Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
ba, saidai data tuna yadda take balakin son ganin Aliyu saitaji
zuciyarta na dada dakewa.
Nan ma tafiya akayi da ita sosai sannan mutumin ya juyo yace, "har yanzun ba'a kawo ba?"
Kai Aysha ta daga masa domin ta fahimci tambaya yayi amman bata iya sanin me yace
mata.
Tafiya yayi me nisa sannan ya tsaya ya bude motar yana fadin sakko Hajiya, nan gurin
shine karshe.
Cikin rashin fahimta ta yamutsa fuska cikin kokarin sakkowa tana me kallon garin tare dayin
kwal kwal da idonta, hawaye ke shirin zubo mata.
Motar ya mayar ya rufe sannan ya zagaya ya shiga motar yana fadin, da Alama yariyar
nan batajin Hausa.
Tausayi tabashi dan haka ya kirata da hannun sa yace Ina Zaki ne?
Cikin fullacin tai mgnr dan haka ya yamutsa fuska tare da fadin toh fah, sakkowa yayi ya
nufi wasu maza dake zaune ya basu hannun suka gaisa sannan yace yariya ce na dauko
tundazon da alama batasan garin ba Kuma batajin Hausa ko akwai bafulatani anan?
Bafulatana ce?
Amsa masu yayi da eh sannan ya daga Hannu ya Kira Aysha.
Tahowa tayi ta tsaya gabansu, daya daga cikin sune yace ke ya sunan ki???
Fulacin dai ta sake masu cikin takaici dayan yace ke bamejin fullanci anan gurin sunan ki
akace, Yaya sunan ki??
Wannan karon tafara tsorata dasu domin ta fahimci cikin fada sukayi mgn.
Daya daga cikin sune yace, duk yadda akayi irin yaran nan ne masu guduwa daga gidan
iyayen su, ke bakijin wani yaren ne sai fulatanci kadai?
Kaita daga dumin iya fahimtarta tambaya sukayi, fada mutanan sukaci gaba dayi yayin da
Aysha ta tsaya idonta jawur.
Dayan ne ya kula da takardan dake hannunta batare data ankara ba ya amsa takardan ya
bude.
Dagowa yayi ya kalli sauran tare da fadin, Ina tunanin wannan shine adireshin inda zata
ke yariya wannan shine adireshin inda Zaki??
Kaita daga yayin da daya daga cikin mutanen yace ita kome zakace mata ai amsa maka
zatayi ai daman fulani ba hankali suka cika ba inba hakama kya taso bakisan gariba Kuma
baki da hausa.
Daya daga cikin su ne dai ya sake cewa yanxun abun da za'ayi ka taimaka ka kaita Dan
kunma baro unguwar abaya, Kuma indai da gaske wannan shine adireshin to takwana gidan
sauki, taimakawa zakayi ka kaita har gidan tunda akwai no gidan ajiki.
Eh to bance bazani ba, amman ni gaskiya sana'a nafito, idan tana da kudin da zata biyani
har da bata lokacina toh zan kaita.
Toh babu laifi, kallon Aysha sukayi kina da kudi??
Raba ido kawai Aysha keyi dan haka suka shiga mata kurma kurma suna nunawa da
hannun su.
Hannun tasa cikin akwatin ta dauko cajin da aka bata.
Gaskiya baxani awannan kudin ba.
Nan dai suka lallabe shi akan idan sunje acika masa kudin sa agidan, haka akayi Aysha ta
shiga motar sannan suka dauki hanya.
*******
Sai yau ka tuna Dani agarin nan Aliyu?, Shekaran ka nawa yanzun, tunda naje akace min
kana nan neke zarya gidan ku, Amman kullum nazo ace kana makarantanta, haba Aliyu?
Aini ban masan kinsan ina nan ba, Kuma ita Ummin da ta gaya miki ba itace ta koroni ba?
