Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
lallen ta ji ana labari bayan tafiyata? Tabbas biri
ya yi kama da mutum, daga gidan lallen ne ta ji zancen, idan kuwa haka ne ba zan taɓa yafe wa
wadda ta bayar da labarin b...'
Ta yi maganar tana goge ƙwallar da ke fareti a saman kumatunta. "Me ya sa tawa ƙaddarar ta
zo a haka?"
Ta sake jefa wa kanta tambayar da ta ji amsar a bakin Hajiya da ke bakin ƙofar ɗaki tana
kallon ta. Wadda ta shigo daidai lokacin da take jefa wa kanta tambayar, cike da tausayin Minal
a ranta ta ƙaraso cikin ɗakin ta zauna bakin gado, tare da dafa kafaɗarta tana cewa,
"Ita rayuwar duniyar nan da kika gan ta kowa da kalar jarabawarsa. Ki ɗauka taki ita ce
wannan, kuma in sha Allah za ta juya duk wani ƙunci da damuwarki zuwa alheri. Yanzu ki yi
haƙuri ki goge hawayenki, ki tashi mu je ki ci abinci akwai magungunan da za ki fara sha daga
yau ɗin nan zuwa kwana bakwai. Kuma ki sha da kyakkyawar niyya don in sha Allahu su ne
warakar duk wata damuwar da kike ciki. In dai Jamal ne ki saka wa ranki tamkar kin mallake shi
kin gama. Don Allah ma da ya saukar da cuta sai da ya fara saukar da magani kafin zuwanta.
Sannan in dai ina numfashi babu Jamal babu macen da duk za ta gurɓata mana farinciki da
kwanciyar hankali. Don haka a kodayaushe ki saka wa ranki ke kaɗai ce a wurin Jamal, kuma
ke kaɗai ya mallaka a matsayin babbar kadara rayuwarsa da zuri'arsa gabaɗaya."
Kukan daɗi Minal ta fashe da shi babu shiri, saboda Hajiya ta gama wanke duk wata tsatsar
fargaban da ke cikin zuciyarta. Sannan kuma ta wanke damuwar da Zulaiha ta cusa mata
gabaɗaya. Ranta fes ta sauko daga kan gadon ta duƙa har ƙasa kanta a sunkuye tare da haɗa
hannu wuri alamun roƙo tana cewa,
"Na gode, na gode miki sosai Hajiyarmu. Ubangiji Ya jiƙan magabata kuma ya ƙara miki lafiya
da nisan kwana."
Hajiya ta dafa kanta tana murmushi ta ce, "Amin-amin Amina. Ubangiji Ya albarkaci aurenku
da zaman lafiya tare da zuri'a ɗayyiba."
Cike da jin nauyi ta amsa a ciki kafin Hajiya ta miƙar da ita tsaye tana faɗin, "Mu je ki ci
abincin sannan ki sha maganin. Ga shi rigimar Jamal ma ta hana ni sukunin yaba lalle da kitson
tun lokacin da kika dawo."
Minal ta yi 'yar dariya ba tare da ta ce komai ba suka fice daga ɗakin.
Hango shi kwance a saman doguwar kujera ya sa ta yi turus bayan ƙirjinta ya buga dam-dam.
Ɗan ja baya ta yi kamar ba za ta shiga falon ba. Nan take Hajiya ta fahimci ba ta son zama
falon ne saboda ganin Jamal.
"Tsayuwar me kike yi a nan? Ƙaraso mana."
Hajiya ta yi maganar cikin haɗe rai tare da nuna mata inda za ta zauna a kusa da ita. Tamkar
wadda ƙwai ya fashe wa a ciki ta isa wurin ta zauna idonta a kan Tv ƙirjinta yana bugawa. Plate
ɗin tuwon shinkafa miyar yauɗi ta ja zuwa gabanta tana faɗin,
"Oya cinye mini shi kafin na fito miki da maganin ki sha."
Ta yi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta, Minal ta ƙura abincin kallo tsawon sakonni
kafin ta wanke hannunta a cikin ruwan wata tasa, sannan ta kai hannun cikin abincin ta shiga
juya lomar a cikin miya amma ta kasa kai tuwon a bakinta. Tsabar jin nauyi da kunyar Jamal
wanda ya tashi daga kwance bayan shigewar Hajiya yana aika mata kallon ƙasan ido. Wani kalar murmushi ya yi a lokacin da ya miƙe tsaye ya nufo ta. Kanta a sunkuye ta ji
takunsa kamar zai fice falon, babu zato ta ji ya cafko ƙirjinta da hannu biyu. Ta zabura babu shiri
tana faɗin,
"Innalillahi!"
