Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
ta ƙi daina sharar ƙwallar ya ja ta jikinsa ya shiga shafar ta yana bubbuga bayanta, har
wani sabon bacci ya yi awon gaba da ita. Kafin shi ma baccin ya kwashe shi yana nazarin abin
da zai yi mata, wanda zai faranta mata kamar yadda ta faranta masa.
Ƙarfe sha biyu saura minti uku na rana, waton 11:57am. Wayar Adamu ya tayar da su daga
nannauyan barcin da suke yi. Inda yake sanar da shi ga shi a cikin gidan tare da Dr Jimmai.
Dole ya wartsake barcin ya fara ƙoƙarin zare ta daga jikinsa, hakan ya sa ita ma ta farka.
Bayani ya yi mata sannan ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakinsa. Mintuna kaɗan ya fito da shigar
baƙar jallabiya ya sauka ƙasa cikin sauri ya nufi harabar gidan.
Kai-tsaye ya nufi inda motarsu fuskarsa a sake ya fara gaisawa da Dr Jimmai sannan ya miƙa
wa Adamu hannu suka gaisa.
"Mu je daga ciki, tun da ka tsaya jiran na fito kamar wani baƙo."
Ya yi maganar tare da jan hannun Adamu suka yi gaba Dr Jimmai ta bi su a baya, inda
Adamu yake dariya yana cewa, "Rufa mini asiri, ko karen mahaukaciya ya cije ni ai yanzu ba
zan shiga gidanka kai-tsaye babu notis ba."
"To mene ne a ciki?Ina jin dai ka san amaryar tun ba yau b..."
"Na dai taɓa ganin ta amma ban taɓa sanin ta ba ni kam."
Dariya suka fashe da ita dukan su har Dr Jimmai, saboda fahimtar inda Adamu ya nufa. A falo
suka zauna, Jamal ya koma ɗakin Minal, ganin ta ido biyu har ta gyara kwanciyarta ya gano ba
ta koma barcin ba tun bayan fitarsa.
"Ki shirya matar za ta shigo ta duba ki tana falo."
Narai-narai ta yi da ido hawaye shaa a kan fuskarta. Bai bi ta kanta ba ya fice tare da bai wa
Dr Jimmai damar ganin ta, sannan ya koma wurin Adamu bayan ta shiga ɗakin ya rufo musu
ƙofa.
"Waton mutumina har ka manta babu komai a jikinta na mata, a haka dai yadda take da siffar
mazan ka rufe ido ka yi mata kaca-kaca?"
Wani kallon ka raina ni Jamal ya yi masa kafin ya fashe da dariya yana nuna shi da hannu a
cikin dariyar yana cewa,
"Kai kam Allah ya yi maka tayar da zaune tsaye!"
"Babu wani tayar da zaune tsaye sai gaskiya mutumina. A gabanmu kuma a falon nan aka yi
komai, don da kujerun nan suna magana su ma da za su tuna duk kalmomin da ka faɗa a kan
yarinyar nan. Sai ga shi cikin ɗan lokaci ta tashi daga siffar mazan da kake kallon ta ka gano ita
mace ce kamar sauran mat.."
"Daina faɗar kamar sauran mata. Minal daban ce a cikin duk matan da na sani a tsawon
rayuwata."
Kallon mamaki Adamu ya yi masa kafin ya ce, "Ehhhh! Lalle wannan yarinya ta zo da babbar
sa'a. Amma kuma hakan yana da kyau, kuma na ji daɗin da ta san kan aikin, don Babu mamaki
Allah ne ya tashi kama mana kai a sanadin ta. Don ba a yanke hukunci cikin fushi kuma a cin
alwashi da izgilanci amma kai duka ka yi. Ma sha Allah, hakan yana da kyau Allah Ya ba ku
zaman lafiya."
"Amin-amin."
Adamu ya yi shiru tsawon minti biyu yana nazari kafin ya furzar da abin da ke ransa ya ce,
"Yanzu dai shikenan hankalinka ya dawo ka jefar da zancen Nur ka hut..."
"Adamu...plss ka daina don Allah, ba na son jin ko sunanta a bakin kowa. Saboda na gama
gano ba so na take yi ba ni ne na so ta, wahalar banza kawai na yi ita tana kallo na a ɗage."
Ya yi maganar ransa a ɓace kuma cikin fushi bagan fuskarsa ta sauya daga sakakkiya zuwa
tsukakkiya. "Mene ne abin damuwa to tun da Allah Ya musanya maka da alheri?"
