Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   27 / 34

78K to 81K   out of 101.2K words

Shikuwa Aliyu tsaye yake akanta yake fadin, " malama ki bude fuskarki, ke kike karawa
kanki damuwa da kanki, kece ma zaki jawo mutane su kalleki, da an ganki anga mara gaskiya,
dan Allah ki nutsu sosai karkije kimin shirme, inba kinsan bazaki iya mgn ba kiyi shiru kawai.

Batare data bude idontaba tace, " ai dole kace nayi shiru tunda kanson ka barni da yaron.

Kawar da kansa yayi sannan ya juyo ya kalleta tana kudundune da fuska yace, " eh zan barki
da yaron ne amman ai nine ubanshi.

Shikenan naji bakomai jeka.

Bazan tafiba saikin tashi kin goya yaron nan, kina rufe fuka saikin je kin yadda shi?

Wlh bazan goya shi ba, Kai ka amsa ka goya mana.

Kawar da kansa yayi tare da cizon lebensa yace, " badan wani dalili guda daya ba Dana baki
mamaki"

Kuka Aysha tafara harda shasheka adaidai lokacin da aka fara shiga cikin kotu, cikin sauri
ya bi ta bayanta tare dasa hannun sa akanta yaja hijjabin baya fuskarta ta bayyana sannan ya
wuce ya shiga cikin kotun......

*️ BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

Episode 50- 51




Ahankali akai ta shigowa har aka cika kotun makil da jama'a.


Bayan kowa ya nutsu kotun yayi tsinta yayin da aka shiga kiran kararrakin.

Shari'a biyar akayi sannan aka karanto Karan su Aliyu.

Sosai gaban Innawo Dana Ummi ya buga Jin yadda aka fadi karan.

Hajiya Umma ke Karan Aliyu Moh'd Bello akan cewa yayiwa jikarta ciki ya Kuma ki amsan
d'an.

Kotu ce ta bukaci ganin Aliyu Muh'd agaban ta.

Wani irin mikewa yayi cike da kwarin guiwa ya kamo hanya yana me cire gilashin idonsa ya
maida cikin aljihu sannan ya Isa inda ya dace ya tsaya ya tsaya.

Bayan Aliyu ya tsaya agaban kotu sannan aka bukaci ganin Umma, sosai mutane suke
mamakin Aliyu domin daka ganin shi babu alamar lalacewa ko rashin gaskiya a tattare dashi,
daka ganshi kaga cikakken mutum me mutunci, dan haka dayawan mutane suka shiga mamaki,
gashi ance yayima yariya ciki yakuma ki amsan d'an, gashi Kuma cike da kwarin guiwa.
Fitowa Umma, tayi ta tsaya, yayin da aka bukaci ta maimaita abun da take karansa akai.

Tama kallon Aliyu da nuna kwarewa asurutu Umma tace, "toh wannan yaro dai gashi Aliyu
ya azabtar Dani arayuwuta, wato tun Ayaha na kankanuwarta ya fara lalatata, tare da hure mata
kunne ta guje mu, nayi, nayi, ba yadda banyi ba akan ya rabommun da jika, bayan na dauki duk
matakin dazan iya dauka yaki bari, gurin 'yan sanda ne, kofar sarki, har kotu munje daga karshe

uwarsa ta dauke shi nan ta maidashi Nigeria, shekara biyar kenan da tafiyarsa, duk na saki jiki
bekasar Ashe, Ashe yana lallabowa yana amfani da ita, kawai sai ganin ta mukayi da ciki, dan
haka nake rokon kotu data bima jikata Aysha hakkin ta na rayuwarta daya lalata mata.

Da yawan mutane kallon su suka mayar kan Aliyu har yanzun yana tsaye idonsa akan
Umma sosai yake Jin haushin Umma cikin ransa.

Alkalin ne yace akwai Aysha acikin kotu??

Eh, ranka ya dade, juyawa Umma tayi tana nuna Aysha, yayin da Aysha ta mike, Aunty
Murja ce ta amsa yaron, sannan ta fito cikin sunkuyar dakai har ta Isa gaban kotun bata iya
dago fuskanta ba.

