Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
Bayan Sati biyu ta tashi da matsanancin ciwon mara.
Murkususu take tun safe har rana tana saman katifar ta, ganin har rana tayi, Mama ta
tashi ta leka dakin tana fadin ke lafiya kuwa!
Mama marana ke ciwo.
Lumshe ido Mama tayi tare da fadin, Bismillahir rahamanir rahim, Allah nagode maka daka
jarabceni da ganin wannan mummuna al'amari wadda bame dadi ba agareni.
Umma ce tace lafiya?
Aysha nakuda take yi Umma.
Munshiga Uku,, naka takaine Yaya zamu yi?
Umma ko asibiti zakuje?
A'a ai batai awo ba, adai Kira mata unguwar zoma.
Umma, Amman kinsan Innawo ce kadai keyi anan haka, Kuma Innawo nasan bazata zo.
Gyale Umma ta dauka tana fadin kedai Ina zuwa.
**********
Innawo karkije dan Allah, lallai ma matar nan bata da Kunya ko kunya bataji ba ta iya tskowa
gidan nan meya hana sukaita asibiti.
Bakomai Fatima barin je, wlh taban tausayi, zanje idan naga da matsala zance suje asibiti,
idan ina iyawa Kuma zan amsa, ai da nakowa ne.
Kofar gidan Innawo ta nufa yayin da Ummi ke fadin, kashh, dan Allah Innawo ki dawo
karkije.
********
Wani dan karamin littafi ya bude, ya zubawa shafin ido sannan ya mayar ya rufe, mikewa
yayi ya dauko a kwatin sa tare da zuba kayansa aciki ahankali ya mayar ya rufe, yana daga
tsaye ya zuba hannun sa duk biyun cikin aljihu, guri daya ya tsirawa ido, bakin gilashi sanye a
idon sa cike da kwarin guiwa yake sauke ajiyan zuciya.......
https://youtu.be/2eTqqbS_xq0
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
episode 46- 47
Da Sallama Innawo ta shiga gidan, yayin data samu Umma rike da Aysha acikin dakin Ayashan,
cikin nuna kwarewa Innawo tace, "haihuwa ce , abani leda da reza"
Cikin sauri Umma ta fice adakin tare da daukan gyale tai waje, bata jamaba ta dawo dakin.
Sosai Aysha ke murkususu Innawo na mata sannu su biyu a dakin.
Murkususu take yi tsayon lokaci tare da share hawaye, sosai tagaji iya gajiya, ciwo takeji
bana wasa ba.
Innawo kuwa fadi take daure dai Aysha.
Kusan awa uku aka kwashe ana abu daya, ganin mangariba na gabatuwa Shiru babu wani
lbr yasa Hankalin Mama ya tashi sosai, wani irin tashin hankali takeji, Daman yadda cikin Aysha
ya girma abun tsoro yake bata.
Bayan isha'i ne abun ya tsananta, daga dakin Umma tana jiyo nishin Ayaha, Innawo kuwa
tana rike da Ayaha tana mata addu'ar neman sauki tare da sauka lafiya, kokarin yariyar tagani
sosai.
Misalin tara da rabi na dare kan dan ya fara turowa, cikin kwarin guiwa Innawo ke fadin, "
yauwa Ayaha, kadan ya rage, yi karfi da jikin ki saura kadan ya fita ki huta.
Wannan mgrn ta Innawo ke karawa Aysha karfen guiwa cikin ikon Allah jaririn ya gama
fitowa tare da uwar gaba daya.
Ajiyan zuciya Ayaha ta sauke, hakika haihuwa akwai raradi wadda bashi missaltuwa yanzun
ji tayi kamar an zare mata ciwon.
Innawo kuwa harta yanke ciben ta nade abin da aka samu cikin zanin Aysha yayin da
gidan ya karade da iho, Umma ce ta shigo tana tambayar Innawo ta sauka ne, cike da kwarin
guiwa Innawo tace ta sauka ga danta nan kwaton gaske.
Hmmmm, kawai Umma tace sannan ta juya ta fita.
