Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 26

24K to 27K   out of 77.3K words

Tana ƙoƙarin komawa cikin gidan suka yi kiciɓis da juna a bakin falon yana ƙoƙarin fitowa
cikin gidan. Don yana hangen ta ta sama a lokacin da take sharar tsakar gidan. Wannan dalilin
ya saka shi fitowa daga ɗakinsa, saboda ƙamshin girkin da ya cika masa hanci ko kaɗan bai
saka shi sha'awar fitowa ba. Sai dai ganin tana sharar ya ji tausayin ta ya tsirga masa a zuciya.
Ya fito da niyyar hana ta amma ganin ta gabansa ya basar, raɓawa kawai ya yi ta gefenta ya
wuce ba tare da ya ce da ita komai ba.
Ita kuma ƙirjinta da ke bugawa tun a lokacin da suka yi ido biyu da juna bai daina ba har ta isa
cikin ɗakinta, dafe da zuciyarta ta jingina bayanta jikin ƙofar ɗakin tare da rufe idanuwanta tana
sauke ajiyar zuciya wata bayan wata.

'Me ke shirin faruwa da ni?'

Tambayar da ta yi wa kanta kenan, tare da saka yatsun hannu ta yi watsi da ƙwallar da ta cika
idonta tana ƙoƙarin gangarowa fuskarta. Wanka ta faɗa cikin kasala bayan zuciyarta da ke ta
harbawa tana hasko mata fuskar Jamal da irin kallon da ya yi mata a lokacin da suka yi ido
biyu.

Uhum‍


D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*LAMBA SHA ƊAYA.*


A gurguje ta kammala wankan ta fito cikin yanayin mutuwar jiki. Tsawon minti biyar tana
gaban madubi ba tare da ta yi abin da ya zaunar da ita ba. Jin motsin rufe ɗakinsa ya sa
hankalinta ya dawo jikinta. Cikin sauri ta goga mai da turare tare da zumbula doguwar riga ta
fito jikinta yana tsuma. Da sassarfa ta sauka ƙasa, gudu-gudu sauri-sauri ta fita harabar gidan
cikin bugun zuciya. Saboda hango Jamal yana ƙoƙarin shiga motarsa alamun fita zai yi.
Dole ta ja ta tsaya rungume da hannu tana kumbura fuska a ranta tana jin takaicin kanta a
kan zaman da ta yi ɗaki ba tare da ta taya masa abin karin ba. Hango ta a tsayen a daidai
lokacin yake ƙoƙarin fito da motar a mazauninta; murmushi kawai ya yi don zuciyarsa ta hasko
masa sabon sauyin da ya wanzu gare ta, a tsakanin dare zuwa safiya.
"Zan je restaurant, daga can na biya shago."

Abin da ya faɗa kenan a lokacin da ya nufi bakin gate, ba tare da ya kai kallonsa gare ta ba.
Saboda ba don ma ya ɗaga murya ba ba za ta yi tsammanin da ita yake maganar ba. Mamaki
da tulin haushi suka dirar mata a ƙoƙon ranta, saboda ganin ta ɓata lokaci wurin haɗa masa
abin kari amma ya yi kamar bai san ta yi ba. Bayan motarsa ta bi da kallo kamar ta bi shi ta roƙe
shi don Allah ya dawo ya ci nata girkin. Gudun sammakonta ya tashi a iska, amma aikin gama
ya gama don ya fice fit har maigadi ya kulle ƙofar gate.

Sharr ta ji wani hawaye mai zafi yana bin fuskarta, a fusace ta juya tana danne kukan da yake
ƙoƙarin zo mata, a haka ta isa falo ta faɗa kan kujera tana haki tamkar wadda ta sha gudu.
Ta jima a wurin da tagumi hawaye yana zarya a kan fuskarta, bayan saƙe-saƙen tunani da
kwancewar da take yi. Sannan ta miƙe cike da takaici ta zuba abin karin daidai cikinta, ta fito da

sauran ta miƙa wa maigadi, bayan ta sauya kula. Saboda sai da ta tsaya ta darje sannan ta zaɓi
kular da ta fi burge ta ta zuba wa Jamal abin karin. Da niyyar burge shi kuma don ya ji daɗi ya
yaba wa gwanintarta. Sai ga shi ya lalata mata tsari, tare da ruguza sabon shirin da take ƙoƙarin
shiryawa tun a tashin farko. Don sosai ta ci burin faranta masa ya gano amsar tambayarsa ba
tare da ta furta ba.

