Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
dan ta tabbatar yanzun Innawo ta hakura"
Sai yamma Aliyu ya fito sannu yai masu kamar yadda ya saba Innawo kadai ta amsa har
yakai kofar gida ya dawo, daf da Ummi ya tsaya Ummi nai miki laifi ne??
A'a tafada kai tsaye"
Naga nace muku sannu baki amsa ba"
Bakaji bane na amsa"
Lumshe ido yayi sananna ya sake cewa to natafi kinji Ummi"
Daga murya tayi da Dan karfi tace adawo lafiya"
Allah yasa yafada sannan ya juya ya fice"
Bayan sati daya
Misalin karfe biyu na rana Innawo ta hango farin hannu yana rike labulen falon, adaga arufe
har kusan sau biyar dan haka cikin daga murya tace waye nan?
Ahankali cikin wani irin zazzakar murya tace nice"
Kecewa?
Sakin labulen tayi ahankali tace Aysha ce"
Au Aysha kece kike leke, shigo mana"
Labulen ta daga ta shigo tana share hawayen fuskanta, gaida Innawo tayi sannan ta juya
barayin Ummi tace, Ummi ina yini?
Lafiya Ummi tace cikin kawar da kanta tare da kirne fuska"
Innawo ce ta sake cewa Aysha kwana biyu, ya mamaki?
Lafiya lau"
Madallah, Innawo ta fada sannan ta sake cewa ai Kuna haduwa da Husna amakaranta ko?
Kai ta daga tare da fadin, " Innawo Ya Aliyu na nan inason ne zai dubamin wani abu?
Aliyu baya nan Aysha amman nasan ya daf daf da shigowa.
Idonta cike da hawaye tace tam, juyawa tayi tare da fadin sai anjima.
Abakin kofar fita sukaci karo da Aliyu yana kokarin shigowa gidan
Cikin sauri ta kauce ta bashi hanya ya wuce yayin data shiga wasa da yatsun hannunta, ganin
yana kokarin wucewa abun sa yasata saurin cewa ina wuni cikin fullacin daya rike bakinta ram
Kallonta yayi yayin data karayin kasa da kanta yace, " lafiya ya gida"
Lafiya lau"
Kallon sama da kasa yai mata sannan yace, " meyasa kwana biyu bakizo ba"?
Kanta akasa yayin data tsananta wasa da hannun ta, kur ya mata tsayon lokaci sannan
yaga ta saki hannunta tare da dagawa takai daya tana share hawayen fuskanta, tsayon lokaci
ya dauka yana nazartanta zuwa can ya mika hannun sa ya zaro littafinta guda biyu dake
tsakankanin kirjinta da cinyar hannunta, fuskarta ya sake kallo har yanzun hawaye ne ke
tsiyayowa tana sharewa, dauke idonsa yayi sannan ya bude littafi ahankali ya fara duba
shafukan, abun da ya lura dashi tun daga lukacin da tabar zuwa akwai ci baya a yanayin Makin
da take samu lokacin da take zuwa bayan ya kare bude shafukan da akwai rubutun ta akai ya
rufe littafi sannan yai mata wani irin kallo ya mika mata ta amsa tare da zuba mata rankwashi
akanta sannan ya bude daya littafin kamar ba shine yai rankwashin ba.
Hawayenta ne ya karu, yayin da suke zubowa Babu kaukautawa.
Rufe littafin yayi domin shima dai irin dayan ne mika mata yayi ta amsa sannan ya fara
takawa da sauri da sauri yana nufar kofar da zata sadashi da falon.
Cikin sauri tabi bayansa cikin kokarin son ta cin masa harsai da ta hada da gudu amman
dun da haka kafin tashiga babban falon gidan har ya shige dakin sa.
Hake take sosai lokacin da tabbatar ya shige dakin sa, tsaye tayi tsakiyar falon sai
yanzun ta kulla da hararan da Ummi ke zabga mata afakaice, cikin sauri ta dauke kanta ta
mayar da hankalin ta kan kofar dakin Aliyu.
Ba jimawa ya fito ya zauna afalon, ahankali Itama Aysha ta zauna Dan nesa dashi akasa,
Kamar kullum ya shiga yimata bayani cikin nutsuwa da daukan hankali"
*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata
atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida,
sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na
musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan
kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no 07014197556*
Ummi dake gefe ma kallo tabi Aliyu dashi saboda yadda yake mata bayani daki daki dole
nema mutum ya fahimta sannan daya fara yi mata bayani cikin harcen french yake baya taba
sako kowwanni yare, har suka gama karatun Ummi na kallo Kuma tana saurare, murmushi tayi
har cikin zuciyarta sanan ta sake dagowa ta kalleshi, tunda ya zauna agorin har yanzun idon sa
nakan littafin ko sau daya beyi kuskuren dago idon sa ya kalli wani guri daban ba, gani tayi ya
rufe littafin tare da mikewa yana kokarin shiga dakinsa yake fadin shikenan kije gida sai gobe
kuma.
