Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
yana ƙoƙarin fita Amina kuma
tana ƙoƙarin komawa cikin ɗakinta.
"Ta zauna, sai dare zan dawo na ɗauke ta."
Jamal ya yi maganar cikin sauri saboda bai shirya komawa da ita a lokacin ba. Innarmu ta yi
saurin washe baki tana faɗin,
"To ai shikenan. Tun da ka bar ta yi mana wunin. Amma da ba ka bar ta ba; ƙafa da ƙafa za ka
koma da ita."
Yana murmushi ya yi gaba, Baba ya raka shi har ƙofar gida yana saka masa albarka. Yayin da
suka bar Innarmu dafe da ƙirji saboda ƙaƙƙarfan bugun da yake yi mata babu ƙaƙƙautawa.
Sosai hankalinta ya tashi da jin wata sabuwar magana daga bakinsu, wadda ba ta san da ita
ba. Tsabar ruɗewa kuɗin da ya ba ta ma a nan ta bar su. Jikinta yana rawa ta isa bayan ƙyauren
gidan a sukwane. Sai da ta sha jinin jikinta sannan ta shiga leƙen su ta wata kusufa, tana
hangen duk abin da yake faruwa daga inda take. Sai dai ko kaɗan ba ta jin me suke tattaunawa
a kau. Har suka gama magana Jamal ya fito da kuɗi daga aljihunsa, kamar yadda ya ba ta shi
ma haka ya miƙa masa. Cike da jin nauyi Baban ya ƙi karɓar kuɗin sai da ƙyar Jamal ya ci
kansa ya karɓa yana godiya, sannan ya ƙara saka masa wata sabuwar albarka bayan addu'ar
gamawa da duniya lafiya.
Sai da ya tayar da motarsa ya tafi bayan sun yi sallama, sannan Baban ya koma cikin gidan
a daidai lokacin da Innarmu ta isa bakin ƙofar ɗakinta, inda ta fara haɗa kan kuɗin bayan ta bar
jikin ƙyauren cikin sauri gudun ya kama ta. Don sun saba, a duk ranar da ya gan ta tana leƙen
wa'azin yake zuba mata, sai ta gaji da sauraro ta biye shi sun koma yin faɗa.
Yana ƙoƙarin shigewa ɗakinsa, da niyyar ɗaukar abin da ya dawo da shi gidan. Innarmu ta
biyo shi baya tana cewa,
"Ni kam Malam wai wane irin alƙawari ne ka yi wa mijin Amina ban sani ba?"
Juyowa ya yi yana kallon ta kamar ba zai ce komai ba, amma sanin wace ce ita ya yi magana
fuskarsa a cure ya ce,
"Ina ruwanki."
"Uhum, ko ma dai mene ne ai ya kamata na sani Malam. Saboda ko an dafa a ɓoye ai ba za a
ci ɓoye ba. Don yana da kyau a ce duk wani abu da ke faruwa ka sanar da ni. Idan dai har abin
nan ya shafi Amina."
Murmushin takaici ya yi kafin ya ce, "Idan kuma bai shafe ta ba fa? Shi ma dole sai kin sani?"
Sum-sum ta bar wurin tana cewa, "Allah Ya ba ka haƙuri, ai da ma can na sani ba ka ɗauke
ni a bakin komai ba."
"Ke dai kika sani."
Ya yi maganar yana ci gaba da abin da yake yi, sai da ya gama sannan ya rufe ɗakinsa yana
ƙwala wa Amina kira. Cikin sauri ta fito ta durƙusa gabansa tana faɗin,
"Ga ni Baba."
Tsayuwarsa ya gyara, sannan ya dafa bango ya yi jim na ɗan lokaci kafin ya ce, "Na so na je
har gidanki na yi wasu maganganu da ke. Amma na ƙyale ganin Salame ma ta isa ba sai na je
ba. Don haka kafin na ce komai zan ce ki ji tsoron Allah, kuma ki sani aure ba wasar yara ba ne.
Kada ki yi duba da yadda auren ya zo ki ce za ki yi wa sunnar Ma'aiki riƙon sakainar kashi. Miji
miji ne kuma wajibi ne girmama babba ko da a gidan mashaya ne, ballantana tsakanin mata da
mijinta. Saboda haka ki riƙe aurenki tsakani da Allah kuma ki riƙe mijinki za ki ga ribar hakan a
gaba. Amma ki sani ban ce ki shiga rayuwarsa da bin diddigi ba kamar yadda kika ga Binta tana
yi ba. Saboda kowane namiji da kalar halinsa, idan ita tana yi mini ina ƙyalewa shi ba lalle ne ya
ƙyale ki ba idan kika kwashi halinta. Don haka shawara ce na ba ki, amma ban ce dole sai kin
bi b..."
