dattijon ne ya maido da hankalin sa gareshi
da fadin.
Bismillah.

Akwatunan sa yaga anyi gaba dasu zuwa cikin gidan dan haka yabi bayan su.

'yan mata ne guda biyu suka nufusa aguje cikin fara'a.

Kara tamke fuskarsa yayi dan haka duk sukaje burki daga kokarin fadawa jikin sa suna
fadin, " Yaya Haydar sannu da zuwa"

Ahankali ya amsa da yauwa sannan ya karasa kujerar da ke kallon ta wata tattijowa dake
zaune yana gaidata cikin daure fuska.

Fuskarta asake babu laifi ta amsa tare da fadin ya Anya?, ya mamanka?

Alhamdulillah lillahi ya fada.

Kallon Yan matan tayi tace, Islam kiraka shi dakinsa ke Kuma Meenat ki Kai masa abinci.

Aliyu agaba Islam nabin sa abaya suna daf da Isa kofar dazata sadashi da dakin yace ke
koma.

Momy tace in rakaka dak......

Cikin tsawa yace banso.

Jikintane ya kama rawa daker ta iya mika masa key din tana fadin toh ga key din.

Amsa yayi sannan ya nufa kofar ya bude ya shiga, dakinsa ne dai wadda yasaba
sauka saidai yasha gyara fiye da baya da yake zuwa komai an canza ga manya manyan
hotunan sa kowanne kusurwa wadda alokacin be wuce shekara 18 ba.

Jakar bayan sa ya sauke kan gado sannan ya nufi toilet, yajima sannan ya fito yana tsane
gashin kansa sannun ahankali ya shiga gyara jikinsa, BAyan yasa kaya ya nufi wawakeken
gadon sa ya kwanta tare da lumshe ido.

Bude idon yayi yayin da hawaye suka gangaro masa yana me kewan Ummin sa tare da
tausayin Aisha. Su biyu ne tsaye cikin ransa Ummi sai Aysha.

Turo kofar Meent tayi da sallama abakinta tare da kayan abinci, tana kokarin mayar ta kofar
ta rufe yace, " ke koma"

Abinci ne Momy tace na kawo ma.....

Banci, fita maza kibani guri.

Juyawa tayi da matukar sauri, jikinta na zuba bari saboda tsawarsa me rugugi.

Juyawa Meenat tayi tanaita abincin kitchen sannan ta fito falon tana cewa, " Aunty Islam
abincin ma yace beci"

Momy ce tace, " ku rabu dashi, idan ubanshi ya dawo sa karata, ai kunsan halinsa
jarababben yaro ne, sai kubi ahankali idan ba hakaba duk saiyaji muku ciwo kafin ya tafi.

Meenat ce tace, niko da har murna nayi da zuwan shi amman yanzun du guiwata tai sanyi.

****

Misalin 5 na yamma Alhaji Bello ya dawo gida, Jin dirin motar sa Islam da Meenat suka shiga
rige rike fita ji kake rididiii sabo da yadda suke tika gudu"

Cikin sauri Aliyu dake kwance ya sauko ya nufi window yana son ganin dalilin guje gujen
nasu tare da iface iface"

Mahaifin sa ya gani tsaye yayin da Meenta tace Baffah albishin ka.

Bude baki yayi da nufin cewa goro Islam tai saurin cewa yayan mu Haydar yazo.

Cikin dan zaro ido Baffah yace SOJA?

Eh Islam ta fada yayin da Meenat tace wlh na rigaki fadi"

Yana matsancin murmushi yace toh ku kwantar da hankalin ku, yanzun dai tukuna SAJO
ya iso lafiya?

Lafiya Lau suka hada baki"

Yauwa to duk ku sakeni, yanzun barrin je inga SOJA sai kuzo kowacce ta fada abun da take
so.

Aliyu kuwa tunda yaga Baffah ne sukeyiwa wannan tsallen yaja tsaki sannan ya koma

ya kwanta rigingine tare da daukan sandan hannun sa ya kare idon sa dashi.

Cike da fara'a Baffah ya shigo dakin, tare da sallama abakin sa.

Kasa kasa Aliyu ya amsa yayin da Baffah ya iso dafdashi ya zauna.

Kallon yanayin sa kawai yayi ya gane kamar yana cikin damuwa.

Hankali yace, SOJA?

Batare daya bude idon sa ba yace sannu Baffah.

Hannu Baffah ya mika ya cire hannun Aliyu afuskarsa yayin da hawayen dayake tarewa
suka zobo.

Subuhanallahi, SOJA mene ke faruwa?

Wani hawayen ne ya sake zubo masa kamar an bude famfo daker yace, " Baffah Ummi ce
ta koro ni.

Lumshe ido Alhaji Bello yayi tare da fadin, " yayi kau, Ummin ka ta kauta min, dama kyawun
d'a gidan ubanshi.

Ganin har yanzun Aliyu na zubar da hawaye yace, " meka mata"?

Kasa mgn Aliyu yayi hawaye ne kawai kebi masa fuska wani na korar wani.

Hannu Baffah ya tura acikin gashin kan Aliyu, cikin sigan lallashi yace, kamin mgn
Mana, ko kana son in kira su Islam da Meenat suzo suga katon yayansu SOJA yana kuka?












*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

episode 22- 24


Cikin sauri ya girgiza kansa tare dasa hannun sa ya share hawayen sa

Inajin ka.

Bakomai Baffah

A'a, akwai SOJA.

Babu Baffah kawai tagaji da ganina ne.

Ba gaskiya bane Soja, duk yadda akayi Kaine baka da gaskiya.

