Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 34

33K to 36K   out of 101.2K words

lau, tafada kanta akasa.

Murmushi yayi sannan yace ai da kika nace saikin bini nadauka jaruma ce ashe raguwa
ce duka daya kika birkice.

Kamar jira take ta fashe da kuka da karfita.

Dan zare ido yayi sannan ya karasa ya dafa kanta yana fadin, yi shiru ni ai wasa nake miki
daga wasa saiki kama kuka?, Kiyi hakuri nabari kawata, hannun yasa yana share mata
hawayen sannan yace, Ina ta tunanin wani hali kike ciki agida ne shine nace barin zo in ganki.

Dagowa tayi ta kalleshi tace, ni Mama bata min mgn kowa ma bemin sai dai suyita

zagina ku......

Katseta yayi da fadin, kin masu mgn ne basu amsa ki ba??

Cikin kawar dakai tace a'a

Toh ke kimasu mgn kinji ko?

Kaita daga ahankali.

Yauwa ko kefa, muje in sauke ki.

Zagayawa tayi ta shiga, ko cikin motar hira suka dan taba duk da ya kula Aysha cikin fushi
take, nesa da gidan ya dauketa sannan ya koma da baya yabar unguwar.

Misalin karfe uku ya dawo gida, cikin dakin sa ya zauna tare da bude kwanon abin cin
daya samu adakin , tun da ya dawo yaune yai sha'awar ya cin wani abu, sai dai alokacin da
yake shirin Kai loma bakin sa yaji ana fadin, Sako daga kofar sarki cikin minti 15 ana bukatar
Aliyu Akofar.
Gaba daya gidan saida gabansu ya fadin, domin idan zance yakai kofar sarki to lallai
lamarin ya girmama, aje abincin Aliyu yayi tare da rasa ta yadda zaiyi ya hada ido da mahaifiyar
sa.

Innawo ce tace Kai Aliyu maza ka fito, fitowa yayi yana me Satan kallon dukar Ummin sa,
itako Ummi wannan karon suman zaune tayi domin ko tantama batayi an Kuma ganin Aliyu da
Ayaha ne.

Inawo ce ta dauki mayafi yayin da Ummi ke fadin, Innawo karkije kibarshi yaje shi daya.

Innawo bata saurareta ba tabi bayansa, yana gaba har suka Isa, yayin da suka samu Umma
da Aysha agurin.

Batare da bata lokaci ba aka karanto laifin Aliyu wadda tun kafin suzo gurin Innawo tasan
koma meye dai kan Aysha ne, gashedi tare da Jan kunne akamawa Aliyu da Aisha fahimta
nacin su tare da kinjin mgn sarki ya bada Umarnin amasu bulala, haka akayi bulala goma goma
aka masu a gadon bayan su sannan aka sallame su.

Ko ahanya Innawo batacewa Aliyun komai ba, kurmar karfi da yaji ta zama, hakama Ummi
Koda taga sun dawo da kallo kawai ta bisu tare da nemarwa kanta mafita acikin zuciyarta

Zaune take ta kasa tashi ta saka wancen ta kwance wancen har taga Aliyu yazo ya

wuce ta ya fice agidan.

Innawo ce ta fito tana fadin, Aliyu fita yayi ne?

Fita yayi Innawo.

Zama Innawo tayi kusa da Ummi tana fadin, wannan al'amari ya wuce azauna ana masa
fada fa, tunda dagashi har yariyar kamar ma Kara tunkudasu ake yi, yanzun karki tantamar
gurinta zashi tunda yana kallo kakarta ta saita mata hanya, nifa Ina ganin addu'a ce mafita, dan
wannan lamarin nema yake yafi karfin mu.
Innawo nifa bazan iya ba, gaba daya Aliyu ya sire min, nifa Innawo kudin mota kawai zan
hada mishi ya koma gurin mahaifin shi, karake mgr tayi cikin fashewa da kuka yayin da Ummi
tai saurin dafa bayanta tana fadin, karki mai haka Fatima, ai be saba da mahaifin sa ba, idan
kikai masa haka Zaki cutar dashi.
Cikin matsancin kuka Ummi tace, Nima cutar dani yake anan Innawo, Banda cutar da
zuciyata da yake Kuma yana watsar da mutuncin danginmu a idon duniya, Innawo yaranki basu
jawo miki abun magana ba har kika auren dasu lafiya wani baitaba jawo miki rigimar da aka
kaiki kofar sarki ba sai akan Aliyu, baki taba zuwa police station ba sai akan shi, Kuma ai bashi
kadai bane jikanki.