"Haba Malam! Yanzu shikenan idan ka tashi yi wa 'ya'yanka faɗa ko nasiha ba za ka naɗe
tabarmarka salun alun ba har sai ka saka ni zama bis...?"
Innarmu ta yi maganar ranta a ɓace kafin ya katse ta. Saboda tun da ya fara maganganun ta
saka wa zuciyarta sai sun yi faɗa, don dole sai ya sako laifinta ko kuma ƙarara ya nuna
takaicinsa a kan wani halinta a fakaice.
"Nononki da ta sha nake tsoron ya yi aiki a gidan aurenta. Don muddin ta biye wasu halayen
da kike gwadawa a cikin gidan nan; ba lalle ne halin ya bar ta zama gidan mijinta lafiya ba.
Saboda kin fi kowa sanin yadda aka yi auren, kuma an yi sa'a yaron ya san darajar manya. Ya
kamata a ce ita ma an zaunar da ita an faɗa mata darajar aure ta wuce sanin da ta yi masa."
Ya tsahirta da magana, su ma suka yi shiru babu wanda ya iya cewa uffan. Saboda Innarmu
ruwa ya ci kai, duk da ta gaji da abin da faɗan da yake yi mata a gaban 'ya'yanta. Shi ya sa sau
da yawa tana son gyara wasu abubuwan amma hakan ba zai hana ta sake kwatawa ba.
"Yanzu dai ka yi haƙuri, in dai don na yi tambaya a kan maganar da kuka yi ne; Allah Ya huci
zuciyarka. In sha Allah daga yau ba zan sake tayar da zancen ba. Amina kuma ina fatar ta yi
zaman aure managarci wanda za ta samu aminci tsakaninta da mijinta, ba irin zamana da kai
ba. Tun da har yanzu ban wuce cin fuska da gugar zana a wurin ka ba."
Nufar hanyar fita ya yi ba tare da ya ce mata komai ba. Saboda ya jima da sanin daɗin
bakinta, kuma in da sabo ya saba da halinta. Ta iya yin laifi kuma ta koma yi masa dabaibayi da
maganganun da komai yake son ɗaurkar mataki a kai sai ya sassauta.
Illa maganar da ya yi wadda ke nuna da Amina yake yi. Inda ya juyo yana faɗin,
"Tashi ki je, Allah Ya yi miki albarka."
Daga haka ya fice ya bar su jugum kuma tsaye cirko-cirko a tsakar gidan. Innarmu ce ta
kawar da shirun da cewa, "Ni fa wallahi sai dai Malam ya ga laifina, amma ba na fatar A'isha ta
dawo garin nan ta zauna da mu kamar baya. Saboda muddin ta dawo ba za ki taɓa samun
nutsuwar da za ki samu lada a gidan mijinki ba. Sai inda ƙarfina ya ƙare a kan haka, don ba zan
taɓa bari ki zamo bora ba. Wahalar da nake sha a gidan nawa mijin ta isa, ke kam daɗi za ki ji
da yardar Allah."
Fuska a cure Amina ta ce, "Innarmu..."
"Yi mini shiru Amina. Ba fa zan zuba ido a saka mu kunya biyu ba. Kina kallo babu kalar
surutun da ba a yi mini ba a kan auren nan naki. Amma duk na shanye zagi da ƙazafin da ake yi
mini saboda farincikin kin samu gidan hutawa. To a kan me zan zuba ido A'isha ta dawo
rayuwar mijinki ki koma bora? Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai a yi duk abin da za a yi amma
zama daram ke da shi sai mutuwa. Duk wani ɗan baƙinciki sai dai ya mutu...ke ko ke kika kawo
mini gangancin da auren nan ya lalace wallahi sai na ɗauki mataki kanki. Shi ma ina ɗaga masa
ƙafa ne saboda a zauna lafiya amma ba wai don ina jin tsoron sa b..."
"Don Allah Innarmu ki yi shiru haka nan. Ba na jin daɗin yadda kike sako Babanmu a
maganar nan, saboda shi ma yana so na zauna inda hankalina zai kwanta. Ni ma kuma na yi
alƙawarin zama da shi komai tsanani sai inda ƙarfina ya ƙare. To me ya rage kuma Innarmu?"
Nan take murmushi ya bayyana a kan fuskar Innarmu tana cewa, "Da kin taimaki kanki.
