Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
wani abu da zai fallasa komai har ya gano kalar wainar da ake toyawa. Duk da
zuciyarsa ta gama ba shi satar amsa a kan Jamal ne kawo abin da duk ya haddasa komai.
"Aikin bincike na na ɗauko ko aikin tsaron ƙofa da gadin gida?"
Jamal ya yi maganar a fusace saboda jin haushin shisshigin da yake son yi masa a cikin
gida.
"A'a ranka ya daɗe?"
Ya yi hanzarin amsawa yana ja baya tare da ranƙwafawa alamun girmamawa gare shi.
"To ka tsaya iya aikinka."
Jamal ya yi maganar cikin haɗe girar sama da ta ƙasa tare da barin wurin ya koma cikin gidan
zuciyarsa a ƙuntace.
A kan babbar kujerar falon ya faɗa yana shafa kansa cikin matsananciyar damuwa. Sai dai
duk ya rufe idanuwansa Minal yake gani a cikin shigar ƙananun kayan da ta yi wa Zee
barazana. Idan ya buɗe idon kuma ta koma yi masa gizo yana hango ta da towel iya cinya tana
taku bom-bom ɗin ta suna ta juyawa.
"Ya Salam! Wai me ke shirin faruwa da ni ne?"
Ya furta maganar a kasalance a lokacin da ya isa inda yake hangen ta da sassarfa da nufin
kamo ta ta ƙarfi, ko da zai rage nauyin abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Sai dai wayam ya ji ya
kamo banza babu komai a wurin sai ginin da ya ci karo da shi ya buge hannunsa da Zee ta
gatsa wa cizo. Babu shiri ya bar wurin dafe da hannun ya faɗa ɗakinsa. A gurguje ya yi wanka ya fice gidan
zuwa wani babban Chemist. A nan aka yi masa dressing czon, saboda shatin haƙoran Zee
ruɗu-ruɗu har fatar ta tashi sosai.
Bayan an gama rasa inda zai nufa ya yi, dole ya ƙare rabin wuninsa a wani restaurant. A can
ya ci abincin rana har dare ya zo ya sake cin abincin sannan ya nufi gidansa.
Daren ranar kwanan takaici ya yi yana tsaki, saboda ganin ya yi uku babu. Zee ta tafi Minal
kuma Hajiya ta ɗauke masa ita, Nur kuma ta yi masa nisan da bai san ina zai je ya nemo ta ba.
Juyi ya shiga yi saboda ji yake yi kwanciyar ba ko kaɗan ba ta yi masa daɗi.
***
Minal kam kwana ta yi mai daɗi har da minshari. Saboda zuwanta gidan cikin wuni ɗaya ta
gano tsabagen kirkin Hajiya. Don gaba ta saka ta a kan sai ta cinye abincin da ta zuba mata,
dare ma haka aka yi ita ta bai wa zaɓin abin da take so a dafa. Cike da jin nauyin Hajiyar ta yi
shiru tana sunne kai ta ce,
"Babu abin da ba na ci, kuma komai aka dafa zan ci."
"Kada fa ki takura kanki. Sannan duk abin da kike so ki faɗa mini kada ki ji nauyi."
Bayan sun gama kallo a falo Hajiya ta kai ta ɗakin Amna inda aka ajiye mata jakar kayanta.
Ta ce ta zauna a nan tun da Amnar ta koma makaranta. Kuma ta yi duk abin da take so a cikin
gidan babu mai takura ta, sannan ta ɗauka tamkar cikin gidansu take gaban Innarmu. Kuma
duk abin da take so idan ta yi ra'ayi kawai ta dafa, idan ma babu kayan haɗi ta sanar da ita za a
nemo a kawo mata. Fitaa idan ta yi sha'awa yi ta sanar da ita ba sai ta nemi Jamal ba.
Minal ta shiga jin daɗin asirin Jamal da ya tonu da wuri Hajiya ta ga komai da idonta,
sannan da gatan da take nuna mata tamkar 'yar da ta haifa da cikin ta. Hakan ya sa ta ci
alwashin kafin ta bar gidan sai ta ƙara wa Hajiya ninkin ƙaunar da take yi mata a cikin ranta.
Tun da asuba ta fara gyaran ɗakin Amna sannan ta wanke toilet ta koma gyaran babban falon
Hajiyar. Sai da ta share ko'ina ta ƙwalƙwale tsaf sannan ta sauya zaman kujerun daidai tsarin da
take so. Gari yana fara washewa ta faɗa kitchen cikin zafin nama ta shiga haɗa musu abin kari,
saboda ganin komai yana ajiye a mazauninsa, babu abin da za ta tambayi Hajiya. Ko da Hajiyar ta fito riƙe da baki tana mamakin ayukan da Minal ta yi a cikin duhun asuba
zuwa ƙarfe takwas na safiya.