Alkalin ne ya kalli ta ya cire gilashin idon sa cikin tare gida sosai alamar babu wasa ya
kalli Aliyu, gyaran murya yayi sannan yace, malam Aliyu kaji abun da Hajiya Umma take zargin
ka dasu?, Hane ko kuwa kana da abun da zakace?

Ina dashi ranka ya dade, duk abun da ta fada ba haka suke ba.

Uwarka ce take karya mara kunya, kana nufin ni makarya......

Tsawan da Alkalin ya buga mata ya sata Ummata tai saurin rufe bakinta batare data shirya,
ido ta zubawa Alkalin Jin irin tsawan da ya buga sannan yaci gaba da cewa karki sake yin mgn
batare da an bukaceta daga kareki ba, nan ba filin yaki bane.

Kar me karatu ya manta duk cikin harcen filatanci ne suke mgnr.

Maida hankalin yayi kan Aliyu tare da daukan alkalamin rubutun sa sannan yace Ina
sauraron Aliyu.

Awancen lokacin da Aysha take shigowa gidanmu karamar yariya ce da mata wuce
shekara 13 zuwa 14 ba, Kuma karatu ke kawuta, dalilin tana samun inawa kanwata karatu take
zuwa Ina masu tare, Kuma babu wata alaka da muke da ita nida Aysha bayan ta karatun, banta
nementa da wani abun na iskanci ba iyaka dai inmata karatu ta wuce gida, gata Kuma a
tambayeta, na taba nemanta da iskanci?

Kowa hankalin sa ya ya mayar kan Aysha dake hawaye yayin da taji an sake jeho mata irin
tambayan da Aliyu yayi, kanta ta girgiza tare da fadin a'a.

Rubutu Alkalin yayi sannan ya maida kallon shi ga Aliyu yace, " amaganganun da Hajiya
Umma tayi tafada cewa, tata nuna bata son kula jikarta da kake, wadda har tafada cewa anje
police station, anje Kofar sarki, harta Kara da cewa anjema kotu, meyasa baka rabu da yariyar
ba tunda ka fahimci danginta basa so Kuma Kai kafi Aysha hankali?

Ranka ya dade nashaku da ita sosai, Kuma haka nan Allah yasamin tausayinta acikin
Raina, a wacen lokacin idan bangantaba banajin dadi, duk da cewa babu wata alaka da muke
da ita bayaga karatu kawai.

Jinjina Kai Alkalin yayi sannan yace muje ga zargin Hajiya Umma na gama, munji
Umma tace bayan faruwar duk waddan abubuwan mahaifiyar ka ta turaka Nigeria da zama,
amman saika shigowa ciki Sirri, kana kwatsam sai tsintar Aysha sukayi da ciki.

Kawar dakai Aliyu yayi sannan yace, ranka ya dade ba haka bane, tunda mahaifiyarta ta
turani Nigeria shekara biyar kenan zan iya rantsuwa da alqur'ani me girma cewa banta dawowa
kasar nan ba sai wannan karon.

Sosai cikin Aysha ya luri ruwa, dama cikin hawaye take duk jikinta taji babu karfi, ji take
kamar ta zube akasa domin kafa fuwanta rawa suke.

Cike da mamaki Alkalin ya maida idonsa kan Aysha yana kallon inda take zubar da hawaye
yace, " Aysha Ina kika samu ciki?, Aliyu yace tun bayan tafiyan shi shekara biyar kenan be
dawo ba, ki saki jikin ki kiyi mgn, anan muna kokarin kwato miki hakkin ki ne"

Hawaye kawai Ayaha take zubarwa dataga ma idon mutane yayi cah akanta saita fara
shashshrkar kuka.

Sosai hankalin Aliyu ya tashi ganin inda take kuka, dan haka ya daga hannun sa alamar
yana da mgn.

Kallonsa Alkalin yayi tare da bashi dama.

Ranka ya dade bayan nakwashe tsayon waddan shekarun na fahimci inason Aysha, kullum
bani da tunani sai nata, har nafara kokarin inason indawo in nemi auren ta, saidai Ina tunanin
gidan su da gidan mu, akarshe na yanke shawaran dawowa, saidai yanayin aiki na bansamu
daman ba, kawai wata rana na dawo gidan mu na samu Aysha akofar gidan....
Wanni gidan??, Alkalin ya tambaya yayin da mutane suka Kara baza ido.