Amma muddin kika tsaya kallon ruwa kwaɗo zai yi miki ƙafa. Sannan ko ma wane alƙawarin ne
sai na gano shi, don ba zan zuba ido hannun agogo ya dawo mana baya ba..a kan me..ba zai
yiwu ba...da sake."
Haka Innarmu ta ci gaba da mitar maganar har ƙannen Minal suka dawo makaranta. A nan
suka baje ana ta hirar yaushe gamo da bai wa juna labarin abubuwan da suka faru. A nan Minal
ta ji labarin an hana kowa zuwa gidanta har ƙannenta. Saboda surutu da gulmar auren da ake
ta yi a cikin unguwa da danginsu. Inda aka ɗauki laifin kacokam aka ɗora wa Innarmu, sannan
ita ma aka ce ta ci amanar Nur tun da ta ƙwace mata saurayi. Ɓatan Nur ma cewa aka yi
Innarmu ce ta yi mata kurciya saboda ta yi nisa da inda aka san ta. Surutai kala-kala kuma duk
sun dawo wa Innarmu har shi Babban. Amma kasancewar sun san yadda aka yi auren ko
kaɗan hakan bai tayar musu da hankali ba.
Hakan ya sa Innarmu ta sha ɗamarar babu wata mace a gidan Jamal sai Amina. Shi ya sa
har dare ya yi tana ta maimaita mata zance ɗaya, "Kada ki kuskura ki yi abin da kika ga ina yi a
cikin gidan nan. Ni ma wani lokaci ba don ina so ba nake yi. Don haka ki bi Allah ki bi aurenki.
Sirrin mijinki ki rufe kuma babu ke babu kai ƙarar sa. Idan ma ya cuce ki ki bar shi da Allah shi
ne zai saka miki."
Da ire-iren waɗannan nasihohin ta cinye wunin. Don Innarmu ta hana ta zuwa gidan kowa a
cikin unguwar har maƙota. Saboda saɓanin da ya faru a kan gutsiri-tsomar da ke shiga suna fita
a tsakanin mutanen unguwar tasu. Hakan ya sa ta bushe fitilarta a kan duk uban da ya haɗa
auren ya raba idan ya isa.
Amma har ƙarfe takwas na dare Jamal bai zo ɗaukar ta ba. Innarmu ta matsa ta kira shi a
waya ta ce masa shi take jira. Ba don ta so ba, haka ta ɗaga wayar ta kira shi, amma har ta
tsinke bai ɗaga ba. Mintuna a tsakani sai ga saƙonsa ya shigo a kan ta nemi adaidaita sahu ta
koma bai gama abin da yake yi ba. Har ta fara surutan ɓacin rai a kan ba za ta koma ba a nan
za ta kwana, Innarmu ta tusa ƙeyarta gaba har zuwa bakin titi. Da kanta ta taro mata abin hawa
ta shiga, bayan ta biya ta sake yi mata gargaɗi da jan kunne a kan ta riƙe aurenta hannu biyu.
Haka suka rabu ƙannenta suna ɗaga mata hannu har suka miƙa titi. Tafiya ɗoɗar suka yi
kafin su isa unguwar misalin ƙarfe tara saura minti shida na dare. Da kwatance har adaidatan
ya kai ta ƙofar gidan, bayan ta fito jiki babu kuzari ta nufi bakin gate ɗin tana ƙwanƙwasa
ƙaramar ƙofar. Maigadi ya buɗe mata bayan ya gama yade fuskarta tas da fitilarsa mai mugun
haske. Cike da mamaki ya yi hanzarin faɗin,
"Hajiya da ma ba ki dawo gidan ba ashe?"
Dariyar yaƙe kawai ta yi masa, a lokacin da ya saki ƙofar ta shiga ta hango motar Jamal a
mazauninta. Alamun yana cikin gidan, kuma ya dawo amma ya kasa biyawa ya ɗauko ta.
Zuciyarta a cunkushe ta nufi hanyar shiga cikin gidan tana ƙara danne ɓacin ranta saboda tuno
nasihohin da ta sha, wuni zungur ana yi mata bitar haƙuri da biyayyar aure. A kan haka ta saki
ranta har ta haye sama ta tura ƙofar shiga falon cike da karsashi.
Dam-dam! Sautin bugun ƙirjinta kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal kwance saman
kujera, ya yi matashin kai da cinyar wata mace suna kallo tamkar miji da mata. Hankalinsu a
kwance sai dariya suke yi alamun suna jin daɗin yanayin.
SANARWAR!
INA NEMAN MUTUM MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE
1K GA MAI BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA
WATAN FEBRUARY. LABARI NE MAI ƊAUKE DA RIKICI, HARGITSI, TASHIN HANKALIN DA
RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON SOYAYYA.
