Fansar Kauna Part 1 Hadiza D Auta

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   24 / 26

69K to 72K   out of 77.3K words

Tana maganar har ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ɗauke da wani ƙaramin kwando a hannunta.

"Ban ji ba ne Inna ai da na amsa miki, saboda barcin da ya fara ɗiba ta sai daga baya na ji
sallamar." Ta yi maganar tana runtse ido tare da cije leɓenta saboda yunƙurin tashin da ta yi
kafin ta shigo ɗakin amma ta kasa.
Bakin bed side Inna Ade ta zauna idonta a kan Minal cike da son tabbatar da abin da take zargi
ta ce,

"Allah Ya sa dai lafiya lau kike, don na ji muryar taki kamar ta marasa lafiya."

Murmushin dole Minal ta janwo a kan fuskarta sannan ta ce, "Ƙalu nake Inna, kawai dai ɗan
zazzaɓi ne ya kafce ni cikin dare har sai da aka yi mini allurai."

"Allah Sarki matar yarona, ashe Hajiya ta canka daidai. Don takanas ta tayar da ni na zo
saboda kawai na kawo miki abin da ta dafa miki. A cewarta ma, jikinta ya ba ta kina can kina
kewar ta, ko iya wannan zai sa ki Yi zazzaɓin. Sannu kin ji, Allah Ya ba ki lafiya, amma za ki iya
tashi ko na taimaka miki don ki ci abincin. Saboda ta ce na saka ki gaba har sai kin cinye komai
na dawo mata da kulolinta."

Murmushi Minal ta yi mai sauti, cike da Jin daɗi a ranta ta ce, "Ɗan kama ni dai Inna, jikin ne
nawa ko'ina ciwo yake yi. Ga bakina babu daɗi kamar na yi sati ina jinya."

Ta ƙare maganar tana cije leɓe Inna ta ɗago ta a hankali cikin dabara ta kai ta jikin gadon ta
ɗora mata a bayanta ta jingina. Cike da tausaya wa ga halin da take ciki ta sake ce mata,

"Wannan ciwo ya buge da yawa matar yarona, na ji jikin naki da zafi rau har yanzu kamar
zazzaɓin bai gama sauka ba."

Shiru kawai Minal ta yi cike da jin nauyin ta a ranta, saboda jikinta ya ba ta kamar ta gano
abin da ya faru, tana biye ta ne kawai a yadda take so.

"Me kike son ki fara ci? Akwai farfesun kaji, akwai na kayan ciki da kuma taliyar Hausa."

Minal ta yi murmushi sannan ta ce, "Haɗa mini ruwan tea kawai Inna, saboda bakina babu daɗi
ba zan iya cin komai ba."
Kitchen Inna Ade ta tafi cikin sauri ta haɗa mata tea mai kauri don ta zabga mata madara.
Sannan ta nemo plate guda uku mai faɗi da masu zurfi biyu, tare da cokali ta dawo ɗakin. Cikin
kulawa ta miƙa mata kofin shayin tana fara sha ta koma zuba mata taliyar da Hajiya ta dafo
mata da hannunta, a gefe ɗaya kuma tana ta jera mata sannu. Sai da shanye shayin tas
sannan Inna ta karɓi kofin ta miƙa mata plate ɗin taliyar ta karɓa tana faɗin,
"Kaɗan zan ci Inna saboda Hajiya ta ji daɗi, amma ko kaɗan ba na jin son cin abinci bakina
babu ɗanɗano."

"To ki ci ko ya yake ya fi rashin cin." Kaɗan ta tsakuri taliyar Inna Ade tana matsawa har ta ci
rabin plate sannan ta karɓi plate ɗin ta ɗauko wanda ta zuba mata farfesun kajin da suka sha
dafuwar ruwa sai ƙamshi ke tashi. Minal ta karɓa yawunta yana tsinkewa ta fara ci tana faɗin,

"Wannan daɗin duk ni kaɗai Inna?"

Inna Ade tana 'yar dariya ta ce, ni ma umarnin kawowa kawai aka ba ni matar yarona, yadda
kika gan shi a haka na gani don Hajiyar ce ta yi komai da kanta. "Ubangiji Ya saka mata da
mafificin alherinsa." Ta yi maganar cikin muryar kuka tana goge ƙwalla da bayan hannunta,
saboda har zuciyarta mutuncin Hajiya a idonta ya yi girman da dole sai ta zubar da hawaye. "Kuka kuma?" Inna ta yi maganar tana 'yar dariya bayan ta gama faɗin amin. Minal ma ta yi
dariyar bakinta a washe ta ce,
"Abin da Hajiya take yi mini ko mahaifiyata ban samu wannan darajar a wurin ta ba. Don
haka ban san da wane baki zan ce mata na gode b..."

