Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
ma tayi mgn ya gagareta shige barbadadiya.
Ai maman Sadam kuita dukanta har sai ta sumai.
Weadda Mama takira da maman Sadam ce tace, " me cikin ?, Idan jini ya balle mata fah"
Ummace tace duk abun da zai faru ya faru, ni wlh ko mutuwa Aysha tayi yanzun bani da
asara.
Hada baki sukayi wajen fadin, wlh da haihuwar Aysha gara barin ta.
Tafarfasa kawai zuciyar Aysha kiyi, kuka ya bushe cikin idonta, haka gidan Umma ya
zama kamar gidan makoki wasuma acikin su kwana suke, babu irin tambaya da ba'a ma Aysha
ba taki fada, duka kuwa da Zaki marasu dadi babu irin wadda bata Shashi ba, har takai gaba
daya masa mgn da ita bare ma har akara mata tambaya kowa tirrr da halinta kawai yake, dan
haka arakube take acikin gidan, babban wan Mama ma cewa yayi ahada mata kayanta taje duk
inda zataje, mama ma haka tace, ta tafi gurin wadda yai mata cikin ita ko ganinta bata son yi.
Sosai Aysha ta cansa nan danan ta fita cikin hayyacinta, wuya take shan ba kadan ba
Koda yaushe yawo cike fal da bakinta, ga yawjun sun abubuwa saidai babu me bata haka take
hakuri har aka dauki tsayon sati biyar.
Har wannan lokacin babu mema Aysha mgn acikin gidan, abincima saidai ta faki idon Umma
ta diba, Mama ko ko kallon inda take batayi, dan haka duk ta rame ta lalace, zuro zuro tayi har
yanzun laulayi bebarta ba kamar ma karuwa yake.
Yauma Ayaha ce kwance adakin mama, wadda tun ranar da Akasan tana da ciki takoma
kwana cikin sa, Mama dakin Umma ta koma domin tace ita ko son ganin Aysha batai.
Sati Uku kenan Aliyu ya Kara akan lokacin da yace zaizo, amman har yanzun babu
alamarsa, tun ranar da yacika wata uku kamar yadda yace yake saka ran ganin sa, kullum zura
ido take ganin har andau sati Uku bayan ranar da yace yasa hankalin ta duk ya tashi, kuka taci
sosai, yanzun kam tacire rai da zuwansa, harma ta fara ganin rashin hankalin ta data debi kafa
tabishi can, ahankali tace gashi yanzun ya barni da ciki Kuma yaki zuwa kamar yadda ya min
alkawari.
Sosai taji ta shiga jin haushin Aliyu me tsanani, gashi cikin sosai yake wahalar da ita,
kasa kasa take fadin, shikenan zan haifi shege wadda zai dawwama babu Uba domin yanzun
Aliyu yana ma iya cewa banashi bane tunda kowa yasan baya kasar nan, wayyo ni Allah
nashiga uku
Kuka tayi sosai duk idonta ya kod'e bakinta ya bushe.
Ita kadai azaune a tsakar gida ji tayi tana son ta sha kukar fulani, dan haka ta mike tasa
hijjabi ta fita, hanyar gidan su Aliyu ta nufa tun kafin ta karaso take bin gidan da ido, sosai taji ta
tsana ko ganin gidan dan haka tai saurin dauke kanta, har ta sawo ta dawo bata sake kallon
gidan ba .
********"
Ina kikaje?
Wani irin faduwa gaban Aysha taji tunda taji muryan Umma, Dan ta dade bataji ta mata mgn
ba.
Ledan Hannunta ta nunawa Umma cikin sunkuyar dakai tace wannan na sawo.
Umma taji tana fadin, " Bilkisu yariyar nan fah batasan zuru ba, idan mukayi wasa saidai
muji inya, lokaci yayi daya dace ubanta ya sani, lallai kije ki same ubanta asan abun yi.
Mama batace komai ba har Aysha ta shige daki.
