Author : Fadila Lamido Category : Read Hausa Novels
*️BA'KAR FURA️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
*✍✍BAKAR FURA lbr ne da yafaru da gaske, wanda yake dauke da Soyayya me kayatarwa,
ga tarin Nishadi, ban al'ajabi tare da ban tausayi, gameda fadakarwa, wadan da abun ya faru
dasu muna nan muna cigaba da rayuwa tare dasu cikin wannan duniyar tamu,Allah yabani ikon
isar da sakon yadda ya dace.*
*Episode 1- 2*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Cikin kasar CAMAROON (1995)
_Alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar_
Ke!! Ke!!! dakata maza ki tattara kafafuwan ki ki koma gida.
Cak yariyar da ake dakawa tsawan ta tsaya cikin yanayin rashin jin dadi.
Wasa ta shigayi da fararen yatsun ta, tare da zuba masu ido, saidai ko motsi batai ba bare
ta juya kamar yadda matar dake zaune gefenta ta bukata.
Cikin fullaci matar ta sake mgn kamar yadda tayi da fari tace, " wai badake nake mgn
bane kika min tsaye"?
Har yanzun yariyar na tsaye bata juya ba, ko motsi ma batai ba, fitowan wata dattijuwa
tana fadin yaya akayi ne?, yasa su duk suka kalleta"
Itako wannan matar kawar dakai tayi can gefe.
Kallo tattijuwar tabi matar dashi sannan ta kalli kyakyawar yariyar dake tsaye tayi murmushi
ta matsa gefenta tana fadin *Aysha* zo ki wuce.
Cikin sunkuyar dakai yariyar ta wuce, tana waigen wannan matar, bayan ta kulle ne matar
tabi bayan yariyar da harara ganin dattijuwar na kallonta tai saurin dauke kanta can gefe cikin
yanayin jin kunya.
Matsowa dattijuwar tayi kusa da matar tana fadi cikin harcen fullaci, " Fatima kibar kyaran
ta"
Batare da matar ta juyoba tace " Innawo kina kallon fa yadda 'yan gidan su suke nunawa
baro baro basu son shigowar ta.
Duk cikin harcen fullacin suke mgnr da alama fullacin kawai suke ji bisaga la'akari da yadda
ya rike bakin su.
Me ya dame ki?, wani ne yaje ya kirata ne?, inace ita ta kawo kanta?, babu ruwanki, idan
har basaso su dakatar da ita daga can.
Batare data juyo ba tace shike nan.
Zama sukayi suka cigaba da hira har tsayon wani lokaci, zuwa can *Aysha* ta fito hannunta
dauke da littafai, inda suke ta kalla cikin sakin fuska tace, "natafi"
Innawo ce kadai ta amsa sannan ta wuce ta fita.
Hira Innawo sukaci gaba dayi, zuwa can na hango wani zafgegen saurayi, wankan tarwada
shiba fariba Kuma ba baki ba, dogo, kwantancen saje gewaye da fuskarsa, kananan kaya ne
ajikin sa yana takawa da karfi irin na jajartattun maza, idon sa tubarkallah, mayya ne, ko ince
wadatattu, tafe yake fuskarsa kadaran kadaham, shiba fara'a yake ba, Kuma ba daureta yayi
ba, wuce su Innawo yayi yana kokarin barin gidan yaji ance zonan"
Cak ya tsaya tare da dawowa baya yana binsu da kallon kasan ido yace gani"
Naga ka wuce ne kamar bakasan damu agurin ba?
Naga ganku, nace sannu ku ai"
Cikin lumshe ido matar tace bamuji ba.
Innawo ya kallah sannan yace Innawo kema bakiji ba?....
A'a babu ruwana, wannan mgnr ku ce naga dai kamar ka motsa leben ka ko?
Kawar da kansa yayi sannan ya juyo ya kalli matar data daure fuska sosai ya hadiye
yawu tare da fadin, toh Ummi sannu ku"
Kawar dakai tayi batare data amsa ba, ganin haka ya dan sake kallonta yana sake fadin, bari
naje na dawo"
Ahankali tace adawo lafiya"
Allah yasa, yafada sannan ya juya ya fita.
*******
*Aysha!!!*
Na'am Mama!
Mikewa tayi ta fito da littafanta a hannunta da alama karatu take yi"
Jikin mahaifiyarta ta fada cikin nuna tsananin so ta rungumeta tacin fullacin tace"
*Aysha* baki gajiya da karatu ko?, yau ko abinci banga kinci ba fah"
Mama banjin yunwa"
Inafa zakiji yunwa tunda kin rike littafai"
Karatu nake mun kusa fara jarabawa"
Littafin dake hannunta ta karba ta duba cikin yamutsa fuska tace"
Wannan ba rubutun ki bane, bayan littafi ta duba sannan ta kalli *Aysha* tace, littafin naki
ne, rubutun fa na waye?
Dagowa tayi daga jikin mahaifiyar tata tana me kallon cikin idonta cikin alamun rashin
gaskiya tace"
Ya *Aliyu* ne ya rubuta min.....