Hawaye ne suka sake zubo masa yayin da mahaifin nasa yabishi da kallo tare da fadin, "
shikenan, koma dai menene bakomai, kai nawa ne, Ina tsananin farin ciki da zuwan ka, na dade
Ina jiran irin wannan ranar gashi ayau tazo min, tuni naso ka dawo nan amman amman aka
nuna min fin karfi, saigashi yau da taku ta hado ku ta koro min Kai, duk da haka naji dadi, Kaine
dan da nafara haifa dan haka nake alfari da kai. Hajiya ma kullum cikin mgnr ka take, kareke
mgnr yayi yana share ragowan kwalar dake idon Aliyu yana me cigaba da fadin kayi wanka?

Nayi.

Abinci fah?, Kaci?

Ni Baffah banjin yinwu.

Jimmm, Baffah yayi sannan yace zo muju to masallaci.

Mikewa Aliyu yayi ya nufi toilet, ya wanko fuskarsa tare da dauro alwala, shima Abba nan ya
shiga yayi alwala sannan suka fito.

Kusa da juna sukayi sallah yayin da Baffah yakejin tsananin farin ciki, a yau gashi ga
Haydar. bayan sunyi sallah isha'i gidan Hajiya suka wuce wato mahaifiyar Alhaji Bello, ganin
Aliyu sosai gidan ya dauki farin ciki musamnan da sukaji cewa gaba daya ya dawo, sosai Hajiya

ta shiga farin ciki, sai anan gidan Aliyu yasa wani abu acikin sa.

Sai misalin 10 na dare suka dawo gida afalon yabar Baffah ya nufi ciki.

Ahaji sai yanzun nake ganin ka?

Murmushi yayi kadan tare da fadin, kinsan dai inada bako yau, munje wajen Hajiya ta
ganshi takuma San da zuwan shi.

Amman Alhaji harka shigo gidan nan ka Kuma juya ka fita abinka, toh bakomai Nima nayi
farin ciki da zuwan shi, kannen sama sunata murna, amman na kula shi da d'aci yazo, kareke
mgnr tayi tana yatsuna fuska.

Sauke ajiyan zuciya yayi sanan yace, babu wani daci da yaxo dashi, kawai dai Ina
tunanin anbata mishi raine dan yace ma bazai koma ba.

Bazai koma ba?, anan zai zauna?

Eh, alhajin ya fada yana kawar dakai yayin da Momy tace ai shikenan, to karatun sa
fah"?

Anan zaiyi insha Allahu, kinsa nagaya miki yana da burin yazama Soja tun yana yaro uwar
ce bata so, insha Allahu yanzun zancika mishi burin sa, zan nuna masa kulawata wadda be
sameshi ba abaya ba.

Yayi kau Momy ta fada tare da Kara fadin yamaki cin abinci.

Eh, yaci gidan Hajiya.

Yayi kyau ta sake fadi tare da nufar dakinta cikin tarin takaici.

********

Tun washegari ranar Baffah ya fara nemawa Aliyu makaranta, domin yana ganin Aliyu yariga
daya girma, lokaci dada kurewa yake, sosai yai bakin cikin barin sa tun farko a Cameroon
domin danan yake tun farko da yanzun karatun sa yayi nisa. Yanzun Kashi kusan an bata lokaci
ne kawai. dan haka dole ya mike, cikin ikon Allah cikin sati biyu yasamu masa gurbin a babban
makarantar horaswa dake Kaduna, yayin da aka shiga shirye shiyen tafiya, watan Aliyu daya da
sati biyu ya wuce Kaduna, cikin rakiyar Baffah da kannen sa Meenat da Islam, wadda har yau
be saba dasu ba yaki sakin jikin sa dasu, Kuma har ya wuce makarantar baya baccin kirki
kullum tunanin Ummin da da Aysha shine makale cikin zuciyar sa.

******

Cameroon


Aysha ce zaune adakin Umma, zoben Aliyu ta dauko ta zura a babban ya tsarta ganin
yana shirin fadowa ta yamutsa fuska tare da fadin yaushe zan girma?, yau kwana ya Aliyu dari
biyu da sittin da bakwai amman har yau zoben nan bemin daidai ba� mikewa tayi ta nufi wata
jakar Umma, wani bakin zare ta dauko ta dawo ta zauna, warware zaren tafara tare da nadawa
zoben cikin kokarin yiwa zoben ciko, yi take tana gwadawa a babban yatsanta hartaga ya zauna
sosai sannan ta maida zaren.

Mikewa tayi ta fito ta hada wanke wanke, Umma dake zaune agefe ta kalli Mama tace,
kinga Aysha tunda Ali yabar kasar nan muka samu kanta, duk nukufarcin ta gama shi da wani
zazzabi zazzabi da wani zama shiru duk angamashi.

Mamace tace ai lokacin nan nafirgita sosai da lamarin su, ance ya koma can kenan bazai
dawo ba.

Kallon Ayaha Umma tayi tana fadin, aini iyayen sa sun biyani, dangin su sun burgeni da
suka korashi, su o'i Kuma dole asaki jiki.

Cike da haushi Aysha ta kalli Umma tace, ai yace idan zanyi aure hardai yasani zaizo��

Dariya Umma tayi sosai tana fadin, aifa sai zaizo din, Ashe ya janye soyayar tasa da yake
dake?

Cike da tsiwa Aysha tace to daman yace miki sona yake ne, ni betaba min irin wannan
mgnr ba, karatu kawai muke in dawo gida.

Karya kike muna fuka Umma tafada tana nuna Aysha da yatsarta.

Ji Ummar nan, wlh ni harma kinban haushi, yaya Aliyun ne zaice yana Sona? babba ne
fah, nikuma karama.

Mamace tace ke maza

13 / 34