Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
zuciyarta babu dadi, saidai tana matukar son tabar
gidan dan ayanzun dataga Umma gabanta har faduwa yake, hakama Maman Sadam garama
Aunty Murja mgn ne batayi da ita amman bata gaya mata bakar mgn, washegari ne ya kama
ranar da Innawo tace zasu tafi tun safe ta shirya saidai tana balakin son taga mamanta ba gani
irin wadda ta saba mata ba, ganinta take son tayi mata ido da ido suyi mgn duk da tanajin zafin
yadda take mata amman tana son ganinta.
Sai dai data fita saitaga maman Sadam na mata wani mugun kallo wadda tasan ko taje
gaban mamanta indai maman Sadam na wajen bazata mata mgn ba.
Misalin karfe 6 na yamma Innawo da Sadiya suka shigo, a tsakar gida ta samu maman
Sadam da Umma bayan sun gaisa tace nazo tafiya da Aysha.
Toh Allah ya taima ka, Sadiya ce ta shiga ta dauko akwatin ta fice yayin da Aysha ta fito
sanye da hijjabi Innawo kuwa khalifan ta dauko.
Aysha kuwa kasa daga kafarta tayi daga kofar dakin dan haka Umma tace kije kiyi
sallama da maman ki.
Maman Sadam ce tace a'a tayi bacci, Innawo ce tace eh kotana macci ta shiga haka.
Aysha bata jira amsan suba tashige dakin, yayin data samu Mama kan Sallaya, tsugunawa
tayi gabanta, cikin fashewa da kuka, yayin da Innawo take tsaye saman Aysha take fadin,
Aysha zata tafi gidan mijinta kisa mata albarka
Ahankali Umma ta motsa bakinta tace, Allah ya bada sa'a.
Innawo ce ta amsa da Ameen, sannan ta dago Aysha suka fito tana waiwayen mahaifiyar ta,
suko su Umma har Aysha ta fita agidan maganganu suke marasa dadi wadda ke nuna sun yake
zumunta da Aysha har abada.
Sosai Aysha take ganin bakinsu cikin ranta, badan Mamanta da Daddyn taba da zata iya
fushi dasu da tace ita da gidan har abada, gidan Innawo suka nufa, Ummi da Aunty Rukayya
ne a falon,, Innawo ce ta mikawa Ruqayya yaron sannan ta nunawa Aysha gurin zama tana
fadin, kiyi hakuri kinji ko, insha Allahu wata rana sai labari.
Aysha ta dade kudun dune cikin hijjabi sai bayan Sallan mangariba ta sarara da kukan,
saidai ko mgn bata iyawa, washegari sunyin sallah asuba suka kama hanya, har tasha Ummi
da Innawo suka rako su duk da cewa babu fara'a afuskan Ummi amman ta masu fatan sauka
lafiya, harma ta ziro hannun ta cikin motar ta gyara daurin hulan Khalipa tana fadin a gyara shi
kada iskan mota ya sashi mura, har ma ta Kara da cewa aunty Ruqayya karbe shi ne.
Hanya suka kamo yayin da Aysha takejin babu dadi cikin ranta, sunyi tafiya me nisa sannan
ta tuna da Babanta ko tantama batayi yayi tafiya ne da bazai taba daukan wannan lokacin bezo
ba.
*****
Oyoyo Uncle Aliyu.
Tohowa sukayi gaba dayan su yaran maza da mata suka rungume shi, cikin wani irin
yanayi yake daga kananan sama sannan ya Isa kujera ya zauna yana fadin, " Inna aunty?"
Wani Dan saurayi ne da bazai wuce shekara 16 yace tana Cameroon.
Lumshe ido yayi sannan yace, " yaushe ta tafi??
Yau kwananta 8.
Ta gaya muku ranar da zata dawo??
A'a
Mikewa yayi yasa hannun sa cikin aljihu ya ciro kudi ya mika ma yaron yana fadin, "kabawa
Yaya Fahat Ina sauri ne, idan aunty ta dawo daga nan zuwa gobe da daddare komai dare kazo
ka gaya min.
