Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 34

39K to 42K   out of 101.2K words

kiyi kitashi banson surutun banza, dake ake mgnr ne?

Cikin zunbura baki ta karasa ta tashi tana me fakar idon mama tana hararan Umma.


Gidan Innawo kuwa tunda Aliyu ya tafi hankali ya kwanta, ayanzun Umma da Innawo suna
gaisawa cikin mutunci, idan sun hadu cikin layin kamar basu taba wani rigima ba, gidan juna ne
dai basu shiga saida wani dalili na rashin lafiya ko jaje, sabanin sauran makota da suke iya shi
domin zumuncin mukotaka.

Ahankali kwanaki suke juyawa zuwa watanni watanni najuyawa shekaru Aysha na Kara
tsayo, amman tunanin Aliyu akoda yaushe yana makale cikin zuciyarta, shekaran Aliyu biyu da
tafiya ta ware zaren data nadawa zoben ta, saboda natsarta da yayi, zama yayi dass a babban
Dan yatsan ta, murmushi tayi tana zubawa zoben azufan kallo har ranta takejin sanyi idan ta
kalli zoben.

Ayanzun shekarun Aysha 16 dan haka alamomin girma duk sun bayyana ajikinta,
kasancewarta yar gayu yar kwalisa tuni samari suka fara kawo mata hari, sai dai koda wasa
Aysha vata kula kuwa, karatunta kawai take yayin da har yanzun Aliyu na nan karkashin zuciyar
ta, duk wani wadda zaice yana sonta yanzun balakin haushi yake bata, sannan duk wani
lokacin da zatai tunanin irin zabinta daya take son aura suffan Aliyu kawai take gani.

Haka shima Aliyu anasa bangaren ya kasa goge Aysha cikin ransa, yayin da yakeji abun
nason canza salo daga kanwa ko kawa yana son komawa soyayya, domin dayayi tunanin
macen da ya keson aura Aysha ce ke zuwar masa inda yake kimanta matakin girmanta
ayanzun.
Sosai ya Kara girma da cika, yayin da fatarsa ta Kara murjewa, bashi da matsalan kudi
akoda yaushe Baffah cikin turo masa da kudi yake, sosai girma ya kama shi horon da suke
karfa yasashi ya Kara budewa yana sheki ga wani gasumba daya tara wadda akoda yaushe
cikin gyara shi yake.
Sosai 'yan mata ke kokarin shige masa saidai ko kallo yariya bata isheshi ba bare har yayi
mgn da ita, duk da cewa yana kallon yadda sauran abokan karatun sa suke tara mata suna
sauke bukatarsu akan su amman hakan beta sa yaji wai shima bari ya nema ba, duk kuwa
dacewa jikinsa yana tabbatar masa da cewa yana bukatar abokiyar raguwa, shi kansa yasan ya
girma.


Bayan shekara Uku

Duk iya inda ake son cikar budurwa Aysha takai, sosai wani farin ciki ke lillube Umma idan ta
kalli yadda Aysha take da cikar halitta kirjinta cike yake tab da dukiya, yayin data kasance
yariyar yar kwalisa wadda ta hada ilimin addini Dana boko, sosai uwa da uba ke alfari da Aysha
domin ta hadu iya haduwa, Aysha irin matan nan ne wadda duk inda suka gifta sai an waiga
bama ga namijiba har mace saboda wani irin kyawu da Allah ya bata.

Tuni manyan mutane suka fara kawo mata hari, yaran manyan mutane masuji da kansu ne
ke zuwa nemanta amma da sunzo sau daya basu Kara dawowa koma mutum ya dawo ba
kulashi take ba.

Awannan lokacin Aysha tana da shekara 19 wadda hakan yayi daidai da shekara 5 da
tafiyan Aliyu, Kuma awannan lokacin ne ta kare makarantar secondary, ranarce kuma ta cire

zoben Aliyu daga babban yatsar ta maidashi kusa da dan karamin ya tsanta.

Har yanzun zanen fuskar Aliyu nanan acikin idonta, Kuma yanzun ne ta fahimci tana son
Aliyu.