Misalin biyar na yamma taji Muryan Daddy ta acikin gidan dan haka jikinta duk ya kama
rawa domin tunda tasan Daddyn ta bata taba ganin bacin ransa ba dan haka ma yanzun duk
jikinta ya dau rawa.
Ke! Aisha fito ga Baban ki?
Fitowa tayi tana sanye da hijjabi Daddy na hango Aysha ya yamutsa fuska yana fadin"
Lafiya?
Umma ce tace matso nan ki zauna ki gaya masa.
Kallo Daddy yake kare mata sama da kasa duk ta rame ta d'ashe idonta duk sun zurma
yace Aysha menene ya same ki??
Wasa Aysha ta fara da yatsunta yayin da wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.
Juyawa yayi ya kalli Umma yace Meya sameta?
Ciki tayi.
Cikin sauri ya runtse ido, sannan ya juya ya kalli Aysha yana fadin, " cikin haihuwa ?
Kuma anyi anyi ta fada wadda yai mata ta ki, duka ba irin Wanda bata sha ba amman
takk mgn, amman taki mgn.
Daddy ne ya sake cema Aysha, Aysha waye yai miki ciki?
Har yanxun bata dago ba kuma batar wasa da yatsun ba hawayenta kawai yake gani
yana diga, dan hska ya mike yaje gabanta cikin tsananin baccin rai ya watsa mata mari.
Sosai zafin ya rudata tana jinshi acikin kanta taji Daddy ya sake cewa, "
Bazaki bude bakimin mgn ba?
Durkushewa tayi cikin matsanancin kuka take cewa, Daddy kayi hakuri, wallahi Nima bansan
kowaye ba, dan Allah kuyi hakuri ku yafe min.
Wani irin kuka take me shiga rai dan haka Daddy ya Isa gabanta ya dagata, kirjinsa ya sata
rungumeta yayin data tsananta kukan ta, ahankali Daddy ke share hawaye yayin da take dafa
bayanta cikin sigar lallashi, sosai ya rungumeta zuwa can ya dago ya sunbaceta sannan ya rike
hannunta ya kalli Umma yana fadin, " Umma bari muje muyi mgn nida ita kawai.
Toh kaje, ka tirketa ta fada maka idan ba hakaba kuwa ni bame haifar min d'ana shege
agida....
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 43- 45
Rike da hannun Aysha suka fito, cikin motar yasata, suka bar unguwan, wani asibiti yakaita
bayan an tabbatar masa da Aysha tana dauke da cikin daya kusa cika wata 4.
Baro Asibintin yayi cike da tashin hankali daker ya Isa saita kansa ya juyo ya kalli Aysha
dake matsanan cin kuka yace' " ba kuka zakiyi ba Aysha, bude baki zakiyi ki gaya min wadda
yai miki, ba zancen rigima bane ko tashin hankali, abun bukata kawai yasan da cikin, Kuma ya
amince cikin nashi ne, matsala anriga an sameta, kuskure Kuma an riga anyi, waye ne Uban
cikin?
Daddy kayi hakuri dan Allah, wlh basani ba.
Baki sani ba?, Kina nufin baki san waye yai miki cikin ba?
Kaita daga ahankali.
Shiru Daddy yayi tare da tsurawa guri daya ido tsayon lokaci sannan yace, " shikenan, idan
cutarki akayi Allah ya saka miki,ya Kuma kawo miki mafita, idan Kuma kece nan kika Kai kanki,
toh sai nace miki ki nemi sunan da Zaki Kira 'yarki ko danki, sannan ki neme amsar da Zaki
bawa abin da kika haifa aduk ranar daya tambaye ki ubanshi, inason ki sani, idan baki yi mgn
yanzun ba bayan kin haihu babu wani mataki dazan iya dauka, baza 'a zubar da cikin nan ba
kamar yadda Kakarki ta bukata dole saikin haifi shi.
Kuka Aysha keyi sosai, bayan sunyi tafiya me tsayo ya tsaya yai mata sayayya sannan suka
kama hanyar.
