Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   29 / 34

84K to 87K   out of 101.2K words


Zuwa wannan lokacin zuciyar Aysha ta fara tafarfasa take dan haka ta juya tabar gidan

batare da tasan inda take saka kafarta ba.

Tunawa tayi da yaron, haka nan taji gabanta ya fadi, bata taba jinsa aranta kamar yau ba,
cikin sauri ta shiga gidan iro, halin da take ciki ta gayawa matar iro cikin tsananin tausayawa ta
bata ruwan zafi cike da bokiti, cikin sauri ta koma gida saidai tun daga zaure takejin ihun yaron
a tsakiyar gidan ta aje bokintin ta shiga dakin, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un ta fada lokacin
data hangeshi akasa.

Cikin sauri ta daukeshi tana jijjigawa, tsananin tausayin yaron ne ya dirar mata lokaci kuda
daker yai shiru sannan tasa masa nono a baki, zuwa can yayi gyatsa dan haka ta masa shin
fida akasa sannan tai sauri tayi wanka da dawo, bayan ta shirya a gurguje tai masa wankan ta
shirya sa.
Tun daga wannan lokacin saidai taje gidan iro ta roko ruwa ranar da basu dashi kuwa rushi
matar iro take bata ta tsuna na tsayon lokaci, sannan ta bata ruwan zafin da zata sha, da
Wanda zatama yaron wanka, yaron ko yanayin kwana biyu zuwa uku babu wanka saboda
itama matar iro tsoron Umma take ji.
Ahaka har sati hudun da Aliyu ya fada suka cika, gashi komai nata ya kare wadda ya bar
mata, ranar da ya cika sati biyar da tafiya Husna da Innawo sukazo da ledoji kayayyakin da
suka mata sayayya, awulakanci Umma da Maman Sadam suka amsa gaisuwar su.

Sosai sukaga Ayaha ta fige ta lalace duk alamu ya nuna azabtar da ita sukeyi, yaron ma
daganin sa babu wani cikkiyar kulawa a tattare dasu gaba daya, sosai Innawo ta tausaya mata
har suka koma gida tanajin damuwan Halin data sameta aciki.

Ranar da Aliyu ya cika sati na shidda Aysha ta tsinta kanta da tsananin haushin sa ganin
idan yai alkawari baya cikawa, fushi tayi dashi sosai tare da rasa inda ya dusa, tuni taso ta gudu
tabar gidan malam idi da matarsa suka hanata, dan haka yanxun takejin yakai lokacin da zata
gudu tabar garin batare da sanin kowa ba barema a hanata.
Cikin dare tai niyayyar barin gidan dan haka tun yamma ta shirya kalifa taimasa wanka
bayan kwana uku daya dauka babu wankan, goyesa tayi ram abayanta yayin da zuwa yanzun
ya cika bayan nata.

******

Momy gaskiya garin ku da nisa, har yanzun bamu Isa gidan Ummin Uncle Aliyu ba.

Da nisa Sadiya shiyasa kikaga Ina dadewa banzo ba.....

*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

Episode 54- 55



Akofar gidan Innawo motar ta tsaya, ahankali suka fara fito da kayan su sannan suka nufi cikin
gidan Innawo.

A'a lale lale, kune tafe da yamman nan.

Wlh Innawo tun shekaran jiya muka taso, motar ba sauri.

Afalon suka baje tare da cire mayafin su, Ummi ce tafito daga bayin cike da murmushi ta
fada Sadiya tana fadin an girma rabon ki da kasar nan tun kina goye.

Cike da fara'a Aunty Ruqayya tace, aitace girin ku da nisa.

Dariya akayi yayin da Innawo ta juye masu ruwan wanka, bayan sunyi wanka sukayi Sallah
magariba domin lakacinta yayi sannan Ummi ta baje masu abinci.


Bayan sun gamaci ne Aunty Ruqayya da 'yarta sadiya suka kwanta nan tsakiyar falon suna
hira yayin da Innawo da Ummi suke zaune, hiran suke cike da nishadi suna ta dariya zuwa can
Innawo tace, " wai Aliyu ne ya gaya miki ina kiranki koko kawai dai kinzo ne?

