Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
takaicin baƙin kishinta da ke cin
zuciyarta.
Minal dai har lokacin tana tsaye a inda take ba ta fasa dariyar ba, kuma idonta a kansu suna
ta kokawa a ƙarshe abin ya koma faɗa a tsakaninsu. Saboda haushin Jamal ya hana ta isa
wurin Minal ta yi abin da ta yi niyya; ta ware haƙoranta ta gatsa masa wani mahaukacin cizo a
damtsen hannu. Zafin cizon ya saka shi yin tsalle tare da fasa ihu kafin ya sauke mata wani
lafiyayyen mari da bayan hannu. Cike da mamaki ta riƙe gefen fuskar tata inda naman
kumatunta ke rawa tsabar ƙarfin saukar marin tana kallon sa. Ta jima idonta a kansa bakinta a
sake kamar wata gaula, kafin ta ɗora hannu a ka ta fasa wata uwar ƙara ta faɗi ƙasa tana
birgima. Saboda takaicin tozarcin da ya yi mata a gaban Minal bayan don shi ta zo gidan,
saɓanin tunanin da ta yi a kan ya ci zarafin Minal kuma ya sauke mata ƙananun iskancin da ta
hango a tsakiyar kanta.
Jamal kam ɗakinsa ya nufa riƙe da hannun da ta gatsa masa cizon ransa a ɓace yana tsaki.
Minal ta ƙara fashewa da wata mahaukaciyar dariya tana tafa hannuwa, kafin ta faɗa a kan
ɗaya daga cikin kujerun falon tana ta dariyar mugunta har da riƙe ciki. Musamman da ta kalli
Zee a dunƙule tana gunjin kuka ta koma kallon jakar kayanta da ke yashe ga banza. Sannan ga
Jamal ya shige ɗaki, zogin cizo ya hana shi tsayawa a ƙarasa wasar.
Dariyar da Minal ke yi ta ƙara ziga Zee ta fusata, idanuwanta a rufe ta zabura tamkar wata
kububuwa tana huci ta yi kanta da duka babu ji babu gani.
'An zo wurin.'
Minal ta faɗa a ranta, don da ma can a shiryenta take a kan duk yadda ta faɗi rataya. Saboda
ganin Jamal ya bar ta daga ita sai ita jikinta ya ba ta Zee za ta kawo mata wani raini. Babu ɓata
lokaci ta saki ƙwanji suka yi ta kai wa juna duka.
Kaf! Kif! Kakakaf! Sautin doke-doken da suke yi kenan. Dambe ya kacame suka dinga
neman makasar juna, kowace da ƙudurin ta illata 'yar'uwarta. Kasancewar Zee tana da ƙiba,
Minal tana samun sa'ar kai ta ƙasa da ƙyar ta haye ruwan cikinta tana kai mata duka ta ko'ina.
Duk ƙoƙarin Zee da ƙarfin halinta; bai sa ta ɓanɓare Minal daga maƙalewar da ta yi mata ba
tana aikin jibgar ta inda duk hannunta ya je. Dole ta sa Zee fasa ƙara tana jera kiran sunan
Jamal babu ƙaƙƙautawa ganin da gaske Minal illata ta take son yi ƙarfi da yaji.
Ko da Jamal ya fito baki a sake ya dinga kallon abin da yake faruwa, kafin ya isa wurin a
fusace ya fisgo Minal cikin fushi ya wurga ta gefe tana haki. Ransa a matuƙar ɓace ya dinga
aika mata kallo cike da takaicin ganin ɓarnar da ta aikata wa Zee. Domin gabaɗaya ta sauya
mata fuska, bakinta jini hancinta jini. Hatta idanuwanta ajin jini ne a ciki saboda yakushe mata
fatar ido da Minal ta yi. Bayan kumburewar da fuskar ta yi sumtum a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
"Ke wace irin mahaukaciya ce ban sani ba? Kina ganin yadda kika mayar da yarinyar mutane
kamar babu imani a zuciyarki! To wallahi duk abin da ya biyo baya babu ruwana duk inda take
ta kai ƙarar ki za ta ja haƙƙinta a kan wannan rashin imanin da kika gwada mata... wannan ai
rashin hankali ne mai lasisi..kai jama'a!"
Ya ƙare maganar a firgice bayan ya ɗago fuskar Zee da ke kife cikin tashin hankali, ganin
jinin da ke zuba daga hancinta har ya ɓata gaban rigarta.
"Wallahi! Wallahi ko gobe wata kwartuwa ta zo gidan nan, kuma ta nemi ta dake ni sai na yi
mata abin da ya fi wannan..."