Ganin haka Innawo ta tsaya ta gyara komai tare da wanke kayan da aka b'ata, ganin inda
Umma ke shashsharewa Innawo tace abata ruwan zafi tama yaron wanka.
Nan danan ko Umma ta kawo ruwan, bude yaron Innawo tayi tana kokarin saka shi aruwan
wankan take fadin, wai, wannan yaron baki ne, beyo farin uwarshi ba, juyawa tayi ta kalli
kunnen yaro sannan ta kalli keyarsa, zabura Innawo tayi tare da dan zaro ido.
Mamace ta shigo ta fita da Aysha domin yi mata wanka, dan haka Innawo ta shiga duba
yaron dakyau.
Gani take kamar Aliyu ne yayi kaki ya tufar, cikin tashin hankali ta furta Innalillahi wa inna
ilaihir raju'un, wannan yaron bashi da banbanci da Aliyu, haka yake sak lokacin da aka haifeshi,
katon gaske ga tsandara ihun tsiya, haka wannan yaron tunda yazo duniya be rufe baki ba
Kona sakan daya.
Cike da rude Innawo ta shirya yaron cikin wani kayan sanyi da Umma ta kawo.
Gashi an samu karuwa Amman Umma da mama zuciyar su babu dadi, fitowa Innawo tayi
adaidai lokacin da Aysha ta fito wanka, godiya Umma tai mata sannan ta fita ta nufa gida.
Har Allah Allah Innawo take ta Isa gida, dumin hankali ta atashe yake, lokacin har Ummi ta
kwanta dan haka tasa hannunta tana bugunta tana fadin, Fatima tashi ki zauna.
Innawo sai yanzun kika dawo, tun rana ko lekowa gida ki koma bakiyi ba fa.
Katseta Innawo tayi da fadin, "ke Fatima ba wannan ba, akwai matsala"
Matsala wacce iri Innawo?, bata haihu bane?
Ta haihu, ki zauna dakyau nace miki.
Gyara zama Ummi tayi tana daga bakin gado.
Innawo ce tai kasa da murya tace, "dan da Ayaha ta haifa kamar Aliyu ne yayi kaki ya tofar"
Dirowa Ummi tayi daga gadon, tsintan kanta tayi akasa wanwar, Innawo ban fahimceki ba?
Hmmmm, Fatima yaron kama yake da Aliyu, kama bana wasa ba.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Innawo dan Allah ki bari, kin manta shekaran Aliyu biyar
baya kasar nan gaba daya?, Innawo karki sake fada, bazamuga shege ba insha Allahu, Aliyu
bazai haifamana dan xina insha Allahu.
Ai saidai Kar akuma Fatima, amman duk inda akeje aka dawo wannan yaron namune ko
shakka bana yi.
Innawo kiyi shiru dan Allah, kibar jingina mana shege, kamace kawai tai yawa.
Shiru kawai Innawo tayi domin bata son jayayyan nan da Ummi ke yi.
******
Wannan abun bakin ciki dame yai kama, ni dan takaici ma na kasa kallon yaron, ita kanta
Aysha yaron kwana yayi yana tsandara ihu taki daukan kasa, danaji najin da jin kukan sa nace
mata tashi ta bashi nono sai tasa min kuka, haka muka kwana ita tana kuka danta nayi, ba irin
abin da ake gudu kenan ba, yanzun da aure ne ya kawo wannan yaron me shegen kwakwazo
haka nan zamuyita ririta shi, amman wlh yanxun danaji muryan yaron sai inji kamar in hadiyi
zuciya in mace.
Kawar dakai mama tayi tare da fadin, tana daukan alhakin yaron ne, shi meye nashi nashi?
adolenta ta shayar dashi. ni yanzun abun dake cimin rai ace wai Aysha ta rufe ido tace ita Sam
batasan uban yaron ba, wlh Umma ban yadda da wannan ba.
Ita ta jiyo, yanxun dai ai ga tukuicin rashin Jin mgn nan Allah ya bata, idan ta yaye shi idan
Allah ya bata miji ko wanni iri ne sai a kukuta ta tafi, hankalin mu ya kwanta.