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Dsn5IB2qqtYAG3EDJ04sce
*Assalamu alaikum*
*Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?*
*Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?*
*Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar
kasuwa; Rukayya Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids
clothes. Kitchen Ware's. Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.*
*Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.*
*LAMBA SHA HUƊU.*
Tsaye ta yi tsawon sakonni tana ƙare musu kallo, zuciyarsa ɗauke da kalmar Innalillahi wa
inna ilaihirraji'un. Kafin ta cira ƙafafuwa babu kuzari ta fara taku gumi yana tartsatso mata a jiki.
A haka ta isa tsakiyar falon daidai ta gabansu ta ja ta tsaya idonta a kansu, zuciya ta shiga nuna
mata ta cakumo macen ta rufe ta da duka kawai. Yayin da wata zuciyar ke yi mata kashedin
babu ruwanki gidansa ne kuma shi ya kawo ta.
Zumbur macen ta yi ganin Minal tsaye a gabansu cikin tsoro ta kalli Jamal a firgice ta ce,
"Babe, da ma kana da mata amma ka ce na zo gidanka na taya ka kwana?"
"No, wannan ba matata ba ce. Kada ki wani damu ki tayar da hankalinki a banza. Idan za ki
zauna kawai ki zauna gidana ne ina da ikon kawo duk wanda nake so."
Daga haka ta faɗa jikinsa ya shiga shafa ta yana shinshinar ta tana faɗin,
"Ohhhh... baby ina son...ka."
Nan take Minal ta fara ganin dishi-dishi jiri yana kwasar ta ta yi hanzarin barin wurin da
sassarfa kafafuwanta suna harɗewa. A haka ta nufi bakin ɗaki jikinta Yana rawa ta murɗa ƙofar
cike da jarumta, sannan ta tura a hankali ta shige tare da mayar da ƙofar ta rufe ruf har da
makulli.
Tsaye ta yi jikin ƙofar bayanta jingine kanta a sama yayin da wani zafafan hawaye ya shiga
bin fuskarta wani bayan wani. Saboda jin sautin dariyar da suka bi bayanta da ita babu
ƙaƙƙautawa. Tsawon lokaci tana haka kafin ta samu kuzarin furta La haula wala ƙuwwata illah
Billah. Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Haka ta yi ta faɗa a fili da cikin zuciyarta, faɗa take yi
tana maimaita kalmomin cikin saurin murya. Kamar almara jarumta ta yi mata lulluɓi, don cikin
ɗan lokaci ta samu wani ƙarfin zuciya da nutsuwa suka sauka jikinta.
Ta bar jikin ƙofar ƙirjinta yana harbawa ɓil-ɓil ta shiga zare kayan jikinta. Ta ɗaura towel
kenan da nufin shiga wanka, ta fara jin ana ƙwanƙwasa mata ƙofa. Kamar kada ta kula, don
jikinta ya ba ta Jamal ne kuma babu abin da zai faɗa ta saurare shi. Amma a haka wata zuciyar
ta ba ta umarnin je ki buɗe ki ji me ya kawo shi. Cikin ƙunar zuciya ta isa bakin ƙofar ta buɗe,
abin mamaki babu Jamal sai matar da ta gani tsaye ƙiƙam. Suna haɗa ido ta yi hanzarin juya
bayanta tana kallon Jamal ta ce,
"Babe ka faɗa mata da kanka."
Da ido Minal ta bi Jamal ɗin da kallo tana jiran ta ji me za a faɗa mata. Daga can inda yake
zaune ya yi Magana cikin isa ya ce,
"Indomie take so ki dafa mata. Kuma kada ta yi yaji kada ki bar ta ta ƙame ruwanta ya
tsotse."
Mamaki ya so kashe Minal a tsaye, bakinta a sake ta shiga ƙare wa Zee kallon sama da ƙasa
riƙe da ƙofa a hannunta. Kafin wani tunani ya faɗo ranta ta yi wani murmushin ba zata a kan
fuskarta ta ce,
"Ok, yanzu ake so ko za a jira na yi wank...?"
"Je ki yi wankan. Ita ma za ta fi jin nutsuwar cin abincinki?"
Kafin ma ta kai ƙarshe ya ba ta amsa, tana ƙoƙarin mayar da ƙofar ta rufe Zee ta yi hanzarin
daka tsalle tana buga ƙafa cikin shagwaɓa ta ce,
"Babe, ni ba zan bari ta yi wankan ba ka ce ta je ta dafa mini a hakan yunwa nake j...."
"Ahhhh sorry sorry...je ki