Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
kansa yayi cikin sauri ya nufi hanyar dakin sa yayin da yai saurin juyowa
ya nufi kofar gida.
Innawo ce Kai Ina zaka?
Tafiya kawai yake da alama baya sanin inda yake saka kafar sa, kofar gidan ya zauna tare
da hada kansa da guiwa.
Ya dade zaune agurin sannan yaji taku kafafuwa na kusanto su dan haka yai saurin dago
kansa, Maman Sadam ce da aunty Murja rungume da jaririn sai Umma dake binsu abaya, cikin
sauri Aliyu ya mike yayi saurin saka kafarsa daya akan dukin kofar gidan yayin da daya take
kasa hannun sa duk biyun cikin aljihu.
Ja sukayi suka tsaya, Maman Sadam ce tace bamu hanya zamu wuce"
Kubar walar da kanku na zuwa nan gidan, na shirya zuwa duk koma inane, Inanan akan
bakana bazan amsa yaron ba, nan gidan ma babu me amsa, dan haka kujuya kawai
Kai, wani ni shin in tambaye ka?, Dan naka ne wai ko ba naka ba?......
Katseta yayi da fadin, nawa ne, amman baxan amsa ba, duk inda za'aje aje bana so nabar
maku, bazan amsa ba.
Wlh baka Isa ba, indai nice kamar ka amsa ka gama, idan Kai baka amsaba sabo da
idon ka atsaye suke Uwarka zata amsa
Cikin tsawa yace, zaku tabbatar bazan amsa bane idan wata mata ta sake takowa kofar
gidan nan, domon duk wata kafa data sake takowa nan saina balla ta
Zaro ido sukayi gaba daya, cikin sauri Umma ta juya tana fadin kuzo mutafi, saida
sukayi nisa sannan Umma ta tsaya tace, " Idan kana takama ne kafi karfin hukuma ai baka fi
karfin alkali ba, dani kake mgnr.
Innawo kuwa zuwa tayi bakin kofar ta cikin gidan take fadin wai Kai kana ma da hankali
kuwa, ko hauka kayi ne?
Lafiyana lau Innawo, Ina sane.
Akofar gidan ya wuni
da yammacin ranar misalin 4:34pm ta kardan sammaci ta samu Aliyu, bude takardan yayi
fuskarsa cike da murmushi......
*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 48- 49
Mikewa yayi da takardan a hannun sa ya shiga gidan, tunda ya bude ta be rufeba.
Afalon ya samu Ummi sai faman sheshekar kuka take yi, yayin da yaji muryan Innawo daga
cikin dakin maccin ta tana fadin, " tunda bazaki bari ba saikije kita yi, idan wani ciwo ya sameki
sai kizo kiyi jinya, ace mutum ya wuni yana kuka, komai yayi zafi maganin sa Allah, ni ko Aliyu
bezo yanzun ba na tabbatar koma yaya ne d'an nan nasa ne.
Jikin Aliyu a matukar sanyaye ya zauna afalon nesa da Ummi, yayin da kowanni saukan
hawayen ta yakejin takaicin sa cikin ransa, dan haka ya shiga fadin, " Ummi dan Allah kiyi
hakuri"
Cike da tsananin zafi tace, "ranka zai baci ka sake ka sake min mgn, babu ruwana dakai,
mara mutunci kawai, wadda besan mutunciba, Dan iska kawai wadda ya dauki zina ba abakin
komai, gara daka nunana min ka zama tantirin dan iska, kaje ka amsa kazantarka tun wuri ga
kaima Ubanka, nan bama rike d'an iska bare mu rike kazantar ka.
Ji Aliyu yayi kamar Ummi na watsa masa wuta, dan haka duk jikin shi ya Kara sanyi, cikin
sanyi sosai yace, " Ummi kiyi hakuri dan Allah ki Kuma tsaya kiji Uzurina.
