Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
"Duba da kanki, sai kin tabbatar ke ce ko za a ɗauki matakin da ya dace da ke."
Nur ta yi maganar cikin wata kalar murya tana dariya tare da miƙa wa Zulaiha wayar ta ƙi karɓa.
Saboda ta gama sarewa da lamarin Nur, kuma ta karɓi laifinta ba tare da wahalar da shari'a ba.
Don ƙin karɓar wayar bai hana ta furta kalaman da ke nuna ta aikata abin da Nur ke tuhumar ta
ba. Saboda kai-tsaye ta haɗe fuska tana haɗiyar yawu tare da goge gumin da ke feso mata a
kan fuska ta ce,
"Idan ma ni ce ai ba ki san dalilin da ya sa na aikata ba. Sannan kuma duk ƙoƙarin da kike yi
a kan so. tozarta ni ba ki isa ki ce guba ce na zuba ba. Don haka ko ina aka je zan faɗa ba guba
na zuba masa a cikin abincin ba, idan kuma kina tantama yanzu zan ci abincin don ki tabbatar
ba na kisa, kuma babu niyyar a cikin rain..."
"Yi mana shiru!"
Shugabar Restaurant ɗin ta buga mata tsawa cikin tsananin ɓacin rai, hakan ya ta shanye
sauran maganar da ba ta gama amayowa ba. Ta shiga sosa kai tana muzurai duba da yadda
wurin ya cika da mutane kowa yana kallon ta.
"Kin ba ni kunya Zulaiha. Yanzu duk halaccin da na yi miki da irin wannan sakayyar za ki yi
mini? Ki tuna lokacin da kika zo wurin gwanin ban tausayi kina neman aiki na ɗauke da zummar
taimakon ki. Ashe tsintacciyar mage ce ke wadda ba ta mage! To daga yau kin daina aiki a
wurin nan, kuma zan koya miki hankali a kan ɓacin sunan da kika jawo wa masana'antata.
Wadda na rayu da ita sama da shekara goma cikin gaskiya da rufin asirin Allah. Amma a yau
kina neman lalata mana tsari...to ba ki isa ba..ranka ya daɗe a tafi da ita kawai har zuwa lokacin
da zan neme ku."
Hajiya Inno mai abinci, ta ƙare maganar fuskarta a cure saboda ɓacin ran da Zulaiha ta
ƙumsa mata.
"Don Allah Hajiya ki yi haƙur..."
"Babu wani haƙurin da zan yi da ke, saboda lokacin da kika shirya munaƙisarki ban sani ba.
Kuma idan na bar ki ban san iya wanda za ki cutar a sanadin aikin ba. Gara kawai ki tafi hannun
jami'ai su sanar da ke bambancin riƙon amana da riƙe gaskiya tsakani da Allah."
Ihu Zulaiha ta fasa a daidai lokacin da ta ga 'yansanda sun zagaye ta.
"Babu wani shaiɗan! Ai ba yau kika fara ba. Kin jima kina yin abin da kike so kawai asirinki ne
yau ya ton.."
"Ko aljana ce ke sai na ga bayanki wallah.."
Zulaiha tana maganar ta yi kan Nur cikin zafin nama da nufin kai mata bahagon mari, sai dai
kafin ta isa ta fara jin ɓarin makauniyar kalolin mari a kan fuskarta. Hakan bai yi masa ba sai da
ya yi cikin ta da harbin ƙafa yana ta ƙwallo da ita, yayin da aka samu majiya ƙarfin da ke wurin
suka rirriƙe shi, inda ya fara aman magana cikin matsanancin fushi yana nuna ta da hannu yana
faɗin,
"Duk ranar da hannunki ya sauka a jikinta da sunan duka sai na jijjige shi a mazauninsa na
wurgar. Kuma ko da wasa na sake ganin ki a inda duk nake sai na ɗauki mummunan mataki a
kank..."
"Wallahi ina son k.."
Zulaiha ta yi maganar cikin kuka tare da ɗaga murya a lokacin da 'yansanda suka kai mata
wawuya tana ƙoƙarin tashi ta yi kansa.