Gidan mahaifina a Kano Nigeria.

Cikin tsananin mamaki kowa ya Kara baza kunnen sa yayin da Umma tabi Aysha da kallon
cikin ranta take fadin kaji tsinan ne matsiyaci.

Itako Aysha kuka kawai take.

Taya Ayaha tasan gidan ku a Nigeria bayan kun rabo da Aysha tana da shekara 14 kamar

yadda kaima da bakinka ka fada?

Ranka ya dade akwai adireshin Dana bata na gidan mahaifina, Alokacin da zanyi tafiyar
nazo nai mata sallama, ganin tana kuka nai mata alkarin idan aurenta ya tashi ta rubuta ta aiko
min zanzo, dan haka na bata adireshin da zata aiko sakon, wadda dashi tayi amfani tazo gidan
mu.
Mamaki jama'a suka shiga yiyin da alkalin ajuya ya kalli Aysha yace, Aysha kinji abun da
Aliyu yace, " da gaske ne kinje Nigeria?

Kara kudundunewa Aysha tayi, sheshekar kukanta kawai take, yayin da Umma ta daga
hannunta.

Dama aka bata, Dan haka ta fito tace, " ranka ya dade, karya yake, ni jikata babu inda take
zuwa, daga makaranta tana gida bata tabayin kwana daya ma bata gida ba, dan haka babu
inda za'ayi Aysha ta tafi har Nigeria batare da sanin mu ba, Kuma Aliyu ya riga ya amsa mana
ba sau daya ba cewa dan nasa ne, yanzun Kuma yanata mgn Kashi Kashi, yace zai rantse be
taba zuwa ba, yanzun Kuma yace Aysha ce ta bishi.

Kallon Ayaha dake kuka Alkalin yayi sannan ya kalli Aliyu yace, "Malam Aliyu Ayaha
acikin rana daya taje Nigeria ta dawo?

A'a tayi kwanakin da suka Kai wata uku da kwana sha biyu, kuma ta gaya min cewa
gidan mahaifinta aka turata hutu.

Sosai jama'ar gurin suka zaro ido, ciki harda Umma da tai saurin kallon Daddy Aysha, yayin
da Aliyu yacigaba da cewa, " nayi kokarin nayi mata fada wancen lokacin sannan na kaita cikin
gidan mu wajen kannaina ta zauna, tafiya tsakanin Cameroon da Nigeria ba karamin tafiya
bace dan haka nafara neman ranar da zan iya kawota gida da kaina nakuma nemi aurenta,
sabo da Ina sonta, Kuma nasan itama soyayya ce ta kawota da rauni irin na mace, amman
yanayin aikina be bani dama ba, ganin lokaci nata tafiya gashi wata tafiya harna tsayon wata
Uku ta taso min na yanke shawaran sakata amota ta dawo gida, bayan na fito da ita daga gidan
mahaifina ne Kuma awannan ranar garin sallama tsautayi yasani na kusanceta, hawayen gefen
ido Aliyu ya cire sannan yai saurin ciro gilashin sa ya maida.

Zuwa wannan lokacin dayawa agurin sunyi kuka, shiru kotun yayi tsayon lokaci yayin da
alkalin ya sunkuyar da kansa tsayon lokaci sannan ya fara rubutu akan takardan dake gaban
sa, zuwa can ya maida kallon sa kan Aysha yace, " Aysha abun da Aliyu ya fada haka ne ko
kina da jah?
Cikin sauri ta girgiza kanta.

Abun da Aliyu ya fada gaskiya ne??

Eh ta fada ahankali.

Alkalin ne yace, " Ina Hajiya Umma"

Mikewa Umma tayi ta fito sarari.

Kin gamsu da da bayanin Aliyu?

Nasan Aysha taje gidan mahaifinta tayi wanan kwanakin kamar yadda yace inaso naji daka
bakin mahaifin ta Aysha taje gidansa ko bata je ba?

Bayan mahaifin Aysha ya fitone ya tabbatarwa kotu da cewa, tun wani zuwa da Aysha tayi
ta kwana daya bata sake zuwa gidansa ta kwana ba.