Ƙamshin da ke dukan hancinta ya sa ta nufi kitchen ɗin zuciyarta cike da jin daɗi, saboda halin
kirkin Minal ya burge ta matuƙa. Har ƙasa Minal ta durƙusa cikin ladabi tana yi wa Hajiya ina
kwana, fuskarta cike da walwala ta amsa mata tare da saka mata albarka, kafin ta gyara
tsayuwarta da carbi a hannunta ta ƙara cewa,
"Kin hana idonki barci kina ta wahalar da kanki Amina."
"Babu komai Hajiya. Ai kaina na yi wa."
"To, Allah ya yi albarka."
Hajiya ta juya ranta fes ta koma falo ta zauna tana nazarin gyaran da Amina ta yi wa falon. A
ranta ta ce,
'Yarinyar kirki.'
"Hmmmmm!" Ta sauke ajiyar zuciya saboda tuno Jamal da irin sagegeduwar da yake ƙoƙarin yi
wa kansa. Amina ta haɗa komai a tire ta kawo wa Hajiya, daidai lokacin da 'yar aikin Umma Ade
ta shigo gidan suna gaisawa da Hajiya.
Amina ma cikin girmamawa ta rusuna ta gaishe da ita, sannan ta koma kitchen ɗin. Umma
Ade ta biyo ta tana faɗin,
"Amarya, da kin jira na zo wannan duka aikina ne. Yau ma wani jikana ne muka tashi da shi
babu lafiya shi ya sa ban yi sammakon da na saba yi ba."
Amina tana harhaɗa kayan da ta ɓata da nufin wankewa ta ce, "Ki yi zamanki kawai Umma
Ade, tun da na zo gidan ai ni ce mai yin komai.."
"Ba za a yi haka ba! Ba ni kwanonin kawai na ƙarasa aikin, ke ki je ki huta ai kin yi mai wuyar."
Ganin da gaske Umma Aden ba za ta bari ta yi aikin ba ta ɗebi nata abin karin ta shige ɗakin
Amna cike da jin kunyar Hajiya. Saboda ba ta son zamanta falon ya takura Hajiyar, kuma ita ba
za ta sake ta yi karin yadda ya dace ba.
Bayan ta gama karin ta faɗa wanka, cikin ɗan lokaci ta shirya da ɗaya daga cikin kayanta na
gida. Saboda lokacin da ta haɗa kayan gabaɗaya babu kayan Nur ko ɗaya a cikin jakar. Iya
nata kawai ta ɗauka, don ta ci alwashin bar mata kayanta kamar yadda suke har zuwa lokacin
da za ta waiwayi abin ta.
Misalin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na safiya, Jamal ya yi parking motarsa a harabar gidan
Hajiya. Zuciyarsa cike da fargaba a kan irin tarbar da za ta yi masa, bayan ta yi masa kashedin
kada ya zo mata cikin gida ba ta buƙata. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shiga babban
falon, a inda ya fara yin tozali da Minal ita kaɗai zaune a cikin falon tana kallo, gabaɗaya
hankalinta ya tafi a kan wata diramar da ake yi Bollywood. Ƙirjinsa ya buga dam-dam, amma
cikin basarwa ya raɓa ta gefenta ya wuce zuwa ɗakin Hajiya fuu tamkar bai gan ta ba.
Ita ma sai da ta ji motsin mutum hankalinta ya kai kansa yana ƙoƙarin shigewa ɗakin Hajiyar.
Ƙirjinta ya dinga faɗuwa don ta firgita sosai da ganin sa tsidik, saboda sallamarsa ma a ciki ya yi
ta ballantana ta ji shi ta amsa.
"Ummmm!" Ta yi wani abu da baki sannan ta ci gaba da kallon amma hankalinta ko kaɗan ba
ya wurin. Don ta rasa nutsuwar da take da ita kafin zuwansa. Haka kawai ta tsinci kanta da
tausaya masa don a kallo ɗayan da ta yi masa ta fahimci babu walwala a tattare da shi kuma
ba ya cikin jin daɗi.