Bayan ta gama karin ta nufi ɗakinsa kanta a tsaye, zuciyarta cike da tunani kala-kala. Cikin
zafin nama ta gyara masa ɗakin tsaf ta feshe ko'ina da turaren wuta.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ta koma kitchen ta shiga haɗa masa girki, waton shinkafa da
wake. Ɗaya daga cikin kalolin abincin da Hajiya ta sanar da ita yana so. Bayan man ƙuli da yaji
har da miyar tarugu a gefe ɗaya ko da zai yi ra'ayin haɗawa. Wayarta ta lalubo ta shiga neman
lambarsa, wadda Nur ta yi mata saving lambar da hannunta. A watarana da ta ari wayar Minal
ta kira sa saboda tata wayar babu caji.

'Jaan.'

Ta maimaita sunan a cikin zuciyarta kafin ta danna masa kira ƙirjinta yana bugawa fat-fat. Sai
dai har ta gama ruri ba ta ji an ɗaga ba, babu ɓata lokaci ta sake danna wani sabon kira. Caraf
ta ji an ɗaga kiran tare da yin magana a lokaci ɗaya. Nan take hawaya ya shiga bin fuskarta
tsabar takaicin da ta ji.
"Sorry, idan na dawo za mu ƙarasa maganar."

Daga haka ya katse kiran, saboda tsammaninsa a kan maganar da suka fara ne ta neme shi. Ta
jima sandare da wayar a hannu kafin tunanin tura masa saƙo ya faɗo ranta. Cikin ɗan lokaci ta
rubuta masa ya turo yaro ya karɓi abincin da ta dafa masa.

'Ki jira zan dawo.'

Tsaki ta ja tare da wurgar da wayar a gefenta tana faɗin, "Kayan haushi." Ganin amsar da ya
mayar mata mai kama da an kwaɗa mata mari. Ɗaki ta nufa ta yi sallar Zuhur saboda a lokacin
har biyu ta gota. Ta jima a wurin tana lazumi kafin ta naɗe sallayar ta koma falo zaman jiran sa.
Zuciyarta cike da haushi da fargaban hukuncin da zai zartar a kan zamansu idan ya dawo.
Jamal kam bai dawo gidan ba har aka yi sallar Isha, kuma da gangan ya ƙi dawowar ya yi
zamansa a shagonsu. Hada-hadar saye da sayarwa ya saka shi rage jin kewar Nur da ke cikin
zuciyarsa. A gefe ɗaya kuma ba ya son zamansa cikin gidan gudun su sake samun matsala da
Minal ta nemi kashe kanta a banza. Sai da ya biya Restaurant ɗin da ya saba zuwa cin abinci, sannan ya je gidan Hajiya suka yi
sai da safe ya nufo gidansa. Zuciyarsa a sake saboda tun bayan aurensa bai leƙa shagon ba.
Aikinsa kuma yana cikin hutun da ya ɗauka da niyyar cin amarcinsa a kan kari.

Minal kam zuwa lokacin ta gama cika tana batsewa, don duk ta wurga ido ta hango abincin da

ta yi masa sai ta buga dogon tsaki. Wanka ma bayan na safe sai da ta sake wani saboda, ta
kashe ɗaurin ɗankwali da baza turare a jiki amma har ta gaji da jira bai dawo ba. Hakan ya sa
lokaci da ta ji shigowar motarsa gidan ba ta motsa daga inda take kwance tana kallo ba.
Har ta ji takun hawansa saman ba ta yi niyyar tarbon sa ballantana ta nuna farincikin ganin
sa. Illa dukan luguden uku-ukun da ƙirjinta ke yi tun lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar
motarsa. Da guntuwar sallama ya shigo falon waya a kunnensa yana magana har ya shige
ɗakinsa. Jim kaɗan ya fito falon bayan ya gama wayar ya tsaya gabanta fuskarsa babu yabo
babu fallasa ya shiga ƙare mata kallo.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,

"Lafiyarki ƙalau kuwa?"

Banza ta yi masa kamar ba ta ji ba, hakan ya sa ya leƙa fuskarta yana faɗin,
"Ko barci ne kike y...?"

Ganin idonta wuƙi-wuƙi tana muzurai ya yi hanzarin fashewa da dariya sannan ya zauna yana
faɗin,

"Ke kam wa ya taɓo ki bayan ke kaɗai ce a cikin gidan? Ko maigadi ya bar wani ya shigo
gidan nan ban sani ba?"

Tashi zaune ta yi, tare da wurga masa wani kallo sannan ta ce,

"Babu komai"

Ta miƙe da nufin barin falon ya dakatar da ita, ta hanyar faɗin, "Ina abincin da kika ce kin dafa
mini? Saboda sai a lokacin ya tuno da saƙon da ta tura masa. Har a ranta ta ji daɗin
maganarsa ganin ya fara damuwa da sabgoginta, saboda haka ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta
nufi kitchen ta jawo kwandon abincin da ta haɗa masa tun ƙarfe ɗaya na rana. Cikin ƙumaji ta shiga baje kayan abincin a gabansa, zuciyarta cike da jin daɗi ta fara buɗe
kular shinkafa da waƙen. Bumm warin waken ya daki hancinta, bayan sandarewar da ya yi a
cikin kular ya sauya ƙamshinsa daga wake zuwa warin tusa. Babu shiri ya toshe hancinsa
bayan ya miƙe yana nuna kular da hannu ya ce,
"Wannan shi ne abincin da kike so na ci? Cabɗijam! Allah Ya taimake ni ban da rabon
wahala..ahhhh..."