Dallah gafara cen, Kai dan baka da Kunya har kake tunanin ni zan saurara ta tsuniyar ka?,
Mara kunya kawai, kama yariya ciki saboda tsabar rashin kunya jiya tana haihuwa har ka iya
shigowa garin nan, kowa na kallon ka bakajin kunya Kai?, to idan Kai baka da digon kunya mu
muna dashi, nasan ka riga ka zubar Mana da mutunci kowa yasan wannan lbrn acikin unguwan
nan, harma da kewayeta, dan haka yau yau dinan kaje ka amsa danka kabar kasar nan, baxaka
kwanar Mana agida ba kaji Kuma na gaya maka.
Mikewa Aliyu yayi cikin rasa abun yi, adaidai wannan lokacin Innawo ta fito tana fadin, " ni
yanxun ba wannan ba, surutun nan bashi da amfani, ke ki bari yayyan ki suzo kwai anemi
mafita.
Innawo idan Ina kaunar ganin Aliyu toh Ina kaunar ganin mutuwata, wlh banson kallon shi
idan Ina kallon shi raina namin zafi, zuciya ta nafarfasa, jibeshi kawai, katon banza mazinaci
dan isaka fasiki matsiyaci kaw......
Cikin sauri Innawo ta katse Ummi da fadin, " ke!! , Ki dawo cikin nutsuwarki, naga kina da
niyar yi masa baki, karki fara, wlh ranki zai baci.
Toh Innawo wadda ya aikata irin wannan abun kuma meya rage mishi?, ai ya riga da ya
lalace.
Nace miki kiyi shiru ko, bakama yima yaron mugun baki ba kenan inaga ka mishi?, Kai
Aliyu tashi ka shiga ciki.
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke me karfi sannan ya mike muryan shi can kasa yace, " Ummi
kiyi hakuri dan Allah, nasan ni me laifine, bacewa nayi akan daidai nake ba, matsala kawai aka
samu, kokarin shiga dakin yake ya sake cewa Innawo kema kiyi hakuri ba ason raina bane,
tsintan kaina kawai nayi ahaka.
Sosai wannan kalamin nasa ya shiga jikin Innawo, tausayin Aliyu taji ya dan shige ta dan
haka ta hada abinci ta nufi Kai masa, sai dai tana dire abincin yace Innawo bazan iyacin komai
ba, hankali na ba akwance yake ba.
Murmushi Innawo tayi me kama da yake sannan tace, " duk jarumtar daka taho da ita
Aliyu?, ai naga ka taho da jarumta, naji kanace ma Umma d'a naka ne, amman bazaka amsa
ba, wai kabata, toh Kai kanka kasan ba abu me iya yuwa kake fada ba, kasan masifa da balaki
irin na Umma, da ace ba Umma bace sai mu roki tashayar da yaron bayan tagama shayar dashi
tabamu, toh Umma kota amince da haka na tabbatar hankali bazai taba kwanciya ba idan ba
dan nan aka amsa ba......
Innawo nifa baxan amsa yaron ba.
Bangane ba Aliyu?, kafa amsa d'an naka ne?
Amman wlh Innawo bazan amsa ba, ko ita ta kirkiro masifa.
Ashe kuwa Umma zatai karan ka.
Ai tamayi, ga takardan yanzun aka kawo min.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, shikenan zancen ya wade duniya, naso arufe abun.
Ninafi son haka Innawo.
Aliyu bakajin kunya?, Wannan fa babban abun kunya ne, ace acikin zuri'armu muna da
shege.
Kashhh, Aliyu ya fada, Innawo shege fa kuke cewa, shige shine wada ba'asan ubanshi ba
ai,
Ai ba aure kukayi ba?, Ko auren sirri kukayi?, Idan kuwa har ba aure Aliyu ko kaki ko kaso
sunan sa kenan.
Yamutsa fuska Aliyu yayi tare da kawar da kansa yake fadin, " amman Inawo wannan yaron
ba sunan sa kenan ba, kuma idan har ana gaya masa haka za'a dinga samun matsala.