Ai Kai kajawo komai, idan bata koreka Yaya zatai dakai.
Eh shine Nima ai nakoma gefe.
Gara taka koma gefen, yanxun ma dakasani ai bakazo ba, wato sai abarka kayi abun
da kaga dama.
Daure fuska Aliyu yayi sosai yana zaune falon Hajiya Rukayya cikin kakin sojojin sa
fuskar nan tasa kirtim, lumshe ido yayi sannan yace, Ina Yaya Fahat?
Yana wankacan dakin ta numa masa da hannunta.
Kallon dakin yayi sannan yasake cewa ya jikin sa fah?
Jiki Alhamdulillah.
Amman akwai wani cigaba??
Toh Alhamdulillah yana nan dai a yadda yake.
Har cikin ransa yaji ba dadi mikewa yayi yana kokarin nufar dakin Aunty Ruqayya tace, "
yaushe zaka je gida?"
Yanzun Yaya Fahat kawai zan gani na wuce"
Can gida nake nufi gurin Ummi"
Dan waigowa yayi ya kalleta sannan yace Aunty itafa ta koreni, ni bazani ba sai in ita ta
nemeni, haka tace min ita burin ta in zauna gidan ubana.
Mikewa Anuty tayi tabi bayansa cikin dariya take fadin, dan auta sunyi fada da Ummi, bafa
ason ranta bane.
Nima ai ba ason raina bane, da haka suka Isa dakin fahat, cikin wani irin farin ciki fahat din
yake kallon Aliyu domin rabon su da juna sun dade sosai.
Zama yayi gefen sa yana me kura masa ido ko kiftawa babu, idon Aliyu cike da kwallah ya
kama hannun sa yana fadin, Yaya Fahat nine Aliyu, Yaya kake?, Ya jikin ka?
Bude baki yake cikin kokarin amsawa da irin mgnr sa wadda ba'a ganewa sosai.
Hawaye ne ya zubowa Aliyu cikin sauri ya kawar da kansa ya share sannan yasa hannun
sa cikin aljihu ya ciro kudi yasa a hannun fahat yana fadin, gashi inji Ummi tace na kawo maka.
Amsa yayi da murna akan fuskarsa, mikewa Aliyu yayi yana fadin barin je ai muna tare zan
dawo kaji.
Amsawa yayi,yayin da Aliyu da aunty Rukayya suka fito har motar sa, BAyan ya shiga ya
zauna ta kalleshi tace, " Auta an girma, to yaushe zakayi aure?, gaka yadda kai katoto kuwa,
dan Allah kaje Ummi ta ganka.
Hmmmm, aunty yaushe rabon ki da can?
Sakera biyu, amman nakusa komawa.
Tada motar yayi tare da fadin, idan kinje ki gaishe ta, amman Banda innawo.
Cikin dariya tace ita Kuma Innawo meta maka?
Itace nan ta zuga Ummi, tada motar yayi batare yajira me aunty zatace ba.
******
Ana Kiran sallan magarib suka iso kofar gidan kallon Ayaha yayi ya mika mata takardan
tare da numa mata cewa wannan bayanin nata ya nuna wannan ne gidan dan haka ki shiga ki
amso min cikon kudina.
Ganin kamar bata gane ba yai mata kamar mgnr kurame har saida yaga ta daga Kai
sannan ya zauna saman motar tare da fadin ina nan.
Itako Aysha gidan ta nufa duk da cewa girman gidan yabata mamaki cikin dar dar ta shiga
bugawa.......