"Ko me ta yi miki ai bai kamata ki yi mata irin wannan aika-aikar ba! Don taƙamar ta zo cikin
gidan nan..ni na kawo ta kuma ba gidanki ba ne!"
Wani kallon uku kwabo ta yi masa kafin ta mayar masa da amsar cewa, "Kai da ka kawo ta
ma ka kwaɗa mata mari saboda ta cije ka. Sai ni zan zuba ido na ƙyale ta dake ni a banza? To
duk matakin da za a ɗauka kaina a ɗauka amma wallahi ban yi danasanin sauya mata fuska
ba...kai ko mutuwa ta yi a sanadin hakan Allah ba zai kama ni ba don kare kaina ne na yi. Tun
da ita ma ta so kashe ni ba don ka karɓe cokalin ba da ba a san me za ta aikata mini da shi
ba...to ta yi duk abin da za ta yi ina jira! Tun da ita kaɗai ce mai gata ni ce ba a bakin komai b..."
"Yi mini shiru mahaukaciya! Kin yi laifi kina yi wa mutane surutun banza."
Ya yi maganar a ƙufule yayin da ya tallafo Zee tana layi tare da ɗaga kanta sama yana
bubbuga goshinta cike da zummar jinin ya tsaya idan ma haɓo ne ta yi. Suna ƙoƙarin ficewa
daga falon Zee tana gunjin kuka a jikinsa aka turo ƙofar falon.
Dam-dam! Ƙirjin Jamal ya buga, saboda firgicin ganin Hajiya a irin wannan lokacin. Ita kanta
Minal sai da ƙirjinta ya buga, jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta da sassarfa. Da hanzari ta sauya
kayan jikinta da wata doguwar riga ta ɗaura ɗankakwalinta a ka ta fito. Saboda sautin Hajiyar da
ke tashi a sama tana faɗa ko'ina ana jin ta.
Amma mamakin ganin shu rungume da Zee bai hana ta isa falon ta zauna ba. Fuskarta a
yamutse ta dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya. don ganin ta ya yi saurin sakin Zee ya
rakuɓe gefe yana muzurai.
Zee kuma ƙasa ta zube saboda ƙafafuwanta sun yi sanyin da ba za su ɗauki gangar jikinta
ba. Don ganin Hajiyar ya sa ta shiga tashin hankalin da ya saukar mata kyarmar jiki, ta shiga
haɗiyar yawu tare da ƙara sautin kukanta wiwi.
"Macen banza har a cikin gidanka Jamal?"
Hajiya ta yi maganar cikin tsurewa, tsabar mamakin ganin abin da idonta ya yi tozali da shi.
"Ashe Allah Ya kawo ni ne rabon na ganar wa kaina irin ta'asar da kake aikatawa ba tare da na
sani b..."
"Wallahi Hajiya sau ɗaya ne...kuma yau ne kawai kin ga jakarta ma gida za ta je yanz..."
Jamal ya yi maganar a ruɗe saboda ta gama ganin komai, kuma bai san da wace kalma zai
musa mata ba. Kafin ta katse shi da salati tana tafa hannu alamun ya gama kashe ta da wani
mamakin.
"Ana ganin ta fasa mini baki da hanci amma ba za a yi ta kaina b...to wallahi idan na mutu duk
sai kowa ya yi bayani."
Zee ta yi maganar tana ƙara bajewa ƙasa tare ƙara sautin kukanta cikin matsanancin hali ta
koma birgima.
"Ke daƙiƙiyar ina ce da za ki zo gidan matar aure da mijinta ki yi tsammanin za ki fita lafiya
lau? To bari ki ji ko kashe ki aka yi ke kika jawo kuma babu wanda zai kai ki asibiti a cikin mu. Ki
tashi ki ja jakar kayanki ki fice tun kafin na haɗa ki da 'yan sanda su tafi da ke wallahi!"
Hajiya ta ƙare maganar cikin matsanancin fushi alamun ta kai maƙurar ɓacin rai. Zee ta miƙe
da ƙyar cikin tashin hankali tana layi ta ja jakarta kamar ta kifa da tangaɗi ta fice ta ƙofar falon.
Jamal ya bi bayanta da niyyar rage mata hanya ganin halin da take ciki.
"Kai kuma ina za ka je?"
Hajiya ta katsa masa tsawa cikin haɗe guyska ta jefo masa tambayar. Muryarsa tana rawa ya
ce,
"Rufe ƙofar zan yi idan ta fice."
"Rufe ka zo."
Ta sake magana a taƙaice kafin ta mayar da kallonta a kan Minal da ke rakuɓe jikin kujera
tamkar ruwa ya ci ta.