Cikin zafi ta make bakin Aysha tana fadin, yaushe kika sirare kika fita?, wato ke bakijin mgn
ko?
Rike bakin Aysha tayi idonta na tsiyayan hawaye tace, Mama idan banje ba waye ne zai
koya min karatun?
Mama ta bude baki zatayi mgn wata tsohowa ta fito daga wani daki tana fadin"
Ai sai kinyi da gaske idan kina son ki raba Aysha da yaron nan, ai ina kallonta sanda ta fita
zuba ido kawai nayi, tun dake kin bari ni yaya zanyi?
Nifa Umma bahaka bane, ai dole sai kun tayani, idan anga tayi abun da ba daidai ba a
kwaba mata"
Cikin kawar dakai tace shikenan, abin da yafi Sam ahana ta shiga wannan gidan, gaba daya,
idan mu kin rainamu baki tsoron mu nasan dawa zan hadaki, gaba daya yayyen uwar ki zan
sanar abun da kike yi"
Ganin Inda Umma ta Kura mata ido ta kalli mama sannan tai kasa da kanta.
Umma kuwa haka taita maganganu yayin da Mama ke taya ta, *Aysha* kuwa saurare kawai
take"
Washegari da misalin karfe 2 *Aysha* ce ke tube kayan makaranta sannan ta saka yar
karamar riga da siket dinta daidai guiwa, irin me budewa gaba daya, littafinta ta ciro guda daya
tare da biro ta zauna tana fakan idon su Umma dake aikin girki can bakin kitchen, ganin sun
maida hankalin su sosai kan aiki ta wuce suf suf ta fice"
*******
Ahankali ta tura kofar bakinta dauke da sallama.
Dagowa saurayin yayi ya kalleta sama da kasa sannan yai saurin dauke idon sa ya maida
kan yariyar dake zaune gaban sa tana rubutu cikin littafin dake gaban ta"
Karasowa tayi kusa da yariyar ta zauna yayin dataga saurayin ya sake dagowa ya kalleta
akaro na biyu, kallo ta bishi dashi yayin dataga kamar yana motsa lebensa, kallo taita binsa
dashi Kamar yadda shima yake binta dashi saidai bata ankara ba taji ya buga wata irin tsawa
me rugugi wadda yasata sakin littafin da biron batare data shiryar ba, bata ankara ba sai
ganinta tayi akofar gidan cikin yanayin haki ta tsuguna tana maida numfashi"
Dariya taji asaman kanta dan haka tai saurin dagowa ta kalli yariyar sannan tayi ajiyan
zuciya tace"
Husna me namai?
Cikin matsanancin dariya wadda aka Kira da suna Husna tace yace kizo"
A'a nikam bazani ba"
Dariya Husna ta sake yi sannan tace tashi muyi sauri mukoma karyace mun dade, muje ba
abun da zai miki"
Cikin rashin fahimta tace mena mai toh?
Ke dai muje mana"
Wlh Husna masifar tsoron wannan tsawar tasa nake"
Jikin Aysha Husna ta kalla yadda jikinta ke buga uban rawa ta kara fashewa da dariya tana
fadin, " aikuwa kina da aiki"
Daker Aysha tace kemafa kina firgita idan yayita"
Ina firgita amman jikina baya rawa, waigawa tayi ta kalli fokar gidan nasu sannan tace kitashi
muje.
Ahankali suka shiga dakin, Husna agaba *Aysha* nabinta abaya cikin tafiya ahankali har
suka isa gaban shi"
Zama sukayi duk su biyun yayin da *Aysha* ke Satan kallon shi, ganin da tayi Kamar bashi
ne ma ya buga tsawar dazon ba tayi ajiyan zuciya adaidai lokacin da yace, matso ke"
Cikin tsoro sosai ta matsa gabansa, wani irin radadi taji a tsakiyar kanta, dan haka tai
saurin runtse ido tare da yamutsa fuska cikin yanayin dake nuna tanajin zafi"
Shikuwa Aliyu kalabar dake kanta ya rike tsoro biyu tun daga tushen su yake fadin meyasa
baki rufe kanki ba?
Macewa nayi ya *Aliyu* kayi hakuri.
Mantuwa fa kika ce?, Shekarun ki nawa?
Dan Allah kayi hakuri bazan Kara ba"
Tambayan ki nake ai, shakaran ki nawa?
Kasancewar yana Kara matsewa hakan ke Kara sata rikecewa cikin sauri tace, goma sha
uku"
Kawar dakai yayi batare daya saki kan nata ba yace, toh kinji goma har sha uku, amman kika
iya tsallako gida nawa kika taho ahaka, gida nawa kika tsallake kafin kikazo nan?
Wayyo Allah, dan Allah kai hakuri kaji"
Sakin kan yayi da sauri yana fadin nayi hakurin, amman karna Kuma ganin ki ahaka"
Kanta ta gyada tare da kokarin share hawayen ta.