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Comment BA'KAR FURA *Sumayya Magaji*
*Tabdijam gsky yakamata iyaye sudauki darasi anan koba komai wani lokacin iyaye sukan
dinga tsanantama yaransu akan abinda baikai yakawoba su aganinsu tarbiyace suke koya
musu kuma yaro yanada wani Abu dik abinda yaga ana tsananta mishi akai koda abin baije
yadawoba tofa shiyake qoqarin aikatawa aikatawa, Wanda aganina dik abinda zaman lpy
baikawo ba to tabbas tashin hankali bazai taba kawoshiba, tin farko inda iyayinsu sunbi abin
ahankali dayanxu hkn batafaru ba, yanxu wagari yawaya idan har iyayin Aisha suka sami lbrn
tagudo har Nigeria wajan Aliyu?*♀️
*Sann ko Yara wani lokacin danasu laifin iyaye fa sunfi qarfin wasa duniya daka rasa iyaye
baxaka taba samun wasuba kuma dik abinda mukaga iyayen mu sukeyi mana bawai Dan basu
sonmu bane Aa kwe dae sunayi ne dansuga sunkare martabar mu d mutuncin mu sann kuma
susauke nauyin da ubangiji yadora musu.* Kowa ya aikata daidai ba shakka zaiga daidai ammh dae wann yaxama ixina awurin iyaye kai
harma damu yaransu♀️
*Tin ba'aje ko inaba wann lbrn yafara bayyana irin darasin da yake dauki dashi,*
*Ubangiji Allah kabamu ikon yiwa iyayin mu biyayya adukkan wani abu dasuka doramu akai
muddin baisaba maka*
*Ya Allah kasa mugama d iyayin mu lpy*
*Wadan da iyayinsu suka rigamu gidan gsky Allah yagafarta musu yayi musu rahama Amin ya
rabbi*
*Sis @Fadeela Lamido muna gdy sosai Allah yaqara basira da daukaka yasa kifi hk yashirya
miki zuri'arki*
episode 27- 29
Kwankwasawa take ahankali cikin sanyin jiki, daga can taji an fara bude gidan.
Me gadine ya leko ya kalli Aysha tare da fadin Yaya dai?
Cikin fullacin tayi mgn wadda baya fahimtan koma sai Aliyu da take Kira.
Cikin tsananin mamaki yace Aliyu?, Iya sanin sa dai Aliyu ko mgn ba cika yinta yayi ba,
tsareta da ido yayi, neman sa kike Aliyun?, tunawa da yayi fulacin takeji yasashi yace, Aliyu
baya nan.
Wannan mutumin daya kawo Aysha ne ya matso yana faddin, waishin baka fahimci sunan
wadda take Kira bane? Ko banan gidan yake ba?
Eh toh anan madai Akwai Aliyu amman Ina tunanin ba wadda take nema bane.
A'a Sam nan ne, gashinan Zane hannun ta, wannan yariyar bakuwa ce ba yar
garibace tun da sauran rana nake yawo da ita acikin motar nan, yanzun dai bude mata ta shiga
ta amso min kudina.
Gurin wa?
Aliyu take Kira Kuma Aliyu baya nan.
Toh ai saika bude mata kofar ta shiga ta jirashi ko, nadade Ina yawo da yariyar nan ba inda
zani da ita kuma.
Tsaki Me gadin yayi sannan ya juya rufe gidan.
Cikin wani irin yanayi Aysha ta juyo ta tsuguna akasa saboda yadda kafarta tagaji, ga tarin
yunwa a tattare da ita.
Ganin garin yayi duhu ta fara hawaye gaba daya cikinta ciwo yake mata ga wani masifar
fiya yunwa da yake ji.
Mutumin ko na nan zaune sai masifa yake yayin da Aysha ta tsuguna a gefe tana share
hawaye.
Wata katuwar mota ce ta shigo layin, yayin da duk hankalin su ya karkata kanta ahankali
harta karaso gurin su, nan suka fahimci gidan zata shiga dan haka suka kauce.
Gate din gidan aka bude yayin da motar tasa hancin ta cikin gidan.
Fitowa Aliyu yayi daga cikin motar da saurin sa domin gani yake kamar Aysha ce awaje,
idan kuwa ba Aysha bace lallai suna tsananin kama.