"Allah Ya tsine wa irin wannan son naki da babu komai a cikin sa face haɗari. Don abincin da
kika zuba masa da ya ci Allah ne kaɗai ya san me zai faru, saboda kin saba cutar mazan
mutane don ba yau kika fara haɗa musu tarko ba. A tunaninki kin isa da kanki saboda bokayen
da kike biya suna yi miki ƙulunboto kina wasa da rayuwarsu, hakan ya aa kika zaton shi ma za
ki yi nasara a kansa? Kin kuskure, don kin yi shuka a idon makwarwa. Saboda duk abin da kika
tura wa 'Yan Ajin Tubarakallah Group duka na gani kuma na ji duk zagi da cin zarafin da kika yi
kuma kika sa aka yi wa Minal. Sannan na bi diddiginki na gano shirin da kike ƙoƙarin yi a kansa,
wannan dalilin ya sa na hana kaina zama har sai da na tabbatar na kama ki da laifin hannu
dumu-dumu. Saboda ki gano ba kowane lokaci Allah yake dafa wa mutum a kan zalunci ba.
Kuma ina so na karya alkadarinki ko don ki gano ba a fi kare iya kwanciya ba sai dai a nuna
masa lulluɓi da bargo. Sannan faɗuwa tana farawa ne daga ba zan iya ba, amma ke taki
faɗuwar ta fara ne tun daga lokacin da kika yi iƙirarin tabbatar wa duniya cewa, kin kai kuma kin
isa wanzar da duk abin da kike so kuma a lokacin da kika ga dama. Ina miki fatan hakan ya
zamo babban darasin da za ki tuba ki dinga bar wa Allah komai tun kafin mutuwa ta ɗauke ki
kina zaluntar mutane."
Daga haka 'yansanda suka wuce da Zulaiha tana muzurai bayan sun saka mata ankwa, ta yi wa
Nur wani kalar kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa tare da ƙwafa tana cije leɓe.
Nur ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ta kai kallonta ga Hajiya Inno, minti biyu bayan
wucewar 'yansandan da Zulaiha, ta sake cewa,
"Na gode sosai Mama, da kika ba ni damar gano gaskiya a kan wannan baiwar Allah.
Ubangiji Ya ƙara girma kuma ya ƙara yi wa kasuwa albarka da ma'aikatanki gabaɗaya. Ni zan
wuce saboda jirgin ƙarfe biyar zan bi na koma gida."
"Babu komai 'yata Allah Ya yi miki albarka, kuma Ubangiji ya kai ki gida lafiya, tun da na karɓi
lambarki ai za mu dinga zumunci."
Taku ɗaya biyu ta yi da nufin ficewa daga Restaurant ɗin Jamal ya yi hanzarin riƙo hannunta.
Kallon kallo suka shiga yi wa juna tsawon sakonni kafin ya yi jarumtar faɗin,
"Ina za ki je?"
Cike da mamaki ta bi shi da kallo bakinta a sake tana cewa, "Zan koma gida ne, saboda na
gama aiwatar da abin da ya kawo n..."
"Ba zai yiwu ba! Ke ma kin sani ba zan bar ki ki sake yin nisa da ni ba."
Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce, "Kada ka dawo da hannun agogo baya, saboda yanzu da
inda aka fito akwai bambanc.."
"Na fahimci bambancin da kike nufi tun a ranar da kika gudu kika bar ni. Kuma a yau zan
tabbatar miki babu inda za ki je ballantana ki koma gudu na. Na yarda na amince ba kya so na,
amma hakan ba zai sa na yi sakacin da za ki sake kufce mini ki ɓace wa idona b..."
"Har da idan na sanar da kai ni matar wani ce?"
Wayyo
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA BIYAR.*
"Wani? Wani fa kika ce!"
Shiru ta yi masa maimakon amsar da yake jira. Nan take ransa ya yi ƙoluluwar ɓaci ƙirjinsa ya
shiga harbawa cikin sauri. Kafin ya haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya masa
maƙwagwaro ya sake cewa,
"Yanzu ni kike faɗa wa ke matar wani ce? Yanzu ba ki ji kunya da nauyin idona ki kalle ni ki
furta mini irin wannan maganar ba?"
Ya yi maganar cikin wani kalar sauti mai cike da laushi bayan ƙwalla ta cika masa idanuwa taf.
"Gaskiyar kake so na ɓoye maka?"
Hannu ya saka ya bugar da ƙwallar da ke ƙoƙarin gangarowa a saman fuskarsa sannan ya
jinjina kai yana cewa,
"Tabbas sai yau na ƙara tabbatar da ba kya so na. Don haka ki je ki zauna da wanda kika
zaɓa a madadina. Alhamdulillah na samu Minal a yadda ban yi tsammani ba, ko iya haka na
sani Allah Ya mini kyakkyawar sakayya a kan abin da kika aika min...ki je..ki je..kawai...matar
wani ko? Humm...ya yi kyau."
