Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
mafita kawai nake nema, yanzun fa Kila gurinta
yaje, ko Ina suke haduwa ma oho
Innawo ce ta mike tana fadin, Ina zuwa barin leko shi.
******
Ya akayi kika fito daga gidan?
Duk bacci suke.
Lumshe ido yayi tare da fadin, ban zaci zaki fitoba ai, kawai fitowa nayi in kalli kofar gidan ko
in koma in kwanta .
Dariya Aisha tayi irin Wanda kesa Aliyu nishadi cikin ransa sannan tace, " Yaya ka kalli kofar
gidan fa kace?
Eh Mana, da babu ai gara ba dadi ko? Yanzun bani lbrn makarantar Yaya karatun kwana
biyu.
Yau banje makarantar ba gidan kitso naje har sai yamma nadawo.
Shine baki aiko aka kirani ba?
Banga motar ka ba ai"
Ban dawo ba kenan lokacin, kice yau kitso kikasha?
Eh cewa nayi amin irin wadda namaka ranar nan.
Cikin sauri ya shafa kansa tare da fadin, aini babu wani kitso akaina kindai har batsamin
gashi kawai.
Wlh na maka kitso ranar. Matsawa tayi daf dashi tana daka tsalle domin ta samu ta taba
kansa tace daya yabi tanan dayan Kuma tacen yabi.
Dariya yayi sannan yace ni banga komai ba akwai dai alamun an cuccure min gashi.
Toh sai in warewa yayi daman kanka ya cika santsi
Kedai kice baki iya ba kawai.
Yaya kasan me?
Sai kin fada.
Gashin kanka fari ne shima.
Fari Kuma Aysha??
Eh sabo da farin shima da kadan fuskarka tafishi haske.
Dariya ne ya kamasa yana me kallon fuskanta tare da yanayin girmanta so da yawa idan
tayi wani abun mamaki take bashi, tunda tai mgn ta koma can gefe tana rufe bakinta.
Shikowa Aliyu murmushi yake tare da fadin kizo nan ni ba abun da zan miki, d'anawa kika yi.
Motar da Aysha ta hango ta faka kofar gidan su yasa Aysha ta saurin waigawa.
Umma ta iya shaidawa tare da wan mahaifiyarta sai wasu maza guda biyu, cikin tsananin
firgici da tashin hankali ta koma bayan Aliyu tana fadin nashiga Uku yaushe Umma ta fita?
Aliyu kuwa hannunsa duk biyun ya zuba cikin aljihun tare da tsayawa tsaye babu alamar
fargaba cikin fuskarsa.
Gadan gadan suka nifo garin yayin da Umma ke fadin, " gashi nan katon ballagagge yana
neman hurewa yariya kunne domin ta bujirewa mgnr iyayenta.
Shikuwa yayan Mama fadi yake ku tafi dashi, Ina Aishan?
Police ne guda biyu suka rike Aliyu yayin da Aysha tai saurin ta rike rigar Aliyun ta baya tare
da share hawayenta jikin sa.
Duk yadda suke jansa yaki jawuwa fadi yake ku sakeni intafi da kafata.
Baza asake kaba, kuja shi Dan iska ne mara mutunci, me kokarin raba yara da iyayen su
muje can ofishin su amana iyaka dakai
Cikin sauri Aliyu ya fixge kadarsa daga hannun Dan sandan dake rike dashi yafara takowa
gaban Umma yana fadin, adai rika Jin tsoron Allah, Kuma na tabbata rana tana nan zuwa.
Cikin kufula Umma tace haka kaima taka ranar tana nan zuwa, kada ka jinkirta tuba wai
dankai saurayi ne, ah'ah, dan amakabarta babu inda aka rubuta tsofi kadai.
Tafe yake Aysha na rike dashi har yanzu yayin da Aliyu ke sake fadin, inda kika nufa
kenan ke?, to kisa azuciyar ki jiya ta wuce bazata taba dawowa ba.
