Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
shafe shi.
Kiyi hakuri, cikin bacin rai nake, abu me dadi shi kake rawar jikin gaya, Ina wannan yariyar
da ya taba sauka agidan nan?
Eh naji matar abokin sa.
Karya yamin kawai matar sa ce.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, lallai ma Aliyu.
Baffah da beson zancen yai nisa mikewa yayi kawai ya nufi dakin gidan mahaifiyar sa.
******
Ai danaga har 08:30pm baka zoba na dauka baza kazo ba.
A'a aunty, na tsaya gurin Baffah ne, kince ya fahimta amman naga daker yake min mgn.
Cikin ido ta kalleshi sannan tace karka damu da wannan, Kai inda ace da yariyar da 'Dan
kazo mishi ai da kun kwasa 'yan kallo, karka damu ai abun ma yayi kyau, kama godewa Allah,
har cewa yayi fa ga guri nan ka zauna kafin ka nemi wani.
Karyar dakai Aliyu yayi yana fadin, toh yanzun aunty bani sakon in wuce sauri nake yi"
Toh shiga daki yana nan gefen gado ka dauko.
Mikewa yayi yabi hanyar data nuna masa, be taba shiga dakintaba amman Kai tsaye ya tura
kofar.
Babban dakine me dauke da wawakeken gado, idon sa ya sauka akan wani yaro dake ta
wasa da kafarsa da hannunsa, sai kushin kushin yake, tsintan kansa yayi da saurin karasawa,
saidai idon shi na sauka akan yaron yaga kamar gizo ne dan haka yasa hannun sa yana
kokarin daukan yaron tare da saurin juyawa yana Kara kallon yaron.
Cak ya atsaya alokacin da yaga Aysha ta fito daga wanka towel daure bisa kirjinta yayin da
ta yafa wani a kafadanta.
Binta da kallon yayi sosai yake mamaki yana Kuma tsareta da ido.
Itako Aysha ganinsa ya sata daure fuska sosai, tasan dole ne yasan tana gidan Amman
bata zaci zasu hadu da wuri haka ba, ganin inda yake binta da kallo tundaga sama har kasa
yasa tai saurin komawa toilet din yayin da yai saurin takowa tare da mika hannun sa, adaidai
wannan lokacin ta bugo kofar tare da fadin, wayyo aunty!!!
Runtse idon sa yayi saboda zafin da yaji sosai kofar ta matse hannun sa, yayin daya kara
rike Khalipa dakyau da hannun sa daya yana fadin, "Aysha menene haka?, daman kun taho
tare?, Aysha ki bude kofar mana"
Arikece Aysha ke Kiran sunan aunty ganin haka Aliyu yace, " ki bude ki fito, kibar kiran
aunty haka.
Nika fita, bana son ganin ka.
Ni din?
Eh.
Haba Ayaha nine fa yaya Aliyu malamin ki, daman d'aliba tana fushi da malaminta ne???
Toh bakai bane saikamin alkawari baka cikawa dan kawai kaga bana gurin, ka manta
dani
Nidin?, akasi ake samu Aysha, tayaya zan mance ku, arana bana iya kirga so nawa nake
tuna ku, kiyi hakuri kinji.
Ni ba kalmar da zaka gaya min.
Toh naji, yanzun fito ki amsa Khalipa.
Ka ajeshi inda ka ganshi.
Toh zan ajiyeshi, sai yaushe zan ganki to??
Ni karka sake min mgn.
Kawar da kansa yayi daga kallon kofar, Khalipa ya zubawa ido sannan yace, naji bazan sake
miki mgn ba, amman kibani rana da lokacin da zan miki mgnr.
Jinta shiru yace mgn nake fah.
Ni babu ruwana dakai
Lumshe ido yayi sannan yace, aure muka yi fah Aysha, kinta ganin mata tace babu ruwanta
da Mijinta alhalin tana karkashin ikon sa??
Wannan karon batace komai ba,dan haka yaci gaba da cewa, ," baya ga haka Kuma ke
dalibata ce, Kuma har yanzun ni malamin ki ne dan haka ki fito kawai.