Mikewa Innawo tayi tana fadin, Allah ya rabamu da ita, Kuma Ina baka sharawa aje duk
wata rashin kunyarka harsai zuciyar Ummin ka yayi sanyi inba haka ba ta iya gaya maka kalma
mara dadi, dan tana cikin fushi sosai.
Tana gaba fadin haka ta fice yayin da yabi bayanta da kallo.
*******
Koda rana da Alhaji Umar da Sani sukazo gaba sukasa Aliyu, fada babu irin wadda
basu masa ba, sosai ya roki su tsaya su saurari uzurin shi, amman Alhaji Umar yaki bashi
wannan damar, acewar sa, bashi da wani uxuri da zaisa su saurareshi, idan har zina ne ba
aure ba, basu bukatar uzurin shi, dan haka ya sunkuyar takai kawai, cikin yanayin dake nuna
yanajin kunya, daga karshe Ahaji Umar yace, tunda sunkai mgnr kutu babu wani hukunci da
zasu iya dauka abari ashiga kotun.
Cike da fada Ummi tace ai shikadai zaije babu wadda zaije kotu acikin gidan nan.
Kara sunkuyar dakai Aliyu yayi yayin da yaji muryan Ahajin yana fadin, " kedai ki zauna
agida, amman dole asamu wadda zai rakashi, hannun ka baya rufewa ka yanke ka yar, dan
haka yazun mafita ake nema.
Mikewa Ummi tayi tabar dakin, yayin da duk suka shiga yima Aliyu nashiha.
Bayan sun gama da Aliyu gurin Ummi suka nufa, nan ma dai nasiha sukaita mata
akan hakuri, aduk halin daka tsinta kanka aciki.
Washegari misali 7: 30 Aliyu ne ya fito cikin kananan kaya, a kitchen ya samu Innawo
bayan sun gaisa yace, " ina Ummi na?"
Kallon shi tayi tace, " tana kwance sai bayan sallan Asuba ta samu bacci.
Jimmm yayi, sannan yace, " dan Allah Innawo ki bata hakuri, kinji, wlh tsautayi ne kawai.
Hmmmm, toh naji ai Allah ya kawo Mana mafita.
Ameen, ya fada ahankali, sannan ya juya ya fita.
*******
Wannan Zaki mikawa Aysha Idan da hali ki dauko yaron.
Amsan jibga jifga ledojin guda biyu matar malam Idi tayi a hannun Mijinta sannan ta kalli
Aliyu dake gefe ta kada Kai tai waje.
Gurin zama Malam idi yabawa Aliyu sannan ya zauna kusa dashi, kusan minti 10 sannan
matar malam Idi ta dawo rugume da jaririn ahannun ta.
Malam idi ne ya mika hannun ya amsa yaron, sannan ya mikawa Aliyu, nan danan
murmushi ya bayyana afuskan Aliyu yayin da ya kurawa yaron ido.
Daker ya iya dagowa ya kalli Matar malam idin yace, " aunty Aysha tana lafiya dai ko??
Eh lafiya lau take.
Maida Hankalinsa yayi kan yaron dake kokarin wangale baki sannan ya sake dagowa yace, "
bata cikin wata matsala ko?"
Eh toh, gaskiya dai na sameta tana kuka dai, ga yaron ma ba'a masa wanka ba, ita dai
naga alamar tayi wanka.
Jimmm Aliyu yayi cikin sanyin jiki sosai zuwa can yace to ta karya kuwa?
Gaskiya bana tunanin ta karya, da alamar dai tana cikin damuwa sosai, dan kayan da
nakai yanzun ma cewa tayi indawo maka dasu daker tabar su.
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke, sannnan yace, aunty dan Allah kimin kokari kisata taci abinci,
sannan kice mata ta kwantar da hankalin ta, Ina nan bazan tafi ba harsai mun samu mafita, da
yardan Allah, ta kwantar da hankalin ta Ina tare da ita.