Oho maka Mara mutunci, kokarin tura Aliyu suke yayin da adaidai wannan lokacin Innawo
ta karaso cikin rasa abun yi tasa koka tare da fadin, kagani ko, fadi yake Innawo ki koma gida.
Sosai gurin ya ciga duk da cewa darene, wani abun da ya daurewa mutane Kai gadai Aliyu
acikin motar police Amman Aysha taki sakin rikarsa duk da irin dukan da Innawo ke dirka mata"
Jawota ake tana sake komawa cikin matsancin kuka yayin da kukan nata ke Kara jawo
hankulan mutane.
Mamaki jama'ar gurin suka fara yayin da wasu ke dariya wasu ko cewa suke wannan lamari.
Ko na lafiya ne?
Ganin an dauke lokaci bacin rai yasa mahaifiyar Aysha Mama cewa itama atafi da ita aci
ubanta, tunda bata da mutunci.
Da yawan mutane agurin wannan shawaran suka bada yayin da wasu ke fadin gara atafi
dasu a horasu a samu saukin abun, dan haka aka barta Tashaga motar,
yayin da aka wuce dasu gaba daya.
Duk abun da ake Ummi taji, bacin rai ya sata fadin, aje dashi duk abun da za'a mishi
amishi tunda shine ya sayawa kanshi.
Innawo kuwa hawaye yaki tsaya cikin idonta ita kadai tasan me take ji.
Hakama ma mahaifiyar Aysha tsananin bakin ciki yasa take addu'ar Allah yasa suma
Aysha dukan dasai ta kasa tashi ta hakane kawai za'a samu saukin abun........
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
episode 17-19
Wannan daren duk gidaje biyun basu runtsaba, innwo ko addu'a taitayi cikin wannan daren
Allah ya daidaita wannan lamarin.
Itako Ummi tsabar haushin Aliyu ne cikin ranta, fushi tayi dashi me tsanani irin wadda ta
jima batai ba dan kaha ta dauna kawai tare da zubawa waje daya ido.
Hakama gidan su Aisha Umma Banda juyi ba abun da take, yayin da mama ke share
hawayen takaici"
Umma ce ta tashi zaune tana fadin, wai kuka kike ne?, nikaina banso ace har Aisha aka tafi
ba, amman ki duba yadda akejan Aysha tana tana Kara rike yaron, ni babban abun dake daga
min hankali yaushe har sukayi sabo da yaron nan har haka, duk taka tantandin da mukeyi da
yariyar nan Amman bata gani
Hmmmm, Umma inajin takaici sosai, amman gara azane Aysha ta yadda ko kofar gidan su
yaron bazata sake kallo ba, inason amata dukan dasai ta kasa gane yaron, amata dukan dasai
tayi wata da wattanni zana iya taka kamarta, tunda ita tace bata da mutunci muzuba"
Cike da karfin guiwa Umma tace, da ammata haka zamu samu sauki insha Allahu. Shima
Mara kunyan yaron idan jikinsa ya gaya masa ya fita hanyar yariyar.
******
Washegari Innawo taso suje domin duba halin da Aliyu ya kwana ciki amman Ummi tace
kartaje, sannan ta hana agayawa kowa daga cikin 'yan uwanta, acewarta abarshi can saboda
idan yaji wuya ya kiyaye gaba, badan ran innawo yaso ba take hakuri domin kuwa itama tana
son Aliyu ya fita hanyar Aisha.
Har aka kwashe tsayon kwana uku babu wadda yaje gurin Aliyu, da yammacin ranar da
suka cika kwana uku ne Innawo tace, Fatima horon nan ya Isa haka, yakamata aduba yaron
nan fah.
Innawo abarshi dan Allah.
A'a Sam bazai yiwu ba, Kuma kema nasan karfin hali kikeyi azuciyar ki kinajin zafin abun.