Zuwa can yacigaba da cewa, " naso ki zama kamar mamar ki, maman ki yariya ce me
nutsuwa, akanta nafara sha'awan musulunci, Kuma har yanzun itace ta gujeni bani ne na gujeta
ba, ke ko yanzun waye zaiso dansa ya aureki, har dai yaji abun da kika aikata?, Kin bata
wayaun ki, mutanen unguwar ku, zasu dinga yin tirrrr dake, shiru yayi tsayon lokaci sannan ya
sake cewa, kina sa hijjab kina Sallah, kince amiki aure ne ba'a miki ba?
Gargiza Kai tayi idonta cike da hawaye.
Koko akwai wannda kike so ne ban sani ba?
Nan ma hawaye ne suke zobo mata tasa hannun ta share tare da girgiza kai.
Daddy ne ya sake fadin, Ina tsananin son ki Aysha, amman ga abun da kika min, duk cikin
'ya'yana nafi son ki, Ina alfahari dake Amman kinje kinyi abun da mutane zasu min dariya
dangina sun dade suna min korafin nabarki kina Islam, kinci amanata bantaba zaton haka daga
gareki ba.
Daddy kayi hakuri dan girman Allah ka yafe min.
Ya zanyi dake, Allah ya rabaki da cikin lafiya ya Kuma kawo miki mafita.
Daidai wannan lokacin suka Isa kofar gidan, Aysha agaba, Daddy ta nabinta abaya
suka shiga gidan, dakinta ta nufa yayin da Daddy ya nufi dakin Umma.
*******
Batasan Kona waye ba???, Aysha fa da kake ganinta munafukar yariya ce, munafunci ne cike
da cikinta, nafi ganin a tutsuyeta ta fada, idan ba'ayiwa tufkar hanci ba ko, anrabata da wannan
tana iya kwason wani, ba fata nake mata ba, Amman wlh idan ba wani ikon Allah ba zata jima
bata auro ba.
Umma wannan yana daya daga cikin dalilin dayasa nace abarta da cikin, idan aka cire
cikin kamar an bude mata hanya ne, idan ko aka barta dashi shine zata fahimci illar abun,
annan zata gane inda matsalar take, dan haka nake son kuyi hakuri mu rungume wannan
kaddaran.
Cikin sauri Mama dake kan gado tace, " aikuwa saidai ka wuce da ita, baza'a haifi wannan
kazantar anan gidan ba.
Kashhh, Daddy ya fada, kuyi hakuri Aysha tacigaba da zama anan, jama'ar unguwar ku sun
riga sunsa ni, tafiya da ita kamar Kara baza zancen ne, dangine sun dade suna korafin nabarta
tana musulunci yanxun suna Jin wannan lamarin dariya zasuyi, nafi ganin muyi hakuri kawai.
Duk ta yadda Umma ta fillo Daddy toshewa yake, har dai suka yadda sannan yai
masu sallama tare da jadda masu zai ringa zuwa akai akai.
******
Ai kullum Kara godewa Allah nake da ya daddara Aliyu baya kasanan, da yanzun an jingina
mana shege.
Hmmmm, aini nayi farin ciki nagodewa Allah, Kinga yayi zamansa shima yanzun ya samu
abun da ransa ke so, sai dai fah yaci ace zuwa yanzun ya waiwaye mu.
Bazai zo ba, ai kin sanshi da bakin rai, yana can yana fushine ne, yasha zamanshi idan zai
yi aure naje ni.
Dariya Innawo tayi, aifa yai zaman sa fitina bata da dadi, duk da dai yanxun kam ya
girma nasan yayi hankali.
******
Tundaga ranar da Daddy yazo su Umma suka Dan rage zafin su akanta, ayanzun suna bata
abinci, saidai ko taci ko kartaci babu abun da ya dame su, sannan yawancin abincin nasu bashi
take so ba, tsananin damuwar da take ciki be barin ta taci abincin, haka har cikin ya shiga wata
na biyar, har wannan lokacin acikin 'yan uwan mamanta aunty Murja ce kawai take mata mgn,
kowa harara ne da zagi tsakanin su.