Bai bi ta kan buge masa hannuwan da take yi ba ya ranƙwafa daidai fuskarta ya kai sajensa
gefen fuskar yana goga mata gashin sajen har zuwa gemunsa. Sannan hannuwansa a ƙirjin
yana murza tare da yin wani kalar nishin da ya hautsina ta cikin ɗan lokaci.
Motsin Hajiya da buɗe ƙofar ɗakinta ya sa ya yi hanzarin sakin ta ya nufi hanyar fita cikin
sassarfa. Da mamaki ta ƙaraso cikin falon tana cewa,
"Kai da ba ka da lafiya ina kuma za ka je?"
"Masallaci zan tafi na yi Isha na dawo."
Iya abin da ya faɗa kenan cikin wata kalar murya, ba tare da ya juyo ba saboda jijiyarsa da ke
miƙe, sannan kuma ba ya son ta fahimci halin da yake ciki. Ficewarsa ya sa ta dawo da kallonta
a kan Minal tana faɗin,
"Ba dai ko loma ɗaya ba ki ci ba tun da na bar ki?"
Minal ta yi ƙoƙarin saita nutsuwarta tana sosa kanta da hannu ɗaya ta fara kai lomar abincin a
bakinta. Zuciyarta sai zillo take yi tsabar tsantsar jarabar da Jamal ya jefa a ciki ba tare da ta
shirya ba. Yamm! Jikinta ya hau tsuma tana haɗiyar loma da ƙyar tamkar mau cin magani.
"Ikon Allah! Yanzu cin abincin ne har da gumi Amina?"
Cikin sauri Minal ta girgiza kai tana zarar ido tsabar kunya da yanayin da ke son tona mata asiri.
"Ni na ga duk kin firgice a lokaci ɗaya, ko ya yi miki wani abin ne bayan tafiyata?"
Ta sake girgiza kai tana ƙoƙarin yin magana ta sarƙe, babu shiri ta fara tari babu ƙaƙƙautawa.
Hajiya ta ruɗe ta shiga bubbuga mata baya tana faɗin 'Sannu' tare da taimaka mata ta sha ruwa
har aka samu tarin ya lafa mata.
"Ki ci a hankali kada ki sake sarƙewa."
Ta yi maganar cikin kulawa tare da barin wurin ta ɗauko kofi ta dawo ta zauna. Tsawon minti
goma babu wanda ya yi magana a tsakaninsu, har Minal ta gama cin tuwon ta kwashe kayan ta
kai kitchen, sannan ta dawo bayan ta wanke hannunta.
Kofin maganin infection ta miƙa mata, wanda ta cika taf da ruwan maganin sai ƙamshinsa ke
tashi. Babu musu ta karɓa ta shanye a lokacin ɗaya, zuciyarta cike da niyyar samun warakar
matsalolin da ke tsakaninta da Jamal. Don har ranta ta nutsu da cewa kyakkyawan albishirin
Hajiya zai yi tasiri ga rayuwarta cikin ɗan lokaci. Ganin yadda ya fara sauyawa har yana ƙoƙarin
haɗa jikinsa da nata cikin nutsuwa ba tare da kyara ko hantara ba.
Sallamarsa da ta ji ya sa ta miƙe tana cewa Hajiya za ta shiga ɗaki ta yi wanka ta yi sallah. Ta
so hana ta, amma ganin ta fi son tafiyar ya sa ta yi 'yar dariya ta ce,
"Jamal ka daina tsorata mini 'ya, ba na son tana ƙin sakewa a duk lokacin da ta gan ka."
Bai ce ƙanzil ba sai murmushin da ya yi yana sosa kansa tsawon minti biyu sannan ya ce, "A
taƙaice dai na zama dodo."
"Kusan haka, don haka ko ka bari ko na ɗauki mataki a kanka."
"Ai da ma na san kin fi son ta da ni. Ga shi ma ko lafiya ban da..ina jin kamar a gidan nan zan
kwana yau Hajiy..."
"Ka je gidanka gaskiya! Ko ba komai za ka sha maganinka a can kafin ka kwanta."
Bai ba ta amsa ba sai da ya baje kan kujerar sannan ya ce, "Matsalar jikin ne nawa babu
ƙarfin da zan iya yin tuƙi a yanzu. Kuma gidan babu daɗi daga ni sai maigadi."
Wani kallo ta yi masa cike da jin daɗin ganin ya fara damuwa da kewar Minal ta ce, "Ji wani
sanabe, yanzu duk shekarun kwanakin da ka yi kana kwana a cikin gidan ba ka san babu daɗi
ba sai yau da kake son kwana a gidan nan?"
"Kawai ki yarda Hajiya, za. Jaraba kwana a nan ɗin, gobe idan na samu ƙarfi sai na koma
can."
