Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 34

54K to 57K   out of 101.2K words

Ina son nakoma, amman yanzun idan na koma
gida damuwar da zan shiga Kuma saitafi ta da, kashhh, Yaya Aliyu dama nasani da banzo ba.

Jimmm yayi zuwa can yace, Aysha ni zan kaiki gida da kaina, nikaina hankalina bazai taba
kwanciya ba matsawar kina Cameroon ni Ina nan. ko ayanzun kawai Ina daurewa ne kawai
amman Allah kadai yasan me nake ji.

Sheshekar kuka ta fara, domin gani take babu wani hanyar da zasu kasance tare
matsawar Aliyu zai kaita gida, Kuma yace yana neman auren ta, akwai Babban matsala.

Shi kansa Aliyu yana fada ne kawai tare da karfafa ma kansa guiwa amman inya tuna
wacece Umma gaban sa har faduwa yake yi akan irin kinsa da take

Aysha dan Allah ki share hawayen ki Kar Kuma ki sake yin kuka, insha Allahu zamu
rayu tare, muyi zaman aure, mukuma haifi yaran da iyayen mu zasuyi alfari dasu, Allah ne yasa

mana kaunar juna bamu mukasawa kanmu ba, Kuma kisa azuciyar ke abun da Allah yaso ne
kawai yake tabbata, idan kin rike wannan zakiji dadi cikin ranki,

Cigaba yayi da cewa, dana dawo zamu sa rana dan Allah ki kwantar da hankalin ki.

Amsawa tayi dakai tare da fadin, kaje ton, Allah ya kiyaye hanya.

Juyawa yayi yana fadin ki kula da kanki, harya Kai Kuma yaji tace, Yaya Aliyu?

Juyowa yayi yana fadin na'am Aysha.

Ka gaida budurwa ka....

Ke kadai ce.

Yaya Babba dakai?, ni ban yadda ba.

Wlh azim ke kaidai ce bantaba kallon wata 'ya mace naji wai Ina sonta ba.

Dariya take yi yayin da hawaye ke zobu mata, Hannu ya daga mata sannan ya juya ya
tafi cike da tunani.

******

Dakin ta koma tana share hawaye, su Islam ne suka tambayeta lafiya, nunar masu tayi da
tagaji da zama ne, ta kosa Mijinta ya dawo, lallashinta suitayi ganin tana cikin damuwa da
yamma suka ce tazo suje islamiya.


Tundaga ranar suke tafiya makarantar tare, yayin da hausanta ke samun cigaba, ranar da
Aliyu yayi kwana uku ma hausanta yayi kwari wuni suke suma mgn da su Islam sai dai hausar
tsta babu dadi.

Yau kwanan sa shidda da tafiya dan haka suke saka ran gobe zai dawo.

Harabar gidan suka fita su uku can gefe suka zauna yayin da Meenat takewa Aysha
kalaba, Islam kuwa zaune take tana basu lbr, dukan su shiga iri daya ne ajikin su rikace yar
karama me gajeren Hannu, sai siket din da ya wuce guiwa kadan.

Suna cikin hiran wani saurayin islam ya shigo, ganin su agurin yasa shi tahowa ya
Dan tsaye daga nesa dasu kadan yana fadin"

Kitso kike ne??

Mikewa Islam tayi zuwa gurin sa tana fadin eh.

Waccen yariyar fah?, Wacece ita? badai nan gidan take ba?

A'a bakuwa ce, yar uwarmu ce.

Ok Amman kamar ba bahaushiya bace, tana da kyau sosai.

Lumshe ido Islam tayi, fulani ce.

Ku fulani ne daman?, amman bakijin fulatanci?

Muba fulani bane.

Naji kince yar uwarku ce.

Eh, yar uwarmu ce, aikasan yayamu Haydar ko??

Eh nasan shi kwarai kuwa.

Toh wannan kanwar sa ce.

Ok nagane shi yanzun yanajin fulataancin?

Zaro ido Islam tayi tare da fadin, toh ai shima dama cen hausan shi bawani fita take ba, idan
yana hausa saika gane fulatancin ya rike bakin sa, mamasun fulanin Cameroon ce gurinta ya
girma Kuma.

Masha Allah, uwa daya uba daya suke ne?

Me kake tunani?, Itafa wannan ma matar aure ce.

Allah sarki Masha Allah.......

Gate din gidan suka hango ana wangalewa basu ankaraba suka ga hancin motar Aliyu ya
sawo kai cikin gidan, cikin sauri islam ta durkusa bayan fulayoyin dake gurin tare da zaro ido.

Meenat kuwa zamanta tayi tana cigaba dama Aysha kitson take fadin, Yaya Haydar ya
dawo.

Saurayin Islam kuwa tsaye yake hannun sa cikin aljihun sa.