"Ke kuma..."
Dam ƙirjin Minal ya sake bugawa, saboda ta tsorata matuƙa da ganin yanayin Hajiyar.
"Allah ya yi miki albarka."
Wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyar Minal, saboda ta yi tsammanin ita ma za ta juye mata
fushin a kai ganin yadda ta ɗauki zafi sosai.
"Hakan da kika yi ya yi daidai. Gobe ma duk macen da ya sake kawo miki a cikin gidan nan ki
yi kaca-kaca da ita ni na ce! Don babu hukumar da za ta kama ki da laifin dukan macen da duk
kika kama da mijinki a cikin gidan aurenki. Saboda babu babban raini da wulaƙanci kamar
namiji ya kawo wata mace a gidansa ko da matarsa ba ta gidan ballantana tana ciki. Don haka
wallah Jamal duk yarinyar da ka sake ɗaukowa ka kawo ta a cikin gidan nan naka sai na nuna
maka haihuwar ka aka yi ba kai ka haifo kanka ba!"
Shiru ya ratsa falon saboda babu wanda ya iya motsin kirki daga shi har Minal ɗin. A lokacin
Hajiyar ta sake cewa,
"Amina kuma, tun da ba ka son ta; ka shiga ɗaki ka rubuto mini takardar sakinta ka ba ni
yanzun nan! Tun da ka isa da kanka sai ka yi duk abin da kake so! Don ba zan juri ganin kana
wulaƙanta 'yar mutane a banza ba. Idan ba ka so akwai dubunka waɗanda ma suka fi ka a
komai za su so ta kuma su yi zaman aure na tsakani da Allah da ita. Idan ka sauwaƙe mata sai
ka je ga ka ga matan banzan da ka fi so a kant...."
"Ni dai don Allah ki yi haƙuri Hajiya. Na san na yi kuskure kuma ba zan sake makamancinsa
ba. Da ma na yi ne kawai don na gwada ta."
Wani kallo ta yi masa kafin ta yi guntun tsaki ta sake cewa, "Gwaji? Da irin wannan rashin
mutuncin kake gwada matarka? Yanzu idan da ita ce ta gwada kawo wani a cikin gidanka za ka
kalli hakan a matsayin gwajin? A hir ɗin ka Jamal! Wallahi ina jiye maka tsoron ɓata rawarka da
tsalle a kan irin riƙon da kake ƙoƙarin yi wa Amina."
"Don Allah Hajiya ki yi haƙur..."
"Sai fa ka sake ta yanzun nan ba sai anjima b..."
"Wallahi Hajiya ba zan iya tsallake umarninki ba. Amma ki yi haƙuri zan zauna da Amina tun
da kina s..."
Wani kallo ta wurga masa wanda ya saka shi datse maganarsa. Cikin sauri ta miƙe tare da
gyara zaman mayafinta idonta a kan Aminar ta ce,
"Tashi ɗauko mayafinki mu je! Duk ranar da shi ya so auren da ke sai ki dawo gidan."
"To, Hajiya."
Amina ta amsa cikin sanyin jiki da na murya tare da tashi ta nufi ɗakinta. Kafin ta fito Jamal ya
isa gaban Hajiya ya durƙusa gwiwa biyu yana cewa,
"Ki ba ni dama ta ƙarshe Hajiya. In sha Allahu zan gyara duk abin da na ɓata da hannuna."
Banza ta yi da shi, duk da tausayin sa ya sa ta zubar da ƙwalla. Kuma ta so yin jarumtar hana
hawaye zuwa cikin idonta. Amma ƙoƙarinta bai hana ƙwallar zuba ba. Hakan ya sa Amina tana
fitowa ta ja hannunta suka fice. Ya biyo bayansu yana magiya amma ko waige ba ta yi ba
ballantana ta tsaya sauraron sa har suka fita harabar gidan, bakin motar da aka kawo Hajiyar
suka isa. Mazaunin baya ta buɗe mata sannan ta ce,
"Ina kayanki? Idan mun je ba yanzu za ki dawo ba, ki koma duk abin da kika san kina
buƙatarsa ki ɗauko shi mu je, ina jiran ki."
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta
nan 08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D. AUTA CE✍
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA SHIDA.*
Minal ta yi gaba da sassarfa a bisa umarnin Hajiyar na ɗauko kayanta. Caraf ta tuna jakarta
ma tana cikin boot ɗin motar Jamal. Cikin sauri ta dawo ta gefen da Jamal yake tsaye yana
muzurai don ya kasa furta ko kalma ɗaya. Hannuwansa a baya yana kallon ƙasa ya ji muryar
Minal tana faɗin,
"Jakata da ke motarka nake so."