Yana gama fadin haka ya koma bakin gadon ya zauna yana me zubawa kofar ido, zuwa can
yajita cikin kasa da murya tace, " ka dan miko min hijjabina.
Akwai yaro a hannuna kizo ki dauka.
Ka ajeshi mana
A'a, ya fada sannan ya dauke kansa yana cigaba da fadin, Idan sabo da nine na juya baya na
ki fito abun ki.
Lekowa tayi taga ya juya bayan kamar yadda yace, dan haka ta fito tai saurin daukan
hijjabinta ta sanya, shiryawa tafara, yayin da Aliyu ya maida hankalin sa kan Khalipa tsayon
lokaci sannan yace, " idan kin gama zan wuce.
Can kasa tace nagama.
Juyawa yayi ya kwantar da Khalipa tare da tufa masa addu'a sannan ya mike har ya wuce ya
miko hannunsa ya jawota ya hada ta da kirjinshi ya rungume.
Sosai ya rungumeta tamkar wani zai kwace ta, ajiyan zuciya yake saukewa da karfi yayin
da numshin sa yake sauka a tsakar kanta lokacin daya yake kewaye duk ilahirin jikinta, nan
danan taji jikinta na amsawa, bata so ta sauko da wuri haka ba dan haka ta kokarin ta dake,
daker take iya turesa take kaimasa duka.
Duk inda ta nemi ta kubce rokota yake, gashi tanayin abun ne cikin kuka gaba daya.
Aysha kiyi hakuri, bason bacin ranki nan, gaba zaki tabbatar da haka, Ina tsananin sonki
fiye da tunanin ki, kuma zanyi kokarin insaki farin wadda ba'a iya kwatantawa, kibar zargina
akan rashin cika alkawari, na farko nasan da gangan nayi, saboda tun ranar da kika gayamin
jiya kika gama al'adarki na rubuta na ajiye, Kuma saidana kirga wata tara sannan na kamo
hanya, amman wannan karon akasi aka samu, dan Allah ki nutsu ki gaya min matsalar ki
ayanzun dani, nikuma zanyi kokari in gyara komai, zama nake son muyi mekyau, Ina son ki
bani hadin kai, ya kasance ni dake har abada babu mejin kanmu, ko wani abu ya faru tsanin mu
ne kowa banson wani yaji, nasan halin ki kinsan nawa, nasan kina da taurin Kai, ni Kuma ina da
zafi idan raina ya baci, yanzun kinsan me nake so dake???
Tana kwance akirjin sa ta kirgiza kanta.
Bani shawaran hukuncin da zan dinga miki idan kin kureni da taurin kanki, nikuma zan baki
shawaran abun da ya kamata kiyi idan fushina ya tashi har kika rasa inda zakiyi dani......
https://youtu.be/Mt6vnqmJOxM
*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 58- 59
Tsintan kanta tayi da sakin murmushi tana kwance a kirjin sa, saidai ta gaza cewa komai.
Ganin haka Aliyu yadan dagota yana me kura mata ido yace, " inajin ki, kibude baki mu
nemi mafita kinji.
Kwace kanta tayi ta koma ta kwanta jikin shi, ahankali tace, ni bani da taurin Kai yaya Aliyu.
A'a, banson sonkai Aysha, ni na yadda Ina da zafi, idan raina ya baci, kema ki yadda da
taurin kanki sai mu nemi mafita kawai.
Jimmmm tayi, zuwa can tace to ai abu me saukine ya Aliyu, kawai cemin zakayi dauko
littafin ki cikin buga irin wannan tsawar taka dake rudar dani, danaji haka zan shiga hankalina.
Murmushi yayi sannan ya Kara rungume ta tare da sumbatan Kumatun ta, sannan yace,
"cemin zakiyi danaga kin fara tirjewa sai in hade fuska in koma Malam Yaya Aliyu?
Kai ta daga tana mejin wani farin ciki na shiganta cikin zuciyarta, ahankali tace kaifa ya zan yi
dakai toh.