"Abu ɗaya za ki yi mata ki faranta ranta, idan kin riƙe mata yaro tsakani da Allah. Da kin yi
hakan shikenan kin gama biyan ta, don iya abin da take so kenan a wurin ki kada ki sake barin
wasu mata su ɗauke masa hankali. Babban burin Hajiyar kenan, wanda ya sa take sadaukar da
komai nata a kan samun wannan biyan buƙatar."
Shiru Minal ta yi tsawon mintuna tana nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Da yardar

Allah zan riƙe shi irin riƙon da wata mace ba ta isa ta sha gabana a wurin sa ba. Kuma na yi wa
kaina alƙawarin zan yi haƙuri da halinsa ta yadda komai zai yi mini zan jur...."

'Nur fa?' Tsam ta yi da ranta a lokacin da Inna Ade take zuba mata ruwan albarka, ita kuma
zuciyarta ta tafi tunanin ba za ta iya jurar ganin sa da Nur ba. Za ta iya haƙuri da shi a kan
komai amma babu shirgin da ya kwaso Nur a ciki. Don ko sunanta ta tuna ƙirjinta faɗuwa yake
yi, ballantana ta tsunduma tunanin rayuwarsu kafin lokacin aure har zuwa shagalgulan bikin da
ranar da aka kawo ta cikin gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da kai kallonta ga Inna
Ade tana murmushin yaƙe, tare da faɗin,

"In sha Allahu Inna." Saboda duk abin da take faɗa ba ta ji komai ba sai ki riƙe mijinki da take
ta nanatawa a bakinta. Bayan ta gama jera mata kalolin nasihohi a kan haƙuri da zaman aure
da zama jajirtacciya a kan kowace irin matsala. Cikin dabara Inna ta ja hankalinta suna ta hira
har ta kusan cinye duka ferfesun da ta zuba mata sannan ta sha romon duka. Cike da jin daɗi
Inna Ade ta laƙume sauran taliyar da ta rage, kuma lashe sauran abin da ta rage na ferfesun ta
je ta wanke komai da aka ɓata, tare da juye mata da sauran taliyar da ke kula da ferfesun a
nata kalolin sannan ta yi sallama da ita da niyyar tafiya.
Minal ta roƙi alfarmar ta haɗa mata ruwan ɗumi a bahon wanka, sannan ta taimaka mata ta
yunƙura da ƙyar ta kai ta toilet, cikin ƙarfin hali Minal take takawa tare da ƙarfafa zuciyarta a kan
jin sauƙin dole kafin Jamal ya dawo, don ta ci burin yi masa sabuwar kwalliyar da idan ya gani
zai yaba ita ma ta ji daɗi. Hakan ya sa ta ɗauki tsawon mintuna a toilet ɗin tana gasa kanta har zuwa lokacin da ji ƙarfin
jikinta ya dawo. Sannan ta yi wanka tare da ɗoro arwala ta dawo ɗaki, inda ta ga Inna Aden
tana share ɗakin bayan ta gyare gadon tas kamar ba a taɓa kwanciya kansa ba.
A zaune ta yi sallar Zuhur da Asr ganin Inna ta fice daga ɗakin, kafin ta shafa addu'a ta koma
bakin madubi ta shiga tsara kwalliyar tarbon Jamal. Duk da wani gefen zuciyarta yana hango
mata rashin kyautawarsa a kan barin ta daga siyo abinci ya dawo har zuwa lokacin bai dawo
ba. Amma ta yi masa uzuri saboda yadda ya nuna mata kulawa kafin ya fita tana a ji a ranta bai
yi hakan da gangan ba, ta ɗora laifin a kan wataƙila wani babbab uzuri ne ya danne shi wanda
ya hana shi dawowa cikin lokaci.
Bayan ta gama shirin ta fito fes cikin wata sabuwar shadda golden colour mai ɗinkin
doguwar riga ɗauke da aikin baƙin zare da golden ɗin. Sannan ta feshe jikinta da turaruka tana
baza ƙamshi ta fito falon ganin Inna a falon kwance.
Fitowarta ya sa Inna kai kallonta a kanta tana faɗin, "Ma sha Allahu tubarakallah! Yarona ya
yi sa'ar mace mai tsada a gidansa."

Murmushi kawai Minal ta yi ta isa inda wayarta take caji tun daren jiya har lokacin. Sai dai
ganin ta a zare zuciyarta ta tabbatar mata Jamal ne ya cire bayan cajin ya cika.
Zama ta yi da wayar a hannunta bayan ta kunna musu Tv tana 'yar dariya tare da faɗin,
"Alamu ya nuna Inna kin fi son yaronki a kaina."

