Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 34

60K to 63K   out of 101.2K words

ba.

Aysha nace Ina kwana, ya jiki?

Cikin sauri tasa hannun ta tashere hawaye tare da zunboro baki.

Mikewa yayi cikin sanyin jiki yana kokarin dawowa kusa da ita, ganin haka tai saurin
mikewa.

Lumshe ido yayi sannan ya kalleta yace, " shikenan, komawa yayi ya zauna sannan yace,
jiya me ya dawo dake??

Banza tamai, tare da cuno baki.

Ina kayan ki?

Murya can kasa tace, suna can.

Inajinki meyasa kika dawo???

Ganin bata da niyar mgn yace shikenan ki tashi muje.

Mikewa tayi yana gaba tana binsa abaya

Cikin motar ma Aysha baya ta juyo ma Aliyu, Sam beson su rabo ahaka, dan haka ya kasa
tada motar sai kallonta yake yi ahankali yace, " Aysha mufahimci juna dan Allah kafin ki tafi,
kibar fushi nan beda wani amfani, bada gangan nayi ba kema kinsani, idan kika tafi kina fushi
Dani kin zalince ni.
Toni zalincin daka min fa??�� Kara juyo masa baya tayi bayan ta fadi haka.

Naji nazalinceki Aysha, amman banyi da niya ba, nata gudun kada hakanta faru, inaji
azuciyata nafiki damuwa, kwata kwata bansoba Ayaha, amman ki kwantar da hankalin ki aana
dawo zanzo.

Hawaye take sharewa nidai ya Aliyu bansan inda zansa rayuwata ba, nashiga uku.

Aysha ki nutsu Mana, ni bani da burin cutar ki, gaya jiya bayan nasaki amota meyasa kika
dawo??

Ni Yaya Aliyu kasa tafiya nayi, nafison mutafi tare, shiyasa na dawo ince maka kazo mutafi
ne kawai, Kuma ga abun da ya faru���,

Lumshe idon shi yayi, yayin da hawaye suka zobo masa, hannun sa ya mika ya jawota
suka hada kansu waje guda yana fadin, " Nima naso haka Aysha, amman baxai yiyuba bane,
wannan tafiyan dole dani acikin ta, kuma bekamata ki zauna har indawo ba, domin agida za'a
nemeki, zaman naki anan beda wani amfani idan kinyi tunani Ayaha, kiyi kahuri kije gida, kibani
wata uku na miki alkawarin zanzo, zanzo da mgnr auren ki.

Cikin kuka sosai tace zaka zo da gaske??

Zanzo ki yadda dani.

Yaya Aliyu?

Na'am Aysha

Meyasa Allah ya jarabceni da son ka har haka?

Ya jarabce mudai Aysha, Allah ne kadai yasan wannan, Aysha in tambaye ki mana?

Tam Yaya Ina jinka.

Ki share wayen ki, ki saki ranki sai muyi mgnr.

Dagowa tayi daga jikin shi ta koma kujerar tana share hawaye.

Saidai ta gama share hawayen sannan yace kinajina?

Eh.

Nawa ga wata kikeyin al'adan ki??

Cikin sauri ta sunkuyar da kanta sannan tace, " ashirin da hudu"

Jimmm yayi sannan ya kalleta yace" ashirin da hidu?, to ai yau talatin ga wata fah?

Eh, jiya nayi wanka kafin mu fito.

Leben sa nakasa ya cija da hakorin sa sannan ya fita a motar yana fadin Ina zuwa"

Kusan minti shabiyar ya dauka sannan ya dawo, idon sa jawur ya zauna amotar sannan
ya suka tafi, gudu yake dan haka nan danan suka isa

Inda ta bada ijiyan kayanta sukaje suka amsa, sanan yasa mata amotar dake shirin tashi
yanzun, Jakarta ya karba ya bude sannan yasa hannun sa ya ciwo kudi me yawa yasa aciki,
rufewa yayi kalleta, Aysha ki shiga motar karki ce zakisake sauka, nima yanzun ko gidan baxan
koma ba wucewa zanyi daga nan, sannan komenene yake faruwa a Cameroon ko wani hali
Zaki shiga karki sake cewa Zaki dawo Nigeria, ko Ina nan bazan so ki sake kamo hanyar nan
ba bare bana nan, namiki alkawarin dana dawo zanzo, kema kimin alkawarin baxaki sake kamo
hanyar nan ba sai tare dani.