Kanta ya rungume sosai akirjinsa, yana Jin saukan numfashin da take har cikin zuciyar sa,
sannan ya fara fadin, " idan Kinga raina ya baci har na fara fada, kinsan me zakiyi??
Kaita girgiza tare da fadin, " a'a"
Ahankali yace, " kurma zaki zama, duk abun da zance karki kulani, idan Kuma tambaya ce
nayi, amsa kawai zaki bani, iyaka gaskiyar ki, har sai kin Bari na gama sai kice Allah ya huci
zuciyar ka mijina abin alfahari na.
Cikin sauri Aysha ta dago ta kalleshi cikin idon, Yaya toh ai wannan wayo ne kamin, idan
Kuma maganganun ka sun sauka daga kan layi fah???
Eh duk da haka dai hakurin Zaki bani, idan akwai kalmar da kike ganin batai miki ba, bayan
kin tabbatar da na huce saiki same ni da ita, nikum insha Allahu zan miki a dalci.
Ciki da gamsuwa tace shikenan.
Yauwa Aysha barin zo inje gida Kinga dare yayi sosai, gobe zan zo, me zan kawo muku??
Babu"
Akwai, kiyi tunani da kyau.
Allah babu, idan Kuma akwai goben sai in gaya maka.
Amsawa yayi, cike da gamsuwa ya saketa sannan ya juya ya fita.
Koda ya fito falon Abba kawai ya samu, tambayan sa yayi Ina aunty, amsa ya bashi da
tana falon Abban mu, dan haka yace masa kace mata na tafi da safe zan dawo.
****
Gida Aliyu ya koma cike da tunanin Aysha, sosai yakejin nutsuwa na shigarsa mara iyaka,
rabon da yaji irin sa ya manta, bacci yayi me dadi, hakama bayan ya dawo sallah Kara
kwanceya yayi wadda har ya dauke sa 11:30 sannan ya tashi, wanka yayi sannan ya shirya
cikin manyan kaya da hula, fitowa yayi da nufin zuwa gidan aunty, saidai yana fitowa suka hadu
da Baffah, cikin sosa kai ya gaida shi bayan ya amsa ya wuce ya shiga motarsa ya zauna,
harya tada motar yaji Baffah na cewa Hajiya na neman ka.
Amsawa yayi da toh sannan ya fito agidan.
Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce, afalon ya sameta cikin tsananin Jin nauyinta ya gaidata, fada
ta fara masa akan baya kula mutane ko zuwa gidan ta yanxun baya yi, yayin da ya bata uzurin
aikin sa ne baya bashi daman haka akarshe yace zai dinga kokartawa yana zuwa.
Jinjina Kai tayi cike da gamsuwa sannan tace, jiya Babanka yazo min da wani labari mara
dadi, duk da cewa kaddarace amman babu dadi Sam, Kuma baka kyautawa iyayen ka ba damu
baki daya. Kaga na farko daga mahaifin ka har mahaifiyar ka sun jaka ajiki, suna nuna maka
kauna, basuki su mika komai nasu agareka ba dan me zaka rufe su?, Ran Baban ka ya bacci,
amman natunatar dashi cewa idan ka gaya mishi Yaya za'ayi agujewa kaddara, nabashi hakuri
dan haka kaima ka sameshi ka bashi hakuri, dan kayi kuskure gaskiya.
Kawar dakai yayi ya fesar da ajiyan zuciya sannan yace, " toh nagode Hajiya, na karma
kuskurena kuma Ina tabbatar maku ba abun da nayi da gangan kawai na tsinci kaina acikin
kaddara ne, insha Allahu zan kiyaye.
Allah ya baka iko, dan Allah ku dinga neman shawara, yanzun acen matar taka tana gidan
Yayarka ko?
Eh tana can.
Toh ya kake gani, babu matsala?, Idan da matsala ka kawota nan ta zauna dan gaskiya
yariyar tana bukatan kulawa.
Babu wata matsala Hajiya insha Allahu.
Allah yasa, duk wadda yai maka fada cikin 'yan uwa kabashi hakuri, domin jiya Baban ka
dun ya tarasu yace masu kayi aure har matar da haihu babu sanin sa, wasu daga ciki ransu ya
baci nima nayi fushe dakai lokacin saidaga baya yamin bayani, dan haka duk ma wadda yazo
maka fada ka saurareshi kawai bayan ya gama ka bashi hakuri.