Umma waye zai aureta da yaron?
Indai ta samu mijin saidai tabar Dan nan dan musamu ta zauna agidan mijin cikin
kwanciyar rai.
Saidai ubanta ya dauka, wlh ni Umma ko ganin dan bani kauna.
Ai kiyi hakuri kawai, indai ba Koran Aysha zamuyi ta shiga duniya ba toh rayuwa da danta
yazamar mana dole, Kinga lokaci na tafiya barinje ingayowa 'yan uwanki, ke Kuma kije ki ma
yaron wanka ga ruwa can ya gama dahuwa har gurin babanta zanje.
A'a Umma kibari abawa abawa iro kudin mota yaje duk ya gayo masu, ni bad'an dazama
wanka.
Jimmm Umma tayi sannan tace toh shikenan.
Mikewa Umma tayi ta debi ruwan zafin ta koma dakin, itako Mama gyale ta dauka ta nufi
waje domin aika iro.
*****
Wai har yanxun kukan kike?, ai wannan kukan beda amfani, kuma d'an ba laifinsa bane ki
dauke shi maza kibashi nono, kafin asashi a ruwan wanka.
Karawa kawar dakai Aysha tayi, dan haka Umma ta nufi dan ta dagoshi ta daura cinyan
Aysha dake zaune sannan tagama hannun Aysha ta tallabo kan yaron dake ta tsandara uhu,
kallon Aysha Umma tayi tace toh fito da nonon kisa masa abaki.
Hawaye kawai Aysha ki zubarwa yayin da kukan yaron ya dami Umma dan haka ta
daga rigar Aysha ta ciro nonon tare dasa hannunta ta Kara dago kan yaron dumin nonon
yasamu shiga bakin sa, carab kuwa ya rike nonon tare da fara tsotsonsa bada wani bata
lokacin.
Jin yaron yayi shiru yasa Umma takai idonta fuskan yaron tana fadin, " kin bani da tsotso ai
ku......
Cak ta tsaya tana me karewa yaron kallo, Rabon data tuna Aliyu ta mance, dagowa tayi ta
kalli Aysha dake hawaye sannan ta kara maida idonta kan yaro, idonta akan yaron take fadin, "
Bilkisu fito ki gani!!, Bikisu kina ina!!
Tunawa tayi Mama ta fita dan haka tamaida hankalin ta ga Ayaha tare da fadin, "wannan
yaron uwa Aliyu aka zuke ya zama 'kankani. Duk yadda akayi Aliyu nashigowa garin nan,
shiyasa kikace baki san wadda yai miki cikin ba.
Kawar dakai Aysha tayi har yanxun hawaye na zubo mata ga wani irin faduwa dataji
gabanta nayi tunda Umma ta Kira sunan Aliyu.
Cikin wani irin yanayi Umma tace, " rike danki, kan yaron Aysha ta kama yayin da Umma
ta matsa can gefe tana kallon Ayasha sannan ta juya ta kalli yaron tsayon lokaci ta dauka ahaka
sannan Umma tace akwai tashin hankali agarin nan, wlh wlh bazan yi shiru ba, kowa yaci tuwo
dani miya yasha, Sam bazan yadda ba.
Mama ce daga waje take fadin, " Umma Yaya aka yi?
Ai tana kwala miki kira, shigo kiga Aliyu a hannun Aysha, wallahi wannan yaron na Aliyu ne,
ko kaffara banayi jikan Innawo ne.
Cike da sauri suka shiga dakin gaba dayan su, Maman Sadam da Murja Koda suka kalli
yaron salati. Suka fara, Aysha kuwa kawar da fuskanta kawai take babu bakin mgn.
Maman Sadam ce ta fige yaron daga hannun Aysha ta fice adakin yayin da aunty Murja
da Umma suka rufa mata baya.
****"
Innawo ki daina damun kanki, Ina kallon ki Innawo bakiyi bacci ba da daddare, ni Ina da
tabbacin abun da nake fada miki ko kina ganin Aliyu zaizo garin nan ne ya juya batare dayazo
nan ba?