Ya fara yunƙurin amai da gudu ya nufi ɗakinsa ya banko ƙofar. Ya jima yana sauke ajiyar
zuciya bayan feshe jikinsa da turaruka yana shinshina jikinsa don jin warin ya wuce ko ya
maƙale ya biyo shi har cikin ɗakin. oda tana buɗe kular warin waken ya daki hancinta ta yi
hanzarin kawar da kai gefe. Wata irin kafurar kunya ce ta dabaibaye Minal, saboda ita kanta ba za ta iya cin abincin ba.
Tsabar takaici ta kinkimi kular ta fice harabar gidan jikinta yana rawa ta nufi maigadi tana faɗin,

"Baba don Allah almajiri nake nema."

Kallon mamaki ya yi mata, saboda sanin wace unguwa suke da irin mutanen da ke cikin ta.
Maimakon ya ba ta amsa zura hannu kawai ya yi alamun ta ba shi kular. Girgiza kanta ta yi tana
cewa,

"Abincin ya lalace ba za ka iya ci b..."

"Ke dai ba ni Hajiya, mu kashi ne kawai ya rage mana ci a tsawon zamanmu cikin duniya."

Jiki babu kuzari ta miƙa masa kular cike da karsashi ta juya tana faɗin, "Bari na kawo maka
miya ka saka."

Jikinta yana rawa ta kai masa ta dawo feshe falon da turare ranta a jagule tana Allah wadai da
waken da ya tozarta ta gaban Jamal. Bayan ta saita falon ta shiga bubbbga masa ƙofa zuciyarta
a tsinke kuma cike tsoron wulaƙancin da zai tarbe ta da shi.
Tsawon minti biyar tana buga ƙofar kafin ya buɗe fuskarsa a cure yana ƙoƙarin toshe hanci
cike da tsammanin zai sake cin karo da warin waken. Ƙamshin da ya ji yana tashi a falon ya
saka shi sakin fuskarsa riƙe da ƙofar ya zuba mata kallon tuhuma ba tare da ya ce komai ba.

"Ka yi haƙuri, tun ƙarfe ɗaya na rana na gama abincin shi ya sa waken ya buga."

Abin da ta faɗa ya sa ya bar jikin ƙofar ya raɓa ta gefenta ya nufi ɗaya daga cikin kujerun ya
zauna yana faɗin,

"Zo ki zauna mu kammala maganar da muka fara, saboda ba ba so kina wahalar da kanki a
kaina daga yau."

Jiki babu kuzari Minal ta nufi kujerar kusa da wadda yake kai ta zauna a ɗarare. Ƙirjinta yana
bugawa ta shiga sauraron maganganunsa masu kama da ɗigar dalma a jiki.

"Duba da yadda aka yi aurenmu da yadda zaman ya zo mana. Yana da kyau kowa ya san
matsayinsa saboda gudun shiga haƙƙin juna. Don haka daga yau kada ki sake saka abinci da
ni. Ki dafa iya cikinki ba sai kin ajiye mini ba...ke ko da ina gida ban ce ki dafa da ni ba. Saboda
ina da inda nake cin abinci ba na son ɗora miki nauyin cikina."
Shiru ya ratsa tsakani a lokacin da ya tsahirta da maganar sannan ya ɗora da cewa, "Kin
amince za ki zauna da ni a matsayin abokin zama ba miji ba?"

Minal ta wurga masa wani kallo cikin ƙunar zuciya sannan ta yi magana da sanyin murya ta
ce, "Zan zauna da kai a bisa umarnin mahaifiyata. Sannan zan ci gaba da riƙon ka kamar
yadda Nur ta ba ni ajiyar ka, har zuwa ranar da ta dawo gare ka."

Sai da ya yi shiru yana nazarin ta kafin ya sake cewa, "Batu na gaba, tun da kin ji kin gani kina
buƙatar mu ci gaba zaman da muke kai; to duk abin da ya biyo baya kada ki tuhume ni. Saboda
ni ban shirya zaman aure da kowace mace ba. Kuma ina kan bakana kamar yadda na sha faɗa
zan maimaita, da Nur kawai na tsara rayuwa da ita zan yi zaman aure. Amma tun da ƙaddara ta
haɗa mu zama ni da ke ba zan bari mu cuci juna ba. Don haka daga yau ba zan sake shiga duk
abin da ya shafe ki ba, ki yi rayuwarki ni ma zan yi tawa. Kada ki ga na ɗaga miki ƙafa tausayin
ki kawai nake ji, amma idan ke kin zaɓi ci gaba da zaman a haka babu damuwa. Sai dai kafin
nan zan ba ki dama ta ƙarshe don kafa shaidu, gobe idan Allah Ya kai mu zan kai ki gidanku a
yi komai a gaban iyayenki."