Yana daf da shiga gidan me gadin ke fadin, " ranka ya dade, akwai wata bafulatana tazo
batajin Hausa amman tana Kiran sunan ka.
Aliyu bebi takansa ba yayi waje cikin tsananin mamaki yake binta da kallo yayin da itama tai
saurin mikewa ta da tsareshi da ido.
Aysha?, Aysha kece anan ba gixo idona yake min ba???
Kwalkwal tayi da ido har yanzun tana kallon sa, gani take kamar bashi ba, sosai ya canza
mata yayi wani irin kato ya tara kasumba ga Kuma kayan sojojin ajikin sa.
Kara matsawa yayi daf da ita tare da dafa kafadonta yana fadin, kimin mgn Mana inji
muryan ki kece haka??
Fadawa tayi jikinshi cikin fashewa da kuka, yayin dayai saurin rungumeta tsayon lokaci
sannan ya fara dan dukan bayanta tare da cewa ya Isa ya Isa cikin harcen fullacin.
Mutumin dake zaune ne saman motar yace taxo gari ita ba hausa ba tun dazon nake
bulaye da ita agarin nan, tasan batajin ko wanni yare mezaisa tazo n........
Cikin sauri Aliyu ya dago Aysha daga jikinsa sannan ya juya ya kalli mutumin yana fadin, "
Kai me kake jira??
Cikin furgici da tsawan da ya masa yace a'a ni cikon kudina za'a bani.
Hannun yasa a aljhu ya ciro kudin dabesan ko nawa bane ya mika masa.
Cikin sauri mutumin yabar unguwar yayin da Aliyu ya tattara hankalin shi gaba daya gun
Aysha yana fadin kedawa Aysha?, yaya akayi har kikazo nan?
Wasa da hannunta take cikin sunkuyar da kanta tsayon lokaci.
Kallonta yayi sannan yai murmushi tare da cewa, " har yanzun dai ana nan ba'abar wasa da
hannun ba?, Juyawa yayi ya kalli akwatin ta sannan ya sake cewa inajin ki kedawa kikaxo
nan??
Batare data dago ta kalleshi ba tace ni kadai.
Cikin sauri ya zaro ido, ke kadai????
Har yanzun idonta akasa tace eh.
Shiru yayi tsayon lokaci yana kallonta, tsarguwa tayi da kalon dan haka ta Kara saukar da
idonta kasa kafin taji yana fadin.
Aysha ashe baki da hankali?, ina nan ina yabon halayen ki, yanzun ke kadai kika kamo
hanya toh agida ansan kin taho?
Kanta ta girgi alanar a'a
Ina kikace masu Zaki?
Muryanta can kasa tace gidan babana.
Shiru ya sakeyi tsayon lokaci sannan ya sake cewa, amman dai baki da hankali Ayaha
ta Yaya zaki baro gida babu izinin kowa kina da hankali kenan?, kina tunanin idan suka lura
baki can wani irin tashn hankali zasu shiga?
Wasa take da hannunta yayin da hawaye ya fara sauka akan kumatun ta.
Cikin tsareta da ido ya sake cewa Aysha kina son mukara shiga cikin wata matsala ko?
Girgiza kanta tayi da sauri yayin data share hawaye tare da saurin tsugunawa ta dauki
akwatin ta ta juya afusace ta fara tafiya.
Kallo yabita dashi zuwa can yace Ina Zaki???
Tafiya kawai take dan haka ya sake cewa zonan.
Ganin tacigaba da tafiya ya sashi daga murya tare da fadin, " Aysha kinaji nace ki dawo ko?
Ganin har yanzun tafiya take yasashi yabi bayanta, abuka da namiji nan danan yacin
mata, akwatin ya karba sannan yace juya muje, Ina miki mgn kina tafiya,, yanzun bada bane
saina miki duka, wuce muje.
Juya tayi kamar yadda yace, yana gaba da akwatin ta ahannun sa