Itama Aysha littafinta ta dauka sannan ta mike ta kalli inda Ummi take tace, Ummi sai
anjima"
Tsintan kanta tayi da amsa mata, bayan ta wuce ta bita da kallo, me kama da harara"⅝
*********
Ai saidai ki koma inda kika fito tun da ke kince kunnen Kashi gareki.
Mama karatu naje fah"
Wa kika gayawa wa da kika tashi fita??
Mamma kona tambaya ai ba barina kuke yi ba ke da Umma"
Cikin fada Umma tace shine ai aka ce miki ki koma inda kika fito, badai gidan Innawo ba?, ki
koma can ki zauna tunda kince ke sarakan yan naci ne ke"
Mama kiyi hakuri kinji?
Tsawa Umma ta buka mata, bace a gurin wuce kibamu guri marajij mgn kawai.......
Afakaice Aysha ta harari Umma tare da fadin, Umma ba ruwan ki"
Au Babu ruwana ma kike cewa, takalmin dake kamafarta tacire tafara dukan Aysha dashi
duk da cewa bawani da karfi take bugawa ba amman sosai Aysha ta hade fuska tare da kallon
fuskar mamanta, gani tayi mama ta dauke kanta daga kallon su yayin da Umma kecigaba da
fadin, ko tsinken ki karki barmin ki koma gidan Innawo"
Afusace Aysha ta mike ta nufi dakin mama jakar makarantar ta ta goyo tazo ta wuce su ta
fice daga gidan"
Hanyar gidan Innawo ta kamo, idonta bushe, saida tazo kofar gidan sannan ta tuna
fuskar Ummi, cak ta tsaya, ahankali ta juya ta kalli gidan su, hawaye ne taji suna sakkowa kan
idonta, yatsun hannunta ta zubawa ido yayin da take matsa yatsun nata da daya hannun ta tayi
tana dagowa tana kallon gidajen guda biyu wadda tasa su a tsakiya.
Hawaye ta share afili tace, bazan iya shiga gidan Innawo ba, haka Kuma bazan koma
gidan mu ba, wani shashine na zuciyarta ke tambayanta ina zakije toh?, Kara matsa hannunta
tayi sannan tace"
Bansan ko inaba sai makaranta, hawaye ta share sannan ta nemi wani dan tudu ta zauna
tare da fadin anan zan zamana gobe inje makaranta......
Fadeela Lamido ✍️
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
*Episode 5- 6*
Zama Aysha tayi agurin tsayon lokaci, wani irin haushi Umma ke bata domin tasan idan babu
Umma Mama bazata koreta ba.
Yamma ce tayi sosai kasancewar yanayin damina, tuni hadari ya hadu sama na shirin zubo da
ruwa amman Aysha ko ajikinta, tana zaune jakar makarantar ta goye a bayan ta kananan kaya
ne ajikin ta riga da siket, sai hular dake kanta wadda ya matse tarin tudun gashinta a tsakiyar
kanta, kasancewar ta farar bafulata cikin bakaken kaya yai matukar fitar da kyanta, Babu abun
da take sai raba idon ta tana kallon mutane da motocin dake ta rige rige wucewa dalilin iskan
hadarin dake tasowa, bakajin komai sai Karan iska hadari da Karan motoci.
**********
Agoje yake Jan motar domin isa gida akan lokaci, bayan ya faka motar akofar gidan nasu ya
sakkowa tare da waiwayowa bayan sa yana kallon yariyar dake zaune nesa dashi.
Cikin zafin nama ya fara takowa domin tabbatar da abun da yake tunani, gabanta ya tsaya
tare da fadin, ke!!!
Azubure ta mike tsaye tare da tsallaka kwatar dake gurin batare data sani ba.
Cak ta tsaya, kanta akasa.
Cikin kausasassar murya yace me kike anan gurin??
Umma da Mama suka kore ni"
Idonsa akan hadarin dake shirin sakkowa yace me kika musu?
Wai dan nazo kamin karatu"
Lumshe ido yayi sannan yace tun yaushe?
Sai yanzun ta dago ta sata kallon sa tana fadin, tun da nadawo gida"
Kallonta yayi cikin ido yayin da tai saurin yin kasa da kanta, yawu ya hadiye sannan yace,
kika kasa basu hakuri Kuma?
Na basu fa amman sun ki"
Hannun sa yasa daya cikin aljihu sannan yace sau nawa kika basu hakurin"
Uku ta fada tare da gyra siket dinta da iska hadarin ke kokarin yayewa"
Ke! Ya sake cewa karo na biyu bayan ta dago idonta ta kalleshi yace, " ki wuce ki koma
gida ki basu hakuri"
Kwal kwal tayi da idonta cikin shirin yin kuka, tana nifa na basu hakuri basu hakura ba, ni
nan zanyi zamana gobe innaje makaranta sai in zauna acan"
Lumshe idon sa yayin jin ta ambaci makaranta, zuwa can ya bude idon nasa tare da fadin, "
ke wai ina wasa dake ne, ki wuce gida ki basu hakuri nagaya miki, kina nufin anan gurin zaki
kwana??
