Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
Adaidai kofar gidan su Innawo motar ta tsaya, yayin da yake ganin komai ya cansa
masa, akwatin sa ya sauke sannan ya Kira wani matashi yace dan Allah ka shigar min da
kayana nan gidan.
Dauka yaron yayi ya shiga, yayin da Aliyu yai saurin karasawa gurin Idi me shago.
Wa nake gani haka kamar Aliyu?
Cikin murmushi Aliyu yace, " ba kama bace nine"
Aliyu Kaine?, Kallon Aliyu yake sosai yayin da yaga ya zama katon sajo babban mutum.
Nine Idi.
Nayi farin ciki da zuwan ka ta wani bangaren Kuma banyi ba.
Menene yake faruwa?
Hannun idi yasa yaja Aliyu bayan sagon sa yana fadin, " bayan tafiyan ka abubuwa da dama
sun faru, kayi hakuri zan gaya maka wata mgn wadda bata da dadi, Aysha tayi ciki....
Tun kafin ya rufe baki Aliyu yace, " nasani"
Au ka sani???
Eh na sani, idi yanzun Aysha tana Ina?, Cikin na nan ko babu shi?
Ai ciki ma an haifeshi jiya da daddare.....
Bebari ya karasa ba yace ita Aysha tana Ina?
Tana nan cikin gidan su ....
Nan ma be bari ya rufe bakiba ya doshi gidan, acikin zauren gidan ya tsaya hannun sa cikin
aljihun sa, cikin karkausar murya ya rangada sallama Har sau uku sannan aka amsa.
Innawo ce ta tahowa tare da fadin, " waye nan??
Acikin daga muryar irin na sojoji yace, " nine.....
https://youtu.be/2eTqqbS_xq0
*SUBSCRIBE*
*COMMENT*
*LIKE AND SHARE*
*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 46- 47
Kaine wa?, Umma ta fada tana kokarin lekowa.
Shiko Aliyu hannun sa ya ciro cikin aljihun sa yana gyara gilashin idon sa, adaidai wannan
lokacin Umma ta iso tai tsaye tana kare masa kallo zuwa can tace, Yaya dai"
Idon ta na nuna mata kamar Aliyu ne, amman ganin ya Kara budewa da cika sosai fuskarsa
cike da 'kasumba ta tsaya tamtama, yayin da wata zuciyar ke ganin kamar gizo yake mata
kawai dan dai suna mgnr sa ne Kuma suna tsananin son ganin nasa.
Cikin 'Kara kankance idonta tace kamar Aliyu ne nake gani?
Miskilancin sa na baya ne ya dawo daidai wannan lokacin kasa yayi da murya yace, "
shine"
Shine???, Ko gizo ne??
Wani guri ya tsayar da idonsa dake cikin gilashi, ba kizo bane nine Aliyu.
Kai Umma ta gyad'a dake nuna eh lallai, sannan tace, " da wacce kozo?"
Dan Alheri nazon, Ina son naga Aysha ne
Jarr ubancen, Umma ta fada sannan tace Bismillah.
Cikin sauri ta koma cikin gidan tana fadin duk ku fito daga dakin nan in kalli ikon Allah.
Aliyu kuwa Umma na juyawa yabi bayanta, yana tsaye yaga su Aunty Murja na fitowa
daga dakin kowanne fuska cike da masifa, ciki harda maza kawun nan Aysha.
Umma ce ta kalli Aliyu dake tsaye agefe cikin kakin sa na Sojoji sannan ta juya ta kalli
yaranta tace, " ga Aliyu nan wai yazo ne zaiga Aysha
Mazanne suka nemiyin mgn cikin sauri Umma ta dakatar dasu cike da kwarin guiwa tace ku
bashi hanya ya shiga ya kanta.
Ya shiga Kuma??
Eh ya shiga Mana, tunda ita ba iya fitowa zatayi ba, kuzo ku shiga nan ku basu waje.
Matan ne suka fara kaucewa yayin da Mama take a bayansu dan haka yana fara takowa
yai kasa da kanshi yace, Ina wuni?