"Kamar yadda Hajiya ta fi son ki a kansa Kenan!"

Gabaɗaya suka saka dariya, daidai lokacin da ta hau WhatsApp ƙarar saƙonni suka dinga
shigowa cikin wayarta. Kacokan hankalinta ya koma a kan wayar, musamman saƙon wata
ƙawar Nur da ya ja hankalinta kai-tsaye inda take tambayar ta,

"Yaushe Nur ta dawo?"

Ƙirjinta ya buga dam-dam, cike da jin haushi ta fita daga saƙonta ta koma bin groups amma
hakan bai hana ƙirjinta ci gaba da bugawa ba. Ranta a ɓace ta koma Tiktok tsabar haushin
tambayar da Summy ƙawar Nur ta yi mata. Ta shiga Tiktok da niyyar ganin abubuwan da za su
rage mata takaicin Summyn, sai dai kamar haɗin baki tana shiga da bidiyon Jamal da Nur ta ci
karo inda suke rungume da juna suna kuka.
Babu shiri ta zaro ido har da goge su da niyyar gani daidai kada a ce gizo ne suke yi mata.
Hannunta a ƙirji ta bi comments inda take jin kalaman yabawa da jinjinawa a kan irin zazzafar
soyayya. Cikin sauri ta fita bidiyon ta ja shi sama wanda ya biyo bayansa ma su ne a lokacin da
Nur ta kwaɗa masa mari tana kuka tana faɗin,
"Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaaan kuma har gaban Allah. Amma
wallahi! Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan
kai ma ka sani wallahi ina son k..."

Faɗawar da ta yi a jikinsa ya yi daidai da zaburar Minal tsaye, dafe da ƙirjinta da ke dakan
kuguden tara-tara idonta a kafe kan wayar cikin fitar hayyaci tana faɗin,

"Tabbas ba zan iya haƙurin zama da shi ba! Saboda kishin ta zai iya kai ni ƙiyama babu shiri
matuƙar abin da na gani ya tabbata!"

"Innalillahi mene ne kuma ya faru?"

Inna da ke kallo kalaman Minal suka farauto hankalinta da ke kan Tv. Zuwa gare ta. Da sauri
ta isa gabanta da niyyar riƙe ta daidai lokacin da Minal ta wurgar da wayar ta daki bango ta
tarwatse ɗaiɗaya.
Tashin hankali wanda ba a saka masa rana, Minal ta shiga ihu da kururuwar faɗin,

"Sai na kashe ta! Wallahi sai na kashe ta!"

Ta yi maganar cikin ƙaraji tamkar wadda aljanu suka taka kanta. Ta shiga fisge-fisge da niyyar
ficewa falon zuwa barin gidan Inna Ade tana rirriƙar ta cikin tashin hankalin ita ma. Don tsabar
hana Minal fita har zaninta ya kwance ta koma daga ita sai buje amma ko kaɗan hakan bai
dame ta ba. Da ƙyar da gumin goshi Inna Ade ta samo kan Minal da kalaman Innalillahi wa inna
ilaihirraji'un da Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Tana yi tana maimaita a bakinta tare da taro
Minal har ta zube ƙasa ta fasa yunƙurin fitar tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar wanda ya
saurara.

"Ba zai yiwu ba! Inna ba zai yiwu na zuba ido Minal ta kassara mini rayuwa ba! Wallahi Wallahi
sai na kashe ta! Enough is enough! Abin da ta yi mini ya isa ya isa haka nan Inna! Ba zan
lamuci wasa da zuciyar da take son yi mini ba! Na rantse da Allah ni ce nan zan kashe ta da
hannuna!"
"Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Waɗannan lafuzan ba su yi daɗi ba, ko kaɗan
ba furucin mumini mai imani ba ne."
Maganar Inna Ade kenan a lokacin da ta samu ta rufe ƙofar falon da makullin da ke jiki ta
zare makullin a cikin kwagirinta ta mayar da zanenta ta ɗaura. Tsabar firgici da tashin hankalin
da Minal ta saka ta. Hakan ya sa cikin sauri ta ɗaga waya ta kira Hajiya, babu ɓata lokaci ta
sanar da ita ta zo gidan babu lafiya. Sannan ta katse kiran ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun ta yi tagumi. Don har lokacin ba
ta san a kan wace ce Minal ta haukace ba. Amma jikinta ya ba ta budurwar Jamal ce wadda ta
yi wa dukan kawo wuƙa har Hajiya ta kore ta gidan ita kuma ta dawo da ita hannunta. Tunanin
da take yi kenan a ranta saboda Hajiya ta sanar da ita komai kasanacewar ta ɗauke ta 'yar'uwa
kuma abokiyar shawara.