Cikin sauri tace bazan dawo ba ai daman Yaya, amman kacika alkawari.

Insha Allahu Aysha

Rakata yayi har bakin motar ta shiga sannan aka rufe motar, Hannu yaita daga mata itama
take daga masa har suka daina ganin juna, sannan ya koma motar sa ya zauna tare da hada
kansa da guiwa, zaman kusan awa daya yayi agurin ya kasa tafiya, tunanin sa ko Aysha zata
dawo, Koda ya fito cikin tashar ya dade abakin hanga saida ya tabbar yanzun sun bar Kano
sannan ya wuce gidan Aunty rukayya

******

Aunty bani da lafiya.

Meye haka Aliyu, kuka kuma kake katon ka dakai, meke damun ka haka?

Bansani ba aunty, haka nan nakejina wani iri narasa inda zansa kaina naji dadi aunty.

Subuhanallah, kana addu'a kuwa?

Inayi aunty, komai da ya dace inayi, sannan Ina kokarin hana zuciyata sabon Allah, amman
hankalina Kara tashi kawai yake, idan Ina tunanin Ina cikin damuwa sai wani abu yazo ya kifto
min wadda yafi na baya, gaba daya na kasa nutsuwa.

Kana da damuwa ne Aliyu bazaka fada bane dai kawai, toh koma menene kaita addu'a.

Aunty ni ki rarrasheni, ki kwantar min da hankali kamar yadda Ummi kemin

Hmmmm, ka fara kewanta kenan, kayi hakuri kabar kukan nan kada Yaya Fahat ya gani,
idan yagani hankalin sa tashi zaiyi, lallashin ka Kuma babu wadda zai iya maka kamar nata,
waye zai zauna yana rarrashin kato kamar ka ai sai ita Ummin, da kasan danine agarinan
shekaranka biyar amman sau daya kazo gidana.
Kansa ya kwantar kan kafadar aunty Ruqayya yana fadin, kiyi hakuri na bari.

Tausayi ya bata dan haka ta daura hannunta akan sumar sa tace, " Allah ya yaye maka
abun da yake damun ka, ya Kuma kawo maka mafita.

Har cikin ransa yaji dadi sannan yai masu sallama ya fito, daga nan gida ya wuce yayi
wanka tare dayin sallama dasu Baffah, farfe 04:00pm jirgin su ya tashi.

Cameroon

Misalin 01:44pm Aysha ce ake sauke mata kayanta atasha, wata motar ta tare tana zuba
kayan tare da fada masa inda zata.

Cikin motar ta zauna duk jikinta asanyaye hanya suka kama yayin da take kallon garin nasu
duk ya mata wani iri, inda ta shiga tunanin yau watanta Uku da sati biyu rabonta da Cameroon,
gabanta taji yayi mugun faduwa, ko me zataje ta tarar agida?, Me zace masu?, Yanzun Sunan
bana gidan Daddy na, idan suna sani Ina zance masu naje?

https://youtu.be/ejQDIoQWEig

*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

episode. 30- 40



Tsintan kanta tayi da zubar da hawaye, cikin tsananin tashin hakankali take jinta sosai mara
misaltuwa, babban abun dake damun ta ada bewuce taje dan taga Aliyu taji dadi ba, amman
gashi zuciyarta har yanzun babu dadin

Hawaye ta fara sharewa ganin motar ta shiga cikin unguwar su gabanta yaci gaba da
faduwa,

Akofar gidan su motar ta tsaya, fuskarta ta share dakayu sannan ta fito cikin motar, yayin
da ake sauke mata kayanta, ahakali ta shiga Jan akwatin ta tanufi cikin gidan, gabanta na
tsanta faduwa, cikin siririyar muryanta tai sallama.

