Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
bayan Aliyu yafara girma suka sanyashi makaranta sosai yake
maida hankalin sa kan karatun sa, bayan ya kara girma ne suka kula da wasu dabi'u nashi,
yana da son yara kanana, sannan Koda yaushe fuskarsa sake take amman mgnr sa ya kanyita
ne ciki ciki kuma bada kowa yake mgn ba sai yaga dama, ta wani bangaren ana iya kiransa
miskili, shidin kaifi daya ne, yana sa gabansa ne kawai abun da yasa gaba sannan baya daukan
raini, idan ransa yabaci kuwa be iya fushi ba, ahaka Aliyu ya taso cikin kulawan dagin
mahaifiyarsa lokaci bayan lokaci mahaifin sa nazuwa ganin sa, sannan akowanni lokaci yana
aiko masu da sako babu laifi"
Aliyu yana da kimanin shekara 10 yayar sa Ruqayya ta kawo masu ziyara CAMAROON
lokacin data tashi komawa ta nemi da abata Yayanta Fahat ta tafi dashi Nigeria domin neman
masa magani, komai sai an masa baya iya yiwa kansa komai, haka kuwa akayi Ruqayya ta tafi
da Fahat, yayin da Innawo da Fatima suka maida hankalin su gaba daya akan Aliyu, a yanzun
haka Aliyu yana daf da kammala karatun sa na gaba da secondary, Aliyu matashin saurayi ne
meji da kansa, wadda bazai wuce shekaru 25 ba, yana da matukar kokari amakaranta yana da
tsanin tafta wadda har take son ta wuce misali, Kuma har wannan lokacin Fahat yana gurin
kanwarsa Ruqayya kullum cikin nema masa magani take amman har yanzun ba'a dace ba
Kasancewar Fatima Bafulatana ce ita da danginta yasa fullanci ya zauna bakin Aliyu sosai,
dan yanzun haka duk wata magana da zasuyi cikin harcen fullaci sukeyi duk da cewa Fatima
tanajin hausa kadan kadan hakama Innawo tana gane wasu abubuwan, haka Kuma abangaren
makaranta boko anayin amfani ne da french dan haka ya kejin french sosai, saidai Aliyu mutum
ne meson jin yaruka da yawa dan haka ya nemi ajin English tun yana secondary School yana
hadawa dashi, ayanzun haka Aliyu yana jin yaruka 4 Hausa Fulatanci English French.
Wannan kenan.
Abangaren Aisha kuwa, iyayen Aisha gaba dayan su Mutanen CAMAROON ne uwa da
uba, yayin da mahaifiyar Aisha ta kasance Fulani, maifinta Kuma kirista ne, kaddara ta hadasu
aure wanda basu jima tare ba, Aisha nada shekara uku suka rabo, kasancewar sa ba musulmi
bane tai zafin naman tattaro diyarta ta rike gunta, duk da cewa me kudine sosai Babban
ma'akacin gwamnati, Bilkisu wato mahaifiyar Aisha kyakayawace sosai fara tas hakama Aysha
ta dauko farin fatan da kyau gurin uwarta, Koda shima mahaifin Aisha fari ne tas, Kuma yana
tsananin son Aisha tare da kawo mata ziyara duk lokacin da yaso ganin ta, bata nemi komai ta
rasa ba, domin mahaifinta tsaye yake akan karatun ta bashi da wani buri daya wuce yaga Aisha
cikin farin ciki"
Haka itama Aisha tana son Daddyn ta sosai da sosai har bata iya banbance wadda tafi so
tsakanin sa da Maman ta, tun da ta taso yariya ce meson karatu sosai, fiye da tunanin me
karatu, na boko dana bangaren addini, hakama Mamanta da kakarta Umma suna bata kulawa
gurin karatun nata, Aisha yariya ce meson wasa da dariya Kuma me jajircewa akan abun da
tasa gaba, yanzun haka tana aji daya na secondary School, Aisha yaruka biyu kawai take iyaji,
fullanci sai Kuma french wada da dashi ake masu karatu amakarantar boko
*CIGABAN LABARIN*
Lumshe idonsa yayi sannan yace, "eh naganta dazon"
Ka ganta?, Ina take toh??