Nima abun da ya tsaya mun arai kenan Amman fa Fatima koma dai ta yaya ne yaron nan na
Aliyu ne, domin har kafa, hannun, ido, baki hanji ke har sumar kan yaron irin na Aliyu ne, yadda
kikasan Aliyu sanda yazo duniya haka garon yake.
Innawo ki kwantar da hankalin ki, ni Ina da tabbacin banasa ban.....
.
Har gowan mutane yasa suka maida kallon su ka kofar shigowa gidan, inda Maman
Sadam tai saurin daura yaron kan cinyar Ummi tana fadin, ki duba kiga abun da danki ya
shuka.
Mikewa Ummi tayi rike da yaron tabas taga kamar da Innawo ke fadin, cikin azama ta shilla
yaron yayin da Murja tai saurin cabewa tana zare ido, cikin zaro ido Ummi ke fadin nafiku
hauka, wato yarku ta haife d'a kun rasa inda zakiyi dashi zaku kakaba Mana, toh duk inda za'aje
aje bazan taba yadda ba, shekaran Aliyu biyar kenan kwarara baya kasar nan, kowa cikin
unguwar nan yasani tunda Aliyu yasa kafa yabar gidan nan be sake lekowa ba, dan haka bazan
taba karban dannan ba, ko sama da kasa ce zata hade, 'karyar bala'i kuke yi.
Ai kuwa kowa ya kalli yaron nan yasan na Aliyu ne, Umma ke fadin haka tana me nuna
yaron.
Ummi ce tace, " Inna hujar take?, Kije ki nemo hujja ki kawo, idan ba haka ba wlh zanyi
karan ku.
Jiki babu kwari suka fita domin dai basu da wata hujja suna komawa suka tarar Baban
Aysha yazo da kaya niki niki, Aysha kuwa har wannan lokacin kuka take yi nan suka shiga gaya
masa duk yadda aka yi.
Kawar dakai yayi tare da fadin, "aina gaya mata, ita yakamata ta bude baki tai magana tuni,
nayi nayi da ita taki, tunda batai mgn ba kuwa Nima bani da ita, dan haka ku rabu da ita.
Sallama ya masu akan da yamma zai dawo , bayan tafiyan sa yaran Umma duk sun
hallara dan haka suka Kara yanke shawaran akara komawa da yaron gidan Innawo.
Lokacin da suka Isa tunkafin su shiga gidan Alhaji Umar ya taresu, domin harda maza
cikin su, anan Alhaji Umar ya kara tabbatar masu da bazasu karba ba domin babu wata hujja da
ke nuna Aliyu yazo garin nan acewar Alhaji Umar idan akwai hujja suje su kawo.
Haka suka sake komawa da yaron, ayanzun duk uguwar ta dauka, akan wannan tirka tirka
da ake tsakanin gidajen guda biyu, yayin da duk jamar unguwar ke goyon bayan Ummi akan
cewa karta karba, domin dai kowa yasan Aliyu be Kuma dawowa kasar ba, ko Ina cikin unguwar
mgnr da ake kenan.
Gidan Innawo kuwa gaba dayan su tutsiye Aysha sukayi akan ta bude baki tai mgn
amman abu ya gagara, zagi babu irin Wanda basu mata ba yayin da wasu suke cewa amata
dukan ne, wannan abu ya dauke su tsayon lokaci har misalin karfe biyar na yamma so kawai
suke Aysha ta fada masu domin su samu hujjar komawa gidan Innawo.
******
Karfe biyar da kwata ya shiga cikin unguwar, acikin abu biyu yasan tabbas zai tarar da daya,
kodai Aysha tagaji da jiran sa tayi aure, ko Kuma tana dauke da tsohon cikin sa, wadda jikin sa
yafi bashi na karshen, a zuciyarsa yasan mayuwacin abu ne ace Aysha bata da cikin sa, saidai
idan wani ikon Allah, dan haka yanzun bashi da burin daya wuce yaji labarin Aysha tunkafin ya
Isa gida.