Shine ya gaya min Innawo, sau uku yazo musamman ya jaddada min lallai kina son ganina.

Ya gaya miki abun da ya aikata?

Cikin sauri Ummi ta kawar da kanta tare da daure fuska sosai.

A'a me yayi?, nidai yazo kawai yace min ya dawo.

Dan Murmushi Innawo tayi sannan tace ai kanin ki mgn ya dauko mana.

Wacce irin mgn Innawo?, tashi tayi zaune tana kallon Innawo sannan ta juya ta kalli Ummi
data hade rai, ko ba'a fada ba tasan Ummi fushi take da Aliyu.

Innawo ce tace, kunyi d'a, danku nan kato nan gidan Umma.

Cike da mamaki tace bangane ba??

Ummii ce tace, yariya yama ciki harta haihu.

Subuhanallahi, Aliyu?

Shifa, Ummi ta bata amsa"

Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wacce yariya kenan?

Innawo ce tace ita dai wannan yariya Aysha da aka rabashi da ita, kinga rabawar ma beyi
amfani ba.

Kashhh, abu beyi dadi ba Innawo, toh wai ita yariya ba annan take ba?

Innawo ce ta kwashe komai ta gaya mata duk yadda akayi, kama bakinta tayi tare da fadin,
haba, biri yayi kama da mutum, watanin baya Aliyu ya tashi hankalin sa har nima yazo ya daga
min nawa, cikin tsananin damuwa yake zuwa ya kwata min ajiki wai in kwantar masa da hankali
kamar yadda Ummi ke masa, sannan sau uku yana sa ranar tafiya har yazo yamin sallama
amman washegari saina ganshi ya yazo wai shi ya kasa tafiya gabanshi faduwa yake, ba irin
tunanin da tunanin da banyi ba.

Aikuwa dai yanzun anbata da Ummi, dan ta kunkunduma masa zagi manya manya ma
kuwa, badan Ina tsakani bama inajin tsine masa zata yi, dan naga kamar tayi niyya.

Idon Ruqayya cike da kwallah tace, ayya Ummi ba halin shi bane fah, dan Allah kiyi
hakuri.

Kawar dakai Ummi tayi, yayin da Aunty Ruqayya tace toh aini banga ta zama ba, barin
je in dubosu in dawo.

Ki bari saida safe Mana.

A'a Ummi yanzon zani ni daman bansan yariyar ba, yakamata ace komai ya wuce yanzun,

mu rungume yariyar mu nuna mata kauna, tunda yana sonta, wlh Ummi zan iya rantsuwa
tsautayi ne, kanina ko acen bashi da rawan kai, Baffah ma fada yaketa masa akan yiyi aure,
amman wlh ko budurwa bashi da ita.

Cike da taici Ummi tace, " itafa zai yi rawan kai, bayan ya kala rai nan, ai daman hakane,
duk matsalar da abun da mutum zai aikata sai ace tsautsa yi.

Mikewa tayi ta yafa gyalenta sannan tace ma 'yarta Sadiya tashi muje.


******

Tundaga zauren gidan sukejin kamshi, sallama sukayi bayan an amsa musu suka shiga ciki.

Umma ce da Maman Sadam suke cin abin ci, gaisawa sukayi sannan sukace, " Aysha suke
nema"

Umma ce tace, au Ruqayya ce, da hannun suka nuna mata dakin tare da fadin, " tana nan
ciki.

Dakin suka nufa daga yaddda suka mata tasan ba wani shiri suke da itaba, sallama sukayi
daga ciki Ayaha ta amsa, dan haka suka shiga.

Gaisawa sukayi sannan Auny tace, nasan baki sannin ba ko?

Eh.

Ni Yaya Aliyu ce daga Nigeria.

Ayya, sannu dazuwa, fuskarta ta dan sake kadan, kallonta Aunty Ruqayya tayi sannan ta kalli
akwatin dake gabanta, hijjabinta na kan akwatin, itako harda takalmi akafarta, ga dukan Alamu
dai fita zatayi, dan haka Aunty Ruqayya cikin nazari tace, " fitama zakiyi kenan?