Ya yi maganar tare raɓawa ta gefenta yana tafiya da baya da baya idonsa a kanta yana sara
mata. Saboda matuƙar mamakin da ta ba shi, tare da zafin kishin ta da ke caccakar zuciyarsa.
Maganganunsa da tafiyarsa sun saka kukan da take jarumtar ɓoyewa ya fallasa ƙuncin da ke
cin ranta. Don hawaye ya dinga bin fuskarta shaa tana ƙoƙarin haɗiye amma ya ƙi tsayawa. A
haka ta bi bayansa da sassarfa daidai lokacin da ya isa inda ya ajiye motarsa yana ƙoƙarin
buɗewa ya shiga.
"Jaaan!"
Ta kira shi da sunan da ta saba kiran sa. Kiran da ya sa tsikar jikinsa ta tashi yarr kafin ya ɗaga
kai ya kai kallonsa a kanta. Tafiya ta ci gaba da yi zuwa inda yake jiri yana ɗibar ta tare da
dishi-dishin da take gani. Amma hakan bai hana ta isa gabansa ta durƙusa gwiwa biyu ba, kafin
ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo tana cizon leɓenta. Tsawon minti biyu tana haka
kanta a sunkuye ba tare da ta ɗago kai ko ta furta abin da take son furtawa ba. Shi ma idonsa a
kanta ko ƙiftawa babu zuciyarsa cike da jin haushin ta bayan mahaukacin kishin ta da ke kartar
ransa.
"Sauri nake yi. Na baro matata a gida babu lafiy..."
Ya yi maganar cikin ƙunar rai, tare da nuna mata shi ma ya ɗau zafi a kan furucinta. Sai da ta
zuƙe majinar kukan da ke yunƙuro mata, sannan ta yi jarumtar goge hawayen idonta, tare da
haɗiye ɓacin ran da ya cusa mata. Zumbur ta miƙe tsaye daidai lokacin da kira ya shigo
wayarta. Da hanzari ta fiddo ta a jaka ta ɗaga kiran, saƙon da aka isar mata a cikin wayar ya sa
ta magana cikin sauri.
"Ka jira ni, in sha Allah yanzu zan ƙaraso kafin lokaci ya cika."
Ta katse kiran tare da kai kallon ta a kan agogon hannunta tare da cira kai zuwa kan fuskar
Jamal, ido cikin ido suka dinga kallon juna, sai da ta sauke ajiyar zuciya sau biyu kanta a
sunkuye kuma rungume da hannuwanta a ƙirji, sannan ta sauya akalar zancen da ta so furtawa
a farko, cikin murmushin yaƙe ta ce masa,
"Ni zan wuce jirgin da zan bi ya kusa tashi, idan ka je gida ka gaishe da matarka."
Tana ƙare faɗar hakan ta juya cikin takunta na taƙama kamar koyaushe ta nufi bakin titi iska
yana kaɗa ta. Kallo ya bi bayanta da shi hawaye yana bin fuskarsa saboda wani kalar tashin
hankalin da ya dira kansa cikin zaucewa ya ce,
"Har abada, ba zan fasa kallon ki a matsayin wadda ta cutar da rayuwata ba, matuƙar ba ki
sanar da ni laifin da na yi kika yi kyauta ta ga Minal ba. Sannan ki sani duk taku ɗaya idan kin yi,
tamkar tafiya da numfashina ne kike yi. Don muddin kika tsallake ƙasar nan kika sake bari na
kamar yadda kika yi a farko, to ina tabbatar miki kafin ki isa inda za ki je za ki ji saƙon
mutuwat..."
"Jaaann!" Ta kira sunansa tare da juyowa babu shiri, a cikin wani matsanancin firgicin da ya
bayyana kan fuskarta. Ta dawo jikinta yana rawa cikin matsanancin fushi ta isa gabansa tamkar
kububuwa. Idonta a rufe ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari, hawaye yana bin fuskarta ta fara
nuna shi tana magana cikin kuka tamkar ta shiɗe.
"Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaan kuma har a gaban Allah. Amma
wallahi! Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan
kai ma ka sani wallahi ina son k..."
Ta ƙare maganar tare da fashewa da wani mahaukacin kuka, tare da faɗawa jikinsa ta
rungume shi tsantsan tamkar za a ƙwace mata shi. Tsawon minti huɗu tana jikinsa tana ta rera
kalolin kukan da ya ƙara raunata ɗan kuzarin da ya rage masa a jiki da zuciya. Saboda ya
sandare wuri ɗaya ko motsi ya kasa yi, amma idanuwansa ba su daina ɓarin hawayen da ke
malala a kan fuskarsa ba.