Cikin son kwantar wa Ummi da hankali tace au to saime?, duk wannan ba wani abu bane
rayuwar kenan ai, karki fara kokarin turashi inda be saba ba kinjin ko kiyi hakuri zai bari.

Sai bayan sallah isha'i Aliyu ya shigo gida, washe gari ta kama asabar ne Aliyu yana gida,
misalin karfe 11:15am takardan sammaci ta samesu wadda Umma ke Karan Aliyu.

Babu wadda yaji mamakin takardan cikin su, domin kuwa sunsan hakan na iya faruwa,
Aliyu ne ma ya Dan nuna ya shiga damuwa badan kowa ba sai gudun Kar mahaifiyarsa tace
yakijin mgnr ta dan haka ya tsuna gabanta yana fadin, Ummi kiyi hakuri, bada gang......

Katseshi tayi da fadin bakomai jeka kawai, duk yadda yaso yai mgn Ummi taki sauraron sa
dan haka ya mike ya koma dakinsa cikin tashin hankali, daker ya iya kaiwa Monday kafim ranar
harya fada saboda yasan shirun dasu Ummi suka masa shima mgn ce

KOTU


BAyan an gama karanto karar Aysha da Aliyu, babban Alkalin ne ya kalli Aysha sannan ya
juya ya kalli Aliyu, juyawa ya sakeyi ga Aisha yace shekarki nawa?

Cikin harcen fullacin tace , shekarata 14.

Alkalin ne ya ya bukaci datayi mgn cikin harcen French dan haka tai saurin juya harce ta
sake maimaitawa.

Juyawa yayi ya kalli Aliyu tare da fadin, Aliyu kaji laifukan ka da ake tuhumarka dasu?

Eh naji ranka ya dade.

Hakane koko zaka kare kanka?

A'a

Kallonsa Alkalin yayi sosai sannan yayi rubutu a takardan dake gabansa tsayon lokaci
sanan ya dago tare da fadin.

Ina bawa iyayen Aliyu da iyayen Aisha shawara da ku nutsu kusa hankalin ku waje
daya ku masu aure, inaga wannan kadai shine mafita, idan hakan be muku ba kuna iya zaban
wani kotun domin in juyaku zuwa can, eh mafita amasu aure.

Babu halin mgn acikin kotun dan haka Innawo na fitowa wajen kotun tace, Wlh wlh da
Aysha ta aure wannan abun Kara ta mutu yau.

Ummi ma dake gefe cewa tayi, ki kwantar da hankali ki Umma badai Aliyu bane, daga
rana me kamar tayau ki rubuta ki ajiye yabar Aysha har abada, nima bana kaunar Aisha kwatan
kwacin yadda kike kin Aliyu.

Cikin fara'a Umma tace Alhamdulillah, nayi farin ciki dakin Aisha da kikeyi.

Haka suka dawo gida kowa zuciya babu dadi, suna shiga gida Ummi dakin Aliyu ta nufa,
akwatin sa babba ta dauko ta shiga hada kayansa Innawo na tayata, shigowa yayi ya yana
kallon su, Ummi ce tace duk wani abuka dakasan yana da mahimmanci ka tattarashi domin
komai dare yau zakabar kasar nan.
Ina zani Ummi???

Gurin mahaifin ka zaka koma bazan iya ba.