Eh wlh, Aysha ta fada tana kawar da ido.

Toh dan bani yaron ingani Mana.

Mikewa tayi ta kwantoshi ta mikawa Aunty Ruqayya sannan ta koma ta zauna.

Ido Ruqayya ta zubawa yaron fuskanta cike da murmushi, tabbas wannan karamin Aliyu ne,
idonta akan yaron tace Ina zakije naga harda akwati?

Kawar da kanta tayi yayin da hawaye ya zubo mata tai saurin sharewa.

Da kallo Aunty Ruqayya ta bita zuwa can tace, kin dai san akwai aure akanki bekamata ace
kina fita babu izinin mijin ki ba, ko kuwa ya baki dama kije wani waje ne??

Idonta akasa tace a'a.

Shine kike kokarin fita harda su daukan akwati?

Toh aunty yaushe nasan ranar da zai dawo dahar zanzauna Ina jiran Umarnin sa, bakin
ciki ne zai kashi kawai, bazan zauna jiranshi ba.

Kallon Aysha aunty tayi tsayon lakaci, damuwa karara afuskanta tagani dan haka tace,
kenan wannan kayan da kika hada garin Zaki bari?

Kawar dakai tayi sannan tace a'a.

Eh Mana, toh Ina zakije da daddaren nan?, kina jira mutane su shiga daki ko???

Dagowa Aysha tayi suka hada ido sannan tai saurin mayar da idonta kasa.

Aunty ce tace, " toh wlh karki fara, nasan aiki ne ya tareshi ba wani abu ba, sanda na
tahoma baya garin, kiyi hakuri yana nan zuwa ko Kuma ki shirya sai mu tafi tare.

Kawar da kanta tayi can gefe yayin da aunty Rukayya ta sake cewa ki shirya sati daya zanyi
sai mukoma tare.

Ni bazani ba aunty, ai shi yama manta dani yanxun, daman ance min bazai dawo ba Kuma
ko naje bazai bari in ganshi ba�

Cike da Mamaki aunty take kallon Aysha sannan tace, duk wadda ya gaya miki haka ya
fadane kawai, Aliyu ba haka yaje ba, ninasan zai dawo ba haka Aliyu yake ba.

Kawar dakai tayi sannan tace, wlh aunty haka yake, wancen karon ma cemin yayi wata Uku,
Amman bezo ba saida aka kusa shekara, haka yake, beda alkawari, nasan bazai dawo ba ko
zai dawo saina kusan mutuwa da wahala, haka yayi min waccen karon, amman bakomai ba
laifinsa bane, laifinane, da banje gurin saba da yanxun Ina zaune lafiya da 'yan uwana cikin
mutunci, kamar yadda yake zaune da nashi, Ina shan wahala arayuwata, gara min mutuwa da
wannan rayuwar, kowa ya juya min baya cikin harda Yaya Aliyun......

A'a kam, kicireshi aciki, nasan rankine ya baci, Kuma shi besan halin da kike ciki ba......

Ya sani, saidana gaya mishi, yace min in basu hakuri, Kuma nata basu har nagaji, basa sona,
basa son ganina, saidai in fita in sawo abun da zanci, ruwan wanka kuwa sai dai inje makota in

roko, inayin kwana biyu uku banyi wanka ba.

Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, aunty ta fada, sannan ta mike ta mikawa Sadiya dake kuka
yaron ta koma kusa da Aysha ta jawota jikinta ta rungume, itako Ayaha fashewa tayi da kuka
sosai, tana jinta rungume jikin Rukayya rabonta dataji an rungumeta haka tama manta, ashe
rungumewa ma rahama ne, Kara shigewa jikin Rukayya take tamkar zata shige jikinta, ahankali
Rugayya tace Aysha Ina mahaifiyar ki take duk wannan abun yake faruwa?

Tana nan acikin gidan nan, amman ita bata cewa komai, sai abun da su Umma sukace,
nasan ko bataso yadda suke min bazata iya hanasu ba, Kuma itama bazata kulani ba haka take
tuni nasani.

