Bakar Fura Book Compelet

Author :  Fadila Lamido Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 34

21K to 24K   out of 101.2K words

ya dawo cikin dakin yana kallon Aysha tare da fadin, " inje inyi sallah in dawo?"

Cikin sauri ta girgiza kanta alamar a'a

Kallon ta yayi sannan yace lallai kuwa, kenan yau bazan samu jam'i ba?, sabo dake?, tsaki
yaja kadan sannan ya nufa toilet din dake cikin dakin, alwala yayi ya fito yana ware hannun
rigarsa, abakin kofar ya hangeta, dan zaro ido yayi sannan ya tsaya yana tunanin hanyar da zai
billowa al'amarin.
Window dake dakin ta baya ya kalla sannan ya fara takawa ahankali ya isa window,
labulen ya yaye sannan ya leka, juyowa yayi ya kalleta sosai sannan yace, kwaso takalmin ki
mugani ko zaki iya fita tanan.

Cikin sauri ta kwasa takalmin ta ta isa gareshi, daukanta yayi cak ya tura ta, cikin ikon Allah
ta dire tsaf tare da sauke ajiyan zuciya, aguje ta fice agidan, shiko Aliyu murmushi.

Juyowa yayi ya nufi masallaci yayin da ya wuce Ummi tana sallah a tsakar gidan.

*****

Daga ina kike?, Ina kika tsaya har aka Kira sallah?

Jakar makarantarta ta aje tare da yaye rigar jikinta tana nunawa Mama bayanta, Mama yau
duka mukaci, da cewa ma akayi amakaranta zamu kwana, bayana duk ya kunbura.

Yar dariya Mama tayi, radadine ya rudaki Amman bayanki be kunbura ba, saki rigarki.

Muryan Umma sukaji tana fadin, ta dawo ne ne gantalallar?

Eh Umma gata ta dawo.

Gidan ubanwa ta tsaya?

Mamace ta sanar da ita duk yadda akayi yayin da Umma tace yayi kyau ai, yanzun haka
surutu sukai, gara da aka zane kun ai.

Mikewa Aysha tayi tana fadin, " su Umma anji gulma"

Wanni itin kallo Mama taiwa Aysha yayin da Aysha taki kallon ta, Muryan Umma sukaji
tace ga magulmaciya nan agaban ki"

Jimmmm Aysha tayi tsayon lokaci yayin da Mama tace tashi kije kiyi sallah ki dauki
abincin ki.

Mikewa Aisha tayi bayan tayo alwala tana kokarin maida dan kwalin ta taga wucewan
Umma kitchen bayan ta tabi da kallo sannan tace, " Umma dazon naga me kama dake a hanya"

Tukunyan miyar Umma ta dauko sannan ta fito tana fadin, " haba"?

Allah kuwan, Aysha ta fada sannan ta dauki hijjabinta ta zura tare da sake cewa, " Umma
baki tambayen me kama dake din ba"

Toh inajin ki gaya min waye ne me kama dani din?

Birii.

Cikin sauri Umma ta sauke tukunyan miyan tare da kallon Ayaha data kambara sallah,
Mama ma kallon Ayaha tayi tare da fadin, lallai baki da mutunci.

A'a barni da Ita, ai nima ba kanwar lasa bace, kallon Ayaha tayi wanda zuwa yanzun tayi
ruku'u tace, mancewa kikai ai biri namiji ne, wannan mutumin na wancen garin shine katon biri,
dashi sukafi kama, ficewa tayi adakin ta nufi tsakar gida, inda mama keta dariya tana fadin
Aikuwa Umma kinyi maganin rashin kunya.
Ai kibarni da ita.

Zuwa can Aysha ta fito hannunta dauke da kofin da fura me sanyi aciki, Mamace ta kalleta
sannan tace kizo kidauki abincin ki.

Banaci, furar nan ta ishe ni.

Mama batabi ta kanta ba ta jawo abincin dake gabanta, yayin da Aysha ta koma daki,
Umma ce ta zauna kusa da Mama domin cin abincin amman sai ganin Mama tayi tana ya mutsa
fuska.

Yaya akayi?, Umma ta tambaya

Umma miyan nan gishiri yayi yawa.

Hannu Umma tasa cikin miyar ta dandana tare da kallon mama tace, " wlh miyata lafiya
kalau take, Indo ce ta takara min shi.

Batanan akayi miyan ai Umma, kila dai hannun ki ne ya subuce.

Saifa kiyi, Aysha ce ta kara shi, aina zagi ubanta, ta zuba min gishirin ne dan karnaci, toh
sainaci ko inaci ina rufe ido ne.

Aikuwa indai hakane sai mata duka wl....

Kashhh, karkice mata komai, barta kawai, muci abincin mu bamuma san tayi ba kawai.

******

Yau tunda ya tashi dariyar Aysha ta jiya ce ke fado masa, wadda aduk lokacin daya tuno
saiya murmusa, sannan yana yawan tuno yadda hasken ta ya dannen dan hasken da yake
dashi nesa ba kusa ba, afili yayi dari tare da fadin dole kiyi dariya Aysha kinga dan baki me
karfin hali, kallon fatarsa yayi sannan yace kai ina, niba baki bane, kawai dai hasken tane yai
yawa har yana kashe ido.