Wucewanta tayi bata amsa ba, shima be damu ba yasa kansa cikin dakin yayin da duk yaran
Umma sukayi tsaye a tsakar gidan.
Itako Aysha tunda aka fara kiran Aliyu, Aliyu, gabanta ke faduwa bata yadda shid'in bane
saida taga shigowansa sukayi 4 dashi.
Wanni irin kallo ta masa me cike da tuhuma tsayon lokaci, yayin da hawaye ke ziraro mata,
shima kallo yabita dashi fuska adan sake sannan ya fara takawa, bakin gadon da Aysha take
Kai ya zauna, yayin da Aisha tai saurin mikewa tana kokarin barin dakin.
Zo, Ayaha karki fita.
Ficewa tayi sai dai tana d'aga labulen idanuwa suka mata cah cike da tuhuma dan haka tai
saurin komawa tai tsaye abakin kofar.
Kallonta Aliyu yayi cikin sanyin jiki sosai yace, " kiyi hakuri, nasani ni me laifine, zo ki zauna.
Runtse ido tayi, bazan zauna ba kazo ka fitar mana agida.
Murmushi yayi sannan ya Kara komawa bakin gadon ya zauna tare da dauko yaron ya daura
akan cinyarsa tare da zuba masa ido.
Wani irin farin ciki yaji ganin inda yaron yayi tsananin kama dashi, eh lallai da anga
wannan yaron an ganni, dagowa yayi ya kalli Aysha tare da fadin zo ki zauna muyi mgn.
Ka tashi ka fita kafin Umma tazo, duk abun da ta maka kaika saya, dan rashin mutunci ka
shigo har cikin gida
Eh naji, bani da mutunci, amman ni bana tsoron Umma, bama Umma ba, kowa ma, kisani
ba yadda za'ayi mutum ya tashi ya tafi filin yaki shi daya batare daya shirya ba, kuma ni
wannan abun ba zuwa nayi na sawoshi a kasuwa ba, cikin sa na tsinta kaina, duk da cewa nayi
kokarin kauce ma hakan, nasan daman zanzo in tarar da haka daga gareki, tunda na wuce
lokacin da nace zanzo, amman nina ki zuwa ne saboda nasan mawucin abu ne ace baki da ciki,
Kuma har jiya da na taso jikina yana tabbatar min da zan tarar da makamancin wannan.
Cikin zubar da hawaye Aysha tace shine kabarni da wahala ni daya bakazo mukaci wuyar
tare ba ko?, koda yake ba laifinka bane yazon ma kana da damar da zakace dan banaka bane,
tunda kowa yasan baka garin nan nice na kawo kaina dan haka koma mene nic.......
Meyasa kike min irin wannan tunanin Aysha, niba azzalumi bane, kuma niba makaryace
bane, akan me zance ba nawa bane, alhalin jinina ya yafi karfi ajikin yaron ma, yaro nawa ne,
yaron ya sake kallo, sannan ya dagoshi ya sumbace shi, tare da kai Kunnen sa saitin bakin sa,
ya jima, sannan ya sauke shi kan ciyarsa yana fadin, " sunan sa Khalipa, Baba nane shi, Aysha
Moh'd Bello ne, sunan Baffana kenan, Kuma Ina tabbatar miki Ina tsananin son shi.
Waigowa tayi cike da masifa sai dai ganin hawaye akan fuskansa yasa tai saurin kawar da
kanta, shiko Aliyu juyawa yayi ya aje yaron sannan ya mike yana fadin, " zoki zauna kinji,
banshiga gida ba hankali na ne yaki nutsuwa shiyasa na fara zuwa nan.
Kin joyowa tayi har yanzun can gefe take kallo.
Kasa ya karayi da Murya yana fadin, kixo ko zauna ki bashi abincin sa, kinga wawure wawure
yake yi akwai alamar yunwa a tattare dashi.
Wani kofe dake kasa ta tsuguna ta dauka cikin sauri ta maka masa akirji ragowan ruwan
dake ciki ya jika rigarsa.
