Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   34 / 34

99K to 101.2K   out of 101.2K words

" ke dawo nan ki zauna.

Tafiya zanyi Ina son inje gida.

Ke kike da kanki kenan?, idan har a karkashin ikona kike karki fita, faloma ki dawo anan ki
zauna.

Cikin sauri ta saki akwatin tana fito da kayan ciki tana jefan Aliyu dashi, koda kayan suka
kare akwatin ta jafa masa, shidai yana zaune yana kallon ta harta gama haukata dakin da jefan
sa, da abubuwa, ganin komai ta jefeshi dashi yasata fashewa da kuka cikin surutun shine ya
rabata da dangin ta, ganin inda take tone tone Aliyu yayi kasa da murya tare da fadin, " dakata
Aysha, Alfarma daya neke nema agurinki, kibar daga murya kar wani yajiyo ki, indai har ni
kikemawa ki dawo kusa dani kiyi zaifi, dan banson kowa yajiki.

Bazan dawo ba, Aysha ta fada cike da masifa.

Wani irin tsayawa ya buga mata wadda yasata fadawa kan gadon batare data shirya ba,
yayin da ya Kara da cewa dauko qur'anin ki muyi karatu.

Kin motsawa tayi daga inda take, yayin data shiga maida numfashi tsayon lokaci ta dauka
sannan yaji tana fadin, " yi hakuri Yaya Aliyu"

Yawuce Aysha, kiyi bacci da safe zamuyi waya da Daddy zan gaya mishi kina son zuwa
danni yace min karkije

Sabo dame?

Yace sunce basa neman ki karki zo.

Kamar yadda Aliyu yace da safe ya Kira Daddy yayin da ya Kara Jadda masu kada Aysha
tazo kawai.

Har aka dauki tsayon sati biyu Aysha bata cikin wata walwala, yayin da a kaita zuwa mata
gaisu, ita ko mutane gani suke cikin da take laulayi ne ya hanata zuwa.

Bayan wata tara Aysha ta haifi Mubarak yana da wata Uku su Innawo da Ummi sukazo
bikin Sadiya, gidan aunty suka sauka, shima Khalipa tunda bikin ya taho ya koma can, sosai
Khalipa ya shiga zuciyar Ummi komai nasa irin na Aliyu ne sai yake ganin sa kamar sanda yana
karami.
Saidai wani abu da Aliyu ya lura dashi har akayi bikin Sadiya aka gama Aysha bata sakin
fuska gaban Ummi, dan haka ranar da zasu zo gidan su ya sameta da mgnr cikin hikima yace,
Ummi ta huce, yanzun kam, kullum saita tambaye ki ko, ko awaya ne kuwa, zuwanta nan kuwa
na fahimci tana son Khalipa da Mubarak, ko kema kin fahimci haka??
Kawar dakai tayi tare da fadin, " Eh"

Bani labarin yadda kika fahimta kamar yadda Nima nabaki yadda na fahimta.

Ni dai abar maganar.

Me kike nufi?, gaya min menene damuwar ki.

Babu.

Akwai, ki gaya min kawai.

Cikin kasa da murya tace nida ba Sona take ba.

Bangane ba son ki take ba?

Eh Mana, tuntuni bata sona ai.

Kina nufin yanzun kema baki sonta kenan???

A'a, ni ba nufina kenan ba, ai Ina gaishaita hakan ma ya isa..

Cike da bacin rai yace, toh bazai yiwu ba Ayaha, Ashe baki da Kunya, Ummin tawa?, ni
wani irin zagi ne dangin ki basu min ba, wanni irin kiyayya ce basu nuna min ba, mena
musu??? Kakar ki babu sunan da bata kirani dashiba, tuntuni take azabbatar dani, takaini can
takaini can, duk ta gama bata min suna ta zubar min da mutunci, ta jefamu acikin wani hali,
amman duk da haka bayan na aureki ban sake mayar mata da mgn ba, soboda darajar ki da
nake gani, duk wani wadda ya shafe ki dole na girmama shi......

Toh ya ai Nima.......

Cikin tsawa yace karki gaya min mgnr banza, zan miki duka yanzun nan.