Irin wannan tunanin baya awa daya batare daya fado masa ba, dan hakan yake yawan
murmushi musamman idan ya tuno irin amsan da take bashi wadda yafi kama da aje ahaka din.

Aliko yau murmushin me kake ne?

Innawo wanine yabani dariya.

A lallai kuwa yana da abin dariya, yau bazaka kasuwar bane?

Zani amman sai 4 yanzun zuwa zanyi in kwanta.

Mikewa tayi ta nufi daki yayin da Aliyu ma ya mike ya nufi nasa dakin, cikin ransa yake
fadin kila yau bazatazo ba, dan naga jiya ta tsorata.

Kwanciya yayi yana jiran lokacin daya gindaya mata na zuwan, yayi yaji ana kwankwasa
window sa ahankali.

Mikewa yayi ya isa window ahankali ya bude, Aysha ce tsaye cikin kayan islamiyyarta riga
da wando da hijjabinta daidai guiwa, jakar makarantar ta rataye agefenta yayin data bude
madaidaicin bakinta tace, " ina yini"

Lumshe ido yayi batare daya amsa ba, juyawa yayi ya bude kofar data shigo jiya ganin haka
tai saurin zagayawa ta shigo"

Rufe kofar yayi sannan ya dawo ya rufo window tare da dawowa wajen zaman shi ya
zauna, itama Aysha kujeran jiya ta zauna tana kokarin fito da littafin ta.

Aliyu kuwa kur yamata da ido yana me kare mata kallo tsayon lokaci.

Kallon da yake mata yasa duk taji ta tsargu, rasa inda zatayi tayi tayi, tun tana kawar dakai
harta fara buga kafarta akasa, tana dan sheshshekar kuka?

Lumshe idon sa yayi tare da fadin, "Menene"?

Kai ne.

Idon shi lumshe yace me ya faru?

Ya Aliyu kallo na fa kake?

Neman ki nake, hasken ki ke kashe min ido na.

Kyalkyalewa tayi da dariya, tare da fadin gani nan fah.

Daidai ina?

Dariya ta sake sawa, yayin da hakan ke kara sashi nishadi.

Hannunta ta daga tana yawo dashi saitin fuskarta tana fadin, gani nan fa

Kara ware idon sa yayi nadaiga wasu TAURARI guda 10 suna yawo, tare da wani haske
wal wal.

Dariya ta Kara sawa wadda har shima saida yadan murmusa.

Sosai yakejin wani nishadi na shigarsa hakama Aysha mantawa tayi da komai zuwa wannan

lokacin data kalli fuskar Aliyu take yin dariya domin ba karamin dariya yake sata ba.

Muryan sa taji yace nidai tunda ba ganin ki nake ba bani littafi kawai karki hanani zuwa
kasuwa kamar jiya.

Littafin tabashi, har suka gama acewarsa be ganinta, haka ya bude bata kofar ta fita shima ya
fita.

Hakace ta cigaba da kansancewa har tsayon wata Uku, aduk ranakun islamiyya saita fara
shiga gidan su Innawo sannan ta wuce makaranta, wata rana ta fita ta kofa wata wata rana
kuwa saidai ya sakata ta window, tsayon wannan lokacin Babu wadda ya taba sani.

Zuwa wannan lokacin shakuwa me karfi ta shiga tsanin Aysha da Aliyu har yakai ranar da
Babu makarantar suna kewan juna tare da kosawa suka junan su.

Ayanzun Aysha tasan wasu daga cikin halayen Aliyu, sosai take ganin kirkin sa, haka
shima Aliyu ya fahimci Aysha dakyau, akoda yaushe yana yaba kwazonta tare da son karatu
nutsuwa da kunya.

****

Yauma kamar kullum Aysha ce zaune ita da Aliyu, littafin ta kan cinyar sa, kokarin fahimtar da
ita yake, duk da cewa zuwa yanzun idan an bata aiki amakarantar tana jaraba yi da kanta, Koda
za'ayi mata gyara yana zamuwa bame yawa banr, sosai take dauke duk wani abu da zai koya
mata, rufe littafin yayi bayan sun gama ya mika mata sannan yace toh bani kudina.
Wani littafi ta bude cikin Jakarta ta dauko masa kudin ta mika masa.

Amsawa yayi sannan ya daga katifarsa ya tura, juyo yayi adaidai lokacin da Aysha ke mika
masa sweet"

Murmushi yayi sannan yace, " au har da kari?, to bare min"

Bare masa tayi ta mika masa, yayin daya tura mata fuskarsa yana fadin saka min.

Saka masa tayi kamar yadda yace, idon sa lumhe yace, Kai, bantaba shan sweet me dadin
wannan ba.

Cikin yar dariya tace , "Kai, Ya Aliyu duk sweet din da kake Sha?"

Ummm wannan yafi dadi.

Yauwa Ya Aliyu wai meyasa kake saka kudin ka kasan katifa?

Dauke idonsa yayi daga kallonta ina ruwan ki?