"Mu bar zancen nan kawai Adamu, saboda ba za ka taɓa gane abin da nake ji bangane da
yarinyar nan ba. Amma ko ma mene ne na bar wa Allah kuma ta yi wa kanta."
"Fine!"
Adamu ya yi maganar cikin wani yanayi mara misaltuwa. Daidai lokacin da Dr Jimmai ta fito
tana zare safar hannunta ta ce,
"Har an kammala, ɗinki ne na yi mata kamu ɗaya ta ƙasa, sannan za ta dinga shiga cikin
ruwan ɗumi sau biyu a rana. Sannan babu aiki mai nauyi har zuwa lokacin da za ta ji sauƙi
kuma ɗinkin ya warware da kansa."
Jamal ya shiga sosa kai tare faɗin "To..to..to.." saboda tambayar da yake son yi mata amma
yana jin nauyi. Fahimtarsa da abin da yake son faɗa Dr Jimmai ta sake cewa,
"E, ka bar ta zuwa sati ɗaya in sha Allah za ta warware kafin lokacin. Amma a halin da take
ciki yanzu tana buƙatar hutu gaskiya, idan kuma aka yi garaje za ka lalata matarka ne tun kafin
a je ko'ina jikinta ya buɗe."
"A'ahhh! Babu komai Dr Allah Ya ba ta lafiya."
Ya yi maganar cikin sauri saboda ba zai so ya rasa irin daɗin da ya kwasa ba, don ya ƙudurta
bajewa a gidansa tare da killace kansa ga Minal ita kaɗai. Don haka duk abin da zai rage masa
zaƙin wurin ba ya maraba da shi dole zai haƙura a bi wasu hanyoyin kafin cikar wa'adin
kwanakin. Account ɗin ta ya karɓa, bayan ya yi mata godiya ya tura mata kuɗin aikin da ta faɗa har da
tukuici a sama. Cikin farinciki ya rako su suna yi wa Minal addu'ar samun sauƙi suka tafi, yayin
da ya dawo cikin gidan zuwa ɗakin Minal zuciyarsa cike da zallar tausayin ta a ransa.
"Sannu kin ji?"
Ya yi maganar cikin kulawa bayan ya kai mata kiss a saman leɓunanta sannan ya zauna bakin
gadon. Hannunta ya riƙo hawaye yana zuba a kan fuskarta ya ce,
"Me kike so na yi miki ladar shiga gonarki?"
Marau-marau ta yi da ido wani sabon hawaye yana bin fuskarta ta ce,
"Ba na son komai sai zuciyarka."
"Bayan ita fa?"
Sai da ta lumshe ido sannan ta ce, "Ita ɗin dai." Murmushi ya yi yana lakuce mata fuska yayin
da ya ranƙwafa a saman ƙirjinta, cikin wata kalar murya ya ce,
"Dama na ba ki."
Shiru ta yi masa tare da rufe ido ta buɗe sannan ta yi maganar da ƙirjinsa ya buga dam-dam.
"Ina so ka jaddada mini alƙawarin rabuwa da Nur har abada."
Hannunta ya saki, tare da miƙewa tsaye ya yi taku ɗaya zuwa biyu sannan ya tsaya ba tare
da ya juyo ba ya ce, "Ban san mai gobe za ta haifar ba, amma ba na jin zan iya sake rayuwa da
Nur, ko da daga ni sai ita muk rage a cikin duniya."
Tsawon minti biyu babu wanda ya sake magana a cikin su, saboda ƙwallar da ta cika masa
ido ya shiga haɗiye gudun Minal ta gano ɗacin da yake ji a kan Nur har lokacin bai bar shi ba.
"Ina son ki Minal, kuma na shirya zama da ke har iyakar rayuwata. Kuma zan faranta miki
daidai ƙarfina, zan guji duk abin da ba kya so matuƙar bai saɓa dokokin Allah ba."
Wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyarta, cike da ƙarfin hali ta yunƙura a hankali ta sauko daga
gadon. Cikin taku biyu ta isa bayansa ta rungume shi, tare da ɗora kanta tsakiyar allon bayan ta
fashe da wani sabon kuka cikin wani sautin da ya ratsa masa zuciya.