Shiru tayi bata sake mgn ba, yayin da yaci gaba da cewa da wannan maman Sadam din ni
mafa inajim zafin su har yanzun, sabo da yadda suka tsane ni, mamace kawai bana ganin
laifinta, bakuma Dan bata dashi ba, saidan Ina mata kallon mahaifiyata kwatankwacin yadda
nake kallon Ummi, Amman itama tana da laifi, bata nuna miki soyayyar da yakamata uwa ta
nunawa danta, yanzun Ummi nama aina mata laifi, da rashin Jin mgn, ta nuna fushinta amman
nabasu hakuri gashin tun suna nuna fushin ahakali tana hucewa ce, meye laifin ta?, ninasan
halin Ummina, kiyayyar da 'yan gidan ku suke nuna min yasa tai miki abun da tai miki, badan
komai ba, sai dan a zauna lafiya, Mama ko haryau bata nemiki ba, duk da nasan cewa
makusanta ta ne basu da kirki, Umma na neman kusan hada shekara da rasuwa kenan meyasa
bata nemiki ba??, ai tasan kinyi kokarin zuwa Umma tace karkizo, kenan tana nan tana cigaba
da bin Umarnin Maman Sadam, su ya kamata kiyi fushi dasu ba Ummi ba.

Cikin share hawaye tace toh nafahimta, kayi hakuri, bazan Kara ba.

Kima Kara kika abun da zan miki, kema ai ke kika dada jagula abin, nasa ki amota kika
dashi kika dawo.

Wanni irin kallo ta masa sannan tace, " Allah ya huci zuciyar ka, ganin yaci gaba da mgnr ta
cika kofi da ruwan sanyi ta mika masa tana fadin Kai hakuri mana ya Aliyu sai mgn kake ko
bagaji bakai.

Kurban ruwan yayi sannan ya tashi ya fita.


*Game bukatar katin gaiyata kowanni iri, inayi, na aure ko suna, saukan Qur'ani mai girma, katin
sa ranar aure, kati dai kowanni iri, zaku iya tuntuba na ta wannan number 07014197556 Fadela
Lamido, cikin farashi me sauki, Harda Video me motsi, da Kuma wadda zakaga alamar hannun
na rubutawa, ku garzayo kuyiwa 'yan uwa da abokan arziki, babu tsada👌🏻*
Su Ummi kwana biyu sukayi agidan ita da Innawo, sosai Aysha ta tarbe su cikin mutunci da
fara'a ta saki jiki da Ummi sosai itama Ummi taji dadin haka, aliyun sosai yake Jin dadi ganin
yadda Ummi ke kula da Aysha fiye dashi kansa, aranar suka koma Cameroon, bayan sun dawo
daga rakiyar su ne Aljyu ya kula Aysha fushi take dan haka bayan sun dawo gida yace, " Aysha
akwai alamar nayi laifi ko??

Wani irin kallo ta masa sannan ta dauke Kai.

Ina Jin ki gaya min.

Kaine ranar dasu Unmi zasuzo kace min, wai kasani amota na dawo, nina jawo komai.

Ajiyan zuciya yayi sannan yai murmushi yace, bake kijaba nine na jawo, matso kibani kunnen

ki kiji wani abu, kunnen ta bashi kamar yadda ya bukata, mgana yayi sannan Aysha ta dago ta
kalleshi tayi murmushi tana fadin, " ai da na dawo ba iskanci bane ya dawo dani Kaine na dawo
na same ka.... Kasa karasawa tayi tare da fashewa da dariya.

Shima Aliyu dariya yayi tare da fadin karasa bana.

Cikin saura tace a'a wlh bana iya karsawa kunya nake ji.

Kunyawa?

Nidai na yafe, Yaya Aliyu wlh baka da Kunya.

Dariya yayi kamar yadda Aysha ma tayi dariya, sannan yace duk ranar dana Kara ce miki
haka zaki min, karkiji kunya.

Bayan shekara goma, Aysha ce da Sadiya zaune amotar su ta tafiya Cameroon, Khalipa
Mubarak Ahmad sai dan auta shahit duk suma suna zaune dukkan su yaran Aysha ne, Sadiya
danta daya Kuma batazo dashi ba.

Gidan Innawo suka sauka yayin da Ummi taita nan nan da su, sai dai wani abun tashin
hankalin tunda ta sauka suke sunturin zuwa kofar gidan Umma amman Maman Sadam ta
hanata shiga, ita da yaranta gaba daya da sauran dangin mamanta, musamman aka zaunar da
yaran maman Sadam akofar gidan dan karsu barta ta shigo, saidai Aysha ta kasayin hakuri
kamar yadda su Ummi sukace tai hakuri kawai kullum saitaje kofar gidan, suma yaran kirarin
dukanta suke matukar ta taka masu gida.