Mintuna a tsakani ta fara jin sautin Hajiya tana faɗa, kafin ta ji ƙarar buɗe ɗakinta tana ba shi
umarnin ya fice mata daga ɗaki ba ta buƙatar ganin shi. Kamar an ingiza Minal ta zabura cikin
rawar jiki ta isa gaban Hajiyar ta durƙusa tana faɗin,
"Don Allah ki yi haƙuri Hajiyarmu. Kuma ki yafe masa ba don halinsa na san ba zai sake b...."
"Yi mana shiru baƙar munafuka bayan duk ke ce kika haɗa komai! Ai ina sane da ke kika kira
ta don ta tsine mini ki ji daɗi. To wallahi idan kika sake na riƙa ki sai na kakkarya mini ƙafafuwa
baƙar almura mai fuska biyu."
Idon Hajiya a kansa amma sai da ya gama amayar da abin da ke cikinsa. Saboda tunaninsa
gabaɗaya ya tsaya a kan Minal ce ta kira Hajiyar ba tare da ya sani ba. Minal ta shiga rantsuwar
ba ta kira Hajiya ba har da ƙwalla a idonta. Hakan ya sa Hajiyar ta yi hanzarin faɗin,
"Daina yi masa rantsuwa! In dai har da gaske ke ce kika kira ni na je kamar yadda ya faɗa; to
shi kuma dole sai ya yarda ke ce kika ɗauko masa hayar macen banzar, don kawai na gani ki
ɓata masa suna...wallahi Jamal ka fita idona na rufe! Kuma ka fice mini daga gida ka koma
wurin waɗanda suka fi mu daraja a idonk..."
"Hajiy..."
"Yi mini shiru sakaran banza! Allah Ya rufa maka asiri kana ƙoƙarin tona wa kanka....tashi ki
tafiyar ki don na fuskanci kwata-kwata ba gaskiya yake so ba."
"Ni dai don Allah ki yi mini haƙuri na tuba ba zan sake b...ke! Je ki faɗa wa Umma Ade yunwa
nake ji a ba ni abin kari."
Ya yi maganar alamun da Minal yake yi, tare da komawa kan ɗaya daga cikin kujerun falon
ya zauna yana canza channel daga Bollywood zuwa MBC Action. Wani kallo Hajiya ta yi masa
bayan wucewar Minal sum-sum kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki ta nufi kitchen. Ita ma
Hajiyar ta ƙarasa cikin falon ranta a jagule tana faɗin,
"Yanzu Jamal matar taka ta sunnah kake kira 'Ke'?"
Kansa kawai ya shafa, ba tare da ya ce komai ba. "Kowa dai ya yi mai kyau ya sani, kuma
hanyoyin zubar da girma da yawa suke, waɗanda duk mutum ya zaɓi bi a can zai ci karo da
gamonsa. Ina tausaya maka duk ranar da ka cika yarinyar nan ta fara boƙare maka za ka yaba
wa aya zaƙin ta."
A nan ma bai ce uffan, sai da Minal ta dawo ɗauke da abin karin ta ajiye masa tana ƙoƙarin
barin wurin ya yi jarumtar faɗin,
"Ko kaɗan ba na jin daɗin yadda kike ƙoƙarin yi mini baki koyaushe a kan wannan yarinyar.
Hajiya tun da ta shigo rayuwata kika daina tausayi na babu ruwanki ko mutuwa zan yi na je na
yi. Wannan dalilin ya sa ko kaɗan ba ta burge ni, saboda a kanta kike yi mini duk abin da kike
yi..."
"Ci abincin Kawu Bello! In dai wannan ne matsalarka daga yau ta zo ƙarshe. Da ma rashin jin
ka ne yake sa muke samun saɓani, amma idan za ka gyara ni me zai sa na yi maka faɗa
kawuna? Tun da kai ne uban ni ce ɗiya..."
Baki buɗe ya dinga kallon Hajiyar bayan ya guma lomar dankalin turawa a bakinsa. Babu
shiri wata kalar dariya ta kufce masa saboda kiran sa da sunan Kawunta. Nan take ya sarƙe ya
shiga tari cikin rawar jiki Hajiya ta shiga miƙa masa ruwa a ruɗe tana jera masa sannu. Bayan
ya sha ruwan dankalin ya faɗa masa yana murmushi ya sake cewa,
"Ashe dai har yanzu ɗiyar Kawu Bello tana so na."
Kansa ta dungure tana faɗin, "Kai dai daɗin girkin matarka ne ya ɗebe ka sarƙe."
"Wace matar?"
Ya yi tambaya cikin sauri, Hajiya ma ta amsa masa kai-tsaye ta ce,
"Amina."