Ummace tai saurin fitowa daga cikin dakinta tana fadin, "Aysha idon ki kenan' Kinga kayana
nan nadaure Ina shirin zuwa biko, saiki tafi ki share gindi kiyi zaman ki?

Daker Aysha ta iya daurewa tace, keda ba zaman lafiya muke dake ba Ina ruwanki da
zamana.

A'a, ai da baki wlh duk gidan babu dadi, koma dai yayane nafison dai kina gidan Koda zakita
sani surutu ne, juyawa Aysha tayi domin dauko dayan akwatinta, yayin da Umma ta biyowata
abaya cikin tsananin farin ciki take cigaba da fadin"

Wlh ba irin tunanin da banyi ba, nace to ko ubanki ya riki ne, inda ko ya rikeki wlh bazan
yadda ba, ko sama da kasa zata hade saina amso ki, haba, naji ki shiru shiru, itama uwarki duk
kawaicin ta saida tagaji tai mgn, zuwa wannan lokacin har sun shigo cikin gida.

Falon Umma ta zauna akasa tana fadin Ina mamana?

Mamanki yanzun sukaje dubiya ita da Murja.

Ajiyan zuciya Aysha take saukewa ahankali ganin babu wani alamun dake nuna cewa
sunsan bataje gidan Daddyn ta ba.

Hira sama sama sukayi da Umma yayin da Umma keta nan nan da ita, wanka Aysha tayi
tai sallah sannan tahau gado ta kwanta, abun da ya faru tsakaninta da Aliyu jiya taita tunawa
yayin da take share hawayen gefen idon ta.

Wani irin bakin ciki takeji idan ta tuna tarasa budurcin ta, duk da cewa tana son Aliyu
amman wani Shashi na zuciyarta ya shiga Jin haushin sa, musamnan idan ta tuna azabar daya
gana mata duk da irin ihun da take zubawa be saurara mata ba ko ya tausaya mata ba har
saida ya gama abun da yai niyya, wannan dalilin yake sata take danjin zafin sa cikin ranta
saidai duk da haka batabar Jin sonsa ba.

Kuka tayi sosai tana daga kwance taji dawowan su mama ita da Murja, kasa kallon su tayi
dan haka tayi lamo kamar me bacci.

Daga can bacci ya dauketa, bacci tayi sosai domin Daman akwai gajiya ajikin ta, yamma
lilis ta tashi, tsakar gida ta samu Mama da Umma, Mamanta ta gaisar cikin tsanin fara'a Mama
ta amsa sannan tace ya Baban ki?, ai mun dauka ya rike ki ne"

A'a mama nice bance zan dawo ba.

Yayi miki kyau, tunda Umma tana miki zancen aure ke Kuma baki so ko??, Yaya mgnr
karatun naki me yace akai??

Mama yace zaizo da kansa kuyi mgn.

Yamutsa fuska Mama tayi, ni meye nawa, ai kin girma kema aiba yariya bace, ko dake ai
zaiyi mgn.

Umma ce tace tunda yace haka ai shikenan, yazo din munajira.

Da daddare kasa bacci Aysha tayi Aliyu kawai ke fado mata, gashi tun da Aliyu ya
kusanceta zazzabi ya sameta har yanzun batabar Jin zafin jiki ba, duk kuwa da maganin data
sha.