Kafin ya bude baki Umminsa ta karaso ta kure sa da ido, inda Innawo ta sake cewa ina
jinka"
Innawo nace miki dazon naganta zaune a kofar gida nace mata ta Koma ta koma gida"
Wani irin kallo mahaifiyar tasa ta masa me cike da tuhuma sannan tace bayan Kun gama
karatun ina ka kaita?
Ni?
Eh kai fah"
Ummi nifa tasowan hadarin nan da nadawo nasameta awaje ne kawai, Dana mata tambaya
tace min Koranta akayi agida sabo da ta zo karatun daker nasata ta koma gida, Kuma banbar
gurin ba har saida naga shiganta gida"
Cike da bacin rai Ummi tace zo ka fita kaje ka fito masu da yarsu"
Wani irin kallo Innawo tama Ummi ya nemota a ina?, kinaji yace saida yaga shiganta gida,
suje can su nemeta suna sonta ai basa koreta ba, yar karamar yariya kamar Aisha tun rana
basu tashi nemanta ba sai yanzun?, wannan shiri ne kawai"
Innawo ai shima yanzun bashi da mafita fah, tunda an gansu tare"
Yana dashi da karfin ikon Allah"
Juyawa Aliyu yayi ya nufi dakinsa ba jimawa ya fito cikin sauri yana kokarin gyara wuyan
rigarsa daya sanyata yanzunan yana me motsa labban sa, tare da nufan kofar da zata sadashi
da tsakargidan nasu"
Zo nan me kake cewa?, Ummi ta tambaya bayan ta tabbatar daya yayi mgn"
Lumshe idonsa yayi sannan yace cewa nayi saina zane ta"
Cikin yanayin dake nuna taji mamaki tace sabo da kaine ka haifeta?
A'a saboda ta fidda ni acikin ruwa Kuma saida nace ta koma gida, kenan kunnenta bamejin
mgn bane.....
Toh waye ya aikeka fita cikin ruwan?, Innawo ta jefa masa tambayan bayan ta tsare sa da
ido"
Kansa ya dan shafo kadan sannan yayi wuf yashige cikin ruwan saman dake sauka kamar da
bakin kwarya"
Koda ya fito kofar gidan yan gidan su Aysha ne duk acikin ruwan saman sai haske haske
suke yi tare da surutai wadda bayajin me suke fada saboda Karan ruwan saman da ake
kwararawa"
Bebi ta kansu ba ya wuce abun sa, tafiya yake yana duba Aysha duk wani lungu da sako
saida ya duba, gaba daya ya jike sharkaf yana tsiyayan ruwa, gaba daya unguwar ya gama
zagawa babu Aysha babu alamarta
gashi dare nakara nisa, baban abun da yafi tayar masa da hankali kankantar shekarun ta, ko
wani hali take ciki yanzun duk wannan ruwan da ake ina take?, ta fakewa ruwan ko bata fake
ba?, jikinsa ya kallah yadda ya jike sharkaf gawani irin iska wanda yakejin tamkar zatai sama
dashi, sosai hankalin sa ya kara tashi, ruwa yaki tsayawa tsayon lokaci, gashi baya tunanin
akwai inda be duba ba lungu da sako nacikin unguwar, dan haka yayi tunanin komawa gida
watakila zuwa yanzun Aisha ta koma gida"
Zuwa wannan lokacin babu kowa alayin nasu dan haka yaji sanyi cikin ransa yana me
tabbacin anganta, sai dai yana daf da shiga gidan ya hangi su Innawo da Ummin sa sunfito
daga gidan su Aisha duk sun gama jikewa, kasa hakuri yayi ya karasa yana fadin, " an ganta"?
Inafah, suna nan sun kafe cewa ka fito masu da 'yarsu"
Lumshe ido yayi batare da yace komai ba ya juya ya shiga gida"
Koda Innawo ta shigo babu abun da take kira sai sunayen Allah "
Sosai hankalin Ummi dana Innawo ya tashi, baban burin su ayanzun be wuce ganin Aisha
ba, Innawo tagumi ta zuba lokaci bayan lokaci tana fadin, "munshiga uku"
Fitowan Aliyu cikin kananan kaya tare da katuwar rigar sanyi yasa duk suka dago suka
kalleshi, ina zaka?, Ummi ta fada?