Dan Allah"

Toh tarawa nake in sunyi yawa inje makka"

Kaiii!! dariya tayi, ya Aliyu har makka ma?, bama katafi Nigeria ba gurin Baffah?

*Kar me karatu ya manta, duk mgnr da Aliyu yake yi da Aysha sunayin ta ne cikin
harcen fullaci, idan karatu ne kuwa da harcen french domin Aysha batajin hausa, yare nan biyu
kawai take iyaji, hakama iyayen Aysha, gidan Innawo ne kawai sukejin hausa kadan kadan.*

Nace meki kudin zuwa Nigeria nake nema?, wannan kudin aiki nawa zasu baki mamaki,
inason nayi wani abu me daraja dashi sabo da sun fito daga hannun 'kanwata, kawata Kuma
aminayar sirri na.

Murmushi Aysha tayi me sanyi har cikin ranta take kallon fuskan Aliyu dake kawace da
murmushi, cikin yanayin jin kunya take kallon shi dazaran taga kamar baya kallon inda take"

Shikuwa Aliyu daya kulla tana kallon sa yake fara wasa da girarsa tare da gashin idon sa,
wadda hakan kesa Aysha murmushi, shima Aliyu dayaga tana murmushi yake jin zuciyarsa
wasai, suna cikin wannan yanayin suka tsinkayi bugun kofar dakin ta cikin falon, azabure suka
kalli kofar gaba dayan su"
Kai Aliko!!!!

Muryan Innawo yaji dan haka dan haka ya nunawa Aysha bayan kofar da Innawo ke bugawa.

Kusan atare suka isa gurin, yayin da Aliyu ke amsawa tare da bude kofar sukayi ido biyu da
Innawo"

Kallon sa tayi sama da kasa sannan tace, " Kai dawa a ciki ?

Lumshe idon sa yayi, nidawa kuwa Innawo?, ni daya, lafiya?

A'a daman yariyar nan Indo ce ake nema.

Wacece haka?

A'a jeka abun ka, juyawa Innawo tayi batare da ta jira me zaice ba.

Rufe kofar Aliyu yayi sannan ya dawo dakin yana rike da kugun sa da hannun sa duk biyun

yake kallon Ayaha tare da fadin, " wani yaga shigowan ki nan ne?"

Cikin samyin jiki tace a'a.

Bakin gadon ya dawo ya zauna yana me tuna irin kallon da Innawo tamai, be dawo daga
wannan tunanin ba yaji ana buga kofar dakin ta tsakar gida.

Da tsananin mamaki ya juya ya kalli kofar, domin babu wadda yasan cewa yana bude kofar
a yanzun sai Aysha Kuma gata aciki suna tare.......




Fadeela Lamido ✍️





*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_

*Na*
_Fadeela Lamido_


PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

*Episode 13to 14*


Mikewa Aliyu yayi, mamaki cike da fuskar shi, sai dai ya kasa zuwa gun kofar, yayin da yayi
da yai tsaye hannun sa cikin aljihun sa.

Aysha kuwa tuni ta kara gigicewa tana shirin fara kuka.

Kofar kuwa kara tsananta bugunta ake yi, dan haka yace waye?

Nice, muryan Innawo yaji cikin daga murya
Dan haka ya saki ajiyan zuciya sannan ya nufi kofar dakin cikin falon ya fice zuwa tsakar gida
da innawo ke tsaye.

Gaban kofar ya sameta cike da kallon tuhuma ta kalle shi ina Indon?

Kawar dakai yayi can gefe sannan yace wai wace miki tashigo nan din?

Runtse Ido Innawo tayi, Aliko wannan ba halin ka bane ka bude min kofar nan.

Ai kinsan ba'a bude wannan kofar muje ta ciki ki duba ki gani.

Ban zuwa, alamu ya nuna kana amfani da kofar nan Aliko, dan ada ba haka rufuwarta yake
ba. sannan yariyar nan sau uku ana shigowa nimanta ni jikina ya bani indo na dakin ka.

Zuwa yanzun kam bashi da mafita dan haka ya kawar da kanshi tare da fadin karatu tazo.

Raratu?, toh daman har yanzun ba'abar wannan karatun ba?, Maza ka bude mata kofa ta fita
tun kafin uwarka ta dawo.

Lumshe ido yayi, sannan ya koma ta inda ya fito, Aysha ce ke zaune ta fara hawaye ya
cemawa tashi muje"

Mikewa tayi tana raba ido, yayin data rike wani daga cikin littafin ta ahannu, jakar makarantar
ta Aliyu ya dauka sannan suka fito Ayaha na gaba Aliyu na binta abaya, a tsakar gida suka
hadu da innawo, kallo kawai ta bisu dashi yayin da Ayaha ta wuce sumi sumi, ganin da Innawo
tayi Aliyu nashirin fita har kofar gidan tare da Ayaha tace dawo Aliko.
Lumshe ido yayi sannan ya mika mata littafinta ya dawo ciki.

Wanni irin kallo innawo tabishi dashi sannan ta dawo takoma ta zauna tare dasa tagumi.

8 / 34