Tsawon minti biyu suna haka kafin ya juya ya rungume ta a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya
bayan rarrashin da yake yi mata. Hannunta ya riƙo a hankali ta fara taku zuwa bakin gadon
suka zauna. Hannunsa cikin nasa ta ɗora kanta a kafaɗarsa tana faɗin,
"Ina son ka kuma ina tsoron a raba mu. Don Allah kada ka so kowa idan ba ni ba, saboda
zan iya yin komai a kan duk wadda ta nemi shiga tsakanina da kai ko ta nemi raba m.."
"Babu wadda za ta raba mu, don haka ki daina irin waɗannan maganganun kuma ki bar
kawo su a cikin zuciyarki."
"Ni kaɗai na san me nake ji."
Ta yi maganar tana zubar da wani sabon hawaye. Ya shiga share mata sannan ya kwantar da
ita tare da rufa mata bargo yana cewa,
"Bari na je na samo mana abin da za mu ci. Time ya tafi an yi sallar Zuhur."
Da kallo kawai ta bi shi har ya fice ba ta ce komai ba, saboda wani sabon shauƙin son sa da
take ji a cikin ranta.
Shi kam wanka ya faɗa a gurguje ya shirya cikin wani yadi fari ya ɗora hula a kai. Sannan ya
koma yana yi mata sallamar zai je masallaci daga can zai wuce Restaurant ya siyo musu abinci.
Kamar ta hana shi, amma dole tana kallo ya fice yana ɗaga mata hannu cike da kulawa bayan
ya sakar mata kisses a goshi.
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin ta juya kwanciyarta tana jin kishin fitar da ya yi gudun
wasu mata su kalle mata shi a banza.
***
Jamal kam yana gama sallah a masallacin unguwar ya hau motarsa zuwa Restaurant ɗin da ya
saba zuwa. Abin mamaki, tun daga shigarsa wurin ya ji ƙirjinsa ya buga, saboda wani ƙamshin
turaren da ya ji ya saka jin wani iri, cikin sanyin jiki ya isa kan wata kujera ya zauna. Mintuna
biyu a tsakani ya ji muryar wata ma'aikaciyar wurin a saman kansa tana faɗin,
"Maigida, me za a kawo maka?"
Ba tare da ya ɗaga kansa ba ballantana ya kalli fuskarta ya faɗi abin da yake so, da nufin sai ya
ci ya ƙoshi sannan ya riƙa wa Minal nata ya koma gida. Minti biyu a tsakani ma'aikaciyar ta
dawo cikin zunuɗi ta ajiye tiren abincin a saman table, zuciyarta cike da tsantsar farinciki ta
gama daidai zaman komai sannan ta wuce ranta fes fuskarta a washe tamkar gonar auduga.
Ɗan sakonni da tafiyarta ya ajiye wayar tare da jan abincin a gabansa, zuciyarsa wasai ya
cire cokali a cikin ledarsa ya jefa cikin shinkafa da miyar da nufin fara ci. Har ya ciko cokalin zai
kai bakinsa ya ji caraf an riƙe masa hannu. Kafin ƙamshinta ya daki hancinsa ya yi hanzarin
ɗaga kai ya kai kallonsa saman kyakkyawar fuskarta.
"Nurrrrrr!"
Ya ambaci sunan cikin ƙaraji saboda ganin ta a lokacin da bai yi zato ko tsammani ba.
An zo wurin
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA!
1. ABOKIN AIKINA 1K
2. BAƘON YANAYI 1K
3. DAKAN ƊAKA 1K
4. AMFANIN FITILA 1K
5. JIKI DA JINI 1K
6. GIDAN AURE ₦700
7. TARTSATSI 1K
8. MAKANTAR SO 1K
9. ZUBAR HAWAYENA ₦700
10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700
11. BAKAN GIZO ₦700
12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500
13. DIJE ƘARANGIYA ₦500
14. DACE DA JUNA ₦500
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA HUƊU.*
Da ido ta yi masa magana kamar yadda ta saba a kan cewa tabbss ita ce ba gizo ba.
Hanzarin miƙewa tsaye ya yi bakinsa yana rawa tare da nuna ta da hannu ya sake cewa,
"Da gaske ke ce nake gani ko a cikin mafarkan da kika saba zo mini ne ko yau ma?"
Wani tsadadden murmushi ta yi wanda ya saka kansa sarawa, babu shiri ya runtse ido tare
da dafe saitin zuciyarsa saboda ƙaƙƙafan bugun da take yi. Cikin hanzari ta riƙe shi ta baya,
tare da yi masa katanga da jikinta. Yayin da ta yi maganar da ke tabbatar masa da tabbas ita
ce, kuma wadda ta nan take ya fatattaki kokwanton da zuciya ke yi masa.