Gida ya koma cike da damuwa saidai yana shiga falon cikin daga murya Baffah yace,
" Ina Ruqayya?"
Sunkuyar dakai yayi yace bata nan.
Ina wasa dakai ne???
Wlh Baffah bata nan yaranta ne kadai agidan sunce tana Cameroon.....
https://youtu.be/7ZOCexBfeL4
*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 56- 57
Komawa Baffah yayi ya zauna yana cike da bacin rai, yayin da Momy take fadin, " kayi hakuri
kabi komai ahankaali.
Aliyu kuwa kansa akasa ya juya ya koma dakinsa tare da fadawa kan godo yai ruf da ciki
yana fadin, koma me Baffah yake zargina dashi nasan bazai wuce kan wancen auren bane
dan haka sosai yaji hankalin sa ya tashi, addu'a yake Allah yasa aunty ta dawo, domin yasan
dole Innawo zata aikota gurin Baffah, sai dai itama besan yadda zata dauki zancen ba.
Washegari tashi yayi da matukar zazzabi sabo da yadda yake Jin damuwa sosai, gashi
agobe yake son zuwa Cameroon amman Ina, yana tsoron yadda zai fad'awa Baffah.
Daker ya iya daurewa da yamman ya fito misalin karfe 5, bemasan inda zashiba kawai dai
fitowan yayi, motarsa ya shiga ya zauna yana kokarin tadata yaga an bude gate din gidan,
motar gidan su aunty Ruqayya yaga tana shigowa, take ya sake ajiyan zuciya batare data sani
ba, domin yasan duk yadda akayi aunty ta dawo kenan.
Jira yake yaga danta Abba ya fito amman abun mamaki ita da kanta ya gani tana saukowa.
Cike da zullumi ya bude motar ya sauko, ya nufeta, yayin da tana ganin shi ta sake
murmushi.
Dafda ita ya tsaya aunty yaushe kika dawo?
Jiya da Yamma, ance min kaje, Ina ta Allah Allah karka kama hanya.
Gobe nake da niyar tafiya, wani aikine ya taidani.
Ka makara matarka nata fushi dakai.
'Dan kawar takai yayi domin zuwa yanzun yasan tasan komai, cike da sonji yace, " kinje ne?"
Eh bama sau daya ba.
Sunanan lafiya ko?
Lafiya Lau, to Kai yaushe ka dawo?
Jiya da safe, nadawo ma nasamu Baffah sai fad'a yake yi, yana nuna wai yana zargina bani
da gaskiya, jiyan ma shine yace in Kira masa ke.
Dan takatawa tayi da tafiya tana fadin, wani ya kawo masa labari ne?
Shine ban sani ba Aunty.
Jimmm tayi zuwa can tace, " ai yana gida yanzun ko?
Yana nan.
Barin je karka shigo, idan ba kiranka yayi ba .
Amsawa Aliyu yayi sannan ya koma cikin motar sa ya zauna.
Ruqayya ko ciki ta shiga cikin fara'a Momy ta tareta, bayan tace mata gurin Baffah tazo
aka kaita har falon sa, Baffah na sauke ajiyan zuciya suka gaisa da Ruqayya, sannan yace
mata, daman Ina son ganin ki, jiya na aika Haydar ya kiramin ke yace kinyi tafiya.
Eh Baffah Ina Cameroon, jiya da daddare muka shigo, toh daman Innawo ta bani sako tace
Ina dawowa inzo in isar mata da sakonta gurin ka.
Toh toh naji, nima Ina son nai mgn dake, amman kafin nan bani sakon na Mama.
Shiru Ruqayya tayi tama rasa ta Ina zata fara, zuwa can tace, nima zuwa Cameroon din
kirana tayi, tunda naji kira nai saurin tafiya, toh daje sai take min bayanin cewa akwai yariya
data sauka a agidan nan watannin baya, wadda Aliyu yazo da ita.
Eh tabbas matar abokin Aliyu ko?
Eh toh, Innawo tace kayi hakuri kuma ka fahimci zancen dakyau dan Allah.
Inajin ki, muje, muje Ruqayyatu.
