Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
bansan haryar da zanbi in samu
hanyar gida ba.
Dariya sosai Aliyu yayi yana kallon cikin idon ta, hannun sa ya mika ya dafa kafadanta
ahankali yake turata da baya har suka Isa kujera ya zaunar da ita sanan ya zauna agaban ta,
kinaji Aysha?, ki kwantar da hankalin ki, ni bazan gudu in barki ba, kuma Zaki koma gida cikin
kwanciyar hankali inaha Allahu bazaki wahala ba, Ina son muyi hira sosai, sai dai kin San
me??
A'a
Baffah na dazon yayi min mgn akan ki, kacenwar basu sanki ba bakuma Susan komai daga
gareki ba.
Kallo ta tsare Aliyu dashi tsayon lokaci sosai ya fahimci tashin hankali a tattare da Aisha.
Bude baki tayi cikin shirin yin kuka yayin da Aliyu yai saurin daga mata Hannu tare da fadin,
" a'a karki tada hankalin ki, nagaya masu ke matar abokina ce, tafiyar gaggawa ta kamashi ya
bukacin ki zauna anan, dan haka daga yanzun ke matar abokina ce.
Sunkuyar dakai Aisha tayi har yanzun fuskarta babu sukuni, ido Aliyu yabita dashi sosai ya
gama fahimtar ta sannan ya cire hannun sa daga kafadanta ya ruko habarta yana fadin, " karki
damu kinji ko, wannan ba wani abu bane, bason su fahimci komai game dake, har na kaiki gida
sannan na neme auren ki.
Kwallah ta share, har yanzun zuciyarta babu nutsuwa gata ga Aliyu amman kwanciyar
hankali babu.
Tunanin me kike Aysha?
Hawaye ta sake sharewa akaro na biyu tare da fadin, ya Aliyu na damu sosai, inajin wani
iri acan hankalina ba akwance ba anan ma hankalina be kwanta ba.
Toh meyasa?, Bana son ki koma gida kinajin haka, inason kiji dadi sosai, Ina son ki kasance
cikin farin ciki domin hakan ne zaisa ki koma da walwala, Nima in tunaki inyi murmushi, Amman
idan kika koma gida kina cikin wannan halin zuciyata zata kasa nutsuwa, yanzun kinsan me
nake so dake?
Kaita girgiza yayin da Aliyu ya mika hannun sa yana kokarin share hawaye yake fadin, " ke
mata aure ce Aysha karki yadda wani ya gane cewa baki da aure, nace haka ne badan Ina
tsoroba sai gudun Kar abun da ya faru abaya ya sake faruwa, Ina son na maidake gida sanan in
Kuma daukoki alokacin da kowa ya shaida nine mamallakin ki.
Sosai taji zuciyarta tai sanyin har ta sauke ajiyan zuciya.
Murmushi yayi tare da fadin ko kefa.
Itama murmushi tayi kadan tare da turi hannun sa daya rike habarta dashi, cikin sauri ya
dauke hannun nasa yana fadin, " yi hakuri, na mance kin girma dauka nake dace.
Wani irin kallo ta masa wadda yasashi ya kumayin murmushi, amman naga kinyi sanyi da
yawa bakiyin wannan darigar take dake Dani murmushi.
Yaya toh ai Kaine baka bani dariyar.
Shikenan, naji, ki shirya gobe idan na dawo aiki zan fita dake musha hira, kibani lbrn
Cameroon.
Amsawa tayi da toh.
Juyawa yayi ya dauko ledan dake bayansa ya mika mata, tare da fadin, wannan Hijjab ne Ina
son ki rika sasu.
Godiya tayi sannan ta mike ta tai masa sallama.
*****
Ina zashi da ita Kuma?, amman sun matukar dacewa wlh, duk da cewa cikin nikaf take
amman abun ya dace.
Babu ruwana ki, ki daina mgnr sa, kinsan halin sa saikiga kamar ba kallon ki yake ba
amman duk yadda bakin ki ya motsa yasan me kike nufi.
Kara kintse hakora Islam tayi tana fadin, daka nace sun dace, gani nayi tayi kamar matar
shi, gashi Kuma yace matar abokin sa ce, Kuma wlh ki waiga ahankali ki kalli wani kallon love
da yake mata.
Kallon so?, matar abokina sa ce fah?
Nidai Naga ya Aliyu soja ne, Kuma bashi da aure bashi da mata, baya zama gari daya,
abokai kala kala, 'yan mata kala kala, karuwai burjik, Kuma wlh daganin ya Haydar ba kanwan
lasa bane nan dai gidan ne yake mana mazurai.
Cikin sauri Meenat ta kalli Islam tace me kike nufi?
Bance komai ba, nidai fatana Allah yasa kada ranar da abokin nasa zaidawo daukan matar
sa ya tarar ya fita masa yawo da mata.
Lumshe ido Meenat tayi, sannan tace toh Ameen.