"Babu wani mafarki Jaan! Ni ni ce dai Nur."
Saukar zazzaƙar muryarta kenan a lokacin da ta daki dodon kunnensa, bayan tsadadden
murmushin da take jifar sa da shi, wanda hakan ya jawo masa jirin da ya so jefar da shi ƙasa ba
tare da ya shirya ba.
"Ba na son sanabe! Me ye haɗin ki da shi?"
Zulaiha ta yi maganar a fusace tare da buge mata hannun da ta riƙe shi gudun ya faɗi.
Saboda haushi da takaicin da suka haɗe mata wuri ɗaya a kuma lokaci ɗaya. Tsabar ganin
samu fili amma rashi ya nemi kulle mata ƙofar nasara. Hakan ya sa kallon mamakin da Nur take
yi mata ya ƙara ɓata mata rai ta shiga auna mata harara tare da nuna ta tana faɗin,
"Tun da kika hana shi cin abincin, kuma kika yi sanadin da wani ya zube ƙasa; wallahi sai kin
biya mu kuɗinmu don ba za mu yi asara b..."
Wata kalar dariya mai cike da tura haushi Nur ta yi, kafin ta fito daga bayan Jamal bayan ta
zaunar da shi a kan kujerar da ya tashi. Taku ta yi a hankali cikin ƙasaita har ta isa gabanta tana
faɗin,
"Ki saka wa ranki cewa daga yau kin ƙulla ƙawance da asarar da kike gudu. Duk da ban so
na fito miki a irin wannan sifar ba, amma sanin halinki da kalar hatsabibancinki; na zaɓi yin
ƙwaƙƙwaran shiri tun kafin zuwan wannan ran.."
"Me kike nufi? Kina magana cikin isa da gadara tamkar kin jima da sani na, ko kuma na yi
miki babban laifin da kika kama ni dumu-dumu."
Nur ta sake yin wani guntun murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Kwantar da hankalinki
ƙawata, mene ne abin firgita tun yanzu kafin mu shiga fagen buga wasar? Ni fa na ɗauka a
yadda kike gwanar jarumta kin shirya taron aradu da ka a kowane lokaci...hummm!"
Ta ƙare maganar tana zagayen ta kafin ta koma kan plate ɗin abincin da ta ajiye wa Jamal ta
yamutsa shi da cokali tana faɗin,
"Abin da kika zuba a cikin abincin nan nake so ki yi bayani da bakink..."
"Kin yi kaɗan ki zo har wurin aikina ki nemi cin zarafina! Me na zuba da za ki yi mini ƙazafi
bayan ban san ki ba kuma ban taɓa ganin ki sai a yau, yau ɗin ma a yanzu da kike ƙoƙarin
manna mini sharr..."
"Sharri? Sharri fa kika ce?" Sai da ta yi wata 'yar dariya sannan ta girgiza kai tana faɗin,
"Ni A'isha ba na sharri alheri nake sadawa. Hakan ya sa na baro ƙasata takanas na zo Nigeria
saboda kare Jaan daga sharrink...."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wai ke mutum ce ko aljan? Ni fa gabaɗaya kin tayar mini da
hankali na kasa yarda da mace iri na nake magana ko macen aljana?"
Zulaiha ta yi maganar tana nuna Nur da hannu tare da ja baya tana zaro ido, tsabar tsoro da
fargaban da ya yi mata mugun lulluɓi, haɗi da gumin tashin hankalin da ya gama fesowa a
jikinta tamkar an watsa mata ruwa.
"Saurin me kike yi, ke da za ki ga komai a idonk ..?"
"Me zan gani? Ni fa wallahi ban san ki ba kuma ban san na yi komai b.."
"Yanzu za ki sani?"
Nur ta waiga gefenta, tare da nuni ga wani ma'aikacin wurin ya ƙaraso cikin rawar jiki. Umarni
ta ba shi da ido ya shiga danna wayar da ke hannunsa, fuskarta a cure ta karɓa ta kai kallonta a
kan wayar kafin ta cira kai ta kai kallon ta ga Zulaiha da ke tsaye tana waige-waige. Tsabar
ruɗewar da ta yi tare da sabon tashin hankalin da ya yi mata ƙawanya. Gabanta ta isa duk da ja
bayan da take yi har ta jingina bango ta tsaya.