Washegari Umma ta kula da yawan kwanciya da Aysha keyi dan haka ta mike tana fadin,
" barin sa miki ruwan dumi kiyi wanka, na kula ke ragowa ce wannan dan tafiyan da kiya sai
wani nan nad'ewa kike yi"

Cikin kankanin Lokaci Umma ta juyewa Aysha ruwan wanka, sosai taji dadi bayan tafito
wankan maganin zazzabi tasha tare dana ciwon jiki sannan ta koma ta kwanta, kusan kwana
hudu Aysha tayi akwance sannan ta fara zuwa islamiyya, sai dai ko a islamiyyar hankalin ta
rabuwa biyu take yi, wani lokacin har a tashi bata fahimtan me ake yi, babban abun da yafi
dama mata lissafi kusantanta da Aliyu yayi ne, gashi wani shashin nazuciyarta yana ce mata
anya kuwa Aliyu zai dawo, fakar idon mutane take ta share hawaye ita kadai tasan me zuciyarta
yake mata.


Satin Aysha biyu da dawowa suna zaune ita da Umma a tsakar gida wani yaro ya
shigo yai sallama, Umma ce ta amsa tare da bin yaron da kallo.

Wai ana kiran Aysha, yaron ya fada tare da raba ido.

Cikin sauri Aysha tace babu Aysha anan gidan.

Umma ce tai saurin kallonta tana fadin, me kike nufi?, Kai jekace gata nan zuwa.

Juyawa yayi yayin da Aysha ke fadin, wlh saidai in ke kije amman ni bazani ba.

Mama nadaga daki takwala mata Kira Aysha?

Na'am.

Banson iskanci tashi kije.

Mama nace babu Aysha tace akwai, toh ita basai taje ba.

Wlh Aysha nasameki gurin nan ranki zai baci, sa'arki ce ita?

Mikewa tayi cikin kokarin yin kuka take fadin, wlh Umma nan kin cika hada rigima, ko Ina
ruwanki dani oho, duk kinbi kinsa min ido.

Eh naji, Kuma bazan bar saka miki idon ba sai ranar da kika fidda miji kikayi aure.

Dan karamin hijjabi Aysha ta dauka tana fadin wlh idan wannan satin ya kare Daddy be
zoba komawa zanyi yasani makaranta ni bawani auren da zanyi yanzun.

Ficewa tayi yayin da Umma tabi bayan Aysha da kallo tana fadin, Bilkisu wannan yariyar
taki duk yadda akayi aljanu gareta bantaba ganin gandareriyar budurwa kamar Aysha dake kin
aure ba har haka.

Umma rashin kunya ke damun ta, bata da komai tana sani, yanzun haka ita da babanta

suka shirya cewa bazatayi auren yanzun ba.

Cikin gamsuwa Umma tace toh Allah ya zama mana abun da yafi alheri.

Ranar da Aysha ta cika sati Uku da dawowa ta shirya zuwa gidan Babanta wannan
karon bata dauki kaya ko kala daya ba, daya daga cikin hijjabinta da Aliyu ya saya mata tasa
wadda yakai mata har kasa.

Mamace ke fadin, Aysha karki zauna kiyi sauri ki dawo.

Amsawa tayi, Kai tsaye gidan mahaifin ta nufa, acikin tafiyan da batafi ta awa daya ba ta iso.

Babban gida ne babu laifi, motarsa ta hanga tayi ajiyan zuciya duk da cewa daman tayi
tunanin zata same shi a gidan.

Tana shiga cikin falon wasu yan mata biyu suka tasu suka rungumeta, itama rungume su
tayi yayin da wani dan saurayi da bazai wuce shekara 16 ba ya roko hannun Ayaha yana fadin,
har Daddy yace zai kawo mu gidan ku kin dade bakizo.

Wayyo inataso inxo makaranta ne ya hanani zuwa kuyi hakuri, karasawa cikin falon tayi
yayin dataga Daddyn ta yayi saurin mikewa zai fice

Sakin hannun kannenta tayi tabi bayan Daddy tare da saurin riko hannun sa tana fadin,
Daddy yi hakuri.

Batare daya kalleta ba yace nasan yau ma batan hanya kikayi.

Wlh Daddy gunka nazo, makaranta ne kawai yake hanani zuwa.

21 / 34