Zumbur ta miƙe zuciyarta tana harbawa ta shiga juyi a gabansa cike da jarumta ta ce, "Dube
ni da kyau Jamal, daga halittar jikina har halayena babu abin ƙyama. Don haka ban ji haushi
don ka nuna ban kai matsayin ka yi zaman aure da ni ba. Saboda haka na zaɓi bin umarnin
mahaifiyata da riƙe amanar da Nur ta bar mini duk da zuciyata ba ta farinciki."
Sheƙeƙe ya dinga ƙare mata kallo har ta gama tumbuɗin maganganun bakinta. Murmushin
takaici ya yi kafin ya ce "Ki daina yaudarar kanki, ko da mazan duniya ke son ki ni ba kya cikin
tsarin matan da nake so. Kuma zan dawo da sabgogina da nake yi tun kafin haɗuwa ta da Nur,
alƙawarin da na yi mata kuma zan riƙe amma ba zan fasa yin abin da zai rage mini sha'awa ba
tun da ta iya tafiyarta ta bar ni. Saboda haka duk abin da kika ga na yi a cikin gidan nan ido ne
naki. idan kin gaji da irin zaman kawai ki sanar da Hajiyata, ita ce za ta sa na sauwaƙe miki a
duk lokacin da kika buƙaci hakan."



Akwai littafina DAKAN ƊAKA...na fara ɗora shi ArewaBooks. Kuma akwai complete book 1-2 1k
ga mai buƙatar ya taɓo ni ta nan; 08022014771.

D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*LAMBA SHA BIYU.*

Wani ƙololon baƙinciki ya tokare mata a maƙoshi. Saboda maganganunsa ba ƙaramin ƙuna
suke yi a zuciyarta ba. Amma da ta tuna ita da nata shirin, hakan ya sa ta yi murmushin takaici
ta ce,

"Har kullum ina yi wa Allah godiya da babu saka hannuna a cikin ɓatan Nur. Saboda haka idan
ma ka ɗauki haƙƙina Ubangiji Yana kallo kuma ba zai bar ka ba."
"Duk abin da za ki faɗa kina da damar hakan a yau kuma a yanzu. Amma ki sani daga gobe
damarki ta wuce matuƙar kin amince da sharuɗɗaina."

"Uhumm!"

Iya abin da ta faɗa kenan tare da miƙewa zuwa ɗakinta. Kallo ya bi ta da shi cike da mamakin
yadda ta zaɓi zama da shi duk da tarin ƙalubalen da za ta fuskanta. Jiki babu kuzari ya yi
ɗakinsa zuciyarsa cike da kewar Nur da irin alƙawurran da ta ɗaukar masa idan sun yi aure.

'Me ya sa kika bar ni bayan kin san saboda ke na shiryu? Me ya sa za ki bar wa wata ni bayan
kin sani ba zan so ta ba?'

Zancen zucinsa kenan saboda gabaɗaya kewarta ta addabi ransa. Kwana ya yi yana juyi
saboda sha'awar da ta yi masa mugun kamu. Duk da maganin da ya lalubo da ƙyar ya gan shi
ya kora da ruwa yana rawar sanyi. Amma hakan Bai nutsar da shi ba har daren ya yi nisa,
zuciyarsa sai hango masa Minal take yi amma yana ƙoƙarin kawar da kansa a matsayin
haramtacciya gare shi. Don ya gama keɓe ta a cikin matan duniya waɗanda zai iya yin
mu'amalar aure da su.
Ɓangaren Minal kuma kwana ta yi a kan sallaya tana kai wa Allah kukanta. Ita ma ba ta yi
wani barcin kirki ba sai Bayan sallar asuba nannauyan barci ya yi awon gaba da ita.

Washegarin safiyar dukan su babu wanda ya tashi da wuri. Misalin karfe goma na safiya ta jiyo
motsin buɗe ƙofarsa, a lokacin tana tsaka da shiri bayan ta tashi da ƙyar ta yi wanka. Don ranar
ba ta yi tunanin yi masa gwaninta ba ballantana ta yi asubancin shiga kitchen. Saboda ita ma ba
ta tashi da son cin komai ba, kasanacewar ta dafa indomie bayan Jamal ya shige barci, sai da
ta ci ta yi ƙat a

9 / 26