Ummi karki min haka"

Karka sake min mgn Aliyu wannan tafiyar taka babu fashi.

Runtse ido yayi yayin da hawaye sukai saurin sakkowa kan fuskar sa......

*Yanzun ne zamu shiga cikin LAMARIN*



*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️



episode 20-21


Innawo da Ummi basubi takan Aliyu ba haka saida suka gama tattara masa kayan sa tsaf,
Mayan akwati biyu suka masa sannan Ummi ta kallesa kazo ka duba idan akwai wani abu me
mahimmanci naka.

Ficewa Sukayi, yayin da Aliyu yabi bayan su da kallo, share fuskarsa yayi sannan yabi
bayan su.

Afalo ya samesu harda Alhaji Umar ahankali ya Isa gurin kafar Ummin sa ya zauna, Ummi
dan girman Allah kiyi hakuri, Ummi ki yafe min badan halina ba, wlh Ummi zan shiga cikin wani
yanayi.

Cikin daga murya tace, Kai Aliyu?

Na'am Ummi na.

Wlh wlh babu wata kalma dazakai amfani da ita da zaisa najenyi gudurina, matsawar kana
son kwanciyar hankalina katashi ka tattara ka wuce tukan dare ya maka. Magiya bazata
amfanar dakai komai ba.

Juyawa yayi ya kalli Alhaji Umar, saidai tukan ya bude baki aljaji Umar din yace' " kayi sauri
Aliyu zanje na dawo yanzun na sauke ka atasha.

Zuwa yanzun kam ya fahimci bashi da mafita, dan haka ya koma dakin ya dauki duk wani
abo nasa me mahimmanci, daga karshe ya daga katifar sa, kudin da Aysha ke bashi ne suka
bayyana agurin ahankali yasa hannun sa ya kwasa sannan ya shiga shirya su cikin wata

karamar jaka yana zubawa wadda takardun sa ke ciki sannan ya goyata abayan shi ya zauna
bakin katifar tare da daura kansa kan kafar sa.

Aysha ce ta fado masa, ko Yaya zataji idan tasan baya nan?, wani hali Aysha zata shiga
idan ta waiga ta kula ayau Nabar garin nan batare Dana mata sallama ba, tana iya yin fushi
dani, zata shiga wani hali sosai, da wannan tunanin ya bude kofar nan wadda zata sadashi da
tsakar gida ya fice agidan.
Bekobi takan motarsa ba, gani yayi gaba daya yanayin garin ya canza masa, zuciyar sa
babu dadi komai na jikin sa zazzabi yake masa, bakin shagon idi ya Isa cikin sanyin jiki ya mika
masa hannu suka gaisa yayin da idi yace Allah ya kauta fah.

Ameen Aliyu ya amsa masa dashi sannan yace ai komai ya kare daga yau Nigeria zan
koma.

Sosai idi yaji faduwan gaba Nigeria gurin wa?

Ai mahaifina dan Nigeria ne.

Allah sarki, yanzun can zaka koma kwata kwata"

Eh kawai ya iya cewa.

Shiru idi yayi zuwa can yace Amman ko yariyar nan Indo zata shiga wani hali.

Shine nake tunani idi, gashi yanzun nan zan wuce gashi Kuma inason nai sallama da ita.

Shiru idi yayi tsayon lokaci sannan yace zo muje"

Ahankali suke takawa har suka Isa gidan idi yayin daya mishi shinfidan tabarma a tsakar
gida tare da fadin, Ina zuwa.

Idi na fita matarsa ta aje ruwa gaban Aliyu ahakali ya mika hannun sa ya dauka, kurba
yayi yayin da yaji wani dan sanyi cikin zuciyar sa.

Muyar Ayaha yaji tana sallama cikin sauri ya juya ya kalleta, itama kallon sa tayi yayin da
ta danyi murshi sosai tare da aje ledan hannunta kofar dakin tana fadin, mmn Ahmed ga
cefanan nan.

Amsa mata tayi daga daki sannan ta karasa kan tabar tana fadin, Yaya me kakeyi anan
gidan?