Toh Baffah wannan yariyar ba matar abikon sa bace kamar yadda ya gaya maka.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Baffah ya fada sannan ya tsare Rukayya da idon sa yana
fadin inajin ki.
Baffah wannan yariya ta dalilin ta Ummi ta koro Aliyu daga can Cameroon ya dawo nan da
zama, domin sun nuna suna son juna, Kuma anyi anyi su rabu sunki, a yadda suka bani labari
family yariyar ba inda basukai mgnr ba har kotu anshiga, amman sunki rabowa da juna, dan
haka ta turoshi gurin ka kawai.
Subuhanallahi, kinji irin abun ko?, amman da Aliyu yazo nan, ba yadda banyi dashi ba inji
dalili yaki fada min, daga karshe nabarshi kawai tunda Naga bason fada yake ba.
To Kuma Baffah sai gashi ya kumayin wani kuskuren agaba, domin da yariyar ta biyo shi
nan kasar bayan shekara biyar da rabuwan su Ya kamata ya sanar maka sabo da abashi
shawaran abun da ya sace.
Shiru Baffah yayi yana jinjina zancen, cikin ransa zuwa can yace, " a'a ikon Allah, bana
mantawa lokacin na mishi fada akan zuwanshi da ita, amman saiya rufemin baki da fadin
ajiyansa aka bashi Kuma ma matar Aure ce, toh abun da yasa ban damu ba lokacin, yariyar
cikin su Meenat ya barta, daga baya yace min Mijinta ya dawo, tazo tamin sallama na mata
alheri, duk ta saba da yara, yanxun haka ko jiya sunata cewa zasu zasu Cameroon gurin ta.
Ai Baffah da yace maka Mijinta ya dawo mota yasata ta koma gida, Innawo tace dan Allah
Kai hakuri karka dauki zancen da zafi dan kafin ta koma gida wani abu ya shiga tsakanin sa da
yariyar........
Batakai ga karasawa ba Baffah ya dafa kansa yana fadin Innalillahi wa inna ilaihir raju'un.
Yana rike da kansa aunty Ruqayya tace Baffah dan Allah kayi hakuri abun da suka guda
kenan suka turoshi nan, amman dake kaddara ta riga fata soyayya najanta, saida ta biyo shi
nan, bayan Kuma ta koma da wata uku iyayenta suka gane tana dauke da ciki, wadda aka rasa
inda ta samushi, domin bata kula kowa, Baffah saida yariyar ta haihuwa aka tabbatar d'an na
Aliyu ne, domin jinin sa ya nuna sosai Koda yariyar bata fada ba yaron yayi kama dashi kamar
an tsaka kara.
Motse baki Baffah yayi idon sa akasa sannan ya dauke gilashin sa dake gefen kujera yasa a
idon sa, daker ya iya bude baki yace, shikenan sai ya aureta kawai.
Jimmm, Aunty tayi sannan tace, " eh bayan yaje lokacin ta haihu kotu suka kaishi, nan ta
kwashe komai ta gaya masa har tahowan da tayi da yariyar.
Bayan ya gama sauraron Ruqayya yace, " shikenan Ruqayya bakomai, ni musulmi ne dole
in amshi kaddara mekyau da mara kyau, ni daman naji kishin kishin din yayi aure a Cameroon,
naji daga wani abokina da nake bawa sako na musashi, ganin wani ya sake min mgn nace
barin tuntube ki, su Kuma iyayen yariyar ai bekamata suyi watsi da ita ba, wannan auren da
akayi shine maganin abun, Kuma wannan ya Isa yasa zuciyar su ta huce, Amman fa laifin na
Aliyu ne, inda ya gaya min tunfarko da ke zan nema kisata agaba ki mayar da ita gaban
iyayenta, su Kuma iyayen idan suna da hankali lokacin zasu gane auren shiyafi dacewa dasu.
Ai Baffah iyayen yariyar nan banjin kome za'ayi zasu bada ita.