Zan dauki mota ne in kara bincikata"
A'a kazauna agida, tunda sun tura kanin Mamanta ya kira police"
Lumshe ido yayi tare da Kara tura hannunsa cikin aljihun rigarsa sanyin dake jikin sa
sannan ya fara takowa ahankali, daf da Innawo ya zauna tare da daukan kafarsa daya ya daura
kan daya, ahankali ya fito da hannun sa na dama daga cikin aljihun sweet ya shiga barewa
sannan ya jefa abakin sa ya shiga tsotsa ahankali"
Ummi ce ta bishi da kallo yadda yake tauna cigam dinsa bakace wani abu na damun sa ba
har wani dan girgiza kafarsa yake yi, kwayar idon sa fari karrr gawani farin ruwa kwance acikin
sa, kwayar idon kawai kake gani suna juyawa, motsin da Ummi taji a tsakar gidan nasu yasata
maida hankalin ta ga kofar falon, mamakin da taji yasata kallon agogo karfe 01:15am.....
Fadeela Lamido ✍️
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
*Episode 5- 6*
Zama Aysha tayi agurin tsayon lokaci, wani irin haushi Umma ke bata domin tasan idan babu
Umma Mama bazata koreta ba.
Yamma ce tayi sosai kasancewar yanayin damina, tuni hadari ya hadu sama na shirin zubo da
ruwa amman Aysha ko ajikinta, tana zaune jakar makarantar ta goye a bayan ta kananan kaya
ne ajikin ta riga da siket, sai hular dake kanta wadda ya matse tarin tudun gashinta a tsakiyar
kanta, kasancewar ta farar bafulata cikin bakaken kaya yai matukar fitar da kyanta, Babu abun
da take sai raba idon ta tana kallon mutane da motocin dake ta rige rige wucewa dalilin iskan
hadarin dake tasowa, bakajin komai sai Karan iska hadari da Karan motoci.
**********
Agoje yake Jan motar domin isa gida akan lokaci, bayan ya faka motar akofar gidan nasu ya
sakkowa tare da waiwayowa bayan sa yana kallon yariyar dake zaune nesa dashi.
Cikin zafin nama ya fara takowa domin tabbatar da abun da yake tunani, gabanta ya tsaya
tare da fadin, ke!!!
Azubure ta mike tsaye tare da tsallaka kwatar dake gurin batare data sani ba.
Cak ta tsaya, kanta akasa.
Cikin kausasassar murya yace me kike anan gurin??
Umma da Mama suka kore ni"
Idonsa akan hadarin dake shirin sakkowa yace me kika musu?
Wai dan nazo kamin karatu"
Lumshe ido yayi sannan yace tun yaushe?
Sai yanzun ta dago ta sata kallon sa tana fadin, tun da nadawo gida"
Kallonta yayi cikin ido yayin da tai saurin yin kasa da kanta, yawu ya hadiye sannan yace,
kika kasa basu hakuri Kuma?
Na basu fa amman sun ki"
Hannun sa yasa daya cikin aljihu sannan yace sau nawa kika basu hakurin"
Uku ta fada tare da gyra siket dinta da iska hadarin ke kokarin yayewa"
Ke! Ya sake cewa karo na biyu bayan ta dago idonta ta kalleshi yace, " ki wuce ki koma
gida ki basu hakuri"
Kwal kwal tayi da idonta cikin shirin yin kuka, tana nifa na basu hakuri basu hakura ba, ni
nan zanyi zamana gobe innaje makaranta sai in zauna acan"
Lumshe idon sa yayin jin ta ambaci makaranta, zuwa can ya bude idon nasa tare da fadin, "
ke wai ina wasa dake ne, ki wuce gida ki basu hakuri nagaya miki, kina nufin anan gurin zaki
kwana??