Daga idi har matarsa cike da tausayawa suke kallon Aliyu, hakika shima cikin damuwa
yake, ruwa matar malam Idi tasa taiwa yaron wanka sannan ta nadeshi da nufin idan ta mayar
dashi zata canza masa kaya cikin Wanda takai yanzun.
Aliyu bebar gidan ba harsaida ya tabbatar Aysha taci abinci sannan yabawa matar idi kudi
yace ta dinga lekata akai akai abun da babu acikin kayan asaya idan ana bukatar wani abu
Kuma amasa mgn.
Ranar da Aysha tayi kwana 4 haihuwa ranar ce ta kasance ranar da za'a shiga kotu,
misalin 8:00am Aliyu ya gama shiryawa tsaf cikin manyan kaya shadda ce wadda ta amsa
sunanta, sosai ta karbesa matuka yayi kyau sannan ya daura hula, baka taba kallon sa kace
baida iyali agida sabo da kwarjinin sa, Aliyu kyakyawa ne na gaske hasken fata ne kadai beda
ita, dogone me dogon hanci uwa uba iya daukan wanka, Dan koga yasa kaya saika dauka ya
shirya yin gayune Koda kuwa cikin damuwa yayi ta.
Afalo yacidda Innawo tana tana fadin, kawun ka yace daga can zai wuce nikuma Ina nan
zuwa.
Gyada Kai yayi sannan ya fice agidan.
Cike harabar kotun yake da mutane, Babban kotune da ake shari'a kala kala, ganin
ba'a fara shiga kotun ba ya nemi guri ya zauna, bega wani daga cikin yan gidansu Aysha ba,
hakama kawun nansa basu zoba, zuwa can ya hango Umma da gayyan yaranta sun sakko
daga mota saidai babu Aysha acikin su, balakin kosawa da yayi yaga Aysha yasashi Jin
hankalin sa ya fara tashi.
Zuwa can Hankalinsa ya koma gun Innawo ganinta tare da Ummin da abun yai matukar
bashi mamaki, zuwa wannan lokaci bakin babban kotun cike yake da dan mutum, saidai har
wannan lokacin bega Aysha ba.
Duk inda zai kallah ya kalla Amman babu ita, daga can ya hangi wata mota ta faka,
wani mutumi yaka ya fito dattijo ya zagayo ya bude kofar motar, Aysha yaga ta sako kafa tana
rungume da yaron a hannunta, saidai bata iya dago kanta harta fara takowa tana boye sukanta
da hijjabinta, can gefen su Umma ta koma ta rakube yayin da Daddyn ta ta Isa gurin su Umma.
Tunda ta sako kafarta kasa Ummi take mata kallon tsana tare dabita ita da dan nata da
kallon sosai takejin tsanar Ayaha ita da abun da ta haifa har cikin kokon ranta.
Shikuwa Aliyu, tunda Aysha ta zauna kallonta yake yi, yadda ta takure sosai ita daya
agefe yaji beson hakan dan haka ya mike ya fara takawo kai tsaye yake ratsa mutane har ya
Isa gurinta fuskanta yana daga cikin hijjabi.
Tsaye yayi akanta ya kalleta ya kalli yaron yayin da duk idon mutane ya koma kansu.
Umma kuwa wani irin tafarfasa zuciyarta keyi, hakama maman Ayaha gaba daya jitake ta
tsana Aliyu hukunci me nauyin gaske take son amasa wadda zai raina kansa, gaba daya yaran
Umma hakalin sune ya tashi yayin da suke ganin yaje ne ya dada hure mata kunne ta basu
kunya.
Sukuwa jamar dake gurin waddan suka San abun dake faruwa mamaki sukeyi sabo
yadda suka kula kamar Aliyun na nuna kulawan sa akan dan dayaki karba dan ganin ya mika
hannun sa ya gyara ma jaririn hular dake kansa.
Da yawa mutanen dake gurin kosawa sukayi ashiga kotun ciki harda iyalan gidajen guda
biyu domin duk kusawa sukayi ya tashi daga gaban Aysha.