Toh shikenan, abun da ya faru ya riga ya faru, yanzun abun da za'ayi tunda Aliyu beda
gurin zama, besa zaiyi aure ba bare ya nema, wancen part din daman can danshi na gina shi,
yariyar tazo ta zauna aciki amman fa duk abun da zanma Aliyu yanzun zan masa domin yariyar
ne, domin yariyar ce abun tausayi idan bata samu farin ciki ba akwai matsala dole Aliyu ya
riketa dakyau, idan har yana son in huce dashi ya kyautatawa yariyar nan, akanta zan bashi
mamaki matsawar yace zai wulakantata. Tun shine silar lalata mata rayuwarta, Ina da 'ya'ya
mata idan aka masu bazanji dadi ba, dan haka itama yariyar nasoko cikin yarana idan ya nemin
ya wulakantata zan rufe idon incimai mutunci, wannan shine sharadina.
Cike da farin cike Aunty tace toh mungode Baffah insha Allahu zasu zauna lafiya.
********
Aliyu taganin tahowan Aunty ya fito cikin motar, yadda yaga fuskanta yasashi ya sake
murmushi yana fadin, " kungama?"
Eh, ya fahimta, amman kasan dole zaiji babu dadi, ya Kuma ce babu wulakanci, Kuma a
kanta zai iya saba maka, yana nufin dai beson rigima, yana son ka rike ta amana.
Ba rigimar da zamuyi aunty, ko munyi ma babu meji kanmu.
Murmushi tayi sannan tace Allah yasa, amman ai koni yanzun najiku, tunda Aysha bakaramin
fushi take dakai ba, samunta nayi fa ta hada akwati zata shiga duniya, sabo da fushin da take
dakai.
Nashiga uku, ya fada yana zare idon, tare da fadin, har kin Kara min tashin hankali, Anya
kuwa baxan tafi yau ba?, toh aunty kinji dai nayau, amman insha Allahu wannan ne nafarko da
kikaji kanmu kuma na karshe.
Dariya aunty tayi sannan tace, zafi kowa farin ciki da hakan kuma lokacin ne zan
tabbatar daku masoya ne, Aysha kuma daker na dakatar da ita, Amman zakazo gidan mu da
daddare ko?
A'a kam, muyi sallama kawai yanxun?
A'a kaxo.munyi da ita zam bada sako ka Kai mata.
Kansan ya sosa kadan sannan yace saina zo toh.
Motar ta shiga suka bar gidan yayin da Aliyu ya koma cikin gida yana sauke ajiyan zuciya.
Misalin 8:00pm Aliyu ya fito da nufin zuwa gidan aunty saidai yana son ya sanar da Baffah
gobe zai wuce Cameroon dan haka ya fara zuwa falon sa, da sallama ya tura kofar ya shiga,
Islam da Meenat ne suka amsa Baffah ko juyar da kansa yayi can gefe.
Zama yayi agefen sa yana fadin Ina wuni Baffah.
Lafiya, kawai ya iya cewa fuskan sa babu alamar walwala, Su Meenat ne suka gaidashi ya
amsa sannan ya sake kallon Baffah yace, " gobe zanje Cameroon.....
Tun be rufe baki ba Baffah yace, " ka gaishe su.
Kasa tashi yayi domin ba haka suka saba sallama ba idan zaiyi tafiya, ya dade zauna sannan
ya tashi jiki ba kwari ya fito.
Baffah kuwa Aliyu ta nafita ya mikawa su Meenat key din part din da Aliyu zai zauna yana
fadin, " ku rike wannan masu aiki zasuzo gobe su karba.
Baffah na meye ne key din?
Na wancen part din ne, yayan ku zaizauna aciki da matar sa.
Baffah zaiyi aure ne??
Yamayi a Cameroon.
Idon suka zaro saidai sun kula kamar Baffah bayajin dadi dan haka sukayi cikin gida.
Basu dade da fita ba Momy ta shigo lokacin Baffah yana dafe da kansa, kallon sa tayi
sannan tace Alhaji wani lbr naji abakin yara, wai da gaske Haydar yayi aure a Cameroon??
Eh, yayi.
Amman Alhaji kana nuna min iyakata agidan nan, wato sabo da banice uwar shi ba bazaka
gaya min komai da ya