Innawo kina kallon dajin yadda naita masa mgn aranar Kuma yacigaba da abun da yaga
dama.
Fatima hannun ka baya rufewa ka yanke ka yar.
Toh Innawo ita Aisha da suka bari acen fa, macece itafa ba namiji ba, amman tunda sunga
abun nasu bana lafiya bane sai suka barta acen ai kaza tana taka danta badan bataso bane.
A'a, ai ita Aysha tun washegari akace sun tafi su dawo da ita.
Innawo ai tabawa tace min basu dawo da itaba har yau tana can itama.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un to wanna wacce irin masifa ce, cikin sauri Innawo ta
saki aikin da take tana fadin banga ta zama ba kuwa, wlh duk daukata sun karbo yariyar nan
Mayafi Innawo ta dauka ta nufi gidan Umma, cike ta samu gidan duk iyalan Umma sun
hallara, Koda sukaga Innawo ce daker suke amsa mata gaisuwar da take masu, kin kallon duk
wani daure daure da suke mata tayi tare da fadin, ashe Aisha har yanzun tana can, wlh ji nake
tun washegari kun dawo da ita, shiko dama Aliyu mahaifiyarsa tayi fushi tace abarshi can tunda
bayyajin mgn.
Daya daga cikin kannin Mama ce tace, tana can, ai yariga ya gama hure mata kunne,
yariya yar karama an canza mata tunani gaba daya ta zama wata iri.
Muryar wata can taji tana fadin, waya Sani ma ko tofi yaimata aruwa tasha, yariya kamar
Aysha ace ta guji danginta sai wani katon banza baki mummuna dashi me BAKAR zuciya.
Ummace tace ai wlh inaga mgnr nan saitaje kofar sarki, dan idan yana ganin ya iya
sammako toni atafe nakwana.
Insha Allahu mgnr bazata kaimu kofar sarki ba, yanzun zanje in sabo kawun nan shi gobe
muje can akashe mgn,, da yadda Allah Aliyu yabar Aisha, kuyi hakuri mu masu laifine, haka
Innawo taita basu hakuri sannan ta baro gidan bayan sun amince gobe zasu hadu a police
station.
******
Misalin 10:00am duk gidajen guda biyu sun hallara, bayan tattaunawa da mazan sukayi tare da
police din aka yanke shawaran zane su gaba daya.
Fito dasu akayi yayin da Innawo naganin Aliyu ta fara hawaye, shike dauke idonsa yake,
haka yaki yadda ya hada ido da kowa cikin dangin mahaifiyarsa duk iya kokarin su na su hada
ido dashi yaki barin hakan ta faru.
Itako Aysha lokacin da aka fito da ita share hawaye take, yayin da duk ta fada tai zuru zuru
da ita.
Yan uwan mahaifiyarta kuwa zaginta suka fara tun daga nesa suke fadin, duba idon
shigeya wannan yariyar kuwa jinin mu ce?
Dayar ce tace kika Sani ko jinin ubanta yafi yawa ajikinta?
Da alama kuwa wlh natsana yariyar nan, iri irin wannan mgnr sukaita yi, yayin da police din
suka shiga daure hannun Aysha da kafarta kamar yadda suka gama daure na Sadiq.
Mutum biyu ne akansu kowanne da zafgegiyar bulala a hannun sa kusan atare aka fara
zuba masu bulalar yayin da tun ana farko Aysha ta fara ihu, shikuwa Sadiq runtse idonsa kawai
yake tare da cije leben sa.
Kafarsu da hannun su kawai ake duka, saboda azaba tumi Aysha ta fara burgima tana fadin
tabari ayafe mata bazata Kara ba, daga bisani ta shiga Kiran Yan, uwana mahaifiyarta saita
suka tabbatar da tayi lilis suka barta.
Aliyu kuwa tuni kafarsa da hannun sa suka kunbura sai dai har yanzun bece kala ba har
aka gama aka barshi.