Farinciki fal zuciyarta ta ce, "Ba kwanan ba, ba na son ka takura mini yarinya, saboda haka
tashi ka je ɓangarenka ni zan rufe ƙofarmu gudun na manta ta kwana a buɗe ban sani ba."
"Idan na tashi zan sanar da ke ki ruf.."
"Ba fa zan bar ka a nan ba! Tashi ka je na rufe ba za ka saka ni surutu a cikin dare ba."
Ta yi maganar tare da tsare gida alamun babu wasa, haka ya miƙe ba don ya so ba ya koma
ɗakinsa da ke harabar gidan. Sannan ta rufe ƙofarta ruf ta bar makulli a jiki tana tofe ko'ina da
addu'a. Jamal kam barci ya yi cikin kewar Minal, sai da ya kira Zee a waya suka yi abin da suka
saba yi sannan ya rage zafi. Amma a zuciyarsa bai fasa shan alwashin yi wa Minal muguwar
mamayar da zai koya mata hankali ba.
Da safe bai tsaya kari ba ya fice gidan a gaggauce saboda kiran da aka yi masa wurin aiki.
Kasancewar yana da wasu kaya a gidan bai koma gidansa ba daga nan ya zarce ma'aikatarsu.
***
Tsawon kwana bakwai Hajiya tana tsaye a kan Minal, sannan da takatsantsan a kan kusancinta
da Jamal har ta kammala shan magungunan ta cinye kazar sababi. Don tun daga ranar da ya
kwana gidan ya tare a nan bai koma gidansa da kwana ba. Hakan ya sa Minal ta shiga feshin
wanka da kalolin shiga cikin sababbin kaya tamkar tarwaɗa. Saboda Hajiya ta sa an yi mata
dilka da halawa fatarta ta ƙara murjewa har da haske sai da ta yi.
Gyaran da ya ƙara susuce Jamal ya zama bita-zai-zai, Hajiya tana korar sa yana mannewa.
Wani lokaci da gangan yake naɗewa a cikin ɗakinsa, saboda kawai ya ce bai da lafiya a kawo
masa abincinsa a nan. Don kawai ya yi amfani da damar ya rage zafin da ke ƙona masa jiki
tsabar fitinanniyar sha'awar Minal ta yi masa mugun kamu. A farko Hajiya ba ta gano lagonsa ba, sai a wata rana da ta ji Minal shiru ba ta dawo daga kai
masa abincin ba, babu jinkiri ta bi bayanta cikin zullumin kada ya samu kanta tun kafin ta gama
gyaran. Saboda haka Minal tana shiga ya rufe ɗakin ya shiga luguiguita ta son ransa, don ita
ma magungunan da take sha sun fara aiki a jikinta. Ta yadda babu abin da ta fi so a lokacin
kamar ya yi mata abin da ya koya mata a cikin 'yan kwanakin. Ko boren da take yi masa da
zabura idan ya taɓa ta gabaɗaya ta daina yi, wani lokacin ma har ɗoki take yi da dakon sa a kan
cewa a kawo masa abincin don kawai ta je ya ɗora mata sabon darasi.
Ranar da Hajiya ta rutsa su a cikin yanayin da ba ya faɗuwa, dole ta tattara mata kayanta ta
kai ta gidansa da kanta ta ce Allah Ya ba da zaman lafiya. Da ma Umma Ade ta ba ta shawarar
ta miƙa masa matarsa tun da ya kasa haƙuri ya biyo ta gidan ya tare. Amma Hajiya ta kafe a
kan babu inda za ta je sai ta gama gyara ta tsaf kuma sai kayan matan sun bi jikinta.
Kasancewar bai san Hajiya za ta mayar da ita ba, sai bayan ya dawo gidan bayan magrib cin
abinci. Yana zancen abincin, Hajiyar ta ce masa ya je gidansa matarsa ta yi masa girki sai ya ci
a can. Sake da baki ya dinga kallon Hajiya sannan ya ce,
"Shi ne aka mayar da ita ba tare da na sani ba?"
Wani kallo ta yi masa kafin ta ce, "Da na zo da ita izininka na nema?"
Sosa kai ya shiga yi yana 'yar dariya saboda har zuciyarsa ya ji daɗin damar da aka ba shi
don ya ci karensa babu babbaka. Amma sai ya koma alayen jan Hajiya da hira kamar ba ya son
tafiya, har da cewa shi a nan gidan zai kwana bai tashi komawa can ba.
Gaba Hajiya ta saka shi da abin bugu ta koro shi har harabar gidan tana yi masa Allah Ya
tsare. Cikin wani ƙumaji a ransa ya fice gidan aguje maigadi yana ɗaga masa hannu da addu'ar
sauka lafiya. Bai zame ko'ina ba sai Yahuza suya, a nan ya zaɓi ƙosassun kaji biyu da sauran
tarkacen ci da sha ya buga motarsa zuwa gida. Zuciyarsa cike da ɗokin zama ango a daren
ranar, ranar da ta zamo daidai wata biyu da aurensu.