Sosai Innawo da ma duk wadda yake cikin kotun yai mamaki.

Cike da tsabar takaici da kunya Umma tace toh shikenan, yanzun ya masa yaron yaje ya
rainesa ahannun shi.

Rubuce rubuce Alkalin yayi sannan yace, " Aliyu yanzun ka amsa cewa dan da Aysha ta
haifa naka ne?

Ranka ya dade naw ne"

Toh Hajiya Umma ta bukaci daka amsa d'an ka,

Ranka ya dade ni bazan amsa shi ba.

Meye dalilin cewa baza amsa ba bayan ka tabbatarwa kotu dan naka ne?

Nawa ne, amman banaso bazan amsa ba, na bar masu.

A'a toh tsaya,, acikin biyu dole zaka zabi daya, mata ko d'an??

Kai tsaye Aliyu yace mata

Ciki da mamaki Alkalin yayi akbara, sannan yace wadda ya dauki uwa ai ya dau d'anta.

Rubuce rubuce yayi sannan ya dago yace, yaci ace iyayen Aysha dana Aliyu tun
ashekarun baya sun ma abun kallo mekyau su masu aure, da ace tunda akaga sunki rabuwa an
masu aure da an haifi dan sunnah, amma dake iyaye sun turje gashi abin da ba'aso ya faru, duk
da cewa kuna ganin kun raba tsananin su rabuwa me nisa, tsakanin Cameroon da Nigeria,

amman dake rabon ya rantse saida Aysha tayi takkakiya tabishi Nigeria aka dawo gida da
tsaraba, wannan ya isheku ishara, ku duba tsayon shekarun amman sabo da soyayya nacinta
arai bata manta ba, da wannan nake Kira ga iyayen Aysha dana Aliyu da aje a gaggauta daura
masu aure.
Cikin sauri Umma tace ranka ya dade, Ina rokon wannan kotu me adalci datamin adalci
kamar yadda ta saba, Aliyu ya karbi danshi kawai ya tafi, domin bana fatan hada zuri'armu da
tasu.

Kokarin maga Ummi keyi yayin da Innawo ta ke girgiza mata Kai dan haka ta fasa mgn
saidai fuskanta na cike da fushi.

Gyaran murya Alkalin yayi sannan yace, Hajiya Umma wannan shine adalcin, be
kamata ace zuwa yanzun kuna jayya ba, Kuma Aliyu bashi da da aibun da za'a hana shi aure
auren ta, Kinga na farko yana da sana'a, sannan duk mutumin da zaiyi abu laifi ya amsa cewa
eh yayi Kai tsaye da karshe ya nemi abashi auren ta, sannan ita kanta Aysha auren shine
mutuncinta, Kuma Aliyu yana son Aysha haka itama Aysha alamu sun nuna tanason Aliyu har
yanzun dan haka ku ajeye wani son rai naku agefe, am Ina fatan mahaifin Aysha yana cikin
wannan kotun?


Amsawa Daddy yayi sannan ya fito gaba,. Yayin da alkalin ya sake cewa mahaifin Aliyu
ba?

Innawo ce tace mahaifin sa ba dan nan bane.

Akwai wadda zai wakilce sa?

Alhaji Umar Innawo ta nuna baysn ya fito Alkalin yace, kotu zata daura auren nan take
bisaga wasu dalilai.

Aliyu zaka bada Sadakin Aysha"

Cikin sauri yasa hannun sa duk ya tattaba aljihun sa tare da fadin, " ranka ya dade na mance
ban fito da kudi ba"

Alkalin ne ya maida kallon sa ga kotun yana fadin, Aliyu bai fito da kudi ba, akwai wadda zai
fanshe shi akotun nan??

Daga can baya wani ya daga hannu, mikewa yayi yayin da Aliyu yaga abukin sa wadda
sukayi karatun tare anan Cameroon ne ke fadin ranka ya dade Jaka biyar ce a hannu na.

Juyawa Alhakalin yayi ya kalli Aysha yace,

toke Aysha jaka biyar dinan ta Isa amiki Sadaki dashi?

Batare data dago ba tace, eh

Abokin Aliyu aka umarta daya mikawa Aliyu

27 / 34