Aliyu kuwa Husna ya kallah yace, kuje kibata zani da hijjabi, Amman kuyi sauri fita zanyi"
Cikin kankanin lokaci suka dawo sannan yai masu karatun kamar yadda suka saba, cikin
lokacin dabe wuce awa daya ba suka gama, a tare suka fito cikin sauri yabar gidan yayin da
*Aysha* ma ta nufi gida.
*******
Innawo!!!
Gaban Innawo ne ya yanke ya fadi jin Kira cikin fada da hargowa, fitowa tayi tana zare ido
ganin Umma tsaye atsakar gidan yasa tace"
Au kece?, Lafiya kika shigo babu Sallama?
Kashedi na kawo miki, *Aliyu* ya fita harkar *Aysha*, idan ba haka ba kuwa wlh zan dauki
mummunan mataki akan shi"
Subuhanallahi, to wai me yake faruwa ne?
Babu komai kawai ni alakar tasu ce banaso"
Ai basu da wata alaka, Umma ki kwatar da hankali ki, inace *Aysha* gurin Husna take
zuwa, so da yawa zatazo tasamu Aliyu nama Husna karatu dan haka itama tafara zuwa da dan
littafin ta, ni banga abun tashin hankali ba anan"
Kece baki ganshi ba, nikam na ganshi, banso ne Sam idan ba haka ba duk abun da ya
faru karkuga laifina"
Babu abun da zai faru sai alheri, kuma jikarki indai baki son ta shigo gidan nan ki tare ta
acan gidan ki dan nikam ba me gadin ki bace......
Muryan Ummi sukaji tace, "Umma jeki duk ranar da *Aysha* ta shigo gidan nan zan mata
korar wulakanci"
Aikuwa dakin birgeni, juyawa tayi tanacigaba da fadin maganganu yayin da Ummi ta Kara
kulewa sosai"
**********
Tsayon kwana biyu aka kwasa *Aysha* bata shigo gidan ba, yayin da duk Husna taji wani
irin, domin ta saba kullum zasu hadu bayan sun dawo makaranta, gaba dayan su zaune suke a
tsakar gida har Aliyu, Ummi ce ta kalli Husna tace, "waike meke damun ki?"
Ahankali tace babu komai"
Aliyu ne ya kalleta ta gefen idon sa tsayon lokaci kafin yace, ke me yake faruwa?
Ummi da Innawo ta kalla ganin basa kallon ta tai kasa da muryar tare da fadin, kwana biyu
*Aysha* batazo ba, Kuma Ummi ta hanani fita"
Kallon Husnah yayi sosai sannan ya maida hankalin sa gurin kallon su innawo yana fadin
jeki Kira min ita.
Wa za'a Kira maka?, Innawo tayi tambayan tana tsaresa da ido"
Kai tsaye yace *Aysha*"
Aysha?, *Aliyu* Aysha fa iyayenta bason shiguaarta gidan nan suke ba, ko shekaran jiya
bayan kagama masu karatu nan kakarta tashigo taita fadar maganganu marasu dadi, ku fita
harkar yariyar nan"
Wai akan me take mgnr wai, ya fada yana kallon fuskan Innawo"
Au tambaya keke ne?, Ana cemaka ku fita hanyarta kana tambayan dalili? Ummi ta fada
hakan cikin tsare sa da ido, dan haka yadanyi kasa da kansa sannan yace
Naga ai karatu ne ke kawota ba wani abu ba, amman ni meye nawa, shiguwar tata mezata
kara min?
Mikewa Ummi tayi tana fadin nima abun da nagani kenan"
**********
Abincin dake gabanta take ta juyawa tare da fakan idon aunty Murja dake gefen ta, tana bude
jakar makarantar ta ahankali ta jawo littafin ta wadda tasaba zuwa dashi karatu kowanni lokaci,
rigarta ta daga ta tura shi cikin siket dinta, agogo ta kalla domin tasan ya Aliyu 3 yake fita gashi
yanzun biyu har da kwata"
Aunty Murja taita satan kallo daga can taga ta mike ta shiga dakin Umma dan haka tai saf saf
ta fice agidan.
*********
Babu kowa a tsakar gidan cikin siririyar muryarta ta shiga sallama daga can Husnah ta amsa
mata.
Falon taji Muryan Husna dan haka can ta nufa inda ta hangesu Husna zaune akasa yayin da
Ya *Aliyu* ke zaune kan kujera idonsa akan littafin Husna dake hannun sa"
Har Aysha ta zauna beyi mgn ba, Kuma be dago ido ba, ahankali Aysha tace " Ya Aliyu ina
yini"?
Lafiya lau ya fada batare daya dago ya kalleta ba"
*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata
atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida,
sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na
musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan
kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no 07014197556*
Bayan yagama duba littafin Husna yace matso, gaban shi ta isa ta zauna, cikin nutsuwa
yake Kara fahimtar da ita saida ya tabbatar ta gane sannan ya tura mata littafinta yana fadin,
*Aysha* muga naki"
Mika masa tayi tunda ta shigo har yanzun beko kallesu ba, duk bayanin da