Babu shiri ya shiga kakarin amai yana cewa, "Dole na sarƙe na ci abincin mayya."
Kuma dai
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta
nan 08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA BAKWAI.*
"Wace irin mayya kuma?"
Maimakon ya ba ta amsa, ya shiga kakarin amai tare da nufar hanyar ficewa falon
gudu-gudu sauri-sauri. Ya bar Hajiya riƙe da baki tana kallon sa da mamaki ɗauke a fuskarta
har ya fice. Yayin da wani zafaffen hawaye ya dinga bin fuskar Minal cike da takaicin tozarcin da
yake ƙoƙarin yi mata koyaushe. Bakin famfon da ke tsakiyar gidan ya tsaya yana ta faman wanke bakinsa, don ya gama
kakarin aman amma ya ƙi zuwa kamar yadda ya so. Sai da ya ja lokaci a wurin yana mayar da
numfashi, sannan ya koma cikin gidan yana ɓata fuska. Sauya mazauni ya yi a cikin falon dafe
da cikinsa yana faɗin,
"Wash Allah!"
Hajiya ta yi banza da shi kamar ba ta san ya dawo ba, hakan ya saka shi tsarguwa ya tashi
tsam ya koma kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta yana faɗin,
"Don Allah a nema mini wani abu na saka wa cikina Hajiyarmu, kin ga cikina babu komai a
cikinsa yunwa nake ji sosai."
Hajiya ta yi masa kallon uku kwabo sannan ta ƙwace hannunta tana faɗin,
"Me za ka yi da abincin mayu?"
Da hanzari ya rufe bakinsa saboda dariyar da ta kufce masa, saman kafaɗarta ya kwanta
cikin marairaice murya ya ce,
"Yarinyar ce ba ta iya komai ba Hajiyarmu. Shi ya sa ba na son cin abincinta. Amma ki yi
haƙuri don Allah a sama mini wani abin da zan ci fisabilillahi Hajiyarm...."
Hajiya ta ture kansa cikin ƙunar zuciya ta ce, "Wai har yaushe za ka daina halinka Jamal? To
daga ni har Ade babu wanda zai sake wahalar da kansa a kanka! Mu ma abincin mayyar muka
gama ci yanzun nan, kai kuma da kake tsoron a kama maka kurwa sai ka nemo waɗanda ba
mayu ba su ba k..."
"Hajiy..."
Cikin hanzari ta katse shi da cewa, "Ba fa za a sake dafa komai a cikin gidan nan ba, sai girkin
rana idan za ka jira. Idan kuma ka matsu kai da ba mayen ba ka shiga kitchen ɗin da kanka ka
nemo abin da za ka ci."
Ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi yana faɗin, "Allah sarki ni Jamal marayan Allah!"
Ya bar wurin yana sosa kansa ya nufi kitchen ɗin, zuciyarsa cike da son sake ganin Minal.
Amma tsabar bauɗaɗɗen hali irin nasa ko ƙofar ɗakin bai kalla ba ya wuce abin sa. Dam,
ƙirjinsa ya buga a lokacin da ya hango Minal cikin kitchen tana aiki. Turus ya yi fuskarsa babu
yabo babu fallasa ya gaisa da Umma Ade, sannan ransa a haɗe ya kalle ta ya sake cewa,
"Wai ke ko'ina kina nan?"
Minal ta yi banza da shi kamar ba ta ji abin da ya faɗa ba. Amma ta gama gano maganarsa
sarai da ita yake yi, sai dai ta ci alwashin sassauta wa kanta damuwa a kan halayensa. Hakan
ya sa ta ci gaba da markaɗa kayan miyan da take yi a cikin bulanda kamar ba ta san da shi ba
a wurin ba. Don duk da maganarsa ta ƙona mata rai har ta shige ɗaki ta yi kuka, amma hakan
bai hana ta sakin ranta ta koma kitchen taya Umma Ade aiki ba. Saboda zuwansa gidan ya sa
zaman falon ya fi ƙarfinta.
"Wai ke ba kya ji ina magana ne?"
Jamal ya sake yin magana yana matsawa kusa da ita cikin wata kalar murya, saboda ganin
Umma Ade ta fice daga kitchen ɗin ta bar su.
A nan ma banza ta yi masa tana ƙoƙarin zube kayan miyan, bayan ta gama markaɗawa a
cikin wata roba kamar ba ta san yana wurin ba. Saiti da bayanta ya tsaya zuciyarsa sai zillo
take yi masa tsabar sha'awar nan take