Yanzu wasar za ta fara.
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442
Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555
Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.
JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA!
1. ABOKIN AIKINA 1K
2. BAƘON YANAYI 1K
3. DAKAN ƊAKA 1K
4. AMFANIN FITILA 1K
5. JIKI DA JINI 1K
6. GIDAN AURE ₦700
7. TARTSATSI 1K
8. MAKANTAR SO 1K
9. ZUBAR HAWAYENA ₦700
10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700
11. BAKAN GIZO ₦700
12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500
13. DIJE ƘARANGIYA ₦500
14. DACE DA JUNA ₦500
D. AUTA CE✍
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA BIYU.*
Minal kuwa, tun bayan gama sallar Isha ta kwaɗa wanka tare da feshe jikinta da fitinannun
turaruka, waɗanda Hajiya ta yi mata kyautar su a matsayin tsarabar zaman aure. Ta sha
gayunta cikin wani tsadadden lesi fari mai adon golden. Bayan ɗan kunne da sarƙa har da
agogo da 'yan hannu ta saka. Ta fito shar da ita ta ko'ina sai juyi take yi zuciyarta cike da jin
daɗin yanayin da farincikin zuwan ranar. Saboda jikinta ya ba ta daga ranar farincikin da Hajiya
take hasashen zuwansa zai wanzu, matuƙar Jamal ya gano darajarta.
Ta zauna falo tana kallon Bollywood tare da dakon dawowarsa. Don ta ci alwashin nuna
masa ita daban ce a cikin matan bariki, kuma ta san darajar kanta. Sai dai a gefe ɗaya na
zuciyarta yana yi mata gargaɗin kada ta yi abin da zai lalata musu daren, don ta jima tana
tsumayin zuwansa. Hakan ya sa tun da ta ji ƙarar buɗe gate da ƙugin motarsa jikinta ya hau tsuma. Saboda
tsananin bugun da ƙirjinta yake yi, babu shiri ta zabura ta faɗa ɗaki jikinta yana rawa. Haka
kawai ta tsinci kanta cikin wani matsanancin tsoro, ƙirjinta ta dafe tare da rufe ido a daidai
lokacin da ta ji motsin buɗe ƙofar falo. Jinin jikinta ta sha saboda jin sautinsa yana faɗin,
"Ina matar gidan ne?"
Cikin sauri ta kwanta bakin gado tana rufe ido da nufin yin baccin ƙarya. Amma kuma dukan
luguden uku-ukun da ƙirjinta yake yi, ya tona asirin lamfon da ta yi a lokacin da ya shigo ɗakin
ya yi tsugunno bakin gadon yana ƙare wa fuskarta kallo. Hannunsa ya kai saman leɓunanta
yana murmushi ya ce,
"Da ma kin tashi don bugun zuciyarki ya tona miki asiri ba wani baccin da kike yi."
Dariyar da ta so yi ya sa ta yi hanzarin juya kwanciya ta ba shi baya. Bombom ya ɗin ta ya
ƙura wa kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe, shi ma ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da
rungumo ta jikinsa yana shinshinar ƙamshinta. Ya shiga goga mata gashin sajensa a wuya cikin
shauƙi yana faɗin,
"Wannan amarya so take yi kawai ta ja mini aji."
Ya yi maganar cikin wata kalar murya a lokacin da ya zura hannunsa ɗaya ta ƙarƙashinta,
sannan ɗaya a saman jikinta ya rungumo ta gabaɗaya yana sauke ajiyar zuciya. A lokaci ɗaya
ya yi nasarar kai hannuwan saman ƙirjinta yana aikin da zuciya take ta kwaɗaita masa. Cikin
ɗan lokaci daga shi har ita suka fita cikin hayyacinsu, saboda ya koma samanta yana yi mata
wani kalar wasannin da ya jima da sanin su ne makamar kowace mace. Numfashi ta shiga
saukewa tana ɗan kukan da ke ƙara hautsina masa lissafi. Hakan ya sa ya nemi haukacewa
gabaɗaya yana neman kan hanyar da zai ɓillewa a sukwane. A lokacin nata hankalin ya dawo
jikinta cikin tsoro ta shiga ture shi tana ƙoƙarin hana shi abin da yake ƙoƙarin aikatawa.
Kasancewar jikinsa ya yi laushin da ba zai iya komai ba, ba ta sha wuya wurin zare jikinta daga
nasa tare da tashi zaune tana faɗin,
"Malam abincinka yana falo."
Ta yi maganar cikin harɗewar numfashi tare da ƙoƙarin