Wani irin sako kafa Aliyu yayi daga cikin motar, cikin kakinsa na sojoji fuskarsa daure
tamau yake kallon inda su Aysha ke zaune, sannan ya hange saurayin dake basarwa yana
kallon can gefe, lumshe ido yayi cikin tsananin bacin rai, gashin Aysha yake hangowa ana
kitsashi a titi, bude ido yayi ya sake kallon su, cikin sauri ya waiga ya kalli bakin gate din gidan
cikin wani irin tafiya ya Karasa gurin wayar wutar datakai wuta dakin megadin ya kallah, wani
irin tsalle yayi ya finciko ta sannan yayi kansu Aysha aguje.

Meenat ce tai saurin sakin kan Aysha ta kwasa aguje hakama Islam mikewa tayi tana fadin
Momy!!

Shima saurayin na Islam asttin ya bar gidan Aliyu kuwa bayan su Mennat yabi yayin da
yajefesu da wayar wutar daya ciro.

Azaban zafin da sukaji saukan wayar wutar ajikinsu yasa suka tsananta gudu tare da Kiran
Momy.

Arikece Momy ta fito cikin tsananin tashin hankali tace Haydar me sukayi ne, run gumesu
tayi ajikinta adaidai lokacin da Aliyu ya karaso gurin

Wayar wutan ya dauka yana fadin kuxu nan.

Sakin su Momy tayi tana me dada turosu duk da riketa da suke yi, adai dai wannan lokacin
Aysha ta shigo dan kwalinta rike ahannunta, wucesu take kokarin yi yace kema zo nan.

Zaro ido Momy tayi tana fadin, itama dukan ta zakayi ne?

Be saurareta ba, fadin yake zakuci ubanku yau, daman kasuwa akeci agidan idan ban nan,
ganin yana murde wayar Aysha tai saurin shiga bayan mommy tanama Aliyu wani irin kallo
gaba daya ya canza mata.

Tana kallo ya Zane su Islam sai ihu suke sannan ya nufo gurin Momy yana fadin saura ke.

Sai dai ka zanemu tare, baka da hankali ne, aiko amakaranta ba'a dukan matar wani, sabo
da darajan aure.

Wlh saina daketa, aitafi su laifi.

Toh Bismillah kazo ka dakemu tare bakomai, Kuma tunda ni baka ganina da mutunci barin
aika akira baban ka idan mahaifiyar kace ai bazata ce bari kaki bari ba.

Sakin wayar yayi da sauri yabar dakin cikin sanyin jiki Aysha ta fara kuka.

Su Meenat ma duk kuka suke
Domin bakaramin duka ya musu ba.

Tunda abun ya faru yau kwana uku kenan bataga Aliyu ba, tasan fushi yake da ita
shiyasa be nemeta ba, tagumi tasa yayin dataga Islam ta shigo tana murna.

Meenat ce tace Yaya dai?

Yaya Haydar zaiyi tafiya harna tsayon wata hudu

Cikin sauri Meenat tace, wow, abun ya burge, kice zamu huta kwana biyu.

Gane me suke nufi yasata ta mike da sauri ta nufi kofar fita, tafe take tana tunani harta Isa
falon sa, ahankalin ta tura kofar tare da sallama.

Kasa kasa ya amsa sannan ta shiga ta zauna, zaune yake akujera da alamar bayajin dadi
dan harya dan rame, ahankali tace Ina kwana.

Lafiya Lau

Cikin in Inna tace Yaya Kai hakuri dan Allah kaji?

Murmushi yayi mekama da yake sannan yace naji, ya wuce Aysha, na huce tuni ko baki
zoba yau nai niyar yau na kiraki, Ina son ki aramin hankalin ki.

Dagowa tayi ta kalle shi.

Kinaji Aysha, naso in kaiki gida da kaina amman tafiya ta taso min ban shirya ba, zanfi waje
harna tsayon wata hudu.

Nan danan hawaye suka zubo mata.

Kawar dakai yayi tsayon laci batare daya juyoba, zuwa can yace, kibar kuka, ki yadda dani,
zan dawo na miki alkawari, jibi zan wuce ki shirya gobe zansaki a mota ki koma gida, jiya na
gayawa Baffah gobe mijin ki zai dawo.......

Idonta cike da hawaye ta kalleshi yayin da yai saurin kawar da kansa tare da cire kwallar
dake son zubo masa.....


https://youtu.be/tfX94RbdUxE

*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

episode 35- 36



Gaba dayan su wani irin tashin hankali suka shiga ciki lokaci daya.

Ahankali yakejin sheshekar kukan Aysha yayin da ya kasa kallonta, Kuma ya kasa hanata
kukan.

Tsayon lokaci suka dauka ahaka sannan Aysha ta mike tana kokarin fita taji yana cewa.

Kibar kuka kinji.