Ta yi maganar a hankali saboda ba ta so Hajiya ta ji me take faɗa, gudun ta fahimci abin da ya
kai jakar kayan nata cikin motarsa ya ƙara yin wani laifin. Amma sassauta muryar da ta yi bai
hana Hajiya yin magana cikin ɗaga sautinta ta ce,
"Ke fa muke jira? Tsayuwar me kike yi a wurin?"
Inda-inda Minal ta fara yi tana sosa ƙeya, kafin Jamal ya yi hanzarin barin wurin ya isa inda
motarsa take ajiye yana faɗin,
"Ashe ta saka jakar kayanta a motata ba tare da na sani ba."
Wani kallon mamaki Minal ta bi shi da shi kafin wata kalar dariya ta so kufce mata. Saboda
ganin ya fuske ƙiri-ƙiri alamun da gaske abin da yake faɗa. Idon Hajiya a kansa har ya buɗe
boot ɗin ya ciro jakar ya nufi bakin motar Hajiyar ya ajiye yana sunne kai tare da kumbura fuska.
Cike da mamakin abin da ya kai jakar kayan a motarsa ta ce masa,
"Kai Jamal! Dube ni mu haɗa ido! Za ka faɗa mini dalilin zuwan jakar a cikin motarka ko sai
mun raba 'yan kallo da kai? Saboda jikina ya ba ni akwai abin da kake shiryawa ba tare da na
sani ba."
Gefe ya ja yana zarar ido tare da shafa bayan kansa yana faɗin,
"Ki tambaye ta Hajiya, idan ni na ce ta haɗa kayan ta saka a motar."
"Ba zan tambaye ta ba kai na tambaya! Amma ka bar amsarka don na gama gano komai.
Kuma hakan da ka aikata ba ƙaramin burge ka yi ba. Don haka na hutar da kai rage mata
hanyar zuwa gidansu da ka yi niyya. Da ma can zamana take yi kuma daga yau ta koma
hannuna. Kuma ko da wasa kada na ga ka taka ƙafarka zuwa inda nake....wuce mu je ke kuma!
Tun da ba za ki iya faɗa mini abubuwan da ke faruwa ba sai da idanuwana suka ganar mini
komai."
Ta ƙare maganar a daidai lokacin da take shiga motar, bayan ta zuba wa Minal ido har ta
shige motar ba ta daina furzar da abin da ke bakinta ba.
"Hajiya don Allah ki yi haƙur..."
Jamal ya yi maganar a lokacin da ya zuro kansa ta gilas saitin Hajiyar bayan ya marairaice
kamar mara lafiya.
"Ni matsa ka ba ni wuri! Gida ne an bar maka ka kawo duk wadda kake so. In dai gindi ne
kullum safiya sai an kawo sabon samfur a cikin duniya. Kuma duk ƙwarewarka ga iskanci wata
macen sai dai ka hango ta daga nesa ka bar ta. Don haka ya rage naka ka zaɓi rayuwar da duk
ka fi hangen za ta fisshe k....tafi mu je Malam Habu tun kafin zuciya ta ɗebe ni na yi abin da zai
dame ni daga baya."
Tana maganar tana zuƙo gilashin motar da ƙarfi ta rufe har tana ƙoƙarin dantse wa Jamal
hannu da gangan.
Minal dai ta sha jinin jikinta, har suka bar gidan maigadi yana ɗaga musu hannu ba ta daina
mamakin Hajiyar ba. Saboda ba ta taɓa tunanin ita ma ta iya masifa kamar Innarmu mu ba.
Ganin lokacin auren ba ta tsaurara wa Jamal kamar yadda ta yi masa yanzu ba.
Jamal kam ya jima tsaye a inda suka bar shi kansa a ƙasa, hannuwansa zube cikin aljihu
yana nazarin abin yi. Saboda ko kaɗan bai ji daɗin abin da Hajiyar ta yi wa Zee ba, hakan ya sa
ya ji ba zai iya neman ta ba ballantana ya tafi ganin halin da take ciki.
"Maigida akwai wani abun ne?"
Zancen maigadin gidan kenan yana 'yan duƙe-duƙen alamun girmamawa. Duk da zuciyarsa
cike take da son sanin abin da ke wakana a cikin gidan. Tun lokacin da Jamal ya zo da Zee har
zuwa lokacin da Minal ta dawo, kashe yake da kunne yana so ya ji wace irin waina ce ake
toyawa a cikin gidan. Ganin zuwan Hajiya da fitar Zee a yanayin da take jikinsa ya ba shi babu lafiya. Ya shiga
tsumayin jin