Cikin zare ido yace, " washess Allah na, akwai zafi, akwai zafi sosai, ya fada yana sosa
wajen,, dan Allah badan halina ba kibashi yasha.
Batare data kallesa ba tace Allah ya 'kauta nabawa wannan dan bura'uban yaron nono na
sha.
Subuhanallahi, kallonta yayi cikin ido sannan yace ni bansan lokacin da kika zama
masifaffiya har haka ba, shikenan ynzun ki samo bulala kita dukana harsai kin huce tunda naga
kamar kina sha'awan dukana.
Wuceshi tayi ta dawo bakin gado ta zauna, cike da bacin rai take kokarin hana idonta kallon
shi.
Shima kallon ya gama kare mata sannan yace barin je gida kinji.
Tabbatarwa da yayi bazata amsa ba ya sashi ya kad'a kansa ya fita adakin, yayin da ya
tardasu cirko cirko a tsakar gidan.
Ganin Aliyu zai fito duk suka taho kusa, yayin da yake kokarin ratsasu kawun Aysha yace Ina
zaka bayan baka fito da d'anka ba?
Ba abin da ya kawuni kenan ba, Aliya fada fuskarsa ahade"
Innawo ce tasha gaban Aliyu cike da bala'i tace, " me kake nufi Aliyu?, kowa ya kalli Dan
nan ya ganka, dan haka d'a naka ne, maza ka koma ka dauko d'anka, ke Murjanatu dauko min
yaron nan.
Cikin daga murya Aliyu yace Bafa zan amsa ba, dan ba abin da ya kawoni kenan ba.
Sosai gaban Aysha ya buga, bugawa me tsanani, ganin yanzun ya amsa nasane harga
masa hud'uba, me hakan ke nufi to, mikewa tayi azubure ta fito ta tsaya ta rike labulen tana
kallon cikin idon Aliyu da zuwa yanzun ya canza launi ya zama jawur.
Umma ce tace, " Wlh Aliyu baka Isa ba, idan Kai dan duniya ne nikuma yar guguwa ce, d'a
naka ne, idan ba naka bane meya kawo ka?, Me kazoyi gurin Ayaha?
Maman Sadam ce tace, a'a Umma tsaya, Kai d'an naka ne ko banaka bane??
Kawunnan Aysha ne suka fara cewa akan me Zaki masa wannan tambayan?
Shikuwa Aliyu kallon fuskar Aysha yayi sannan ya kawar da kansa tare da fadin, " nawa ne,
d'ana ne"
Alhamdulillah, Umma ta fada, yayin da tai saurin komawa dakin ta dauko yaron ta mikawa
Aliyu tana fadin' " amshi kayan ka"
Bazan amsa, bana so, nabar miki"
Ka bar min, kace dai ka shirya babban masifa garin nan, domin kuwa idan Kai baka amsa ba
Uwarka zata amsa dole, mara mutunci kawai, dan iska, fitsararre, na dade da sanin baka da
Kunya, baka da mutunci, ka kalli tsabar idona kace wai ka barmin, ka barma uwar ka dai.
Kawun Aysha ne ya daki kirjin Aliyu tare da fadin, " dan ubanka ka amsa danka kabar
mana gida.
Cikin zaro idon tare da hargowa Aliyu ya nuna shi da yatsa tare da cewa, " karka kara tabani
ko zagina Ida ka Kara zan rama.
Yadda yayi mgnr cikin hargowa yasa duk gidan saida suka zabura har Aysha, da kallo kawai
suka bishi harya fice a gidan.
Umma kuwa saida Aliyu ya dade ta fita sannan a sauke ajiyan zuciya tana jinjina kanta take
fadin, " jar Uban can"
Kawun Aysha ne yace wai yaron nan dame yake takama ne??, kiduba kiga yadda ya shigo
Mana gida, naso in hanashi ganin Aysha ai Umma ke kikace abarshi.
Aini duk tunani na d'ansa yazo dauka.