Batace komai ba ta fita cikin wani irin yana yi, kafin ta Isa danin su Islam saidata share
hawayen ta sannan ta Isa, Kai tsaye bayi ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta fito ta fara
tattara kayanta, wannan karon akwati biyu tayi domin zaman ta anan Aliyu yakan mata sayya
hakama Baffah indai zaikawowa su Islam wani abun to tare yake kawo masu.
Bayan tagama hada kayanta tsaf ta ta mike ta Isa dakin Momy acan ta samu su Islam,
Meenat naganin ta tafara fadin.

Aysha ashe gobe Zaki wuce yanzun Baffah ke gaya mana.

Murmushi tayi kadan tace eh nima yanzun ne yaya Aliyu ya gaya min gobe zai dawo

zamu wuce.

Wayyo Allah sarki wlh kamar karki tafi, kamar kiyi zaman ki anan.

Islam ce tace ta zauna mijin nata fah?, kawai dai musa rana muje Cameroon din dama
bamu taba ganin Ummi ba.

Momy ce tace eh ai yayan naku ne wani irin mutum ne, amman yanzun in kunso zuwa
kwaje kota dalilin Aysha sai dai Kuma baku da Dan jagoro.

Zanwa Baffah mgn, wata rana idan Yaya zaije yace masa yaje damu.

Lallai kuwa, toh Allah ya kaimu muga ni.

Haka sukaita hiran kewan Aysha, misalin karfe 04:30pm Aliyu ya dauki Aysha, sayya ya
kaita tayi, acewarsa wai tsaraba ne kaya da yawa ya saya mata naci Dana sawa sannan ya
kamo hanya gida da ita.

Ganin haka Aysha tace yau bazamu gidan ka bane?

Kawar da kansa yayi sannan yace eh,

Jimmm tayi tsayon lokaci sannan tace, bazamu yi hiran sallama ba??

Atakaice ya sake cewa eh.

Wani irin abu ta hadiye sannan ta sake cewa , sabo dame?

Juyowa yayi ya dan kalleta kadan sannan yace, sabo da kiyayewa.

Bangane ba?

Eh tana iya yiyuwa ki kasa ganewa, Ina nufin Kinga kowa yana dauka ke matar abokina ce,
Kuma nace masu gobe Zaki wuce bana son su zarki wani abu.

Kallon shi tayi sosai sannan tace, " aiko da kowa yasan da wannan amman muna fita"

Kawar da kansa yayi sannan yace, mubar wannan mgnr Aysha, duk abun da kikaga
nayi kisa azuciyarki Ina da dalilina nayin shi, nafi kowa son mu kasance tare harke kanki, tun da
kikaga na zabi hakan toh nayi zurfin tunani ne Naga hakan ne mafita.

Har yanzun Aysha bagane inda ya nufa tayi ba dan haka taji ya bata haushi, Koda suka
Isa gida ficewa tayi batare data masa sallama ba, shi da kanshi ya dauki kayan ya bita dashi

tare da fadin, gobe kina idar da sallah asuba Zaki wuce, dana dawo masallaci zanzo na dauke
ki.

Kasa kasa tayi da murya tace ka kaini tun dare ma kawai ai daman nasan ka kosa na
wuce.

Tsayawa yayi yana kallonta tsayon lokaci sannan yace, kin kasa ganewa ne Ayaha, amman
bakomai duk me zakice naji, ninasan Ina da dalilina nayin hakan, ficewa yayi abin sa yayin da
Ayaha tabi bayan sa da kallo.

Daren yau Aliyu be iya Koda runtsawa ba haka yaita mutsu mutsu agado cikin wani
irin damuwa wadda baya tunanin ya taba shiga cikin sa,

Haka itama Aysha ji take tamkar bata taba shiga wani damuwa ba sai yau, idon ya bushe
kandas babu alamar bacci acikin ta gashi batasan me zataje ta tarar a gidan ba.

Tunkafin akira sallah ta tashi tai wanka ta shirya.

Kamar yadda Aliyu yace ana fitowa masallaci ya taho dakin su Islam yana fadin idan kin
gama muje.

Momy ce taji muryan Aljyu ta fito tana fadin Aina dauka mijin nata me zaizo ya dauke ta?

Eh yana tasha, cikin dare suka iso, yace nakaita kawai daga baya zaizo ku gaisa.

Toh Babu laifi, amman taje tayi sallama da baban ku.

Haka akayi cikin rakiyar momy Aysha tayi sallama da Baffah yayin da yaita masu addu'a Isa
gida lafiya da zaman lafiya tsakanin ta da mijin ta, sannan ya dauko kudi ya mika mata, fitowa
sukayi cikin rakiyar su Islam da Momy har bakin motar Yaya Aliyu, sunso suje harcen Amman
Aliyu yace a'a
*******

Cikin motar ma zaman kurame akayi, kin mgn Aysha tayi tare da kin

19 / 34