Cikin sauri ta daga kanta"
Wani irin kallo yai mata sannan yace shikenan, juyawa yayi ya nufi gida, binsa da kallo
Aysha tayi harya kule sannan sannan ta koma ta zauna"
Zuwa can ta hangosa ya Kuma fitowa cikin sauri ya nufa masallaci"
*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata
atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida,
sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na
musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan
kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no 07014197556*
Zamanta tayi tana kallon duk wani me wucewa, zuwa can aka fara fitowa masallaci dauke
idonta tayi dan gudun kar karsu hada ido da Aliyu, muryar sa taji daga dan nesa da ita yana
fadin, " kina da taurin kai ko"?
Mikewa tayi ta shiga wasa da hannunta Kamar yadda ta saba kanta akasa tace, " ni a'a
fah kaine kace in zauna"
Ni Kuma?, ke baki san gatse ba?
Shiru tayi idonta akan yatsun hannun nata
Domin batama gane me yake nufi da gatsen ba, duk da cewa cikin fulatanci suke mgnr
Kara daure fuskan sa yayi sosai sannan yace, " ke kin sanin kuwa?, maza kije ki basu
hakuri nasake fotowa naganki anan gurin saina baki kashi wlh, kinji Kuma na rantse"
Tafiya ta fara yayin dayai tsaye agurin yana kallon ta, itako tafe take tana waiwayen sa
saida Aliyu ya tabbatar ta isa kofar gidan nasu sannan ya nufi gida, cikin ikon Allah yana shiga
gidan ruwan saman daya dade yana hada hadari ya sakko, ruwa ne ya kece sosai.
*********
Dadin yanayin da ake cikin na ruwan sama yasa Aliyu zama cikin su Ummi yaci abinci, Koda
ba mgn yake yi ba, Amman yana sauraron hiran Innawo da Ummi saidai in sunyi abun dariya
yai murmushi har yagama cin abincin ya mike yana fadin, saida safe"
Amsa masa sukayi sannan suka cigaba da hirar su.
Aliyu kuwa bayan ya shiga daki wanka yayi
Sannan yai shirin bacci ya kwanta tare da rufa cikin bargonsa me shigen laushi, addu'ar
bacci ya karanta sannan ya lumshe idonsa yana mejin saukan ruwan saman da aketa zugawa"
Sosai yakejin dadin yanayin idonsa alumshe yanajin saukan ruwan saman daketa kwaranya,
hiran Ummi da Innawo ya tuna dan haka yadanyi murmushi tare da gyara kwanciyarsa"
Bacci ne ya dauki sa, yayin da can cikin baccin yakejin hayaniya sama sama, ahankali ya
bude idonsa har yanzun ruwan ake zubawa sannan ga hayaniya yanaji wanda be sanin me ake
cewa, tashi yayi ya zauna yana me Kara baza kunnen sa, yaye bargon yayi gaba daya ya
sauko ya nufi window tare da yaye labulen, Kakar Aysha yagani tare da mahaifiyarta da wasu
maza biyu manya sai masifa suke cikin tsakiyar ruwan sama duk sun jike, cikin sauri ya saki
labulen tare da nufar kofa, karo sukaci da Innawo cikin yanayin rudu tace kai *Ali* kaga Aisha
wai??
***********
JIGON LABARIN
*Aliyu* dane ga Alhaji Bello Kano, shahararren dan kasuwa Kuma masu fada aji, mahaifiyar
Aliyu mutuniyar Cemaroon ce, bafulatana, yar asalin kasar Camaroon, sun hadu da Alhaji Bello
ne a kasar Camaroon alokacin dayaje domin kasuwanci, Soyayya ta kullo tsakanin su har
takaisu ga aure, saidai kafin aurenta da alhaji Bello ta taba aure har da yaranta biyu namiji da
mace wadda alokacin ita macen me sunan Ruqayya an auren da ita tana zaune da mijinta a
Kano Nigeria, dan haka da Alhaji Bello ya nuna ra'yin sa akanta tai farin ciki domin zata zauna
kusa da 'yarta, shiko Alhaji Bello irin mazan nan ne wadda suka jima basuyi aure ba, sai akan
Fatima, cikin farin ciki Fatima ta taho aure Nigeria tabaro Babban danta Fahat can CAMAROON
gurin mahaifiyarta, Fahat shine yayan Ruqayya, sai dai shi yana da lalurar tabin hankali, sai dai
Allah be kaddara dogon zama tsakanin Fatima da Alhaji Bello ba, domin kuwa tana da cikin
Aliyu wata daya suka rabo, dan haka ta tattaro ta dawo CAMAROON anan tayi rainon cikin ta,
bayan wata 8 ta Haifi danta katon gaske saidai bashi da hasken Fata kamar na Fatima,
mahaifin sa Alhaji Bello yazo ya ganshi, inda yai masa huduba da Aliyu, sannan yayi duk wani
abu da yadace uba yayi alokacin da aka haifan masa da, sannan ya koma Nigeria"
Fatima tacigana da rainon Aliyu cikin so da kauna, hakama mahaifiyar ta Innawo tana nuna
tsananin soyayyarta wa Aliyu,