Cikin sauri ta daga kanta"
Wani irin kallo yai mata sannan yace shikenan, juyawa yayi ya nufi gida, binsa da kallo
Aysha tayi harya kule sannan sannan ta koma ta zauna"
Zuwa can ta hangosa ya Kuma fitowa cikin sauri ya nufa masallaci"
*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata
atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida,
sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na
musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan
kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no 07014197556*
Zamanta tayi tana kallon duk wani me wucewa, zuwa can aka fara fitowa masallaci dauke
idonta tayi dan gudun kar karsu hada ido da Aliyu, muryar sa taji daga dan nesa da ita yana
fadin, " kina da taurin kai ko"?
Mikewa tayi ta shiga wasa da hannunta Kamar yadda ta saba kanta akasa tace, " ni a'a
fah kaine kace in zauna"
Ni Kuma?, ke baki san gatse ba?
Shiru tayi idonta akan yatsun hannun nata
Domin batama gane me yake nufi da gatsen ba, duk da cewa cikin fulatanci suke mgnr
Kara daure fuskan sa yayi sosai sannan yace, " ke kin sanin kuwa?, maza kije ki basu
hakuri nasake fotowa naganki anan gurin saina baki kashi wlh, kinji Kuma na rantse"
Tafiya ta fara yayin dayai tsaye agurin yana kallon ta, itako tafe take tana waiwayen sa
saida Aliyu ya tabbatar ta isa kofar gidan nasu sannan ya nufi gida, cikin ikon Allah yana shiga
gidan ruwan saman daya dade yana hada hadari ya sakko, ruwa ne ya kece sosai.
*********
Dadin yanayin da ake cikin na ruwan sama yasa Aliyu zama cikin su Ummi yaci abinci, Koda
ba mgn yake yi ba, Amman yana sauraron hiran Innawo da Ummi saidai in sunyi abun dariya
yai murmushi har yagama cin abincin ya mike yana fadin, saida safe"
Amsa masa sukayi sannan suka cigaba da hirar su.
Aliyu kuwa bayan ya shiga daki wanka yayi
Sannan yai shirin bacci ya kwanta tare da rufa cikin bargonsa me shigen laushi, addu'ar
bacci ya karanta sannan ya lumshe idonsa yana mejin saukan ruwan saman da aketa zugawa"
Sosai yakejin dadin yanayin idonsa alumshe yanajin saukan ruwan saman daketa kwaranya,
hiran Ummi da Innawo ya tuna dan haka yadanyi murmushi tare da gyara kwanciyarsa"
Bacci ne ya dauki sa, yayin da can cikin baccin yakejin hayaniya sama sama, ahankali ya
bude idonsa har yanzun ruwan ake zubawa sannan ga hayaniya yanaji wanda be sanin me ake
cewa, tashi yayi ya zauna yana me Kara baza kunnen sa, yaye bargon yayi gaba daya ya
sauko ya nufi window tare da yaye labulen, Kakar Aysha yagani tare da mahaifiyarta da wasu
maza biyu manya sai masifa suke cikin tsakiyar ruwan sama duk sun jike, cikin sauri ya saki
labulen tare da nufar kofa, karo sukaci da Innawo cikin yanayin rudu tace kai *Ali* kaga Aisha
wai??
***********
JIGON LABARIN
*Aliyu* dane ga Alhaji Bello Kano, shahararren dan kasuwa Kuma masu fada aji, mahaifiyar
Aliyu mutuniyar Cemaroon ce, bafulatana, yar asalin kasar Camaroon, sun hadu da Alhaji Bello
ne a kasar Camaroon alokacin dayaje domin kasuwanci, Soyayya ta kullo tsakanin su har
takaisu ga aure, saidai kafin aurenta da alhaji Bello ta taba aure har da yaranta biyu namiji da
mace wadda alokacin ita macen me sunan Ruqayya an auren da ita tana zaune da mijinta a
Kano Nigeria, dan haka da Alhaji Bello ya nuna ra'yin sa akanta tai farin ciki domin zata zauna
kusa da 'yarta, shiko Alhaji Bello irin mazan nan ne wadda suka jima basuyi aure ba, sai akan
Fatima, cikin farin ciki Fatima ta taho aure Nigeria tabaro Babban danta Fahat can CAMAROON
gurin mahaifiyarta, Fahat shine yayan Ruqayya, sai dai shi yana da lalurar tabin hankali, sai dai
Allah be kaddara dogon zama tsakanin Fatima