Nagode Hajiya.
Toh shikenan, Sai Kuma mgn ta gaba, Abbas yace baka taba lekawa gidan shiba tunda yai
aure?
Juyowa yayi ya kalli Hajiya sannan yace, " lallai ma yaron nan ya raina ni, me zanje gidan shi
inyi?, auto zuwan da nake ma gurin aikin sa mu gaisa be ishe shi ba har ma so yake Kuma in
dinga zuwa gidan shi.
A'a to meye dan kaje gidan nasa?, Baka so kuyi zumunci ne??
Haba kanina ne fah Hajiya..
Wani irin kallo ta masa sannan tace ta yaya ya zama kanin naka?, kenan Kai baka da
azumunci.
Ni ba haka bane Hajiya gidan sane dai bazanje ba, duk sanda nabi ta office din su in shiga,
amman kawai saina tashi gotai gotai dani inje gidan sa.
Waini Tsaya in tambaye ka kaita Abass din waye gaba ne??
Cikin sauri yace, nine Hajiya.
Bakai bane, ai inajin Abbas yayi shekara da watanni yana shakar iskan duniya sannan aka
haifika.
Wai da gaske Hajiya??
Sosai ma kuwa, kaje ka tambayi iyayen ka, shi bece ya girme ka ba yake son zumunci sai
Kaine zakace wani wai gotai gotai son girma kamar gyanbo.
Dariya Aliyu yayi sanan ya mike yana fadin karma ki gaya masa wai ya girmeni dan Allah
Hajiya, idan na samu lokacin zanje.
Da haka sukayi sallama da hajiya, masallaci yaje daganan bayan yayi sallah ya wuce gidan
aunty yana me cike da farin ciki.
Tun kafin ya shiga falon yakejin muryanta ita da Sadiya suna hira cikin fulatanci dake
aunty najin yasa itama Sadiya ta iya, sallama yayi ya shiga, yayin da duk suka waigo suka
kalleshi cikin girmamawa, Aunty ya gaida yayin data amsa cike da sakin fuska, itama Sadiya
gaidashi tayi yayin daya sata kallon Aysha dake durkushe gaban aunty tana rufe wata roba.
Kawar da idon sa yayi adaidai lokacin data ce Ina wuni?
Lafiya Lau ya fada kansa agefe yayin da yaci gaba da cewa Aunty me kuke hadawa ne naga
duk hankalin ku ya dauke?
Kanina turare ne irin na wuta, jiya kuma saika wuce babu sallama bare godiya.
Murmushi yayi sannan ya maida da hankalin sa kansu yana cewa, "aini aunty baki taba
sani farin ciki kamar yadda kika Sani jiya ba, sai jiya na dada tabbatar da cewa lallai bakaramin
so kike min ba.
Dariya Anuty tayi tare da fadin, " gara daka gane, ai Ina son ka, Kaine kaita shareni agarin
nan, Kuma abun da yasa ban gaya maka ba, Aysha cewa tayi indai gunka zan kawota bazatazo
ba, dan tana fushi dakai....
Satan kallon Aysha yayi sannan yace, " aunty wannan mgnr fa babu ita, an dade da wuce
gurin ko Aysha??
Satan kallon Aunty Aysha tayi sannan ta sunkuyar da kanta.
Cike da murmushi Aunty ta dubi Aysha tace wai babu ita Aysha??
Cike sauri ta kawar da idonta sannan ta daga Kai.
Aliyu ne yace da baki Zaki gaya mata.
Cike da Kunya Aysha ke buye fuskanta yayin da aunty tashiga tafa Hannu tana fadin,
"yanzun duk wannan uban fushin da kikayi tashi daya kanina ya rugujeshi
Shiko Aliyu fadi yake, "Aysha ki bude baki kiyi mgn, ganin tana kara boye fuska ya mike
yana kokarin zuwa gurin su, ganin haka Aysha tai saurin mikewa