Itako Umma ayanzun ko tuna Aliyu batai hakama mamah ayanzun burin su be wuce Aysha
tai aure ba.

Abangaren Aliyu kuwa shekaran sa daya da gama karatun sa wadda yayi shi na
tsayon shekara 4 ya fito a matsayin BSc Security and Intelligence Science, Aliyu kenan banban
yaro meji da takama wadda akafi sani da *(BS) Aliyu Moh'd Bello* saboda jajircewan sa kan
aikin sa yayi suna sosai, kwarewarsa dabawa aikin sa mahimmanci. Be fiye zama agida ba
Koda yaushe yana kan aikin sa dan haka be cika samun lokacin kansa ba.

Shekaransa daya kenan da fara aiki, saidai wani babban al'amari kulum Aysha Kara shiga
ransa take, acikin idon sa yake kimanta girmanta ayanzun yayin da duk inda yaji an Kira Aysha
saiya waiga.

******

Baffah?

Na'am Islam

Wai ya sunan Ummi na gaskiya?

Wacce Ummin? Baffah ya tambaya bayan ya tsare Islam da ido.

Ummin Cameroon.

Murmushi Baffah yayi sannan yace sunanta Fatima.

Toh Baffah wace Aysha?

Meenat ce tace, " Eh Baffah dan Allah wacece Aysha?

Aisha kuma?, bansanta ba meyasa kuke tambaya?

Islam ce tace Baffah kasan dai Yaya Haydar baya dariya ko?, Baffah mgn ma bayi yake ba,
Amman sau biyu Ina shiga motar sa zamu gidan Hajiya wlh har muje mu dawo bin wakar Aysha
yake yi"

Jimmm Baffah yayi zuwa can yace Sojan ne ke waka?, Karake mgnr yayi cikin fashewa da

dariya.

Meenat ce tace wlh Baffah, toh yana son sunan Aysha Idan yanabi har mantawa yake damu
amotar kaji yana bi kasa kasa nina dauka ma sunan Ummi ne

Dariya Baffah ya sakeyi yayin da Momy tadan yi murmusa tare da fadin Kila budurwar sa ce.

Baffa ne yace Anya kuwa wannan son girman shi zai barshi ya nemi budurwa?, Inaga fa
saidai a nemo wata amanna masa.

*****

Ayanzun Aliyu ya gama tabatar da cewa Aysha yake so, kullum ya zauna bashi da wani
tunani daya wuce nata, fuskarta yake tunuwa tana wasa da yatsunta kamar yadda ta saba,
murmushi yayi ko yanzun Yaya take? Allah sarki Aysha yariya me hankali, yariya me
nutsuwa ga kunya ba irin yanmatan nan ba, Aysha me sanyin hali, yariya me ilimi da son
nemansa Koda yaushe, afili yace yazama lallai inje inga Aysha, Ina tsananin son ganin ki.


Cameroon


Mama kinsan dai na dade banji ba, dan haka wallahi idan naje sai kun ganni.

A'a Aysha karki zauna, tunda kinki sauraron kowa toh kawai kice masa ya nema miki
makaranta kafin Allah ya kawo mijin, duk kin ki da aure idan mijin ki yazo dole zakiyi, Umma ke
fadin haka tana kallon Ayaha.

Ke Umma badamar afarq mgn saikice aure, komai aure, wlh natsana inji ance auren ma.

Baki Umma takama tare da fadin waike Aysha kanki kalau kuwa?, to ko lafiya ce bata ishe ki
ba?, Dan ubanki aure ne ya samar dake idan baki sani ba.

Cikin tsiwa Aysha tace to waike Umma idan auren dadi garai me ya hanaki yi?

Mamace ta kawo ma Aysha duka, yayin da Ayahar tai saurin kaucewa.

Umma kuwa fadi take rabo da ita babu ruwanki, juyawa tayi gurin Aysha tana fadin, dan
kasararki kifarawa uwarki fada dan tafini yarinta.

Dariya Aysha tayi sannan ta faki idon mama taiwa Umma gwalo.