Sosai rashin zuwan Aliyu har wannan lokacin yake dagula mata lissafi, ashe bazai zoba,
amman yace min in bashi wata uku, gashi har yanzun shiru, besan da ciki ba, nasan ko yanzun
yazo bazai karba ba, dan haka babu amfanin Kiran sunan shi, shekaran sa biyar baya kasar
nan yana cewa karya nake shikenan ta zauna, kowa cewa zaiyi sharri zan masa tun da narasa
uban cikina, kuka ta kwana tanayi wadda yai dadlili Kafin safiya ta tashi da matsanancin ciwon
mara me tsanani.
Ganin tun safe Aysha bata leko ba Mama ta faki idon Umma ta shiga dakin.
Yau Yaya dai?
Mama cikina ne ke ciwo.
Allah ya sauka ta fada sannan ta fice, ganin har anyi azahar Aysha bata fito ba yasa Mama
ta koma dakin.
Kudi mama ta mika mata amshi kije asibiti.
Daker Aysha ta iya mikewa tana tunanin ta Ina zata fara zuwa asibiti ita daya.
Tana fitowa layin aka fara binta da kallo rabon data fito ta manta, dan haka taji sai hardewa
takeyi, daker ta karasa gidan.
Da fada aunty Murja ta rufeta dashi, meyasa tazo mata gidanta, acewarta bata son mijinta ya
sani.
Irin wannan abubun sunyiwa Aysha yawa Dan haka saita yi da gaske hawaye ke zuwar
mata.
Meya kawo ki?, taji muryan aunty Murja bayan ta gama fadan.
Cikinna ke cewa shine na fito inje asibiti.
Ba dole cikin ki yai ciwo ba, kina sane sarai, cikin ki ya girma, ko bakici abinci Dan kanki ba
dole kice sabo da abun dake cikin, yunwace kawai take damun cikin.
Cikin sauri Aysha tasa hannunta ta dafa cikin, jinsa tayi ya cure guri daya, sai yanzun ta
tabbatar eh lallai me raine acikin ta.
Kunun gyada Murja ta damawa Aysha tashashi da lumishi, yayin da tana gamawa bacci ya
dauketa.
Bayan ta tashi ruwan wanka Murja ta bata tai wanka sannan ta kamo hanyar gida tana
mejim dadin jikinta ba kama sanda ta fito ba.
********
Sannun ahankali kwanakin suke juyawa zuwa watanni, ayanzun cikin Aysha ya cika wata 9,
wani irin girma yayi naban mamaki, tuni tabar saka kayanta domin duk sun mata kadan, Kuma
har cikin ya tsufa nan wuya kawai take sha, bama kamar daya girman nan yafi bata wahala,
zama daker tashi dake babu wani me taimakonta, komai ita takewa kanta har wannan lokacin
da ta tabbatarwa kanta cikinta ya kusa fita.
Babban abun da yafi kona mata rai shine watanta tara da dawowa Nigeria amman har yau
wata ukun Aliyu basu cika ba, wani irin zafi sa takeji fiye da misali, sosai ranta yakebaci data
tunashi domin kuwa yanxun ta tabbatar ya yaudareta, cikin matsanancin kuka ta shiga rokon
Allah ya dauki ranta wajen haihuwar ita da cikin baki daya, saidai tana addu'ar tanajin yadda
dan cikin nata ke zillo kamar zai barka cikin.
Cikin matsancin kukan da sai zuwa yanzun hawaye ya fara zubo mata tace, "ya rabbi na
rokokeka, ko a lahira karka hadani da Aliyu, Allah kasa nagama ganin shi kenan har rayuta ta
kare, Allah ka hanini ganin duk wani abun daya shafe shi barema shi da kansa. Mugu kawai
azzalumi wadda besan girman alkawari ba, yasan ya cuceni shiyasa bazaizo ba.
Cikin matsancin kuka take Kiran sunan Allah tare da addu'ar ya dauke ranta ita da dan
cikin nata.