Mama Sadam ce tace kinji yace d'ansa ne amman beso, wai yabarwa Umma wato tunda
kece nan kika hana masu aure yabar miki, ku dan iska.
Aunty Murja ce tace ga yar iska cen adaki, aini wlh nadawo daga rakiyar Ayaha, ba irin
horon da ba'a mata ba ta fada nawaye tace ita sam bata san meshi ba.
Maman Sadam ce ta amshi xance aini Aysha taban tsoro, muguwar yariya ce me taurin ran
tsiya, ko aina suka hadu oho, ita uwarsa tace shekaransa biyar be kasar
Rabu da munafukai duk su biyun munafukai ne nikuma sainaga uban daya tsayawa Aliyu.
*******
Da Sallama ya shiga falon yayin da akwatin sa yake tsakiyar falon, cikin murmushi ya ware
hannun sa tare da fadin Oyoyo Ummi na, jikinta yai saurin fadawa tana zaune kusa da Innawo.
Ya dade rungume da ita duk da ya lura bata cikin walwala, fuskan ta daure tamau be hanasa
dagawa ya sunbaceta ba, cikin sauri tasa hannun ta ta share inda ya sunbata tare da fadin, "
meya kawo ka?, Aliyu me kazo yi awannan lokacin?"
Mika hannun yayi ya riko na Innawo yana fadin matass anya kuwa kinyi farin ciki da ganina.
Banyi ba, duk ka tsofa kayi gemo biya biya sannan zaka waiwaye mu?, Wai ma Ina kaje ne
ka iso ka kasa shigowa gida??
Wani sako na bada, duk kuna lafiya.
Lafiya Lau Innawa ta fada sannan ya juya ya kalli Umminsa da har yanxun yana kan kafadan
ta yace, " Ummi ke fa"
Cikin daure fuska tace na tambaye ka baka bani amsa ba, Kuma kana tambaya ta, nace
me kazo yi kasar nan adaidai wannan lokacin.
Ni, Ummi nazo na ganku ne.
Karya kakeyi Aliyu, Ina kaje yanzun kafin ka shigo nan??
Jimmm Aliyu yayi tare da kauda kansa, zuwa can ya juyo yace"
Can gidan naje.
Innawo ce ta kalleshi ta kauda kanta tare da sa tagumi.
Itako Ummi tsare shi da idon tayi tana fadin, " gidan su Ayaha??
Kasa amsawa yayi yayin da Ummi ta sake jefa masa wata tambayar, d'an naka ne ko kuwa
banaka bane?
Lebensa na kasa ya cija da karfi sannan ya sunkuyar da kansa sosai tare da fadin, " Ummi
ki tsaya nai miki bayani.
Tambayan ka nayi, Aliyu kabani amsa, d'an naka ne ko banaka bane?
Shine zan miki bayani ai yanzun Ummi.
Wlh Aliyu zanci ubanka, bana wasa dakai, niba sa'arka bace, na tambaye ka ka bani amsa
daya tal, idan ba hakaba wlh ranka zai baci.
Juyawa yayi ya kalli Innawo cikin tsananin tashin hankali yace, innawu dan Allah kice
mata ta tsaya nayi mata baya ni.
Kin juyowa Innawo tayi kota kalleshi, cike da tashin hankali yace, Innawo kema fushi
kikayi, dan Allah ku tsaya ku fahimce ni"
Ba wadda zai tsaya ya saurareka anan magana daya nake son ji agurin ka, naka ne ko
banaka bane d'an?
Jimmm yayi idon shi cike da hawaye, sosai yake kokarin maidasu ahankali yace, " nawa ne
Ummi.
Tirrrrr, kayin asara Aliyu, ashe baka da mutunci, ashe dan iska ne Kai wawa mazinaci.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un Aliyu yake maimaitawa da karfi.
Dole ka kira Allah, munafuki kawai wadda bejin tsoron Allah, saikaje ka dauki dan ka kaima
ubanka kusan yadda zakuyi ni babu abun da ya dame ni.
Rasa inda zaisa