Tuni su Umma suka wuce da Aysha dan haka bayan ankama na Aliyu su Alhaji Umar
suka kamoshi.
Koda suka shiga cikin motar bece kalama illa kansa daya hada ga guiwa duk
yadda su Alhaji Umar ke kara fadan duk wani abu da zai nisantashi da yariyar, har suka iso gida
fada ake Kara masa sai dai har wannan lokacin bece komai ba Kuma be kalli kowa ba.
Duk da cewa kafarsa tayi tsame be kulataba su nafara fita shima ya fita abun sa,
Innawo agaba yayin da su Alhaji Umar ke bayanta Aliyu akarshe suka shigo gidan alokacin da
Ummi ke alwalan la'asar.
Da kallo Ummi tabishi har ya karaso saitin ta, kallon sa tayi sama da kasa, kafarsa
kunbure take sutum hakama hannunsa duk biyun, akan fuskarta ta sauke idonta, idonsa jawur
tagani.
Sai wannan lokacin Aliyu ya dago ya kalli fuskar Ummin sa tare da fadin, sannu Ummi.
Kasa kasa yai mgnr dan haka ta tabe baki tare da dauke idonta daga gareshi tana fadin, ka
nemi Ummi tun wuri.
Duk juyowa sukayi suna mata nasiha nan suka Kara yiwa Aliyu fada tare da Kara jadda
masa ya rabo da yariyar nan, daga karshe Kuma suka bashi umarnin yabawa Ummin sa hakuri.
****
Kwana biyu yayi agida yana fama da zazzabi kafarsa kuwa daker yake iya takata, haka ma
hannun sa.
Cikin wannan kwana bitun Ummi sama sama take amsa gaisuwar sa, Innawo ce kadi ke
matsa masa yaci abinci amman baya iya yin hakan.
Ranar kwana na ukun ne ya farajin dadin jikin sa, har ya shirya zuwa makaranta, fitowa
yayi yaiwa Ummi sallama daker ta amsa sannan yaje har kofar Innawo yana mata sallama.
Adawo lafiya me gidan, kadai karya ko?
Zan karya idan nafita Innawo.
Toh adawo lafiya Allah ya bata sa'a.
Kofar gidan ya fito, tsaye yayi yana kallon gidan su Aysha yana tuna sanda ta rike
rigarsa tana me nuna batason a tafidashi cikin matsancin kuka, duk yadda yaso daya banbare
hannunta Kara rikeshi take, wani irin yanayi ya shiga game da Aysha cikin zuciyarsa wadda
yake tunanin ada babu shi, bagar yayi daga dogon tunanin da ya tafi sannan ya kama hanya
cikin tsabar tunanin Aysha.
*****
Tunda suka dawo da Aysha bataiwa kowa mgn ciki harda mahaifiyarta, koda yaushe fuskarta
cikin fushi take, bakomai ke sata wannan bacin ranba sai irin zagin da kannai mahaifiyarta tare
da yayyen mahaifiyar tata sukaita mata, ta yadda suka fadin wannan halin nata saidai idan can
dangin ubanta ta kwaso su ba a dangin su ba, babvan abun da yafi bata haushi mama ma biye
masu take babu wani ko mutum daya dake bayanta koya tausasa harshen sa akan kalamin da
suke gaya mata, kwana biyar ta kwashe kwance sannan ta nufi makaranta.
Misalin karfe 2 Aysha ta fito daga makaranta, abin hawa take nema ta hangi mutun daga
nesa kamar Aliyu yana kiranta, azabure ta fara takawa harta Isa gare shi, murmushi ne ya
bayyana akan fuskarta haka shima Aliyu.
Karasowa tayi ta tsaya tana wasa da hannunta yayin data kasa kallon sa.
Ahankali yace, " Aysha ya jikin ki"
Ni lafiyata