Jimmm tayi, sannan tace, toh kishirya rana ita yau zan kaiki gurin mijin ki.

Cikin sauri ta dago daga jikin aunty ni bazani gurin saba aunty ai yana sane Dani yabarni
anan.

Amman Aysha ki masa uzuri mana.

Baya ta juyawa aunty tana wasa da hannunta ganin haka aunty tace shikenan nasani Aliyu
yayi laifi, be kyauta ba, yanzun abun da nake rokon alfarma wajen ki, tunda ba xaki gun Aliyu
ba, ni kibini ki zauna gurina tunda yanzun inma fitan kikayi bakisan inda Zaki ba.

Cikin kuka Aysha tace Aunty bazani ba dan Allah kiyi hakuri.

Ajiyan zuciya aunty Ruqayya tayi har ga Allah ta damu da lamarin Aysha, hannunta ta daura
akan gado bayan Aysha, sannan tace, " yanzun kenan inda Allah be kawo ni yau ba garin Zaki
bari?, In kin fita kinbar gida yanzun kinsan hannun wa zaki fada ne?, haba Aysha, shikuma Aliyu
idan ya dawo akace mishi ba'asan inda kike ba kina tunanin awanni hali Zaki sashi??
Aunty ni babu abun da ya dameni dashi, ba halin da zai shiga, yana sane yake yin haka, ni
daman ban sanshiba arayuwata, tunda nasanshi nake shiga cikin matsala gashi kullum kara
gaba take, shikuma janyewa yake, garama mota ta takeni na mutu in huta.

Cikin tsananin tausayawa Aunty tace kibar irin wannan tunanin, Kuma ki daukeni kamar 'yar
uwarki, koma uwa kika maidani daidai ne, ko ban haifi kamarki ba kadan ya rage nafahimci kinyi
fushi da Aliyu sosai dan haka mu aje zancen Aliyu agefe, ba Ina kareshi bane wannan kibarshi
a tsakanin ku, kibini muje gidana ki zauna tare dani.
Amsawa tayi kawai dan takula aunty ta tausaya mata sosai, Kuma yadda take rarrashin ta da
Kunya tace mata a'a

Aunty ce ta share mata hawaye sannan tace kin fasa tafiyar ko?

Kai Aisha ta daga.

Yauwa nagode Aysha, yanzun bari muje da Khalifa amishi wanka sai adawo dashi.

Na mishi wanka da yamma ma aunty ko za'a bari da safe?

Toh aini kin banin tsoro ne Aysha, ganin nake kamar idan banje da yaron ba tafiyar ki zaki
yi.

A'a ba inda zani Aunty na miki alkawarin bazanje ko Ina ba.

Toh nagode da safe Sadiya zatazo ta dauke shi.

*****

Koda Ruqayya ta koma gida labarta masu halin da ake ciki tayi, sosai Innawo ta tausayawa
Aysha, haka kuwa washegari da sassafe Ta tura adauko Khalipa, wanka tamai tamai tana zubar
da hawayen tausayin yaron, bayan ta gama shirya shi jikin Ummi ta daurashi tana fadin Ummi ki
kalleshi dan Allah kisa mishi albarka ba laifinsa bane ?
Tunda Ummi ta daura idonta akan yaron ta fashe da kuka, shikuwa yaji dadin wanka sai
wuntsula kaba da hannuwa sama yake yi, sai rana aka mayar mata dashi, tundaga wanna.
Ranar kullum Sadiya take kaiwa Ayaha ruwan wanka sannan ta dauko yaron amasa har suka
cika kwana biyar, aranar ne Innawo ta shiga gidan ta kanta ta sanarwa Umma gobe za'a tafi da
Aysha gurin Mijinta Nigeria, tana bude baki kuwa tace Allah ya rakata taki gona.

Tun aranar Aysha tafara hada kayan ta, bawani abu me yawa ta diba ba, akwati daya
tayi nata Dana Khalifa, haka takejin duk

29 / 34