Tabbas yanzu aka fara

GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.


D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA TAKWAS.*

Tsawon awa ɗaya Hajiya ta ɗauka kafin ta isa gidan Jamal , amma tsawon lokacin Minal ba
ta daina kukan da take yi ba. Saboda kaiwa maƙura har jakar kayanta ta haɗa Inna Ade tana
rarrashin ta a kan ta jira sai Hajiyar ta zo a san abin yi, amma hakan bai hana ta harhaɗa duk

abin da take so a jakar ba. Duk da ba ta yi wata maganar da ke tona asirin zuciyarta a kan
makomar aurenta da Jamal ba. Amma haɗa kayan da ta yi ya bayyana wa Inna Ade manufarta
da shirin barin gidan da take yi. Ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi ya sa Inna Ade fita daga ɗakin
cikin sauri ta buɗe ƙofar. Kallon juna suka yi da Hajiya dukan su fuskokinsu ɗauke da damuwa.
Don kai-tsaye Hajiyar ta nufi ɗakin Minal zuciyarta a tsinke, saboda tunanin da ta zauna kansa
ɗaya ne, a kan cewa Jamal ya ɓarke 'yar mutane saboda ya ji daɗin wuri. Cike da tsoron abin
da zai je ya dawo, gudun hakan ya jawo musu surutun jama'a a gari, idan har zancen ya fita.
Sai dai abin mamaki, tana tura ƙofar ɗakin ta hango Minal tsaye a tsakiyar ɗakin rungume da
hannu tana jijjigar jiki. Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyar Hajiya, duk da hankalinta bai gama
kwanciya ba musamman da ta hango jakar kayanta a gabanta. Sannan yanayinta ya nuna babu
lafiya duba da kiran gaggawar da Inna Aden ta yi mata. "Amina, me ke faruwa ne?"

Nan take ta fashe da wani sabon kuka tare da durƙushews ƙasa ta ƙanƙame jakar kayanta
tare da ɗora kanta saman jakar tana ta rero kukan. Shiru Hajiya ta yi na ɗan lokaci kafin ta yi
tattaki zuwa wurin ta cikin sanyin jiki da bugawar ƙurji falfal.

"Ki faɗa mini abin da ya faru, saboda ni uwa ce gare ki ba suruka ba. Kada ki ji kunyar komai
ki sanar da ni ko ma mene ne zan yi maganin abin idan ina da ikon yin hakan."
Ta yi maganar tare da tayar da ita zuwa bakin gado suka zauna. Kallon yatsunta Minal ta
dinga yi kafin ta gama zuƙe-zuƙen majinar kuka ta ce,

"Nur ta dawo, kuma Jamal yana tare da ita yanzu hak..."

"Anya dai Amina gaskiya ce kika faɗa?" Hajiya ta yi maganar fuskarta a cure kuma idonta a
kanta cike da son tabbatarwa.

"Wallahi-wallahi ba ƙarya na yi musu ba! Suna can suna yawo a cikin garin nan har da yin bidiyo
kala-kala suna watsawa a social media."

"To ke wa ya zo miki da wannan labarin?"

"Da idona na gani suna kuka tare da faɗa wa juna kalaman soyayy...."

Ta ƙare maganar cikin wani sabon sautin kukan da ya so bai wa Hajiya dariya, amma dole ta
fuske tare da ƙarfafa kanta tana faɗin, "Ki kwantar da hankalinki, in dai ni ce na haifi Jamal da
cikina ba zai taɓa auren A'isha ba. Ya dai je ya gama bidiyon da kalaman soyayyar ya dawo ya
iske ni, don babu inda zan je ina nan har sai ya dawo gidan nan ya same ni." Minal ta yi tsam da ranta tana wasa da yatsunta tare da share hawayen idonta da gefen
hannunta jefi-jefi tana ajiyar zuciyar kuka.

"Hmmm! Ni dai Hajiya ina da wata shawara, idan da hali ki hana ta yin wani furuci a bakinta.
Saboda ni dai kam gaskiya na ji tsoron abin da ta faɗa kafin ki zo, don ta tabbatar mini da lalle

sai ta kashe ita A'ishar da ake magana a kanta, kuma ta ce lalle ita ce ajalin ta."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Lalle ire-iren waɗannan maganganun suna da hatsarin gaske
Amina! Don Allah ki daina

24 / 26