Duk da tarin jama'ar da suka tara wa kansu ba tare da sun sani ba. Kamar yadda surutan da
mutanen suke yi a kansu bai sa sun hankalta sun dawo nutsuwarsu ba.
"Woww! An burge ni... Billahillazi an tashi kaina!"
Ire-iren waɗannan maganganun aka shiga yi, tare da bidiyo da hotunan da ake ta ɗaukar su.
Saboda yanayinsu ya fallasa su a matsayin masoyan da suka samu saɓani, sannan kuma
waɗanda ba son rabuwa da juna.
"Lafiya 'yata? Me ya faru?"
Zancen Hajiya Inno mai abinci kenan, a lokacin da aka sanar da ita cincirindon da aka yi mata
a bakin Restaurant. Cikin rawar jiki ta fito gudun a ƙara jaza mata wata fitinar bayan zafin abin
da Zulaiha ta yi mata ko hucewa bai yi ba, wanda ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin ma'aikatanta
da customers har ya so ya koma musu wata sabuwar hatsaniya.
Hajiya Inno ta jawo Nur a jikinta fuskarta a yamutse tana ƙara tambayar dalilin kukanta.
Musamman da ta hango hawaye a idon Jamal sai abin ya ƙara ɗaga mata hankali. Cikin rawar
murya ta sake jefa wa Nur tambaya a ruɗe tana faɗin,
"Kin..ga..kin..ga..don Allah ki sanar da ni abin da yake faruwa. Kalli mutane ki gani gabaɗaya
ku suke kallo! Me ya haɗa ki da shi ne? Ko duk a kan rikicin da aka gama a kan Zulaiha ne?"
Nur ta shiga girgiza mata kai a kan duk tambayoyin da take jera mata. Ranta a ɓace cikin
ɗaga murya ta sake cewa,
"To mene ne? Ki sanar da ni bakiɗaya an ɗaga mini hankali."
Nur ta ja hannunta da nufin su koma cikin Restaurant ɗin, babu musu ta bi ta tare da bai wa
Jamal umarnin shi ma ya biyo su. Rufe motarsa ya yi cikin sanyin jiki ya bi su jiri yana ɗibar shi
tamkar ya faɗi. Tsabar damuwar da yake ciki, a gefe ɗaya kuma tunanin halin da ya bar Minal a
ciki.
Wuri na musamman Hajiya Inna ta kai su inda babu zirga-zirga, bayan sun zazzauna ta kalli
Jamal cike da zaƙuwar jin abin da yake faruwa ta ce,
"Kai ne namiji, da kai zan fara. Duk da na san ka tun ba yau ba, amma ban san tsakaninku
ba, sai dai ga dukkan alamu akwai wata keɓantacciyar alaƙa a tsakaninku ba iya yadda ita 'yata
ta sanar da ni ba. Don ta faɗa mini kai mijin 'yar'uwarta ne, amma kuma yanayinku ya nuna ba
iya wannan alaƙar ce ta haɗa ku ba. Duba da yadda ta ce mini tun daga Niger ta zo nan saboda
kawai ta kare ka daga sharrin Zulaiha. Don haka idan kun ɗauke ni uwa kamar yadda nake yi
muku kallon 'ya'yan da na haifa, ku sanar da ni gaskiyar abin da ke tsakaninku idan har na
cancanci hakan."
Ku yi manage, jiki da jini yau an taɓo nawa file ɗin ni ma Minal ta sakar mini ciwon.
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA SHIDA.*
Ajiyar zuciya Jamal ya sauke mai ƙarfi kafin ya ɗora kallonsa a kan Nur ya ce, "Ban taɓa
tunanin za ki guje ni ba, saboda yarda da amincin da ke tsakanina da ke. Mun gina so da ƙauna
a cikin gaskiya da rashin ɓoyewa juna matsaloli. Amma sai dai ashe ni yadda na ɗauke ki ke a
wurin ki ba haka nan ba n..."
"Kallar ni da kyau ranka ya daɗe, ni za ka yi wa bayanin da na nema, ka ajiye wannan
zancen naku kamar zai fi dacewa a tsakaninku."
Zancen Hajiya Inno kenan a lokacin da ta ji maganar Jamal ta sauka daga layin abin da take
son ji. Murmushin takaici ya yi idonsa a kan Nur