******
Tunda suka shigo babban gate din sojoji kawai take iya gani maza da mata, wasu na tafiya
wasu na zaune wasu ko sintiri suke yi, wannan ya tabbatar mata da cewa waje ne da aka
tanada domin sojoji, ahankali ta fara hango gidajen da bishiyoyi suka masu kawanya, wani abun
mamaki, duk inda Aliyu ya ratso Sara masa ake, duk da cewa yana cikin motar da aka rufe
gilashin ta.
Gidaje ne irin na sojoji, tafiya sukayi me nisa sannan ya tsaya, bude masa motar akayi ya
fita sannan ya zagaya ya budewa Aisha, bayan ta fito rufewa yayi sannan ya shiga gaba tana
binsa abaya.
Awani yalwa tattacen falo suka bayyana wadda yai matukar burge Aysha.
Ganin ya doshi wani daki ta zauna afalon, juyowa yayi ya kalleta sannan yace Ina zuwa.
Zaman kusan minti 39 tayi sannan ya fito yana sanye cikin wadon sojoji da farar riga.
Kallo
Kallon sa tayi sosai, sannan tayi murmushi.
Ahankali ya iso kusa da ita, yana fadin, ko baki fada ba nasan kina kallo nane sabo da
Kinga nakara kyau, fiye da lakacin da Ina Can Cameroon.
Bawani, kana nan yadda kake, tsufa kawai ka Kara.
Tunkarota yayi gadan gadan yana fadin, kice Allah.
Mikewa tayi da sauri tana toshe bakinta yayin da Aliyun yace, Me kike nufi??
Dariya ce ta kamata, ganin inda ya hade ransa yana tunkaro ta"
Ahankali take komawa da baya harta Isa kofar tana fadin babu komai.
Kina nufin har yanzun Ina nan a baki na ban washe ba???
Dariya ta sake sawa, ganin yana dada tunkarota ta bude kofar ta tai waje aguje.
Wani irin dariya yayi har zuciyar sa tare da sauke ajiyan zuciya me karfi sannan ya fito cikin
kokarin boye murmushim sa.
Babu kowa afarfajiyar da bishiyoyi suka zagaye, daga can gefe ana iya hango sajoji nata
zirga zirga sai dai babu ruwan wani da wani.
Ahankali yake takawa zuwa inda take tare dajin dadin yanayin sosai cikin ransa.
Runtse ido tayi tunda ta hango tahowan sa tare da dago hannunta cikin nuna alamar karya
taba ta cikin dariya take kare jikinta da hannunta duk biyu.
Tsaye yayi agabanta sannan yai saurin mamayanta ya cukuikuyi hijjabin ta cak yai sama
da ita tare da fadin muje kimin bayani........ Pls kubi wannan link din ku dannan
min subscribe tare da alamar kararrawa
https://youtu.be/3pYo_wvEN0M
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
https://youtu.be/ebcYnNjGbOI
episode 32- 33
Ganin yayi sama da ita fara fadin, " Ya Aliyu sauke ni wasane nake maka.
Cikin falon ya nufa da ita yana cikuikuye da hijjabinta, Aysha ko dariya take cikin wuntsula
kafarta take rokon sa ya sauke ta tare da magiya.
Bisa kujere dake falon ya sauketa, sannan ya zame yasa guiyoyin sa akasa har yanzun yana
rike da ita, hadiye murmushim sa yayi kina nufin har yanzun din dai abakin nake?
A'a Ya Aliyu yanzun kam kadan washe.
Nadan washe?, Aliyu ya tambaya yana tsare Aisha da idon sa.
Eh Mana ka Kara haske kadan.
Jimmmmm, yayi zuwa cen ya lumshe ido lokaci daya ya bude su tare da fadin, " toh naji ni
baki ne, ahaka Kuma aka kanni ake Sona.
Murmushi Aysha tayi waye keson naka?
Mikewa yayi ya zauna daf da ita yana fadin wadda ya tsargu.
Hannunta ta mika ahankali ta Kara da hannun sa yayin da yai saurin janye nashi, dariya
Aysha tayi Yaya nifa wasa nake maka fari ne Kai tasss.
Bawani, kinsan me??
A'a
Tsoro nake karmuyi aure mu dinga haihuwar bakaken yara.
Dariya Aysha ta Kuma sawa, yayin da Aliyu ya daure kamar ba shine yai mgnr ba, cikin
kallon idon sa tace toh meye?, Yaya Aliyu kaifa ba baki bane, Kaine kake bani dariya da
nafahimci baka son ace maka baki, bakin ka me kyau ne, kana da fari hasken fatane baka dashi
Kuma kamafi kyau ahakan.
Lumshe ido yayi na kaiki?
Kama fini Yaya fa.
Haba?
Allah.
Ninasan duk wayoni kike min, nasan ke zarah ce acikin taurari, kina da kyau Aysha, tun kina
karamar ki, yanzun ko da kika girma kin Kara kyau sosai, ni yanzun ma burina in ga na mallake
ki, Aisha tunda naganki akaro na biyun nan naji na matsu inyi aure, kallon cikin idonta yayi
sannan yace, ko kema kinajin irin wannan abun?
Cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa nidai kawai nasan namatsu ingan ka Kuma dana
ganka naji dadi.
Ki ganni kawai shikenan?, Auren fah?
Cikin kukan shagwaba ta juya baya tare da fadin, " ni kabar wannan mgnr"
Shiru yayi idon sa akan nata tsayon lokaci sannan yace, " kina nufin baki damu da auren ba
koko dai kinajin kunyata ne?
Yaya ni abar wannan mgnr.
Baza abarta ba, sai nayi, baki son muyi aure?
Ni intani a zauna ahaka.
Bangane azauna ahaka ba?, gaya min me kike nufi?, baki son aure?
Ni Yaya kabar mgnr nan muyi hirak kawai.
Ke!!, Karki Raina min hankali, an gama hiran sure nake so ni.
Toh ya Aliyu ai auren lokaci ne.
Kallonta yayi sosai sannan yace, eh lokaci ne, amman ya kusa zuwa me wayau kawai,
kinajin kunyana nasani, daman kin saki jikin ki danni aure nake so nan kusa.
Can kasa kasa tace Kaine ka dade bakayi ba.
Sarai yajita amman sai yace me kika ce?
Nace ya kamata ace kayi tuni.
Kece kika hanani ai.
Ni Kuma Yaya?
Eh kece Amman komai ya kusa insha Allahu.
Jimmm tayi tsoyon lakaci sannan tace nifa banaji ajikina su Umma zasu bari muyi aure.
Lumshe ido yayi tsayon lokaci tare da wani irin faduwan gaba, ahankali ya ware idon sa,
karki Kara irin wannan mgr nan.
Ganin inda ya shiga wani irin yanayi tabishi da kallo kawai kansa ya dafa tsayon lokaci be
gado ba ganin haka Aysha tace, yaya mene haka?
Dagowa yayi yana me sauke ajiyan zuciya tare da fadin, yanzun idan naje neman auren ki
akaki bani Yaya zamuyi toh?
Ya Aliyu Ummi zata yadda ka aure ni ne?
Tunani ya Kara shiga me zurfi yayin da ya waiga yaga Aysha na share hawaye.
Ahankali ya mika hannun sa ya jawota jikin sa, kwanciya tayi akan faffadan kirjin sa
kamar yadda ya bukata, hijjabinta ya tattaro ya cireshi tare da ajewa agefe sannan ya sake
kwantar da ita akirjin sa yana mejin wani irin farin ciki da nutsuwa me wuyar misaltawa.
Lumshe idon sa yayi yana shinshinan gashin kanta dake fitar da kanshi me sanyi, hannun
sa daya yasa yana buga bayanta cikin sigar lallashi.
Saidai shi ana shi banganren yanajin wani abu sosai game da ita yana yawo ajikin sa,
itako Aysha jinta jikin Aliyu taji takara samun nutsuwa.
Wani abun mamaki daya daure kan Aysha akaron farko ta tsinci Aliyu na sumbatar ta kota
Ina batare data ankara ba, shima Aliyu akwai Alamun ba acikin hayyacin sa yake ba, ajiyan
zuciya ta fara saki a jejjere wani na korar wani, kasa hana sa tayi yayin da yake kai mata
sumbatar tsigar jikinta na tashi sosai.
Sosai Aisha ta gigice, harta rasa abin yi, bata taba shiga cikin irin wannan yanayin ba, babu
wanna ya taba rike Koda hannunta bare yakai bakinsa gareta, jitayi Aliyu yana Kara gaba,
domin ayanzun kokarin tura hannun sa cikin rigarta yake dan haka tai saurin mikewa.
Hijjab dinta ta dauka tana daga tsaye, cikin runannun idanun sa yake binta da kallo
Yayin da Aysha ta kasa hada ido dashi.
Kallo yake binta dashi ko cire ido baya yi, idon Aysha akasa tafara kokarin maida hijjabin
ta.
Hannu taga ya miko mata yana kokarin amsa Hijjab din,
Mika masa tayi sai dai har yanzun taki yadda su hada ido, domin balakin nauyin sa takeji,
ko ada tasan yafi karfinta kota Ina bare yanzun daya Kara girma, babu wadda zai kallesa yace
bashi da iyali agida, ga wani kasumba daya tara wadda kesa take ganin kwarjinin sa fiye da
baya.
Amsa yayi idonsa akanta sanna yai wurgi dashi kan kujera.
Juyowa yayi ya kalleta sannan yace xo nan.
Cikin sanyin jiki ta karaso gaban shi yayin dayasa hannun sa ya jawota jikin shi ya
rungumeta tsam, tsayon lokaci sannan ya sunbaci kumatun ta tare da saurin sakinta.
Da saurin sa ya juya dakin yaki bari su hada ido da Aysha.
Bayan sa Aysha tabi da kallo jikinta asanyaye bayan taga ya kule ta koma ta zauna,
hijjabin ta ta dauka ta rike ahannunta hawaye taji sun