Mikewa Ayaha tayi yayin data gyara mayafin dake ganta zuwa wuyanta kadai ta suka
nufi baya hadon bayanta, riga da siket ne ajikinta na yadi me taushi, sosai suka matse ta
gyaleta kuwa daidai wuyanta kawai ya tsaya, tsugunawa tayi ta dauki akwatin ta tace toh natafi.

Adawo lafiya mama tace tana binta da kallo tare da fadin ki gaidashi.

Cikin dan sanyin jiki kadan tace zaiji, Umma kema natafi.

Toh ki gaida Uban naki.

Jimmm ta tsaya tare da fadin, Umma wannan ai zagi ne, Nifa tafiya zanyi kimin addu'a

Matsoraciya, tafiya da intayi yawa awa daya kike kira tafiya, toh shikenan Allah ya tsare
hanya.

Akwatinta ta fara jah harta fito kofar gida tana waiwayen gidan , ta kofar gidan su Aliyu ta
wuce kallon gidan taitayi hartai nisa, tana Isa bakin titi ta tare mota tahau cikin harcen fullacin
tace Tasha zaka kaini.

Cikin kankanin lokaci suka iso, motocine birjik ga matafiya kowa na azama, wasu ta
tambaya dan Allah Ina motar Kano Nigeria. Batare da bata lokaci ba aka nuna mata, yayin da ta
taras mutun daya suke jira, shiga tayi tare da sauke ajiyan zuciya, kudin motar ta kirga tabada
kamar yadda aka gaya mata sannan motar ta tashi batare da wani bata lokaci ba........


Toh ga Aysha ta shiga motar Kano Nigeria, Kar me karatu ya manta, Aysha ba bahaushiya
bace, batajin hausa kwata kwata kozo in kasheka bata sani ba, daga fulatanci sai
French take ita ji, wannan shine mafarin komai


*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_

*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

episode 25- 26

Tafe suke cikin motar tana kallon hanya, tunda take bata taba biyo irin wannan hanyar ba, iya
tafiyanta me nisa gidan Daddy yau gata tana keta dajuka.

Tun tana ganin tafiyar me sauki ce harta fara tunanin kodai duniyar za'a bari, duk kokarinta
na kada tai bacci cikin motar saida tai bacci me tsayo ta tashi, wani mutmi dake kusa da ita ta
tambaya har yanzun ba'a kawo ba??

Ke yariya ai ba'ama soma tafiya ba, baki taba zuwa bane halan?

Eh kam wannan ne zuwana nafarko.

Toh ki shirya zama, akwai zama agaban mu.

Ya mutsa fuska tayi sannan tace da driver inajin fitsari.

Muryan wata mata daga bayanta taji tana fadin ke yariya daure mu Isa masallaci.

Waigawa tayi ta kalli matar tare da fadin ankusa ne?

Eh yanzun zamu Isa.

Bayan kusan tafiyan minti 27 suka Isa masallacin, yayin da Aysha tafice da sauri daman
abakin kofar take domin itace takarshen shiga motar.

Masallaci ne Babba, wadda yake awajen gari, da alama masallacin kusam Dan matafiya
akayi shi, waddan aharabar masallaci akwai masu abubuwan siyarwa nama tsire lemo ta
sauran abubuwan motsa baki.

Cikin toilet din da aka samar domin mata ta shiga zuwa can tafito taga wasu har sun fara
al'wala, itama wata butar ta dauka tayi alwala sannan ta shiga cikin masallacin, sai yanzun ta

tuna bata dauko hijjabin sallanta ba, gyalene kawai ajikinta wadda ya kasance karami ne sosai
wadda be wuce adaurasa akai ba, kuma ko cikin kayanta duk irin sune. Dan haka dole tajira
wannan matar ta idar da sallar sannan tace , " mama dan Allah aramim hijab inyi sallah.

Cirewa tayi ta mika mata, sannan ta zauna agefe, Bayan Aysha tayi sallah ta bawa matar
hijjabin tare da gyara mayafinta.

Atare suka fito da matar wadda ya kasance su kadai ne mata acikin motar, hannunta
matar ta rike suna tafe take matsa hannun Aysha tana fadin Yaya sunan ki?, Cikin harcen
filatanci take mata wannan tambayar.