Kawar dakai yayi cikin dakiya irinta maza nazo miki sallama ne Aysha Ummina ta kore ni.

Kallo tabishi dashi yayin da hawaye ya shiga tsiraro mata layi bibbiyu, yanzun Ina zaka Yaya?

Nigeria.

Nigeria fa kace��

Eh Aysha, Ummi ta koreni, Yaya zanyi?

Yanzun tafiya zakayi ka barni?�

Yaya zanyi Aysha?, nasan wata rana zandawo kodan sabo da Ummi na.

Kanta ta hada da giuwa ta shiga raira kuka.

Ahankali yace Aysha?, kuka zaki min?, Bakison mu rabu lafiya ne?

Banason katafi ne ya Aliyu.

Nima ba'a son raina bane Ayaha, ni abun da nake so dake dan Allah ki nutsu kiyi karatun ki,
Allah ne ya hadamu ba mutum ba, Kuma shine ya kaddari rabuwa adaidai wannan lokacin.

Kuka Aysha take yi hawaye wani na korar wani, ahankali ya mika hannun sa yafara
share mata tare da fadin, Aysha kiyi hakuri idan kin tashi aure dazaran ansa miki rana ki rubuta
ki aiko min zanzo insha Allahu.

Dagowa tayi da sauri ta kalleshi, hawaye ta share sannan tace ta Yaya zan aiko maka da
Sako toh?

Dagowa yayi yasa hannun sa cikin jakar dake bayan sa ya ciro wata takardan ya mikawa
Aysha, " Idan kin samu me tafiya Kano Nigeria kirubuta sako sannan kibashi wanna takardan ya
duba, wannan shine adireshin gidan mahaifina.

Cikin sauri ta amsa takardan tare da kuresa da ido, yanzun tafiya zakayi?

Zan tafi Aysha, Hannu ta mika ta rike hannun sa daya dafa kanta dashi tace.

Yaya kabani wannan zoben kodan in diga tunawa dakai.

Angama Aysha, sai dai ai yayi miki yawa.

Ina so haka.

Daya hannun sa ya mika yana cire zoben dake dan karamin yatsan sa ya nufi hannun Aysha,
gwadawa yaitayi ko a babban yatsanta kinyi yayi dan haka ya mika mata tare da fadin ki adana,
mikewa yayi yana fadin sai mun sake haduwa kenan??

Hmmm, a ina zamu hadu Yaya, kace min kawai sai mun hadu a kiyama.����

Gabansa ne yaji ya fadi, juyar da kansa yayi can gefe ya cire kwallar idonsa sannan ya juyo
yace kisa azuciyarki Allah ne ke kaddara komai ba mutum ba, idan ko har hakane muna iya
sake haduwa, shinekenan Ayaha ni zan wuce Ina miki fata alheri.

Shiru Aysha tayi tana wasa da yatsunta yayin da hawayenta ke sauka kan sandar hannunta.

Ganin haka yace bakice komai ba?, nima kimin fatan alheri"

Cikin matsancin kuka tare da share majina tace toni me zance?�

Kawar dakansa yayi sannan ya juyo yace cewa zakiyi inai maka fatan alheri"

Cikin fashewa da kuka tace inai maka fatan alheri����

Fashewa tayi da kuka dan haka ya matso ya rungumeta akaron Fargo yana cire kwallar
gefen ido, tsayon lakaci tana kwance ajikin sa zuwa can ya dagata tare da fadin yi hakuri, cikin
sauri ya juya yabar gidan batare daya waiwayeta ba.

Harya Isa kofar gida yana jiyo ihon ta sosai hankalin sa take atashe runtse idonsa yayi
sannan yacigaba da tafiya.


Tuni aka gama zuba kayansa amotar Alhaji Umar duk suna titi jira suke suga ta Ina zai
billo.

Ganin sa yasa ahaji Umar ya zaga ya zauna amzaunin sa, yayin da

12 / 34