Idi ne ya sanar Aliyu halin da ake ciki Dan haka ya kira Aysha awaya yace ta dawo gida
kawai, duk da haka Aysha bataji ba saida taje gidan Babanta suzo tare nan na dai fitowa yayi
yace mata mam tace taje kawai tana mata addu'ar Kuma zai sameta duk inda take, tayi hakuri,
shima Daddy hakuri ya bata yayin da Aysha ke kuka sosai.
Ranar da Aysha zata dawo saida ta koma gidan gida sannan ta tura matar sa tace ma Mama
dan Allah tazo nan su gaisa amman sai ganin matar idi tayi tana fadin, " Aysha kiyi hakuri wlh
har mun kawo zaure da ita Maman Sadam ta biyomu cikin masifa ta rufeta da fada wai ai tasan
gurin ki zataje.
Kuka Aysha tayi sosai sannan ta amshi number matar Idi tace mata dan Allah ta amsan mata
number Mama ta turo mata.

Ko bayan sun koma gida Koke koke Aysha taitayi, rarrashinta sosai Aliyu yayi mata tare
dayin duk wani abun dazai kwantar mata da hankali.

Bayan sati daya matar idi ta turo mata da number Mama, tun daga wannan lokacin suke
gaisawa da mama cikin sirri babu wadda ya sani cikin yan uwanta, Daddy kuwa baya iya hada
shera batare dayazo ya dubata ba, wani lokacin harda kannenta yake zuwa su mata kwana
biyu, sannan yana kawo mata sako inji mamanta, itama tana saya mata abu akai mata amman
har aka sake kwashe shera goma bata ga mama ba, wadda yai daidai da shekaranta 20 a
Nigeria duk da cewa abubuwa sun faro da dama cikin harda rasa Innawo da Ummi, lakacin
rasuwar Innawo Aliyu da aunty Ruqayya ne kawai suke je, yayin da lokacin rasuwar Ummi har
Baffa da su Islam ma sunje, Aliyu kuwa gaba daya yaran shi ya tarkata amman beje da Aysha
ba dan har wannan lokacin yana samun labarin irin kalamin maman Sadam akan Ayaha, Kuma
duk rasuwar nan da akayi masu babu wannda yazo gaisuwa daga dangin Aysha sai Daddy,
tundaga yaran nan hudu Aysha bata sake haihuwa ba, Khalipa ya zama saurayi meji da gayo
wadda ya dauko halin baban sa sak, zuwa wannan locin Aysha ta saki jikinta ta saba da mutane
musamnan Sadiya, dan itace akayi komai gaban ta.

A yanzon Suna waya da Mama duk sanda taso, abangaren Aliyu kuwa, har wannan lokacin
yana tsananin Jin Aysha cikin ransa, sannan duk wani wadda zai kawo masa sukan Aysha daga
ranar sun raba jaha dashi, shera 20 kenan babu wadda ya taba Jin kansu, sosai Aunty Ruqayya
ke mamaki wadda ayanzun ita ta zamewa Aliyu uwa, har take kasa Hakuri tace wai Kai Aliyu
kuna fada kuwa kaida Ayaha, yakan bata amsa ne da fadin, Munayi mu biyu amman kasa kasa
muke da murya dan kada wani yaji mu.

Sosai aunty take farin cike da haka, tare da Kara masu addu'a zaman lafiya, Yaya Fahat
kuwa yana nan yadda yake duk da cewa har yanzun magani ake amman babu wani canji

Aysha kuwa tun wannan sallaman da tayi da mahaifiyarta tun lokacin da Innawo tazo
daukanta domin tafiya Nigeria basu sake haduwa ba, saidai tana nan azaune gidan Mijinta
wadda yake tsananin bata kulawa da nuna soyayya ta hakika fiye da tunanin me karatun, zuwa
wannan lokacin Khalipa yana marantar gaba da Secondary yana da shekaru Ashirin aduniya.



Alhamdulillah
07014197556

Anan na kawo karshen Labarin BA'KAR FURA, Ina rokon Allah ubangiji ya sake hada
fuskar Aysha da Ummin ta, tana raye basai ta mutu ba.🤲

34 / 34