Sunana Aysha.

Ina zakije?, Ina nufin wajenwa zakije Nigeria?

Jimmm, Aysha tayi zuwa can tace wajen Babana zanje.

Babanki, Ina mahaifiyar ki fa?

Mahaifiya ta muna tare da ita anan Cameroon Babana Kuma dan Nigeria ne"

Cikin gamsuwa matar tace nafahimta, Amman meyasa ba'a hadoki da wani babba ba
akabarki ke daya.

Ni kadaice agidan, kakata Kuma tsohowace mamanace take kula da ita.

Allah sarki, nagane, amman duk da haka naga gangancin su, kasancewarki yariya
budurwa yakamata da wani babba atare dake, Amman insha Allahu Allah zai tsareki.

Insha Allahu Mama.


Kallon ta Mama ta sakeyi tare da fadin gaki kyakyawa dake, son kowa kin wadda ya rasa, ko
in inyiwa dana kamo ne?

Murmushi Aysha tayi tare da sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta.

Matar ce ta sake cewa, ko kina da wadda kike so ne?, Ina da yaro na Babba in Zaki soshi?

Murmushi Aysha ta kumayiwa Mama kanta akasa.

Mama ma dariya tayi tare da cewa, Ina baki kunya ko?, Da haka suka Isa gurin motar yayin
da matar ta roki mutumin dake kusa da ita ya dawo gurin Aysha domin Aysha ta dawo kusa da

ita.

Be musa masu ba ya basu guri suka dawo kusa da juna.

Hanya aka sake dauka tsayon lokaci suna keta hanya yayin da Aysha ta gaji da zama
sosai.

Tun tana ganin abun kamar wasa har taga dare ya raba, sosai hankalinta ya Kara tashi, tun
gurin 9:00am tafito, cikin firgice ta kalli Mama tare da fadin Mama ahanya zamu kwana ne?

Eh Mana Aysha Idan Allah ya taimake mu gobe da rana zamu Isa idan Kuma mun samu
tsaiko har jibi muna iya kawai.

Wayyo Allah na mama kafata duk ta sake.

Daure diyata. Insha Allahu gobe war haka kina gidan mahaifinki kina hutawa.

Daren nan Ayaha bata iya runtsawa ba yadda taga rana haka taga dare, washegari
Misalin 3:30pm Aysha ta sauka a garin Kano, sosai gabanta ya shiga faduwa yayin da wani
shashin nazuciyarta ke mata fada anya kuwa hakan ya dace, sosai jikinta yai sanyi hankalin ta
ya tashi har mama take tattare kayanta ta kula da hakan kallonta tayi tace, " Aysha ya dai?"

Bakomai mama.

Jimm tayi sannan mama tace motar Ina Zaki hau?

Akwatinta ta nufa ta bude sannan ta ciro wata farar takarda tace sunan unguwa yana
rubuce anan.

Wani irin kallo Mama taiwa Aysha sannan tace amman dai iyayen ki suna da ganganci. mika
Hannu tayi ta amsa takardan ta bude. dagowa tayi ta sake kallon Ayaha cikin yamutsa fuska
tace, Inazuwa, driver daya sauke su ta nufa ta nuna masa takardan, sakkowa yayi ya yana rike
da takardan yace ta dauko kayanta ga mota can asata.
Daukan Akwatin Aysha tayi yayin da mama tabita abaya har suka Isa cikin motar, shiga
Aysha tayi ta zauna yayin da driver yake ke gaya masa sunan unguwar wannan lokacin bata
sanin me mutumin yace dan bata san wani yare bane.

Takardan ta karba sannan Mama ta juya taiwa Aysha sallama tare da Kara gargadinta cewa
takula da kanta.

Kwallah Aysha ta share domin Jin mama take tamkar mahaifiyarta sabo da yadda ta
nuna kulawanta agareta, hawaye ne ya shiga ziraro mata yayin da can kasan zuciyarta takejin

kamar batawa iyayenta adalci

14 / 34